TARIHI
Jehobah Ya Ji Adduꞌoꞌina
AKWAI ran da na ɗaga ido da daddare kuma na ga taurari suna haskakawa, lokacin ina ɗan shekara goma. Nan-da-nan sai na durƙusa kuma na soma adduꞌa. A lokacin ban daɗe da sanin Jehobah ba, amma na gaya masa dukan damuwata, kuma na soma kusantar Jehobah Allahnmu “mai jin adduꞌoꞌi!” (Zab. 65:2) Kun san abin da ya sa na yi adduꞌa ga Allah duk da cewa ban daɗe da sanin sa ba a lokacin? Bari in gaya muku.
WATA ZIYARA DA TA CANJA RAYUWATA
A ran 22 ga Disamba, 1929 ne aka haife ni, a wani ƙauye mai suna Noville da ke kusa da birnin Bastogne a ƙasar Beljiyam. A ƙauyen akwai gonaki guda tara. Nakan tuna yadda na ji daɗin yin aiki da iyayena a gona lokacin da nake ƙarami. Ni da ƙanina mai suna Raymond mukan je mu tatse nonon shanu kowace rana mu kawo gida. A ƙauyenmu kuma, mutane sukan yi aiki tare don su taimaka wa juna.
Ni da ꞌyan iyalinmu muna aiki a gona
Mahaifina wato Emile da mahaifiyata Alice ꞌyan Katolika ne, kuma ba sa wasa da ibadarsu. Kowace ranar Lahadi sukan je coci. A wajen shekara ta 1939, wasu majagaba daga Ingila sun zo ƙauyenmu. Kuma suka gaya wa mahaifina abin da zai yi don a riƙa kawo masa mujallar Consolation (wanda a yanzu ake kira Awake!) a-kai-a-kai, kuma ya yarda. Da mahaifina ya karanta mujallun, nan-da-nan ya ga cewa suna koyar da gaskiya, kuma ya soma karanta Littafi Mai Tsarki. A dā maƙwabtanmu suna son babana, amma da ya daina zuwa cocin Katolika, sai suka soma tsananta masa. Sun yi ta matsa masa ya ci-gaba da zuwa cocin kuma sun yi ta ƙoƙarin canja masa raꞌayi, amma ya ƙi.
Ban ji daɗin ƙiyayyar da suka nuna wa babana ba. Abin da ya sa na yi adduꞌar da na ambata a farkon labarin nan ke nan. Na gaya wa Allah yadda abin yake damuna kuma na roƙe shi ya taimaki babana. A-kwana-a-tashi, sai maƙwabtanmu suka daina matsa wa babana. Da na ga hakan, na yi farin ciki sosai. Abin ya tabbatar mini da cewa Jehobah Allah ne “mai jin adduꞌoꞌi!”
LOKACIN YAƘIN DUNIYA NA BIYU
A ran 10 ga Mayu, 1940, sojojin Jamus sun kawo hari a ƙasar Beljiyam, kuma abin ya sa mutane da yawa sun gudu sun bar ƙasar. Mu a iyalinmu mun gudu zuwa kudancin ƙasar Faransa. Da muke guduwa, mun yi ta samun kanmu a inda sojojin Jamus da na Faransa suke faɗa.
A-kwana-a-tashi, sai muka koma ƙauyenmu. Da muka dawo, sai muka ga cewa an sace yawancin abubuwa da muke da su a gonar. Ƙarenmu ne kawai aka bar mana, shi ne ya marabce mu. Irin abubuwan nan sun sa na damu sosai, kuma na soma tunani, ‘Me ya sa ake yaƙi da wahala?’
Saꞌad da nake matashi, na kusaci Jehobah sosai
A lokacin ne wani ɗanꞌuwa mai suna Emile Schrantza ya ziyarce mu, shi dattijo ne kuma majagaba ne mai ƙwazo sosai. Ya yi amfani da Littafi Mai Tsarki don ya bayyana min abin da ya sa ake shan wahala, kuma ya amsa wasu tambayoyina game da rayuwa. Hakan ya sa na ƙara ƙaunar Jehobah kuma na yarda cewa shi Allah ne mai ƙauna.
Mun yi ta haɗuwa da ꞌyanꞌuwa da dama a lokacin da ake yaƙin, kuma mun ji daɗin hakan. A watan Agusta, 1943, wani ɗanꞌuwa mai suna José-Nicolas Minet ya zo ya yi jawabi a gonarmu, kuma ya tambaye mu, “Wa yake so ya yi baftisma?” Sai babana ya ɗaga hannu kuma ni ma na ɗaga hannu. An yi mana baftisma a wani ƙaramin rafi da ke kusa da gonarmu.
A watan Disamba 1944, sojojin Jamus sun kawo babban harinsu na ƙarshe a Yammacin Turai, wanda aka fi sani da Battle of the Bulge. Gidanmu yana kusa da inda aka yi wannan yaƙin. Don haka, mun yi kusan wata ɗaya muna ɓoyewa a wani ɗaki da ke ƙasa a gidanmu. Akwai ranar da na fita zan ba dabbobinmu abinci, sai aka jefa bam. Bam ɗin ya yi kaca-kaca da rufin ɗakin dabbobin. Sai wani sojan Amurka da ke wani ɗakin dabbobi ya yi ihu ya ce min, “Ka kwanta!” Da jin haka, sai na yi gudu na je wurinsa, na kwanta kusa da shi, shi kuma ya rufe kaina da hular kwanonsa don ya kāre ni.
YADDA NA YI TA ƘARA KUSANTAR JEHOBAH
Ranar aurenmu
Da aka gama yaƙin, mun samu mun yi magana da ꞌyanꞌuwa da suke wani gari mai suna Liège da ke da nisan kilomita 90 a ta arewa, kuma mun ci-gaba da yin hakan. A-kwana-a-tashi, mun kafa wani ƙaramin rukuni a garin Bastogne, kusa da inda muke. Ƙari ga haka, na samu aiki da masu karɓan haraji kuma na yi karatu a fannin shariꞌa. Daga baya, na yi aiki a wani ofishin ƙaramar hukuma. A shekara ta 1951 kuma, mun shirya wani taron daꞌira a garin Bastogne. Mutane wajen ɗari ne suka zo taron. A cikinsu kuma akwai wata majagaba mai ƙwazo sosai, sunanta Elly Reuter. Ta yi tafiyar kilomita 50 da keke kafin ta iso wurin taron. Ba da daɗewa ba mun soma son juna kuma mun yi wa juna alkawari cewa za mu yi aure. Lokacin an riga an gayyaci Elly zuwa Makarantar Gilead a ƙasar Amurka. Sai ta rubuta wasiƙa ga hedkwatarmu kuma ta bayyana musu dalilin da ya sa ba za ta iya zuwa makarantar ba. Sai Ɗanꞌuwa Knorr wanda a lokacin shi ne yake ja-goranci a ƙungiyarmu, ya amsa da cewa wataƙila wata rana za ta samu damar zuwa makarantar Gilead tare da maigidanta. Daga baya mun yi aure a watan Fabrairu, 1953.
Matata Elly da ɗanmu Serge
A wannan shekarar ce ni da matata Elly, muka halarci taron New World Society Assembly da aka yi a Yankee Stadium da ke birnin New York. A wurin na haɗu da wani ɗanꞌuwa kuma ɗanꞌuwan ya ce min in ƙaura zuwa Amurka zai ba ni aiki mai kyau. Sai muka yi adduꞌa game da batun. Bayan haka, mun yanke shawara cewa ba za mu je ba, za mu koma ƙasar Beljiyam don mu ci-gaba da taimaka wa ƙaramin rukuni na ꞌyanꞌuwa goma da ke garin Bastogne. A 1954 mun haifi ɗanmu mai suna Serge, hakan ya sa mu farin ciki sosai. Sai dai bayan watanni bakwai ya soma rashin lafiya har ya rasu, abin baƙin ciki. Mun gaya wa Jehobah yadda muke ji a cikin adduꞌa, kuma begen cewa za a tā da matattu ya ƙarfafamu.
YIN HIDIMA TA CIKAKKEN LOKACI
A watan Oktoba 1961, na sami wani aiki da zai ba ni zarafin yin hidimar majagaba. Amma ranar da na sami aikin ne aka kira ni daga Ofishinmu da ke Beljiyam. Ɗanꞌuwan da ke kula da Ofishin, ya tambaye ni ko zan iya soma yin hidimar mai kula da daꞌira (lokacin ana kiran mai kula da daꞌira circuit servant). Sai na ce masa: “Don Allah zai yiwu mu soma da yin hidimar majagaba kafin mu zama masu kula da daꞌira?” Kuma an yarda mana mu yi hakan. Da muka yi hidimar majagaba na watanni takwas, sai muka soma yin hidimar masu kula da daꞌira, a watan Satumba 1962.
Da muka yi shekaru biyu muna hidimar masu kula da daꞌira, sai aka ce mu soma hidima a Bethel da ke ƙasar Beljiyam, wato a birnin Brussels. A watan Oktoba 1964 ne muka soma hidima a Bethel, kuma wannan hidimar ta buɗe mana hanyar samun albarku da yawa. A 1965, Ɗanꞌuwa Knorr ya ziyarci Ofishinmu. Da ya koma, bai daɗe ba sai aka naɗa ni in zama mai kula da Ofishin. Abin ya ba ni mamaki sosai. Daga baya sai aka gayyace mu mu je Makarantar Gilead, muna aji na 41. Abin da Ɗanꞌuwa Knorr ya faɗa shekaru 13 da suka wuce ya faru. Da muka sauƙe karatu, sai aka komar da mu Ofishinmu da ke Beljiyam.
KĀRE ꞌYANCIN ꞌYANꞌUWANMU
Na yi shekaru da yawa ina amfani da ilimin shariꞌa da nake da shi, wajen taimaka wa ꞌyanꞌuwanmu su sami ꞌyancin yin ibada a Turai da ma wasu ƙasashe. Wannan ba ƙaramin gata ba ne. (Filib. 1:7) Aikin ya sa na haɗu da manyan jamiꞌan gwamnati daga ƙasashe fiye da 55 da aka hana aikinmu kwata-kwata, ko an hana mu yin wasu abubuwa. Maimakon in riƙa gabatar da kaina a matsayin wanda ya daɗe yana harkar shariꞌa, nakan gaya musu cewa, “Ni bawan Allah ne.” A kullum nakan roƙi Jehobah ya yi min ja-goranci, na san cewa “zuciyar sarki [ko alƙali] tana kama da ruwan rafi a hannun Yahweh, Yahweh yakan juya shi duk inda yake so.”—K. Mag. 21:1.
Na tuna tattaunawar da muka yi da wani ɗan Majalisar Tarayyar Turai. Na daɗe ina neman damar yin magana da shi amma ban samu ba, sai wannan karon ya yarda. Amma ya ce, “Na ba ka minti biyar kacal.” Sai na sunkuyar da kai na soma adduꞌa. Mutumin ya ce me nake yi, sai na ce masa, “Godiya nake ma Allah don kai mai hidimarsa ne.” Sai ya tambaye ni cewa, “Me kake nufi?” Ni kuma na nuna masa Romawa 13:4. Da yake shi ba ɗan Katolika ba ne, ya san Nassosi sosai. Don haka ya so abin da na nuna masa. Ƙarshenta mutumin ya ba ni minti talatin, kuma mun yi tattaunawa mai gamsarwa sosai. Har ya yaba wa Shaidun Jehobah don aikin da suke yi.
Shaidun Jehobah sun yi shekaru da yawa yanzu suna gwagwarmaya a Turai, don su kāre ꞌyanꞌuwanmu a batun yin aikin soja, da biyan haraji, da dai sauransu. Na ji daɗi sosai don yadda Jehobah ya yi amfani da ni wajen taimaka wa ꞌyanꞌuwa, kuma na ga yadda ya ba mutanensa nasara sau da yawa. Shaidun Jehobah sun yi nasara fiye da sau 140 a Kotun Turai na Kāre ꞌYancin ꞌYan Adam!
MUN ƘARA SAMUN ꞌYANCI A ƘASAR CUBA
Daga baya, na sami damar yin aiki da Ɗanꞌuwa Philip Brumley, daga hedkwatarmu, da Ɗanꞌuwa Valter Farneti, daga Italiya, don mu taimaka ma ꞌyanꞌuwanmu da ke Cuba su sami ƙarin ꞌyanci. A lokacin an hana wasu ayyukanmu a ƙasar. Na rubuta wasiƙa ga ofishin jakadancin ƙasar Cuba da ke Beljiyam. Sai suka zaɓi wani ya duba bukatunmu, kuma na sami damar yin magana da shi. Mun haɗu sau da yawa don mu tattauna batun, amma da farko ba mu iya mun warware matsalar ba.
Ni da Ɗanꞌuwa Philip Brumley da Valter Farneti, lokacin mun je ƙasar Cuba
Sai muka roƙi Jehobah ya taimake mu mu san na yi, bayan haka, sai muka roƙe su su ba mu izini mu tura Littafi Mai Tsarki guda 5000 zuwa ƙasar Cuba. Sun yarda mana mu tura littattafan, kuma an raba ma ꞌyanꞌuwanmu. Wannan ya tabbatar mana da cewa Jehobah yana tare da mu. Sai muka sake roƙan izini don mu tura Littafi Mai Tsarki guda 27,500, kuma wannan karon ma sun yarda mana. Na yi farin ciki sosai da na ga cewa ni ma na taimaka wa ꞌyanꞌuwanmu a Cuba su samu Littafi Mai Tsarki.
Na je ƙasar Cuba sau da yawa don in taimaki ꞌyanꞌuwanmu su ƙara samun ꞌyancin yin ibadarsu, kuma hakan ya sa na zama abokin jamiꞌan gwamnati da yawa a ƙasar.
TAIMAKA WA ꞌYANꞌUWANMU A RUWANDA
A 1994 wani abin baƙin ciki ya faru a ƙasar Ruwanda. An kashe mutane fiye da 1,000,000 a wani kisan ƙare dangi da aka yi wa ʼyan kabilar Tutsi, kuma wasunsu ꞌyanꞌuwanmu ne. Jim kaɗan, sai aka ce ma wasu ꞌyanꞌuwa su shirya kayan agaji da za a aika wa ꞌyanꞌuwanmu da ke Ruwanda.
Da muka je birnin Kigali, wato birnin tarayyar ƙasar, sai muka ga ramuka da yawa a bangon ofishin fassara da wurin ajiye littattafai da ke wurin, sakamakon harbin bindiga da aka yi ta yi. An kuma ba mu labarin yadda aka sassari wasu ꞌyanꞌuwanmu da adda har mutuwa. Amma mun kuma ji labarin yadda ꞌyanꞌuwa suka nuna wa juna ƙauna. Alal misali, mun haɗu da wani ɗanꞌuwa mutumin Tutsi, da wani ɗanꞌuwa da matarsa daga kabilar Hutu ne suka ɓoye shi a wani rami, har kwanaki 28. Mun yi wani taro a birnin Kigali kuma a taron mun ƙarfafa ꞌyanꞌuwa maza da mata fiye da 900.
Gefen hagu: Wani littafi da harsashi ya same shi a ofishin fassararmu
Gefen dama: Lokaci da nake aiki da masu ba da agaji
Bayan haka, sai muka haye zuwa ƙasar Zaire (yanzu ita ake kira Jumhuriyar Damokuraɗiyar Kwango). Mun je wurin ne don mu nemi ꞌyanꞌuwa da suka gudu zuwa sansanin gudun hijira dabam-dabam da suke kusa da birnin Goma. Amma ba mu iya gane inda suke ba. Don haka, mun roƙi Jehobah ya taimake mu mu haɗu da su. Bayan haka, sai muka ga wani yana tahowa, sai muka tambaye shi ko ya san wani Mashaidin Jehobah a nan? Sai ya ce: “E, ni Mashaidin Jehobah ne, kuma zan so in kai ku inda kwamitin ba da agaji suke.” Mun yi taro da ꞌyan kwamitin kuma taron ya ƙarfafa dukanmu. Bayan haka, mun yi taro da masu gudun hijira wajen 1,600 don mu ƙarfafa su kuma mu yi musu taꞌaziyya. Mun kuma karanta musu wasiƙa daga Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu. Da suka ji inda aka ce: “Muna adduꞌa kullum dominku. Kuma mun san cewa Jehobah ba zai yashe ku ba,” sun yi farin ciki sosai. Kuma da gaske Jehobah bai yashe su ba, domin a yau, ꞌyanꞌuwa fiye da 30,000 suna bauta ma Jehobah da farin ciki a ƙasar Ruwanda!
NA ƘUDIRI NIYYAR RIƘE AMINCINA
A 2011, bayan da muka yi wajen shekaru 58 da aure, matata abin ƙaunata, ta rasu. Na yi adduꞌa na gaya wa Jehobah irin zafin da na ji a zuciyata don rasuwarta, kuma ya ƙarfafa ni. Wani abin da ya ƙarfafa ni kuma shi ne waꞌazin labari mai daɗi na Mulkin Allah da nake yi wa maƙwabtana.
Ko da yake yanzu na wuce shekaru 90, ina yin waꞌazi kowane mako. Wani abin da yake faranta min rai kuma shi ne yadda nake taimaka wa ꞌyanꞌuwa da suke aiki a Sashen da Ke Kula da Shariꞌa a nan Ofishinmu na Beljiyam, da yadda nake ba wa ꞌyanꞌuwa labarina, da kuma yadda nake ƙarfafa matasa da suke iyalin Bethel.
Shekaru 84 da suka shige ne na yi adduꞌata ta farko ga Jehobah. A lokacin ne na soma kusantarsa da yin rayuwa mai inganci, kuma yanzu ina farin ciki cewa na kusace shi sosai. Ina godiya ga Jehobah don yadda ya yi ta jin adduꞌoꞌina a dukan rayuwata.—Zab. 66:19.b
a An wallafa labarin Ɗanꞌuwa Schrantz a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Satumba, 1973, shafi na 570-574 a Turanci.
b Ɗanꞌuwa Marcel Gillet ya rasu a ran 4 ga Fabrairu, 2023, lokacin da ake kan rubuta wannan talifin.