Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w25 Mayu pp. 20-25
  • Me Ya Sa Sunan Jehobah Yake da Muhimmanci ga Yesu?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Me Ya Sa Sunan Jehobah Yake da Muhimmanci ga Yesu?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “NA KUMA SANAR MUSU DA SUNANKA”
  • “SUNANKA, WATO SUNAN DA KA BA NI”
  • “YA UBA, KA ƊAUKAKA SUNANKA”
  • NA “BA DA RAINA”
  • “NA . . . CIKA DUKAN AIKIN DA KA BA NI IN YI”
  • Sunan Jehobah Yana da Muhimmanci a Gare Mu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Mu Yabi Sunan Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Mene ne Fansar Yesu Ta Nuna Mana?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • “Ku Zaɓi Wanda Za Ku Bauta Masa”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
w25 Mayu pp. 20-25

TALIFIN NAZARI NA 22

WAƘA TA 15 Mu Yabi Ɗan Allah!

Me Ya Sa Sunan Jehobah Yake da Muhimmanci ga Yesu?

“Na kuma sanar musu da sunanka.”—YOH. 17:​26, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga abin da Yesu yake nufi saꞌad da ya ce ya sanar da sunan Jehobah, da yadda ya nuna cewa Jehobah mai tsarki ne, da kuma cewa duk abin da Shaiɗan ya faɗa game da Jehobah ƙarya ne.

1-2. (a) Mene ne Yesu ya yi a daren da aka kashe shi? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna a wannan talifin?

A RANAR 14 ga Nisan, shekara ta 33 bayan haihuwar Yesu, wato, ranar Alhamis da yamma. A ranar, Yesu ya ci wani abinci na musamman tare da manzanninsa masu aminci. Ya san cewa Yahuda Iskariyoti zai bashe shi, za a wulaƙanta shi, kuma maƙiyansa za su kashe shi. Don haka, bayan sun ci abincin, ya gaya wa manzannin abubuwa da yawa masu ban ƙarfafa. Da za su tafi, Yesu ya yi adduꞌa mai muhimmanci. Manzo Yohanna ya rubuta wannan adduꞌar a Yohanna sura 17.

2 A wannan talifin, za mu ga wasu abubuwan da za mu koya daga adduꞌar da Yesu ya yi. Mene ne ya fi damunsa kafin ya mutu? Mene ne ya fi muhimmanci a gare shi lokacin da yake duniya? Bari mu tattauna waɗannan tambayoyin.

“NA KUMA SANAR MUSU DA SUNANKA”

3. Mene ne Yesu ya ce game da sunan Jehobah, kuma mene ne yake nufi? (Yohanna 17:​6, 26, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe)

3 Saꞌad da Yesu yake adduꞌa, ya ce: “Na kuma sanar musu da sunanka.” Yadda ya maimaita hakan sau biyu ya nuna cewa sunan yana da muhimmanci a gare shi. (Karanta Yohanna 17:​6, 26, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe.) To, mene ne Yesu yake nufi? Shin, yana gaya wa almajiransa cewa sunan Allah Jehobah ne? Aꞌa. Almajiransa Yahudawa ne, don haka sun riga sun san cewa sunan Allah Jehobah ne. Kuma an ambata sunan Allah kusan sau 7,000 a Nassosin Ibrananci. Saboda haka, ba sunan Allah ne Yesu yake koya wa almajiransa ba. Amma yana so ya sa su fahimci ko shi wane irin Allah ne. Ya taimaka wa almajiransa su ƙara sanin abubuwa game da Jehobah. Hakan ya ƙunshi nufin Jehobah ga duniya da kuma ꞌyanꞌadam, da abubuwan da Jehobah ya riga ya yi, da waɗanda zai yi a nan gaba da kuma halayensa. Kuma babu wanda zai iya bayyana irin abubuwan nan game da Jehobah fiye da Yesu.

4-5. (a) Ka ba da misali da ya nuna abin da ake nufi da ƙara ɗaukan sunan mutum da muhimmanci. (b) Ta yaya almajiran Yesu suka ƙara ɗaukan sunan Jehobah da muhimmanci?

4 A ce akwai wani dattijo mai suna David a ikilisiyarku kuma shi likita ne. Mai yiwuwa ka yi shekaru da yawa da sanin ɗanꞌuwan. Sai wata rana ka bukaci jinyar gaggawa, kuma aka kai ka asibitin da ɗanꞌuwan yake aiki. Sai ɗanꞌuwan ya yi iya ƙoƙarinsa ya taimake ka ka sami sauƙi. Ko da yake ka daɗe da sanin ɗanꞌuwan, duk ran da ka ji an ambata sunansa, za ka tuna yadda ya taimaka maka, ko ba haka ba? Daga ranar, za ka riƙa ɗaukan David a matsayin dattijo a ikilisiyarku da kuma likitan da ya taimaka maka.

5 Almajiran Yesu sun riga sun san sunan Jehobah, amma sun ƙara ɗaukan sunan da muhimmanci saꞌad da Yesu ya taimaka musu su fahimce shi da kyau. Me ya sa muka ce haka? Domin Yesu ya yi koyi da Jehobah a dukan abubuwan da yake yi da kuma faɗa. Saboda haka, almajiransa sun ƙara sanin Jehobah ta wurin sauraron koyarwar Yesu da kuma ganin yadda yake bi da mutane.—Yoh. 14:9; 17:3.

“SUNANKA, WATO SUNAN DA KA BA NI”

6. Mene ne Yesu yake nufi saꞌad da ya ce Jehobah ya ba shi sunansa? (Yohanna 17:​11, 12)

6 Da Yesu yake adduꞌa a madadin almajiransa, ya roƙi Jehobah cewa: “Ka lura da su da ikon sunanka, wato sunan da ka ba ni.” (Karanta Yohanna 17:​11, 12.) Hakan yana nufin cewa za a riƙa kiran Yesu Jehobah ke nan? Aꞌa. To, mene ne Yesu yake nufi saꞌad da ya ce Allah ya ba shi sunansa? Da farko dai, Yesu wakilin Jehobah ne, kuma Jehobah ya turo shi ya zo ya yi magana a madadinsa. Yesu ya zo cikin sunan Ubansa kuma ya yi abubuwa masu ban mamaki. (Yoh. 5:43; 10:25) Abu na biyu kuma shi ne, sunan Yesu yana nufin “Jehobah Ne Mai Ceto.” Hakan ya nuna cewa maꞌanar sunan Yesu tana da alaƙa da sunan Jehobah.

7. Ka ba da misalin da ya nuna yadda Yesu zai iya magana a madadin Jehobah.

7 Bari mu yi amfani da wani misali, don mu fahimci yadda Yesu ya wakilci Jehobah. Sarki zai iya tura wani ya je ya yi magana da mutane a madadinsa. Saboda haka, mutanen za su ɗauka abin da mutumin ya faɗa kamar sarkin ne ya faɗa. Haka ma, Yesu yana da ikon yin magana a madadin Jehobah, domin Jehobah ne ya turo shi.—Mat. 21:9; Luk. 13:35.

8. Me ya sa Jehobah ya ce Yesu yana da cikakken ikon sunansa kafin ya zo duniya? (Fitowa 23:​20, 21)

8 Littafi Mai Tsarki ya ce, Yesu shi ne Kalman, domin Jehobah ya yi amfani da shi ya gaya wa malaꞌiku da ꞌyanꞌadam abin da yake so su sani da kuma abin da za su yi. (Yoh. 1:​1-3) Mai yiwuwa Yesu ne malaꞌikan da Jehobah ya aika ya kula da Israꞌilawa saꞌad da suke daji. Da Jehobah ya gaya wa Israꞌilawa cewa su yi wa malaꞌikan biyayya, ya kuma gaya musu dalilin da ya sa ya kamata su yi hakan. Ya ce: “Yana da cikakken ikon Sunana.”a (Karanta Fitowa 23:​20, 21.) Jehobah ya faɗi hakan ne domin Yesu yana magana a madadinsa. Shi ne ainihin wanda yake nuna cewa komen da Jehobah yake yi daidai ne, da kuma cewa shi mai tsarki ne.

“YA UBA, KA ƊAUKAKA SUNANKA”

9. Me ya sa za mu iya cewa Yesu yana ɗaukan sunan Jehobah da muhimmanci sosai?

9 Kamar yadda muka tattauna, tun kafin Yesu ya zo duniya, yana ɗaukan sunan Jehobah da muhimmanci sosai. Kuma a lokacin da yake duniya, ya nuna cewa sunan Jehobah yana da muhimmanci a gare shi a duk abin da yake yi. Kusa da lokacin da zai gama hidimarsa a duniya, ya roƙi Jehobah cewa: “Ya Uba, ka ɗaukaka sunanka.” Nan da nan Jehobah ya amsa da babban murya cewa: “Ai, na riga na ɗaukaka shi, zan ƙara ɗaukaka shi kuma.”—Yoh. 12:28.

10-11. (a) Ta yaya Yesu ya ɗaukaka sunan Jehobah? (Ka kuma duba hoton.) (b) Me ya sa ake bukata a san cewa komen da Jehobah ya yi daidai ne kuma sunansa yana da tsarki?

10 Yesu da kansa ya ɗaukaka sunan Allah. Ta yaya ya yi hakan? Hanya ɗaya ita ce, ta wajen bayyana wa mutane halayen Ubansa masu kyau, da abubuwan ban mamaki da ya yi. Ban da haka ma, akwai abin da ya yi don ya ɗaukaka sunan Jehobah. Yesu ya nuna cewa komen da Jehobah yake yi daidai ne kuma sunansa na da tsarki. Yesu ya nuna muhimmancin yin hakan a lokacin da yake koya wa almajiransa yadda za su yi adduꞌa. Ya ce: “Ubanmu wanda ke cikin sama, A tsarkake sunanka.”—Mat. 6:​9, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe.

11 Me ya sa ake bukatar a tsarkake sunan Jehobah kuma a san cewa komen da yake yi daidai ne? Domin a lambun Adnin, Shaiɗan ya faɗi abubuwan da ba daidai ba game da Jehobah. Shaiɗan ya yi daꞌawa cewa Jehobah maƙaryaci ne, kuma akwai wani abu mai kyau da yake hana wa Adamu da Hauwaꞌu. (Far. 3:​1-5) Ta hakan, Shaiɗan yana nufin cewa Jehobah ba ya yin abubuwa a hanyar da ta dace. Wannan ƙaryar da Shaiɗan ya yi zai iya sa mutane su ga kamar Jehobah mugu ne. Daga baya, a zamanin Ayuba, Shaiɗan ya ce mutane suna bauta wa Jehobah kawai ne don abin da za su samu daga wurinsa. Wannan maƙaryacin ya kuma ce, mutane za su daina bauta wa Jehobah idan suka shiga hali mai wuya, da yake ba ƙaunarsa suke yi da dukan zuciyarsu ba. (Ayu. 1:​9-11; 2:4) Ana bukatar lokaci don a san waye ne maƙaryaci tsakanin Jehobah da Shaiɗan.

Yesu yana yi wa mutane da yawa waꞌazi a kan tudu.

Yesu ya koya wa almajiransa muhimmancin ɗaukaka sunan Jehobah (Ka duba sakin layi na 10))


NA “BA DA RAINA”

12. Mene ne Yesu ya yi domin yana ƙaunar Jehobah?

12 Da yake Yesu yana ƙaunar Jehobah sosai, ya yi niyyar “ba da ransa” domin ya nuna cewa Jehobah yana da tsarki, kuma yadda yake yin abubuwa daidai ne.b (Yoh. 10:​17, 18) Adamu da Hauwaꞌu sun yi wa Jehobah rashin biyayya kuma suka bi raꞌayin Shaiɗan. Amma Yesu bai yi hakan ba. Yesu ya zo duniya kuma ya nuna cewa yana ƙaunar Jehobah. Ya yi hakan ta wurin yi wa Jehobah biyayya a kome da yake yi da kuma faɗa. (Ibran. 4:15; 5:​7-10) Ya riƙe aminci har lokacin da ya mutu a kan gungume. (Ibran. 12:2) Ta haka, Yesu ya nuna cewa yana ƙaunar Jehobah da Sunansa.

13. Me ya sa Yesu ne ya fi dacewa ya nuna cewa Shaiɗan maƙaryaci ne? (Ka kuma duba hoton.)

13 Kome da Yesu ya yi, ya nuna cewa Shaiɗan ne maƙaryaci ba Jehobah ba! (Yoh. 8:44) Ba wanda ya san Jehobah fiye da Yesu. Da akwai gaskiya a cikin abubuwan da Shaiɗan ya faɗa game da Jehobah, da Yesu ya sani. Da yake ƙarya ne Shaiɗan ya yi, Yesu ya yi tsayin daka wajen kāre sunan Jehobah. Har ma a lokacin da Jehobah ya daina kāre shi, Yesu ya gwammaci ya mutu cikin aminci, maimakon ya yi wa Jehobah rashin biyayya.—Mat. 27:46.c

Yesu rataye a kan gungume.

Kome da Yesu ya yi ya nuna sarai cewa Shaiɗan ne maƙaryaci, ba Jehobah ba! (Ka duba sakin layi na 13)


“NA . . . CIKA DUKAN AIKIN DA KA BA NI IN YI”

14. Ta yaya Jehobah ya saka wa Yesu don yadda ya riƙe aminci?

14 A adduꞌar da Yesu ya yi a dare na ƙarshe kafin ya mutu, ya ce: “Na . . . cika dukan aikin da ka ba ni in yi.” Ya gaskata cewa Jehobah zai saka masa don ya riƙe aminci. (Yoh. 17:​4, 5) Kuma abin da Jehobah ya yi ke nan. Bai bar Yesu ya ci gaba da zama a kabari ba. (A. M. 2:​23, 24) Ya tayar da shi, kuma ya ba shi babban matsayi a sama. (Filib. 2:​8, 9) Daga baya, Yesu ya soma sarauta a matsayin sarkin Mulkin Allah. Mene ne Mulkin zai cim ma? Amsar na cikin adduꞌar da Yesu ya gaya wa almajiransa su yi cewa: “Mulkinka ya zo, bari a yi nufinka [Jehobah] a cikin duniya, kamar yadda ake yinsa a cikin sama.”—Mat. 6:10.

15. Mene ne Yesu zai yi a nan gaba?

15 Nan ba da daɗewa ba, Yesu zai yi yaƙi da maƙiyan Allah kuma ya halaka mugaye a yaƙin Armageddon. (R. Yar. 16:​14, 16; 19:​11-16) Ba da daɗewa ba bayan haka, zai jefa Shaiɗan cikin “rami mai zurfi,” inda ba zai sake iya yin kome ba. (R. Yar. 20:​1-3) Saꞌan nan a Sarautar Yesu na Shekara Dubu, Yesu zai sa a sami zaman lafiya a duniya, kuma mutane za su zama marasa zunubi. Zai ta da waɗanda suka mutu kuma ya mai da duniya aljanna. Ta haka, zai cika nufin Allah!—R. Yar. 21:​1-4.

16. Yaya rayuwa za ta kasance bayan Sarautar Yesu na Shekara Dubu?

16 Yaya rayuwa za ta kasance bayan Sarautar Yesu na Shekara Dubu? Zunubi da ajizanci za su zama labari. ꞌYanꞌadam ba za su bukaci a gafarta musu zunubansu ta wajen fansar Yesu ba. Kuma ba za su bukaci wani ya tsaya a madadinsu, don su iya kasancewa da dangantaka mai kyau da Jehobah ba. Kuma “Abokiyar gaba ta ƙarshe” wato mutuwa, ba za ta ƙara kasancewa ba. A lokacin, an riga an ta da dukan waɗanda suka mutu. Kuma dukan mutane a duniya za su zama marasa zunubi.—1 Kor. 15:​25, 26.

17-18. . (a) Me zai faru bayan Sarautar Yesu na Shekara Dubu? (b) Mene ne Yesu zai yi bayan ya gama sarautarsa? (1 Korintiyawa 15:​24, 28) (Ka kuma duba hoton.)

17 Mene ne kuma zai faru bayan Sarautar Yesu na Shekara Dubu? Babu wanda zai sake shakka cewa Jehobah Allah ne mai tsarki da kuma mai adalci. Me ya sa? A lambun Adnin, Shaiɗan ya yi daꞌawa cewa, Jehobah maƙaryaci ne kuma ba ya ƙaunar mutane. Tun daga lokacin, bayin Jehobah ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba, sun nuna cewa yadda Jehobah yake yin abubuwa ne suka fi kyau. Kuma bayan Sarautar Yesu na Shekara Dubu, kowa zai san cewa Jehobah ne yake da gaskiya. Ba wanda zai ƙara yin shakka domin Jehobah ya nuna a hanyoyi da dabam-dabam cewa shi Ubanmu ne mai ƙauna.

18 Bayan Sarautar Yesu na Shekara Dubu, kowa zai san cewa duka abubuwan da Shaiɗan ya faɗa game da Jehobah ƙarya ne. Mene ne Yesu zai yi idan ya gama sarautarsa? Shin, zai yi kamar Shaiɗan ya yi wa Jehobah tawaye? Aꞌa! (Karanta 1 Korintiyawa 15:​24, 28.) Yesu zai mayar wa Ubansa Mulkin, kuma ya ci gaba da zama a ƙarƙashinsa. Da yake Yesu yana ƙaunar Jehobah, zai miƙa masa kowane ikon da yake da shi.

Yesu yana miƙa wa Jehobah hular mulkinsa a sama.

Bayan Sarautar Yesu na Shekara Dubu, zai mayar wa Jehobah Mulkin da dukan zuciyarsa (Ka duba sakin layi na 18)


19. Yaya Yesu yake ɗaukan sunan Jehobah?

19 A gaskiya, Jehobah bai yi kuskure da ya ba wa Yesu sunansa ba! Yesu ya nuna mana sarai wane irin Allah ne Jehobah. Yaya Yesu yake ɗaukan sunan Jehobah? Yana ɗaukan sa da muhimmanci sosai fiye da kome. Ya gwammaci ya mutu domin sunan, kuma zai kasance da niyyar miƙa wa Jehobah dukan ikon da Jehobah ya ba shi a ƙarshen sarautarsa. Ta yaya za mu yi koyi da Yesu? Abin da za mu tattauna ke nan a talifi na gaba.

MECE CE AMSARKA?

  • Ta yaya Yesu ya taimaka wa almajiransa su ƙara sanin sunan Jehobah?

  • Ta yaya Jehobah ya ba wa Yesu sunansa?

  • Mene ne Yesu yake da niyyar yi domin sunan Jehobah, kuma me ya sa?

WAƘA TA 16 Mu Yabi Jehobah Domin Ɗansa

a Akwai wasu lokutan da malaꞌiku suka kawo wa ꞌyanꞌadam saƙonni a madadin Jehobah. Shi ya sa a wasu wurare a Littafi Mai Tsarki, ko da yake malaꞌika ne yake magana, ana cewa Jehobah ne. (Far. 18:​1-33) Alal misali, ko da yake Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah ne da kansa ya ba wa Musa Dokoki, wasu ayoyi sun nuna cewa Jehobah ya yi amfani da malaꞌiku ne wajen yin haka.—L. Fir. 27:34; A. M. 7:​38, 53; Gal. 3:19; Ibran. 2:​2-4.

b Mutuwar Yesu ya kuma buɗe hanya don ꞌyanꞌadam su sami damar yin rayuwa har abada.

c Ka dubu “Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu” a Hasumiyar Tsaro ta Afrilu, 2021, shafi na 30-31.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba