Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • ijwyp talifi na 15
  • Sifata Ce Ta Fi Mini Muhimmanci?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Sifata Ce Ta Fi Mini Muhimmanci?
  • Tambayoyin Matasa
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Wasa kwakwalwa: Sifata Ce Ta Fi Mini Muhimmanci?
  • ‘Me ya sa nake da mummunar sifa?’
  • ‘Ya kamata na canza yadda na ke ado?’
  • Ci kwalliya mafi kyau!
  • Me Ya Sa Nake Yawan Damuwa da Surar Jikina?
    Amsoshi ga Tambayoyi 10 da Matasa Suke Yi
  • Ta Yaya Zan Rage Nauyin Jikina?
    Tambayoyin Matasa
  • Me Zai Taimaka Min In Rika Motsa Jiki?
    Tambayoyin Matasa
Tambayoyin Matasa
ijwyp talifi na 15

TAMBAYOYIN MATASA

Sifata Ce Ta Fi Mini Muhimmanci?

  • Wasa kwakwalwa: Sifata Ce Ta Fi Mini Muhimmanci?

  • Me ya sa sifar jikina ba ta da kyau?

  • Ya kamata ne na sake sifata?

  • Sakewa mafi kyau!

  • Labarin Julia

Wasa kwakwalwa: Sifata Ce Ta Fi Mini Muhimmanci?

  1. Wanne cikin furuci na gaban nan ya kwatanta yadda kike ji?

    • Ba na taba gamsuwa da adona ba.

    • A wani lokaci na kan so adona.

    • A ko yaushe ina son adon da nake yi.

  2. Me za ka so ka canza a jikinka?

    • Tsayi

    • Kiba

    • Sifar jiki

    • Suma

    • Launin fata

    • Girman jiki

    • Wasu fannoni

  3. Ka kammala sauran furuci na gaba.

    Ba na son yadda jikina yake. . .

    • sa’ad da na hau ma’auni.

    • sa’ad da na duba madubi.

    • sa’ad da na gwada kaina da wasu, wato, (abokai, ’yan yayi, ’yan wasa).

  4. Ka kammala wadannan furucin.

    Na kan auna nauyi na . . .

    • kowacce rana.

    • kowane mako.

    • Fiye da sau daya a mako.

  5. Wanne cikin furucin ya yi daidai da yadda ka ke ji?

    • Sifar jiki marar kyau. (Misali: Serena ta ce: “Duk lokacin da na duba madubi, sai na ga wata kibabbiya, mummunar sifa. Har sai na ki cin abinci wai don na rage kibata.”)

    • Sifar jiki da ta dace. (Misali: Natanya ta ce: “Ko yaushe za mu ga wani abin da ba ma so a jikinmu, wasun su ba za mu iya maganinsa ba. Wawanci ne mu nace a kan abin da ba za mu iya maganinsa ba.”)

Littafi Mai Tsarki ya gaya mana kada mu ‘aza kanmu gaba da inda ya kamata.’ (Romawa 12:3) Saboda haka, ya dace kuma daidai ne mu aza kanmu yadda ya kamata. Alal misali, abin da ya sa ke nan kake wanke bakinka kuma kana kula da tsabtar jikinka.

Idan kuma kin damu kwarai game da sifar jikinki fa, har ma yana ci miki rai? Idan haka ne, zai yi kyau ki yi tunanin wannan . . .

‘Me ya sa nake da mummunar sifa?’

Da akwai dalilai da yawa. Sun kunshi:

  • Tasirin hanyoyin sadarwa. Kellie ta ce: “Hotunan mutane masu kyaun gani, masu tsini da matasa suke gani a telebijin ko da yaushe yana shafansu. Domin haka, ba ma farin ciki idan ba mu yi irin adonsu ba!”

  • Tasiri daga iyaye. Rita ta ce: “Na lura cewa idan uwata ta mai da hankali sosai da adonta, hakan ya kan shafi yadda yarinyar za ta ji game da yadda take ado. Wannan haka yake game da ubanni da suke da yara maza.”

  • Sai ki ji ba ki da mutunci. Jeanne ta ce: “Mutane da suka fi mai da hankali game da sifarsu suna son mutane su yaba musu idan suka yi ado. Wannan zai sa ba za ki so ku yi tafiya tare da ita ba!”

Ko da mene ne ya faru, za ki iya tunani cewa . . .

‘Ya kamata na canza yadda na ke ado?’

Ki saurari abin da wasu tsararki suka ce.

Rori ta ce: “Ba za ki iya canza sifarki ba, zai dace ki kyale wasu lahani kawai. Idan ki ka kyale lahanin, yawancin mutane ba za su ma san abin da ke faruwa ba.”

Olivia ta ce: “Ki yi iyakacin kokarinki ki kula da lafiyar jikinki. Idan ki ka yi haka fa za a ga kyaunki. Wanda ba ya son yadda ki ke, (da yake son ki yi kama da wata) to, ba ya sonki da gaske.”

Batun shi ne: Ki yi iyakacin kokarinki a adana jikinki. Manta da sauran. Yawan damuwa game da adonki zai iya kasance da hadari (Duba “Labarin Julia.”)

Erin ta lura cewa idan ki ka kasance da halin daidaita abubuwa, zai taimake ki ki daure da yadda ki ke. Ta ce: “Hakika na kan razana, amma na lura cewa ina bakin ciki idan na mai da hankali kan abubuwa marasa amfani. Abin da nake yi yanzu shi ne wasan motsa jiki kuma na ci abinci mai gina jiki. Sai a ci kwalliya kawai.”

Ci kwalliya mafi kyau!

Za ki fi kyau sosai ma idan kin daidaita yadda ki ke ji game da adon jikinki. Littafi Mai Tsarki zai taimaka. Ya ce mu yi abubuwan nan na gaba:

  • Gamsuwa. “Gwamma abin da ido ke gani, da a yi sha’awa barkatai: wannan kuma banza ne; cin iska kawai.”—Mai-Wa’azi 6:9.

  • Ki daidaita a wasan motsa jikinki. “Wasan jiki tana da amfaninta kadan.”​—1 Timotawus 4:8.

  • Kyaun halin kirki. “Mutum yakan dubi kyan tsari ne kawai, amma Ubangiji yakan dubi zuciya.”​—1 Sama’ila 16:7.

Sarah ta ce: “Fuskarmu takan nuna abin da ke cikin zuciyarmu. Idan mutumin ba ya alhini, mai fara’a ke nan.”

Phylicia ta ce: “An fi mai da hankali ga kyaun mutum na zahiri. Amma nagarin halayen mutumin ne musamman ake tuna da su.”

Duba Misalai 11:22; Kolosiyawa 3:​10, 12; 1 Bitrus 3:​3, 4.

Labarin Julia

Lokacin da nake shekara 16, kibata ta zama mini matsala. Ni ba katuwa ba ce kuma ba siririya ba. Ina da dan jiki ne kawai. Ina tsammanin cewa idan na zama siririya samari za su so ni. Sai na kusan kashe kaina da yunwa domin ina son in zama siririya.

Na zama siririyar, amma ya kai ni rashin lafiya. Na sha magani amma babu kwanciyar hankali. Har yanzu, cin abinci matsala ne. A yanzu, na soma daina dauka sifar jikina da muhimmanci. Ina cin abinci na daidai kuma na yi wasan jiki da ya dace. Amma duk lokacin da na yi fushi, na ki cin abinci ina wulakanta kaina.

Da zai yiwu, zan gaya wa sauran matasa cewa kowa da ra’ayinsa. Ko yaya sifarki take, akwai wadanda za su so ki, akwai kuma wadanda ba za su so ki ba. Muhimmin abu shi ne kina da lafiya. Abin da ke da muhimmanci ma ke nan ga wadanda suke son ki da gaske.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba