Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • jl darasi na 9
  • Ta Yaya Za Mu Yi Shiri Sosai Kafin Mu Halarci Taro?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ta Yaya Za Mu Yi Shiri Sosai Kafin Mu Halarci Taro?
  • Su Wane Ne Suke yin Nufin Jehobah A Yau?
  • Makamantan Littattafai
  • Mu Yabi Jehobah a Cikin Ikilisiya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
  • Mu Dinga Karfafa Juna a Taron Ikilisiya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi​—Ka Koya wa Dalibinka Yadda Zai Rika Yin Shiri Don Nazari
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2018
Su Wane Ne Suke yin Nufin Jehobah A Yau?
jl darasi na 9

DARASI NA 9

Ta Yaya Za Mu Yi Shiri Sosai Kafin Mu Halarci Taro?

Wani Mashaidi yana shirin taron ikilisiya na Shaidun Jehobah

Kambodiya

Wani Mashaidi yana shirin taron ikilisiya na Shaidun Jehobah
Mashaidiya tana so ta yi kalami a taron ikilisiya na Shaidun Jehobah

Yukiren

Idan kana nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah, mai yiwuwa kana yin shiri kafin kowane nazari. Hakazalika, idan kana so ka amfana sa’ad da ka halarci taro a Majami’ar Mulki, zai dace ka yi shiri kafin ka halarci taron. Amma za mu amfana sosai idan muna da tsari mai kyau da muke bi a kai a kai.

Ka zaɓi lokaci da kuma wurin da za ka yi nazari. A wane lokaci ne za ka fi mai da hankali wuri ɗaya sa’ad da kake nazari? Da sassafe ne kafin ka fara aiki, ko kuma can da yamma bayan yaranka sun yi barci? Ko da ba zai yiwu ka ɗauki lokaci mai tsawo ba kana nazari, ka ayyana yawan lokacin da za ka yi kana nazarin, kuma kada ka bari wani abu ya hana ka yin hakan da zarar ka fara. Ka zaɓi wurin da babu surutu, kuma ka kashe abubuwa da za su iya ɗauke hankalinka, kamar su rediyo da talabijin da kuma wayar tarho. Yin addu’a kafin ka soma nazari zai taimaka maka ka rage tunanin abubuwan da ke damunka don ka mai da hankali sosai ga Kalmar Allah da kake son ka karanta.—Filibiyawa 4:6, 7.

Ka ja layi a ƙarƙashin amsar kuma ka yi shirin yin furuci. Ka fahimci batun da ake son a tattauna sosai. Ka yi tunani a kan jigon talifin ko kuma babin, ka lura da alaƙar da ke tsakanin kowane ƙaramin jigo da ainihin jigon talifin, kuma ka bincika hotunan da ke talifin da kuma tambayoyin bita da suke nuna muhimman darussa. Ka karanta duk wani nassin da aka ambata a talifin, kuma ka yi tunani a kan yadda suka goyi bayan abin da ake tattaunawa. (Ayyukan Manzanni 17:11) Sa’ad da ka gano amsar tambayar, ka ja layi a ƙarƙashin kalmomin da za su taimaka maka ka tuna amsar da kake son ka bayar. Sa’an nan a taro, kana iya ɗaga hannu don ka yi furuci bisa abin da ka fahimta daga talifin.

Idan kana bincika batutuwa dabam-dabam da ake tattaunawa a taro a kowane mako, iliminka na Littafi Mai Tsarki zai ƙaru.—Matta 13:51, 52.

  • Wane irin tsari ne za ka bi don ka shirya abubuwan da za a tattauna a taro?

  • Ta yaya za ka yi shiri don ka yi furuci a taro?

KA ƘARA BINCIKE

Ka bi tsarin da aka nuna a sama, ka shirya Nazarin Hasumiyar Tsaro ko kuma Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya. Ka gaya wa wanda yake nazarin Littafi Mai Tsarki da kai ya taimake ka ka shirya furucin da za ka iya yi a taro na gaba.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba