Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • th darasi na 18 p. 21
  • Mutane Su Koyi Darasi Daga Jawabin

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mutane Su Koyi Darasi Daga Jawabin
  • Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Yi Magana da Kuzari
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Maganarka ta Ratsa Zuciya
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Ka Nuna Yadda Za Su Amfana
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Ka Bayyana Nassin da Ka Karanta
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
Dubi Ƙari
Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
th darasi na 18 p. 21

DARASI NA 18

Mutane Su Koyi Darasi Daga Jawabin

Nassin da aka ambata

1 Korintiyawa 9:​19-23

ABIN DA ZA KA YI: Ka sa masu sauraronka su yi tunani a kan batun da kake gaya musu kuma su ji sun koyi darussa masu muhimmanci.

YADDA ZA KA YI HAKAN:

  • Ka yi la’akari da abin da masu sauraronka suka sani. Maimakon ka gaya musu abin da suka sani a dā, ka taimaka musu su fahimci batun a wata hanya dabam.

    Shawara mai amfani

    Kada ka ɓata lokaci kana bayyana abin da suka riga suka sani, amma ka bayyana musu abin da ba su sani ba a hankali.

  • Ka yi bincike kuma ka yi tunani. Idan zai yiwu, ka ba da labarin da mutane ba su sani sosai ba don ka bayyana darussa masu muhimmanci. Ka yi tunani sosai game da batun da kake tattaunawa da kuma yadda binciken da ka yi ya jitu da batun.

    Shawara mai amfani

    Sa’ad da kake shirya bayaninka, ka yi wa kanka tambayoyi kamar ‘mene ne, me ya sa, yaushe, a ina, wane ne da kuma ta yaya.’ Sa’ad da kake jawabin, kana iya yin wasu daga cikin tambayoyin nan kuma ka amsa su. Hakan zai sa masu sauraro su ji daɗin jawabin.

  • Ka nuna musu muhimmancin maganarka. Ka bayyana yadda bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki za su taimaka wa masu sauraronka a rayuwarsu. Ka faɗi yanayi da halaye da kuma abubuwan da suka shafi masu sauraronka.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba