Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • th darasi na 12 p. 15
  • Ka Nuna Kauna da Tausayi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Nuna Kauna da Tausayi
  • Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Yi Magana da Kuzari
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Maganarka ta Ratsa Zuciya
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Ka Yi Kamar Kuna Tattaunawa
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Ka Yi Jawabi Mai Karfafawa
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
Dubi Ƙari
Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
th darasi na 12 p. 15

DARASI NA 12

Ka Nuna Ƙauna da Tausayi

Nassin da aka rubuta

1 Tasalonikawa 2:​7, 8

ABIN DA ZA KA YI: Ka nuna wa masu sauraronka cewa kana ƙaunarsu kuma ka damu da su.

YADDA ZA KA YI HAKAN:

  • Ka yi tunani game da masu sauraronka. A lokacin da kake yin shiri, ka yi tunani sosai game da matsalolin da masu sauraronka suke fuskanta, kuma ka ɗauka kana cikin yanayinsu.

  • Ka yi amfani da kalaman da suka dace. Ka nemi yadda za ka ƙarfafa da kuma faranta zuciyar masu sauraronka. Ka guji yin amfani da kalaman da za su sa su fushi kuma kada ka yi maganar da ba ta dace ba game da waɗanda ba sa bauta wa Jehobah.

  • Ka nuna ka damu da su. Ka yi amfani da murya mai daɗi kuma ka motsa hannayenka yadda suka dace, don masu sauraronka su ga cewa ka damu da su. Kuma ka riƙa fara’a.

    Shawara mai amfani

    Ka nuna ka damu da su da gaske. Idan kana karatu, ka karanta ainihin abin da ke a rubuce da muryar da ta dace kuma kada ka sa masu sauraronka su mai da hankali a kanka. Don masu sauraronka su amfana, ka yi magana yadda zai nuna cewa ka damu kuma kana ƙaunarsu.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba