Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • th darasi na 20 p. 23
  • Kammalawa Mai Dadi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kammalawa Mai Dadi
  • Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Bayyana Nassin da Ka Karanta
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Maganarka ta Ratsa Zuciya
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Ka Nuna Yadda Za Su Amfana
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Muhimman Bayanan Su Fita Dalla-Dalla
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
Dubi Ƙari
Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
th darasi na 20 p. 23

DARASI NA 20

Kammalawa Mai Daɗi

Nassin da aka ambata

Mai-Wa’azi 12:​13, 14

ABIN DA ZA KA YI: Sa’ad da kake kammalawa, ka taimaka wa masu sauraronka su amince da abin da ka faɗa kuma su yi amfani da shi.

YADDA ZA KA YI HAKAN:

  • Kammalawarka ta yi daidai da jigon jawabinka. Ka sake maimaita muhimman batutuwan da ke jawabinka.

  • Ka ƙarfafa masu sauraronka. Ka nuna wa masu sauraronka abin da za su yi da kuma dalilin da ya sa za su yi hakan. Ka yi magana da tabbaci.

  • Kammalawarka ta zama mai sauƙi kuma gajere. Kada ka ƙara batutuwan da ba ka sa su cikin jawabinka ba. Ka kammala da kalamai kaɗan sa’ad da kake ƙarfafa masu sauraronka su yi amfani da abin da suka koya.

    Shawara mai amfani

    Yayin da kake kammalawa, kada ka yi magana da sauri kuma kada ka saukar da muryarka. Ka yi magana yadda zai nuna cewa kana son ka kammala jawabinka.

SA’AD DA KAKE WA’AZI

Sa’ad da kake kammala tattaunawar, ka nanata darussan da kake son mai sauraronka ya tuna. Ko da an katse maganarka, ka yi magana mai daɗi kafin ka tafi. Ko da maigidan ya maka baƙar magana, ka yi maganar da za ta sa maigidan ya saurara idan aka sake zuwa gidansa wa’azi.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba