Ƙauna Ta Gina Ka
“Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan hankalinka.”—MATIYU 22:37.
1. (a) Waɗanne abubuwa ne Kirista yake koya? (b) Wannene hali mafi muhimmanci na Kirista, kuma me ya sa?
KIRISTA yana koyon abubuwa da yawa domin ya zama ƙwararren mai hidima. Littafin Karin Magana ya taƙaita muhimmancin ilimi, fahimta, da kuma hikima. (Karin Magana 2:1-10) Manzo Bulus ya tattauna bukatar bangaskiya mai ƙarfi da kuma bege. (Romawa 1:16, 17; Kolosiyawa 1:5; Ibraniyawa 10:39) Jimiri da kuma kame kai ma suna da muhimmanci. (Ayyukan Manzanni 24:25; Ibraniyawa 10:36) Duk da haka, akwai aba da idan babu, za ta ɗauke hankali daga dukan sauran abubuwa, za ta iya mai da su su zama wofi ma. Wannan aba ita ce ƙauna.—1 Korantiyawa 13:1-3, 13.
2. Ta yaya Yesu ya nuna muhimmancin ƙauna, kuma waɗanne tambayoyi wannan ya jawo?
2 Yesu ya nuna muhimmancin ƙauna lokacin da ya ce: “Ta haka kowa zai gane ku almajiraina ne, in dai kuna da ƙaunar juna.” (Yahaya 13:35) Tun da ƙauna ita ce alamar gane Kiristoci na gaskiya, muna bukatar mu yi tambayoyi kamar su, Mecece ƙauna? Me ya sa take da muhimmanci haka, da Yesu zai ce, fiye da kome, za ta nuna almajiransa? Ta yaya za mu koyi ƙauna? Wa za mu ƙaunata? Bari mu bincika waɗannan tambayoyi.
Mecece Ƙauna?
3. Ta yaya za a kwatanta ƙauna, kuma me ya sa ta ƙunshi hankali da kuma zuciya?
3 Wani kwatancin ƙauna shi ne ‘jin ka manne wa ko kana murna dominsa ko kuma son wani.’ Hali ne da yake motsa mutane su yi nagarin aiki domin wasu su amfana, a wasu lokatai ma ya haɗa da sadaukar da kai. Ƙauna, yadda aka kwatanta ta a cikin Littafi Mai Tsarki, ta shafe hankali da kuma zuciya. Hankali, ko kuma azanci, yana da nasa aiki domin mutum wanda yake ƙauna yana yin haka ne da idanunsa a buɗe, da fahimtar cewa shi da kuma waɗansu mutane da yake ƙauna, dukansu raunannu ne kuma suna da halaye da suke da kyau. Har ila ya shafi azanci tun da akwai waɗanda Kirista yake ƙauna—wataƙila a wasu lokatai, ba da sonsa ba—domin ya sani daga karatunsa na Littafi Mai Tsarki cewa Allah yana son ya ƙaunace su. (Matiyu 5:44; 1 Korantiyawa 16:14) Duk da haka, ƙauna ainihi takan fito ne daga zuciya. Ƙauna ta gaskiya yadda Littafi Mai Tsarki ya nuna ba kawai daga azanci ba ne. Ta ƙunshi gaskiya da kuma cikakken so.—1 Bitrus 1:22.
4. A wace hanya ce ƙauna magami ce mai ƙarfi?
4 Mutane da suke da son kai a zuciyarsu da ƙyar su yi abota ta ƙauna domin mutumin da yake ƙauna a shirye yake ya yi abin da wani yake so a gaba da nasa. (Filibiyawa 2:2-4) Kalmomin Yesu “bayarwa ta fi karɓa albarka” gaskiya ce musamman idan bayarwar ta nuna ƙauna ce. (Ayyukan Manzanni 20:35) Ƙauna magami ce mai ƙarfi. (Kolosiyawa 3:14) Sau da yawa ta ƙunshi abokantaka, amma magamin ƙauna yana da ƙarfi fiye da na abokantaka. Soyayya da take tsakanin mata da mijinta wasu lokatai ana kwatanta ta da ƙauna; amma, ƙauna da Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu mu koya ta fi jimrewa fiye da ƙauna ta sha’awa. Idan mata da miji suna ƙaunar juna da gaske, za su zauna tare ko idan babu sha’awa ta jiki kuma domin raunana ta tsufa ko kuma ɗaya cikinsu ya naƙasa.
Ƙauna—Hali da Take da Muhimmanci
5. Me ya sa ƙauna muhimmiyar hali ce ga Kirista?
5 Me ya sa ƙauna muhimmiyar hali ce ga Kirista? Na ɗaya, domin Yesu ya umarci mabiyansa su ƙaunaci juna. Ya ce: “Ku aminaina ne in kuna yin abin da na umarce ku. Na umarce ku haka domin ku ƙaunaci juna.” (Yahaya 15:14, 17) Na biyu, domin Jehovah shi ne ƙauna, kuma masu bauta masa dole ne su yi koyi da shi. (Afisawa 5:1; 1 Yahaya 4:16) Littafi Mai Tsarki ya ce samun sani na Jehovah da kuma na Yesu yana nufin rai madawwami. Ta yaya za mu ce mun san Allah idan ba mu yi ƙoƙarin zama kamarsa ba? Manzo Yahaya ya ce: “Wanda ba ya ƙauna, bai san Allah ba sam, domin Allah shi ne ƙauna.”—1 Yahaya 4:8.
6. Ta yaya ƙauna za ta daidaita ɓangarorin rayuwarmu dabam dabam?
6 Ƙauna tana da muhimmanci domin dalili na uku: Tana taimaka mana mu daidaita ɓangarori dabam dabam na rayuwarmu kuma tana sa abin da muka yi ya zama daga zuciyar kirki. Alal misali, yana da muhimmanci a ci gaba da samun ilimi na Kalmar Allah. Ga Kirista, irin wannan ilimin kamar abinci yake. Tana taimakonsa ya manyanta kuma ya yi aiki cikin jituwa da nufin Allah. (Zabura 119:105; Matiyu 4:4; 2 Timoti 3:15, 16) Duk da haka, Bulus ya yi gargaɗi: “Ilimi yakan kumbura mutum, ƙauna kuwa takan inganta shi.” (1 Korantiyawa 8:1) A’a, cikakken sani ba shi da wani laifi. Damuwar a gare mu ne—muna da muradin yin zunubi. (Farawa 8:21) Idan babu rinjayar ƙauna, ilimi zai iya sa mutum ya kumbura, yana tunanin ya fi wasu. Hakan ba zai faru ba idan ainihi ƙauna ce ta motsa shi. “Ƙauna . . . ba ta yin kumbura.” (1 Korantiyawa 13:4) Kirista da ƙauna ta motsa shi ba ya fahariya ko ya sami ilimi mai yawa. Ƙauna tana sa shi ya zama mai tawali’u kuma ta hana shi son yin suna wa kansa.—Zabura 138:6; Yakubu 4:6.
7, 8. Ta yaya ƙauna take taimaka mana mu mai da hankali ga abubuwa mafifita?
7 Bulus ya rubuta wa Filibiyawa: “Addu’ata ita ce, ƙaunarku ta riƙa haɓaka da sani da matuƙar ganewa, domin ku zaɓi abubuwa mafifita.” (Filibiyawa 1:9, 10) Ƙauna ta Kirista za ta taimaka mana mu bi wannan ƙarfafar mu zaɓi abubuwa mafifita. Alal misali, ka yi la’akari da kalmomin Bulus ga Timoti: “Duk mai burin aikin kula da ikilisiya, yana burin aiki mai kyau ke nan.” (1 Timoti 3:1) A cikin shekarar hidima ta 2000, adadin ikilisiyoyi a dukan duniya sun ƙaru da 1,502, sabon adadin ya zama 91,487. Saboda haka, ana bukatar dattawa sosai, kuma waɗanda suka kai a ba su wannan gatar, an yaba musu.
8 Har ila yau, waɗanda suka kai a ba su gatar kula ya kamata su kasance da daidaici idan suka tuna da manufar wannan gatar. Samun iko ko yin suna ba shi ne abu mai muhimmanci ba. Dattawa waɗanda suke faranta wa Jehovah rai ƙaunarsa da kuma ta ’yan’uwansu ce take motsa su. Ba suna suke nema ba ko kuma rinjaya. Manzo Bitrus, bayan ya gargaɗi dattawan ikilisiya su kasance da ɗabi’a mai kyau, ya nanata bukatar “tawali’u.” Ya gargaɗi dukan ikilisiyar: “Ku ƙasƙantar da kanku ga maɗaukakin ikon Allah.” (1 Bitrus 5:1-6) Ko waye da yake burin, ya yi la’akari da misalin dattawa da yawa a dukan duniya waɗanda suke aiki tuƙuru, masu tawali’u, kuma saboda haka albarka ce ga ikilisiyoyinsu.—Ibraniyawa 13:7.
Zuciyar Kirki Tana Taimaka Mana Mu Jimre
9. Me ya sa Kiristoci suke tuna alkawarin albarka na Jehovah?
9 An gan muhimmancin motsawar ƙauna a wata hanya kuma. Ga waɗanda suka biɗi ibada domin ƙauna, Littafi Mai Tsarki ya yi alkawarin albarka mai kyau yanzu da kuma albarka a nan gaba da ta fi gaban a faɗe ta. (1 Timoti 4:8) Kirista wanda ya gaskata waɗannan alkawuran ƙwarai ya kuma tabbata cewa Jehovah shi ne mai “sakamako ga masu nemansa” ya sami taimako ya tsaya a kan bangaskiyarsa da kyau. (Ibraniyawa 11:6) Yawancinmu muna son ganin cikan alkawuran Allah kuma muna maimaita abin da manzo Yahaya ya ce: “Amin. Zo, ya Ubangiji Yesu.” (Wahayin Yahaya 22:20) Hakika, bimbini bisa albarkar da take gaba idan muna da aminci yana ƙarfafa mu mu jimre, kamar yadda tuna da “farin cikin da aka sa gabansa” ya taimaki Yesu ya jimre.—Ibraniyawa 12:1, 2.
10, 11. Ta yaya motsawar ƙauna take sa mu jimre?
10 To, idan muradinmu na rayuwa a sabuwar duniya shi ne ainihin abin da yake motsa mu mu bauta wa Jehovah fa? Da haka zai zama da sauƙi mu kasa yin haƙuri, ko kuma mu zama masu rashin gamsuwa lokacin da abubuwa suka zama da wuya, ko kuma idan ba su faru yadda muka yi tsammaninsu ba ko kuma lokacin da muka zace su ba. Za mu iya shiga haɗari ƙwarai na bauɗewa. (Ibraniyawa 2:1; 3:12) Bulus ya yi maganar wani abokinsa na dā mai suna Dimas, wanda ya yashe shi. Me ya sa? Domin yana “ƙaunar duniyan nan.” (2 Timoti 4:10) Duk wanda yake bauta domin amfanin kansa yana cikin haɗarin kasance kamarsa. Abubuwan da duniya za ta bayar yanzu za su rinjaye su, ba za su so su sadaukar da kai yanzu ba domin begen albarka da take gaba.
11 Ko da yake ba laifi ba ne mu yi muradin samun albarka na nan gaba da kuma begen samun sauƙi daga gwaji, ƙauna tana ƙara fahimtarmu ga abin da ya kamata ya zama na ɗaya a rayuwarmu. Nufin Jehovah, ba namu ba ne, ya fi muhimmanci. (Luka 22:41, 42) Hakika, ƙauna tana gina mu. Tana sa mu gamsu mu jira cikin haƙuri ga Allah, muna gamsuwa da kowacce albarka da ya ba mu da tabbaci cewa a lokacinsa za mu samu dukan abin da ya yi alkawarinsa—har da ƙari. (Zabura 145:16; 2 Korantiyawa 12:8, 9) A yanzu dai, ƙauna tana taimaka mana mu ci gaba da bauta ba da son kai ba domin “ƙauna ba ta sa sonkai.”—1 Korantiyawa 13:5.
Waɗanne Ne Ya Kamata Kiristoci Su Yi Ƙaunarsu?
12. In ji Yesu, waye za mu yi ƙaunarsa?
12 Yesu ya ba da doka game da waɗanda za mu ƙaunace su lokacin da ya ɗauko furci biyu daga Dokar Musa. Ya ce: “Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan hankalinka” kuma, “Ka ƙaunaci ɗan’uwanka kamar kanka.”—Matiyu 22:37-39.
13. Ta yaya za mu koyi mu yi ƙaunar Jehovah ko da yake ba ma iya ganinsa ba?
13 Daga kalmomin Yesu, a bayyane yake cewa na farko ya kamata mu ƙaunaci Jehovah. Duk da haka, ba a haife mu da cikakkiyar ƙauna ga Jehovah ba. Wannan aba ce da dole mu koya. Da muka ji game da shi da farko, muka jawu wurinsa domin abin da muka ji. A hankali, muka koyi yadda ya shirya duniya domin mutane. (Farawa 2:5-23) Muka koyi yadda ya bi da mutane, bai yashe mu ba lokacin da zunubi ya shigo iyalin ’yan Adam, amma ya ɗauki matakai ya cece mu. (Farawa 3:1-5, 15) Ya yi kirki ga waɗanda suke da aminci, a ƙarshe ya ba da Ɗansa makaɗaici domin gafarta zunubi. (Yahaya 3:16, 36) Wannan ƙarin ilimi ya sa ƙaunarmu ga Jehovah ta ƙaru. (Ishaya 25:1) Sarki Dauda ya ce yana ƙaunar Jehovah domin kulawarsa ta ƙauna. (Zabura 116:1-9) A yau, Jehovah yana kula da mu, yana ja-gorarmu, yana ba mu ƙarfi, kuma yana ƙarfafa mu. Da zarar mun ƙara ilimi game da shi, haka ƙaunarmu take ƙaruwa.—Zabura 31:23; Zafaniya 3:17; Romawa 8:28.
Ta Yaya Za Mu Nuna Ƙaunarmu?
14. A wace hanya ce za mu nuna cewa ƙaunarmu ga Allah ta gaske ce?
14 Ko da yake, mutane da yawa a duniya sun ce suna ƙaunar Allah, amma ayyukansu sun ƙaryata da’awarsu. Ta yaya za mu san cewa da gaske muna ƙaunar Jehovah? Za mu iya yi masa magana cikin addu’a mu gaya masa yadda muke ji. Kuma za mu iya aikata a hanyar da ta nuna ƙaunarmu. Manzo Yahaya ya ce: “Duk wanda ke kiyaye magana ta [Allah], wannan kam, hakika yana ƙaunar Allah, cikakkiyar ƙauna. Ta haka muka tabbata muna cikinsa.” (1 Yahaya 2:5; 5:3) Tsakanin wasu abubuwa, Kalmar Allah ta gaya mana mu riƙa taruwa kuma mu yi rayuwa mai tsabta, ta ɗabi’a. Mu guje wa riya, mu faɗi gaskiya, mu tsabtace tunaninmu. (2 Korantiyawa 7:1; Afisawa 4:15; 1 Timoti 1:5; Ibraniyawa 10:23-25) Muna nuna ƙauna wajen bayar da taimakon kayayyaki ga waɗanda suke da bukata. (1 Yahaya 3:17, 18) Kuma ba ma ja da baya wajen gaya wa wasu game da Jehovah. Wannan ya haɗa da saka hannu cikin wa’azin bisharar Mulki ta duniya gabaki ɗaya. (Matiyu 24:14; Romawa 10:10) Yin biyayya ga Kalmar Allah a irin waɗannan abubuwa tabbaci ne cewa ƙaunarmu ga Jehovah ta gaske ce.
15, 16. Ta yaya ƙauna ga Allah ta taɓa rayuka da yawa a bara?
15 Ƙaunar Jehovah tana taimakon mutane su tsai da shawara masu kyau. Bara, irin wannan ƙaunar ta motsa mutane 288,907 su keɓe masa rayukansu kuma su ba da alamar wannan shawarar ta baftismar ruwa. (Matiyu 28:19, 20) Keɓe kansu yana da ma’ana. Yana ba da alamar canji a rayuwarsu. Alal misali, Gazmend yana ɗaya daga cikin zakarun ƙwallon raga a Albaniya. Na wasu shekaru, shi da matarsa suka yi nazarin Littafi Mai Tsarki kuma duk da tangarɗa, a ƙarshe suka ƙware suka zama masu shelar Mulki. A bara, Gazmend ya yi baftisma, ɗaya daga cikin 366 da suka yi baftisma a Albaniya a shekarar hidima ta 2000. Wata jarida ta buga wani talifi game da shi, ta ce: “Rayuwarsa tana da ma’ana, kuma saboda wannan, shi da iyalinsa suna more kwanakin farin ciki a rayuwansu. Shi kam, abin da zai iya samu a rayuwa ba shi ba ne abu mafi muhimmanci a gare shi a yanzu, maimakon haka, abin da zai yi don ya taimake wasu mutane ne ya fi muhimmanci.”
16 Hakanan, wata ’yar’uwa da ta yi baftisma ba da jimawa ba tana aiki a kamfanin man fetur a Guam, aka ba ta ƙarin girma. Bayan ta sami matsayi mai girma shekaru da yawa, a ƙarshe aka ba ta zarafin ta zama mace ta farko da za ta zama mataimakiyar shugaban kamfanin a dukan tarihin kamfanin. Amma, ta riga ta keɓe ranta ga Jehovah. Bayan ta tattauna batutuwa da mijinta, sabuwar ’yar’uwar ta ƙi makamin kuma ta shirya ta yi aiki na ɗan lokaci saboda ta samu ci gaba ta zama mai hidimar cikakken lokaci, majagaba. Ƙaunar Jehovah ta motsa ta ta so ta bauta masa a zaman majagaba maimakon ta nemi arziki na wannan duniyar. A dukan duniya irin wannan ƙauna ta motsa mutane 805,205 su saka hannu cikin ɓangarorin hidimar majagaba dabam dabam a shekarar hidima ta 2000. Wannan nuna ƙauna ce da kuma bangaskiya waɗannan majagaba suka yi!
Sun Motsa Su Ƙaunaci Yesu
17. Wane misali ne mai kyau na ƙauna muka gani a wajen Yesu?
17 Yesu misali ne mai kyau ƙwarai na wanda ƙauna ta motsa shi. Kafin ya zama mutum, yana ƙaunar Ubansa kuma yana ƙaunar ’yan Adam. Lokacin da aka kwatanta shi da hikima, ya ce: “Ina kusa da shi [Jehovah] kamar mai tsara fasalin gini, ni ce abar murnarsa kowace rana, a koyaushe ina farin ciki a gabansa. Ina farin ciki da duniya, ina murna da ’yan adam.” (Karin Magana 8:30, 31) Ƙaunar Yesu ta motsa shi ya bar wajen zamansa a samaniya aka haife shi jariri. Ya bi da masu tawali’u cikin haƙuri da kirki kuma ya wahala a hannun abokan gaban Jehovah. A ƙarshe, ya mutu domin dukan ’yan Adam a kan gungume da ya sha azaba. (Yahaya 3:35; 14:30, 31; 15:12, 13; Filibiyawa 2:5-11) Misali ne mai kyau na motsawa mai kyau!
18. (a) Ta yaya za mu koyi ƙauna ga Yesu? (b) A wace hanya ce za mu nuna cewa muna ƙaunar Yesu?
18 Lokacin da mutane masu zuciyar kirki suka karanta labaran rayuwar Yesu a cikin Lingila kuma suka yi bimbini a kan albarka da tafarkinsa na aminci ya kawo musu, wannan yana sa su ƙaunace shi sosai ya kasance a zukatansu. A yau muna kama da mutanen da Bitrus ya ce musu lokacin da ya ce: “Ko da ya ke ba ku taɓa ganin [Yesu] ba, kuna ƙaunarsa.” (1 Bitrus 1:8) Muna nuna ƙaunarmu lokacin da muka ba da gaskiya a gare shi kuma muka yi koyi da rayuwarsa ta sadaukarwa. (1 Korantiyawa 11:1; 1 Tasalonikawa 1:6; 1 Bitrus 2:21-25) A 19 ga Afrilu, 2000, adadin mutane 14,872,086 aka tunasar da su dalilin da ya sa za su ƙaunaci Yesu lokacin da suka halarci Tuna mutuwarsa na kowacce shekara. Wannan adadi ne mai yawa kam! Yana da ban ƙarfafa mu san cewa da yawa suna da marmarin ceto ta hadayar Yesu! Da gaske, ƙaunar Jehovah da Yesu da kuma ƙaunarmu gare su ta gina mu.
19. Waɗanne tambayoyi ne game da ƙauna za a tattauna su a talifi na gaba?
19 Yesu ya ce mu ƙaunaci Jehovah da dukan zuciyarmu, ranmu, hankalinmu, da kuma ƙarfinmu. Amma kuma ya ce mu ƙaunaci maƙwabcinmu kamar kanmu. (Markus 12:29-31) Wanene wannan ya ƙunsa? Kuma ta yaya ƙaunar maƙwabci take taimaka mana mu kasance da daidaitawa mai kyau da kuma zuciyar kirki? Waɗannan tambayoyin za a tattauna su a talifi na gaba.
Ka Tuna?
• Me ya sa ƙauna hali ce da take da muhimmanci?
• Ta yaya za mu koyi ƙaunar Jehovah?
• Ta yaya halinmu yake nuna cewa muna ƙaunar Jehovah?
• Ta yaya za mu nuna ƙaunarmu ga Yesu?
[Hotuna a shafuffuka na 20, 21]
Ƙauna tana taimaka mana mu jira ceto da haƙuri
[Hoto a shafi na 22]
Hadayar Yesu mai girma tana motsa mu mu ƙaunace sa