Ka Ƙaunaci Allah Da Yake Ƙaunarka
“Ka yi ƙaunar Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan azancinka.”—MATTA 22:37.
1, 2. Menene ya ta da tambaya game da doka da ta fi muhimmanci?
FARISAWA na zamanin Yesu sun yi gardama sosai a kan wannan tambayar. Wace doka ce ta fi muhimmanci cikin dokoki fiye da 600 da ke cikin Dokar Musa? Dokar da ta ƙunshi yin hadaya ne? Ballantana ma, ana hadayu ne don a sami gafartawa kuma a yi wa Allah godiya. Ko kuwa doka game da kaciya ce ta fi muhimmanci? Wannan ma yana da muhimmanci, tun da yake kaciya alamar alkawari ne da Jehobah ya yi da Ibrahim.—Farawa 17:9-13.
2 A wata sassa kuma, mai yiwuwa masu ra’ayin riƙau sun yi tunanin cewa kowace doka da Allah ya ba da tana da muhimmanci, ko da wasu sun fi wasu muhimmanci ba zai yi daidai ba a ɗaukaka wata doka fiye da wasu. Farisawa sun tsai da shawara su yi wa Yesu wannan tambayar da ake gardama a kai. Wataƙila zai faɗi wani abu da zai ɓata sunansa. Wani a cikinsu ya tambayi Yesu: “Wace ce babbar doka a cikin Attaurat?”—Matta 22:34-36.
3. Wace doka ce Yesu ya ce ta fi muhimmanci?
3 Amsar da Yesu ya ba da tana da muhimmanci sosai a gare mu a yau. A amsar da ya bayar, ya taƙaita abin da ya fi muhimmanci a bauta ta gaskiya. Yesu ya yi ƙaulin Kubawar Shari’a 6:5 kuma ya ce: “Ka yi ƙaunar Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan azancinka. Wannan ce babbar doka, ita ce kuwa ta fari.” Ko da Bafarisin ya yi tambaya game da doka ɗaya, Yesu ya gaya masa wata. Ya yi ƙaulin Leviticus 19:18, ya ce: “Wata kuma ta biyu mai-kamaninta ke nan, ‘Ka yi ƙaunar maƙwabcinka kamar ranka.’ ” Yesu ya nuna cewa waɗannan dokoki biyu sune suka fi muhimmanci a bauta ta gaskiya. Don kada su sa ya lissafa jerin muhimmancin wasu dokoki, ya kammala: “Ga waɗannan doka biyu dukan Attaurat da Annabawa su ke ratayawa.” (Matta 22:37-40) A wannan talifin, za mu tattauna dokar da ta fi muhimmanci a cikin dokokin biyu. Me ya sa dole ne mu ƙaunaci Allah? Ta yaya za mu nuna muna hakan? Ta yaya za mu koyi nuna irin wannan ƙaunar? Yana da muhimmanci mu san amsoshin waɗannan tambayoyi, domin idan muna son mu faranta wa Jehobah rai dole ne mu ƙaunace shi da dukan zuciyarmu da kuma ranmu.
Muhimmancin Ƙauna
4, 5. (a) Me ya sa Bafarisin bai yi mamaki ba game da abin da Yesu ya ce? (b) Menene ya fi daraja ga Allah fiye da hadayu?
4 Kamar dai Bafarisin da ya yi wa Yesu tambaya bai yi fushi ba kuma bai yi mamaki ba da amsar da aka ba shi. Ya san cewa ƙaunar Allah fanni ne mai muhimmanci a bauta ta gaskiya, ko da mutane da yawa ba sa nuna ta. A cikin majami’u, al’adarsu ne su maimaita Shema, wato addu’ar Ibrananci, ko kuma furta bangaskiyarsu, kuma wannan ya haɗa da ayoyin da ke Kubawar Shari’a 6:4-9, waɗanda Yesu ya yi ƙaulinsu. In ji labarin da ke Markus, sai Bafarisin ya gaya wa Yesu: “Malam, ka faɗi daidai shi ɗaya ne; babu wani kuma sai shi: kuma mutum ya ƙaunace shi da dukan zuciya, da dukan azanci, da dukan ƙarfi, ya yi ƙaunar maƙwabcinsa kuma kamar ransa, wannan ya fi gaban dukan bayebaye na ƙonawa da hadayu nesa.”—Markus 12:32, 33.
5 Hakika, ko da yake ana bukatar a miƙa baiko na ƙonawa da hadayu bisa Doka, abin da ya fi muhimmanci ga Allah shi ne ƙauna da bayinsa suke nunawa da dukan zuciyarsu. Allah ya fi daraja gwara da aka miƙa masa cikin ƙauna da ibada maimakon raguna dubbai da aka miƙa da mummunan nufi. (Mikah 6:6-8) Ka tuna labarin gwauruwa mabukaciya da Yesu ya lura da ita a haikali a Urushalima. Anini biyu da ta saka a cikin baitulmalin ba zai iya sayan ko gwara ɗaya ba. Duk da haka, wannan kyautar da ta ba wa Jehobah da dukan zuciyarta, abin karɓa ne a gare shi fiye da wanda masu arziki suka bayar daga yalwarsu. (Markus 12:41-44) Abin ban ƙarfafa ne mu san cewa Jehobah ya fi daraja ƙauna da muka nuna ko a wane irin yanayi muke ciki!
6. Menene Bulus ya rubuta game da muhimmancin ƙauna?
6 Da yake nanata muhimmancin ƙauna a bauta ta gaskiya, manzo Bulus ya rubuta: “Idan na yi magana da harsunan mutane da na mala’iku, amma ba ni da ƙauna, na zama jan ƙarfe mai-ƙara ko kuwa kūge mai-ƙaraurawa. Idan ina da annabci kuma, har kuwa na san dukan asirai da dukan ilimi kuma; idan ina da bangaskiya duka kuma, har da zan cira duwatsu, amma ba ni da ƙauna, ni ba komi ba ne. Idan ina bada dukiyata duka domin a ciyadda matalauta, idan kuwa na bada jikina domin a ƙone shi, amma ba ni da ƙauna, ba ya amfane ni komi ba.” (1 Korinthiyawa 13:1-3) Hakika, muna bukatar mu nuna ƙauna idan muna so Allah ya karɓi bautarmu. Ta yaya za mu nuna ƙaunarmu ga Jehobah?
Yadda Muke Nuna Ƙaunarmu ga Jehobah
7, 8. Ta yaya za mu nuna muna ƙaunar Jehobah?
7 Mutane da yawa sun gaskata cewa ƙauna sosuwar zuciya ce da ke hana mu iya kame kanmu; mutane suna maganar son wani. Amma, ƙauna ta gaske ba kawai yadda muke ji ba ne. Ana nuna ta ta ayyuka ba yadda mutum ke ji ba kawai. Littafi Mai Tsarki ya ce ƙauna “hanya mafificiya” ce da kuma abin da muke “bi.” (1 Korinthiyawa 12:31; 14:1) An ƙarfafa Kiristoci su nuna ƙauna, ba da “baki ko kuwa da harshe; amma da aiki da gaskiya kuma.”—1 Yohanna 3:18.
8 Ƙauna ga Allah na motsa mu mu yi abin da ke faranta masa rai kuma mu ba da amsa game da ikon mallakarsa kuma mu ɗaukaka shi, ta maganarmu da kuma ayyukanmu. Tana motsa mu mu kauce wa ƙaunar duniya da hanyoyinta marasa kyau. (1 Yohanna 2:15, 16) Waɗanda suke ƙaunar Allah suna ƙin mugunta. (Zabura 97:10) Idan muna ƙaunar Allah za mu ƙaunaci maƙwabtanmu, za mu tattauna wannan a talifi na gaba. Ƙari ga haka, idan muna ƙaunar Allah za mu yi masa biyayya. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ƙaunar Allah ke nan, mu kiyaye dokokinsa.”—1 Yohanna 5:3.
9. Ta yaya Yesu ya nuna ƙaunarsa ga Allah?
9 Yesu ya nuna abin da ƙaunar Allah take nufi. Ƙauna ta motsa shi ya bar samaniya ya zauna a duniya kamar ɗan adam. Ƙauna ta motsa shi ya ɗaukaka Babansa ta wurin abubuwa da ya yi da kuma ya koyar. Ƙauna ta motsa shi ya yi “biyayya har da mutuwa.” (Filibbiyawa 2:8) Wannan biyayya, wato, ƙaunar da ya nuna, ta buɗe hanya don masu aminci su kasance da adalci a gaban Allah. Bulus ya rubuta: “Ta wurin kangarar ɗayan nan [Adamu] masu-yawa suka zama masu zunubi, hakanan ta wurin biyayyar ɗayan masu-yawa za su barata.”—Romawa 5:19.
10. Me ya sa nuna ƙauna ga Allah ta ƙunshi yin biyayya?
10 Kamar Yesu, muna nuna ƙaunarmu ta wajen yi wa Allah biyayya. Manzo Yohanna wanda Yesu yake ƙaunarsa sosai, ya rubuta: “Ƙauna ke nan, mu yi tafiya bisa ga dokokinsa.” (2 Yohanna 5:3) Waɗanda suke ƙaunar Jehobah suna son ja-gorarsa. Da yake sun fahimci cewa ba za su iya yi wa kansu ja-gora ba, sun amince da hikimar Allah kuma suna miƙa kai ga ja-gorarsa ta ƙauna. (Irmiya 10:23) Sun yi kama da mutanen Biriya ta dā masu hali mai kyau da suka amince da saƙon Allah da “yardar rai sarai,” suna ɗokin su yi nufin Allah. (Ayukan Manzanni 17:11) Sun bincika Nassosi da kyau don su fahimci nufin Allah sosai, wannan zai taimake su su nuna ƙauna ta ayyukan biyayya.
11. Menene ake nufi da mu ƙaunaci Allah da dukan zuciyarmu, ranmu da kuma ƙarfinmu?
11 Kamar yadda Yesu ya faɗa, za mu yi ƙaunar Allah da dukan zuciyarmu, ranmu da ƙarfinmu. (Markus 12:30) Irin wannan ƙaunar tana fitowa daga zuciya kuma ta ƙunshi yadda muke ji, sha’awace-sha’awacenmu, da tunaninmu kuma muna son mu faranta wa Jehobah rai. Muna nuna ƙauna kuma da tunaninmu. Bautarmu ta sa mu san Jehobah, ayyukansa, mizanansa, da kuma nufe-nufensa. Muna amfani da dukan ranmu mu bauta masa kuma mu yabe shi. Muna amfani da ƙarfinmu ta wajen yin hakan.
Dalilin da Ya Sa Za Mu Ƙaunaci Jehobah
12. Me ya sa Allah yake bukatar mu ƙaunace shi?
12 Dalili ɗaya da ya sa za mu ƙaunaci Jehobah shi ne cewa yana bukatar mu nuna halayensa. Allah shi ne tushe da misali mafi kyau na nuna ƙauna. Manzo Yohanna da aka hure ya rubuta: “Allah ƙauna ne.” (1 Yohanna 4:8) An halicci ’yan adam cikin surar Allah, da haka an yi mu mu nuna ƙauna. Ikon mallakar Jehobah bisa ƙauna ne. Yana son talakawansa su zama waɗanda suke bauta masa domin suna ƙaunarsa kuma suna son yadda yake sarauta cikin adalci. Hakika, ƙauna tana da muhimmanci don salama da jituwar dukan halittu.
13. (a) Me ya sa aka gaya wa Isra’ilawa: “Ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku”? (b) Me ya sa ya dace da Jehobah yake bukata mu ƙaunace shi?
13 Wani dalili kuma da ya sa muke ƙaunar Jehobah shi ne muna godiya don abin da ya yi mana. Ka tuna abin da Yesu ya gaya wa Yahudawa: ‘Ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku.’ Ba su bukatar su ƙaunaci wanda yake nesa da ba su sani ba. Za su ƙaunaci Allahn da ya bayyana musu ƙaunarsa. Jehobah ne Allahnsu. Shi ne ya fito da su daga Masar zuwa Ƙasar Alkawari, shi ne ya kāre su, ya kiyaye su, ya ƙaunace su, kuma ya yi musu horo cikin ƙauna. A yau, Jehobah ne Allahnmu, wanda ya ba da Ɗansa fansa domin mu sami rai madawwami. Saboda haka, ya dace da Jehobah yake bukatar mu ma mu ƙaunace shi! Za mu ƙaunaci Allah domin yana ƙaunarmu. Muna ƙaunar Wanda “ya fara ƙaunace mu.”—1 Yohanna 4:19.
14. Ta yaya ƙaunar Jehobah take kama da ta iyaye masu ƙauna?
14 Yadda Jehobah yake ƙaunar ’yan adam na kama da ƙaunar da iyaye ke yi wa yaransu. Ko da yake su ajizai ne, iyaye masu ƙauna suna aiki tuƙuru na shekaru da yawa don su kula da yaransu, suna hakan ta yin sadaukarwa da yawa. Iyaye suna koyar, suna ƙarfafa, da kuma tallafa, da horon yaransu domin suna son su yi farin ciki kuma su yi girma. Menene iyaye suke so yaransu su yi masu? Suna son yaransu su ƙaunace su kuma su riƙa yin abin da suka koya musu don amfaninsu. Bai dace ba da Ubanmu na samaniya kamiltacce ya bukaci mu nuna godiya don dukan abin da ya yi mana?
Ka Ƙaunaci Allah
15. Menene mataki na farko wajen ƙaunar Allah?
15 Ba mu taɓa ganin Allah ba kuma ba mu taɓa jin muryarsa ba. (Yohanna 1:18) Duk da haka, ya gayyace mu mu soma dangantaka ta ƙauna da shi. (Yaƙub 4:8) Ta yaya za mu yi hakan? Mataki na farko na ƙaunar mutum shi ne ka san mutumin, yana da wuya mu ƙaunaci wanda ba mu sani ba. Jehobah ya yi tanadin Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki, domin mu koya game da shi. Shi ya sa Jehobah ta wurin ƙungiyarsa, yake ƙarfafa mu mu karanta Littafi Mai Tsarki kullayaumi. Littafi Mai Tsarki ne yake koya mana game da Allah, halayensa, mutuntakarsa, da kuma yadda yake sha’ani da mutane shekaru da yawa yanzu. Idan muka yi bimbini a kan irin waɗannan labaran, za mu ƙara fahimtarsa kuma mu ƙara ƙaunarsa.—Romawa 15:4.
16. Ta yaya yin bimbini bisa hidimar Yesu yake kyautata ƙaunarmu ga Allah?
16 Hanya ta musamman da za mu ƙara ƙaunar Jehobah ita ce ta yin bimbini a kan rayuwa da kuma hidimar Yesu. Hakika, Yesu ya nuna halin Ubansa sosai wanda hakan ya sa ya faɗi cewa: “Wanda ya gan ni ya ga Uban.” (Yohanna 14:9) Juyayin da Yesu ya nuna sa’ad da ya maido da tilon wata gwauruwa zuwa rai bai motsa ka ba? (Luka 7:11-15) Ba abin ban ƙarfafa ba ne cewa Ɗan Allah, mutum mafi girma da ya taɓa rayuwa ya wanke ƙafafun almajiransa cikin tawali’u ba? (Yohanna 13:3-5) Bai motsa ka ba da ka fahimci cewa ko da shi mafi girma ne kuma ya fi kowane mutum hikima, ya ƙyale mutane su zo wurinsa, har da yara? (Markus 10:13, 14) Yayin da muke bimbini a kan waɗannan abubuwa, za mu zama kamar Kiristocin da Bitrus ya rubuta game da su: “Wanda kuna ƙauna, ko da ba ku gan shi [Yesu] ba.” (1 Bitrus 1:8) Yadda ƙaunarmu ga Yesu take ƙaruwa, haka ƙaunarmu ga Jehobah take ƙaruwa.
17, 18. Yin bimbini game da waɗanne tanadi na Jehobah ne zai sa mu ƙara ƙaunarsa?
17 Wata hanya da za ta sa mu ƙara ƙaunar Allah ita ce ta yin bimbini a kan tanadi mai yawa da ya yi mana don mu more rayuwa, kyaun halitta, abinci iri-iri, cuɗanya mai daɗaɗawa da abokai, da kuma wasu abubuwa masu kyau da ke sa mu farin ciki da gamsuwa. (Ayukan Manzanni 14:17) Idan muka ƙara koya game da Allah, muna da ƙarin dalili na yin godiya don nagartansa da alherinsa marar iyaka. Ka yi tunanin dukan abubuwa da Jehobah ya yi maka. Bai cancanci ka yi ƙaunarsa ba?
18 Zarafin yi masa addu’a a kowane lokaci, da sanin cewa “mai-jin addu’a” yana saurararmu yana cikin kyauta masu yawa da Allah ya ba mu. (Zabura 65:2) Jehobah ya ba Ɗansa ƙaunatacce ikon yin sarauta da kuma yin shari’a. Amma bai ba wasu, har da Ɗansa ikon jin addu’a ba. Yana saurarar addu’armu da kansa. Da yake Jehobah yana damuwa da mu wannan yana sa mu kusace shi.
19. Waɗanne alkawura na Jehobah ne suke sa mu kusance shi?
19 Muna kusantar Jehobah kuma sa’ad da muka yi la’akari da abin da zai yi wa ’yan adam a nan gaba. Ya yi alkawari zai kawo ƙarshen ciwo, baƙin ciki, da mutuwa. (Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4) Muddin an mai da ’yan adam zuwa kamiltaccen rai, babu wanda zai sha wahalar baƙin ciki, sanyin gwiwa, ko kuma tsautsayi. Yunwa, talauci, da yaƙi ba za su ƙara kasancewa ba. (Zabura 46:9; 72:16) Za a mai da duniya ta zama aljanna. (Luka 23:43) Ba dole ba ne Jehobah ya yi waɗannan abubuwa, amma zai yi su domin yana ƙaunarmu.
20. Menene Musa ya ce game da amfanin ƙaunar Jehobah?
20 Saboda haka, da dalilai da ya sa za mu ƙaunaci Allahnmu kuma mu sa wannan ƙauna ta ƙaru. Za ka ci gaba da ƙarfafa ƙaunarka ga Allah, ka bar shi ya ja-goranci hanyoyinka? Zaɓen naka ne. Musa ya fahimci amfanin koyan yadda ake ƙaunar Jehobah kuma ya ci gaba da yin hakan. Musa ya gaya wa Isra’ilawa na dā: “Ka zaɓi rai fa, domin ka rayu, da kai da zuriyakka: garin ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka, ka ji muryatasa, ka manne masa: gama shi ne ranka, da tsawon kwanakinka.”—Kubawar Shari’a 30:19, 20.
Ka Tuna?
• Me ya sa yake da muhimmanci mu ƙaunaci Jehobah?
• Ta yaya za mu yi ƙaunar Allah?
• Waɗanne dalilai muke da su na ƙaunar Jehobah?
• Ta yaya za mu koyi ƙaunar Allah?
[Hoto a shafi na 15]
Jehobah yana daraja ƙauna da za mu iya nunawa
[Hoto a shafi na 18]
“Wanda ya gan ni ya ga Uban.” —Yohanna 14:9