Jehovah Ne Mafakarmu
‘Domin ka ce Jehovah ne mafakata, . . . babu mugunta da za ta same ka.’—ZABURA 91:9, 10.
1. Me ya sa za mu iya cewa Jehovah ne mafakarmu?
JEHOVAH ne mafaka ta gaske ga mutanensa. Idan mun ba da kanmu gare shi, za mu iya mu “matsu ga kowane sashi, amma ba mu ƙuntata ba; mun damu, amma ba ya kai fidda zuciya ba; ana binmu da tsanani, amma ba a bar mu yasassu ba: an fyaɗa mu a ƙasa, amma ba a halaka mu ba.” Me ya sa? Domin Jehovah yana ba mu “mafificin girman iko.” (2 Korinthiyawa 4:7-9) Hakika, Ubanmu na samaniya na taimakonmu mu biɗi rayuwa ta ibada, kuma mu tuna da kalmomin mai Zabura: ‘Domin ka ce Jehovah ne mafakata, kā maida Maɗaukaki wurin zamanka; babu mugunta da za ta same ka.’—Zabura 91:9, 10.
2. Menene za a ce game da Zabura ta 91 da alkawarin da ta yi?
2 Ƙila Musa ne ya rubuta kalmomin Zabura ta 91. Rubutun saman ya nuna cewa shi ne marubucin Zabura ta 90, kuma Zabura ta 91 ta bi shi ba tare da yin wani furci da ya faɗi sunan wani marubuci ba. Wataƙila an rera waƙa ta Zabura 91 bi da bi, wato, ƙila mutum ɗaya ya rera waƙa (91:1, 2) da farko, da rukunin masu amsawa da ta (91:3-8). Wataƙila an ji muryar mawaƙi ɗaya yana rera waƙa ta (91:9a) sai kuma wani rukuni ya amsa da ta (91:9b-13). Ƙila mawaƙi ɗaya ne ya rera waƙar kalmomin ƙarshe na (91:14-16). Ko yaya dai, Zabura ta 91 ta yi alkawarin kwanciyar rai na ruhaniya ga ajin shafaffu Kiristoci kuma su ba da irin wannan tabbaci wa rukunin abokanansu da suka keɓe kansu.a Bari mu yi la’akari da wannan zabura yadda duka bayin Jehovah suke ganinta.
Kwanciyar Rai Cikin ‘Suturar Allah’
3. (a) Menene “suturar Maɗaukaki”? (b) Menene muka shaida ta wurin “dawwama a ƙarƙashin inuwar mai-iko duka”?
3 Mai Zabura ya rera waƙa: “Mai-zama cikin suturar Maɗaukaki, za ya dawwama a ƙarƙashin inuwar mai-iko duka. Zan ce da Ubangiji, shi ne mafakata da marayata kuma; Allahna, a gareshi ni ke dogara.” (Zabura 91:1, 2) “Suturar Maɗaukaki” wuri ne na alama ta kariya dominmu, musamman ma don shafaffu, su ne Iblis yake tsananta wa musamman. (Ru’ya ta Yohanna 12:15-17) Zai halaka dukanmu idan ba don kāriyar da muke morewa ba mu waɗanda muke tare da Allah, baƙinsa na ruhaniya. Ta “dawwama a ƙarƙashin inuwar mai-iko duka,” muna shaida rumfar kariya ta Allah, ko inuwar. (Zabura 15:1, 2; 121:5) Babu mafaka ko maraya da ya fi Ubangijinmu Jehovah, Mamallaki.—Misalai 18:10.
4. Waɗanne dabaru ne “mai-farauta,” Shaiɗan yake amfani da su, yaya muka tsira?
4 Mai zabura ya daɗa cewa: “[ Jehovah] za ya fishe ka daga tarkon mai-farauta, daga annoba mai-kawo mutuwa kuma.” (Zabura 91:3) Mai farauta a Isra’ila ta dā sau da yawa yana kama tsuntsaye ta wajen amfani da tarko. Cikin tarkon “mai-farauta,” Shaiɗan, akwai ƙungiyarsa ta mugunta da ‘dabarunsa.’ (Afisawa 6:11) An kafa tarkuna a hanyarmu don su jawo mu cikin mugunta kuma su halaka mu a ruhaniya. (Zabura 142:3) Domin mun ƙi rashin adalci, “ranmu ya tsira kamar tsuntsu daga tarkon.” (Zabura 124:7, 8) Muna godiya cewa Jehovah ya cece mu daga mugun “mai-farauta”!—Matta 6:13.
5, 6. Wace “annoba” ce ta kawo ‘wahala,’ amma me ya sa mutanen Jehovah ba sa faɗā ciki ba?
5 Mai Zabura ya ambata “annoba mai-kawo mutuwa.” Kamar ciwo mai hawa kan wani, akwai abin da ke haddasa ‘wahala’ ga iyalin ’yan Adam da masu ɗaukaka ikon mallakar Jehovah. Game da wannan, ɗan tarihi Arnold Toynbee ya rubuta: “Tun ƙarshen Yaƙin Duniya na II, wariyar al’ummai ta yi ninki biyu a jihohi masu zaman gashin kansu . . . Halin ’yan Adam yanzu na daɗa jawo rashin haɗin kai.”
6 Duk cikin ƙarnuka, wasu masarauta ne suka daɗa rashin haɗin kai a jayayyar dukan duniya. Sun ce a bauta musu ko ga siffofi dabam dabam ko alamu. Amma Jehovah bai taɓa barin mutanensa masu aminci su fāɗa cikin irin wannan “annoba” ba. (Daniel 3:1, 2, 20-27; 6:7-10, 16-22) Da yake mu ’yan’uwanci na dukan ƙasashe ne masu ƙauna, muna bauta wa Jehovah shi kaɗai, riƙe tsakatsaki na Nassi, kuma ba tare da son zuciya ba mun yarda cewa “a cikin kowace al’umma, wanda ya ke tsoron [Allah], yana aika adalci kuma, abin karɓa ne gareshi.” (Ayukan Manzanni 10:34, 35; Fitowa 20:4-6; Yohanna 13:34, 35; 17:16; 1 Bitrus 5:8, 9) Ko da muna shan ‘wahala’ a hanyar tsananta mana mu Kiristoci, muna farin ciki kuma muna da kwanciyar rai a ruhaniya “cikin suturar Maɗaukaki.”
7. Ta yaya Jehovah yake kāre mu da “jawarkinsa”?
7 Da yake Jehovah ne mafakarmu, muna samun ta’aziyya daga kalmomin nan: “Za shi rufe ka da jawarkinsa, a ƙarƙashin fukafukansa za ka sami kariya: gaskiyarsa garkuwa ce da kutufani.” (Zabura 91:4) Allah yana kāre mu, yadda uwar tsuntsu ke fuffuka bisa ’ya’yanta. (Ishaya 31:5) ‘Da jawarkinsa yana kāre mu.’ Galibi, “jawarkin” tsuntsu fukafukinsa ne. Da shi, tsuntsuwa tana fuffuka bisa ’ya’yanta, tana kare su daga mahalaka. Kamar ’yar tsuntsuwa, muna da kwanciyar rai a ƙarƙashin jawarki na alama na Jehovah domin ƙungiyarsa ta Kirista ta gaske ne mafakarmu.—Ruth 2:12; Zabura 5:1, 11.
8. Ta yaya “gaskiyar” Jehovah garkuwa ce da kuma garu?
8 Mun dogara ga “gaskiyarsa,” ko aminci. Kamar garkuwa na lokatan dā ne, sau da yawa yana da faɗi kamar ƙofa kuma babba don ya rufe duka jikin mutum. (Zabura 5:12) Gabagaɗi a irin wannan kāriya na ’yantar da mu daga tsoro. (Farawa 15:1; Zabura 84:11) Kamar bangaskiyarmu, gaskiyar Allah garkuwa ce mai kāriya da ke hana jefe-jefen Shaiɗan kuma ya kawar da bugun magabta. (Afisawa 6:16) Garu ne kuma, kāriya mai ƙarfi da muke tsayawa da ƙarfi.
‘Ba Za Mu Ji Tsoro Ba’
9. Me ya sa dare zai iya zama lokacin tsoro, amma me ya sa ba ma jin tsoro?
9 Domin kāriyar Allah, mai Zabura ya ce: “Ba za ka ji tsoron razanar dare ba; ko kuwa kibiya wadda ke tashi da rana; ko annoban da ke yawo a cikin duhu; ko halaka wadda ke lalatarwa da tsakar rana.” (Zabura 91:5, 6) Tun da yake ana yawanci ayyukan mugunta cikin duhu, dare zai kasance abin tsoro. Cikin duhu na ruhaniya da ke rufe duniya yanzu, magabtanmu sau da yawa sukan koma ga ayyukan ruɗu a ƙoƙarin halaka ruhaniyarmu kuma hana aikinmu na wa’azi. Amma ‘ba ma jin tsoron razanar dare’ domin Jehovah yana kāre mu.—Zabura 64:1, 2; 121:4; Ishaya 60:2.
10. (a) Mecece “kibiya wadda ke tashi da rana ke nufi, kuma yaya muke aikatawa game da wannan? (b) Menene “annoban da ke yawo a cikin duhu” ta ƙunsa kuma me ya sa ba ma jin tsoronta?
10 “Kibiya wadda ke tashi da rana” kamar tana nufin zargi ne. (Zabura 64:3-5; 94:20) Yayin da muka nace a sanar da gaskiya, irin wannan hamayya a fili ga tsarkakar hidimarmu tana zama wofi. Bugu da ƙari, ba ma jin tsoron “annoban da ke yawo a cikin duhu.” Wannan annoba ta alama ce cikin duhun wannan duniya mai ciwo na ɗabi’a da na addini da ke kwance cikin ikon Shaiɗan. (1 Yohanna 5:19) Yana kawo yanayin kisa na azanci da zuciya, yana sa mutane cikin jahilci game da Jehovah, da nufe-nufensa, da kuma tanadinsa masu kyau. (1 Timothawus 6:4) Cikin wannan duhu, ba ma jin tsoro, da yake muna jin daɗin haske na ruhaniya a yawalce.—Zabura 43:3.
11. Menene ke samun waɗanda suke fuskantar “lalatarwa da tsakar rana”?
11 “Halaka wadda ke lalatarwa da tsakar rana” ba ta razanar da mu. “Tsakar rana” mai yiwuwa na nufin wayewar kai na duniya. Waɗanda suka fāɗa wa abin duniya suna shan halaka ta ruhaniya. (1 Timothawus 6:20, 21) Yayin da muke sanar da saƙon Mulki da gaba gaɗi, ba ma jin tsoron magabtanmu, gama Jehovah ne Mai Kāre mu.—Zabura 64:1; Misalai 3:25, 26.
12. A gefen wa dubbai suke ‘faɗuwa,’ kuma a wace hanya?
12 Mai Zabura ya ci gaba:“Mutum dubu za su faɗi daura da kai. Zambar goma kuma a hannunka na dama; amma ba za ta kusance ka ba. Da idanunka kaɗai za ka duba, ka ga sakamakon miyagun mutane.” (Zabura 91:7, 8) Domin sun kasa sa Jehovah ya zama mafakarsu, mutane da yawa sun “faɗi” ga mutuwa ta ruhaniya ‘kusa da mu.’ Wato, “zambar goma” sun faɗi a ‘hannun dama’ na Isra’ilawa ta ruhaniya ta yau. (Galatiyawa 6:16) Amma ko mu shafaffun Kiristoci ne ko abokanansu da suka keɓe kai, muna da kwanciyar rai a “suturar” Allah. Kawai za mu “ga sakamakon miyagun,” da suke girbe wahala a kasuwanci, cikin addini, da wasu hanyoyi.—Galatiyawa 6:7.
‘Babu Masifa da Za ta Same Mu’
13. Wace irin masifa ce ba za ta same mu ba, me ya sa?
13 Ko da kwanciyar rai na wannan duniya na ragargajewa, muna sa Allah farko kuma muna samun gaba gaɗi daga kalmomin mai Zabura: ‘Domin ka ce Jehovah ne mafakata, kā mai da Maɗaukaki wurin zamanka; babu masifa da za ta same ka, babu wata annoba da za ta kusanci [tanti] naka.’ (Zabura 91:9, 10) Hakika, Jehovah ne mafakarmu. Amma, muna mai da Allah Maɗaukakin ‘wurin zamanmu,’ inda muke samun kwanciyar hankali. Muna yabon Jehovah shi Mamallakin Dukan Halitta, muna ‘zauna’ wajensa shi Tushen kwanciyar ranmu, kuma muna sanar da bishara ta Mulkinsa. (Matta 24:14) Saboda haka, ‘babu masifa da za ta same mu’—babu kowanne cikin mugunta da aka kwatanta a farkon wannan zabura. Ko ma mun fuskanci bala’i tare da wasu, kamar su girgizar ƙasa, guguwa, rigyawa, yunwa, da wahala da yaƙi yake kawowa, waɗannan ba sa halaka bangaskiyarmu ko kwanciyar ranmu na ruhaniya.
14. Mu bayin Jehovah, me ya sa annoba mai kisa ba ta ɓata mu?
14 Shafaffu Kiristoci kama suke da baƙi da suke zama cikin tanti a ware daga zamanin nan. (1 Bitrus 2:11) ‘Babu ma wata annoba da za ta kusanci tanti nasu.’ Ko muna da begen zama a sama ko a duniya, mu ba na duniya ba ne, kuma irin wannan annoba ta ruhaniya mai kisa kamar su lalata, son abin duniya, addinin ƙarya, da bauta wa “bisa” da ‘gunkinsa,’ Majalisar Ɗinkin Duniya ba sa ɓatā mu.—Ru’ya ta Yohanna 9:20, 21; 13:1-18; Yohanna 17:16.
15. A waɗanne hanyoyi muke moran taimakon mala’iku?
15 Game da kāriya da muke morewa, mai Zabura ya daɗa cewa: “[ Jehovah] za ya ba mala’ikunsa tsaronka, su kiyaye ka cikin tafarkunka duka. Za su talafa ka a bisa hannuwansu, domin kada ka buga ƙafarka a dutse.” (Zabura 91:11, 12) An ba mala’iku iko su kāre mu. (2 Sarakuna 6:17; Zabura 34:7-9; 104:4; Matta 26:53; Luka 1:19) Suna tsare mu ‘a duka tafarkinmu.’ (Matta 18:10) Muna more ja-gora da tsarewar mala’iku mu masu shelar Mulki kuma ba ma tuntuɓe a ruhaniya. (Ru’ya ta Yohanna 14:6, 7) Har ‘duwatsu’ da kamar su hani a kan aikinmu ba su sa mu tuntuɓe har mu yi hasarar alherin Allah ba.
16. Ta yaya farmakin da “zaki” yake yi da na ‘kumurci’ ya bambanta, me muke yi game da su?
16 Mai Zabura ya ci gaba: “Za ka taka zaki da tandara: Ɗan zaki da mesa kuma za ka tattaka ƙarƙashin sawunka.” (Zabura 91:13) Yadda zaki ke faɗā kai tsaye, a fili, wasu magabtanmu suna nuna hamayyarsu a fili ta kafa dokoki da aka shirya don a hana aikinmu na wa’azi. Ban da haka, ana kawo mana farmaki da ba a yi tsammaninsu ba kamar na kumurci da ke kai sara daga inda yake ɓoye. A ɓoye, limamai wasu lokatai suna kawo mana sara ta wurin masu yin doka, alƙalai, da wasu. Amma da taimakon Jehovah, cikin salama muna neman sauƙi a kotu, da haka muna “kāriyar bishara da ƙarfafawarta.”—Filibbiyawa 1:7; Zabura 94:14, 20-22.
17. Ta yaya muke tattaka “zaki”?
17 Mai Zabura ya yi maganar ‘tattaka zaki da mesa.’ Zaki zai iya kasance da ban tsoro, kuma mesa za ta iya zama maciji da girma. (Ishaya 31:4) Ko yaya zaki zai zama da ban tsoro yayin da yake farmaki na kai tsaye, muna tattaka shi a alamance ta yin biyayya ga Allah maimakon mutane ko ƙungiyoyi masu kama da zaki. (Ayukan Manzanni 5:29) Saboda haka, “zaki” mai haɗari ba ya yi mana lahani na ruhaniya.
18. “Mesa” za ta tuna mana game da waye, menene muke bukatar mu yi idan an kawo mana farmaki?
18 A cikin Septuagint na Helenanci, ana kiran “mesa” “babban maciji.” Wannan zai tuna mana “babban dragon, tsohon maciji, shi wanda ana ce da shi Iblis da Shaiɗan.” (Ru’ya ta Yohanna 12:7-9; Farawa 3:15) Kama yake da maciji mai girma da zai iya rugurguje ya kuma haɗiye wanda ya kama. (Irmiya 51:34) Yayin da Shaiɗan yake ƙoƙari ya kama mu, ya halaka mu da matsi na wannan duniya, kuma ya haɗiye mu, bari mu cire kanmu daga bautarsa kuma mu tattaka wannan “mesa.” (1 Bitrus 5:8) Tilas ne shafaffun Kiristoci su yi haka idan za su sa hannu a cika Romawa 16:20.
Jehovah—Tushen Cetonmu
19. Me ya sa muke ɗaukan mafaka wajen Jehovah?
19 Game da mai bauta ta gaskiya, mai zabura ya wakilci Allah da cewa: “Tun da ya ƙallafa ƙaunarsa a gareni, domin wannan zan tsamadda shi, zan ɗaukaka shi, domin ya san sunana.” (Zabura 91:14) Furcin nan “zan tsamadda shi” a zahiri yana nufin “zan ɗaukaka shi,” wato, inda ba za a kai ba. Jehovah ne mafakarmu mu masu bauta masa musamman domin ‘mun ƙallafa ƙaunarmu a gare shi.’ (Markus 12:29, 30; 1 Yohanna 4:19) A nasa kuma, Allah ‘zai cece mu’ daga magabtanmu. Ba za a taɓa share mu daga duniya ba. Maimako, za a cece mu domin mun san sunan Allah kuma kira bisa sunan cikin bangaskiya. (Romawa 10:11-13) Kuma mun ƙudura niyyar ‘za mu yi biyayya da sunan Jehovah har abada.’—Mikah 4:5; Ishaya 43:10-12.
20. Yadda Zabura ta 91 ta kammala, wane alkawari Jehovah ya yi wa bayinsa masu aminci?
20 Yadda Zabura ta 91 ta kammala, Jehovah ya yi magana game da bayinsa masu aminci: “Za shi kira bisa gareni, ni kuma zan amsa masa; a cikin ƙunci ina tare da shi: zan tsamadda shi, zan kuma girmama shi. Zan ƙosadda shi da tsawon rai, zan bayyana masa cetona kuma.” (Zabura 91:15, 16) Yayin da muka kira bisa Allah cikin addu’a daidai da nufinsa, yana amsa mana. (1 Yohanna 5:13-15) Mun riga mun wahala sosai domin ƙiyayya da Shaiɗan ke zugawa. Amma kalmomin nan “cikin ƙunci ina tare da shi” yana shirya mu don gwaji na nan gaba kuma tabbatar mana cewa Allah zai kiyaye mu yayin da aka halaka wannan mugun zamani.
21. Ta yaya aka ɗaukaka shafaffu?
21 Duk da hamayyar Shaiɗan mai tsanani, za a ɗaukaka shafaffu tsakaninmu da sun cika a sama a ayanannan lokaci na Jehovah—bayan “tsawon rai” a duniya. Amma, ceto na musamman da Allah ya yi ya riga ya kawo ɗaukaka ta ruhaniya ga shafaffu. Kuma ɗaukaka ce su yi ja-gora su Shaidun Jehovah a duniya a wannan kwanaki na ƙarshe! (Ishaya 43:10-12) Ceto mafi girma na Jehovah ga mutanensa zai faru lokacin yaƙinsa mai girma na Armageddon lokacin da zai ƙunita ikon mallakarsa kuma ya tsarkake sunansa mai tsarki.—Zabura 83:18; Ezekiel 38:23; Ru’ya ta Yohanna 16:14, 16.
22. Su wanene za su ‘ga ceto ta Jehovah’?
22 Ko mu shafaffun Kiristoci ne ko abokanansu da suka keɓe kansu, mun dogara ga Allah don ceto. Lokacin “babbar rana mai-ban razana ta Ubangiji,” waɗanda suke bauta masa cikin aminci za a cece su. (Joel 2:30-32) Mu da ke cikin “taro mai-girma” da za su tsira cikin sabuwar duniya ta Allah kuma waɗanda suka kasance da aminci lokacin gwaji na ƙarshe ‘zai cika su da tsawon rai’—rayuwar da babu ƙarshe. Zai kuma tasar da babban garke. (Ru’ya ta Yohanna 7:9; 20:7-15) Hakika, Jehovah zai yi farin ciki sosai wajen ‘sa mu ga ceto’ ta wurin Yesu Kristi. (Zabura 3:8) Da irin wannan zato mai girma a gabanmu, bari mu ci gaba da neman taimakon Allah a ƙididdiga kwanakinmu ga ɗaukakarsa. Ta kalmominmu da ayyuka, bari mu ci gaba da nuna cewa Jehovah ne mafakarmu.
[Hasiya]
a Marubutan Nassosin Kirista na Helenanci ba su tattauna Zabura ta 91 daga matsayin annabcin Almasihu ba. Hakika, Jehovah ne mafaka kuma ƙarfi na mutumin nan Yesu Kristi, yadda Yake ga shafaffun mabiyan Yesu da abokan tarayyarsu da suka keɓe kansu rukuninsu a wannan “kwanakin ƙarshe.”—Daniel 12:4.
Yaya Za Ka Amsa?
• Menene “suturar Maɗaukaki”?
• Me ya sa ba ma jin tsoro?
• Ta yaya ‘babu masifa da za ta same mu’?
• Me ya sa za mu iya cewa Jehovah ne tushen cetonmu?
[Hoto a shafi na 15]
Ka san yadda gaskiyar Jehovah take garkuwa a gare mu?
[Hotuna a shafi na 16]
Jehovah yana taimaka wa bayinsa su yi hidimarsu duk da hamayya a fili da farmaki da ba a tsammaninsa
[Inda aka Dauko]
Cobra: A. N. Jagannatha Rao, Trustee, Madras Snake Park Trust