Jehovah Yana Yi Wa Waɗanda Suke Biyayya Albarka Kuma Yana Kāre su
“Amma dukan wanda ya saurara gareni za ya zauna lafiya, za ya zauna da rai a kwance, ba tsoron masifa ba.”—MISALAI 1:33.
1, 2. Me ya sa yi wa Allah biyayya yake da muhimmanci? Ka ba da misali.
‘YAN tsaki masu launin rawaya na saran abinci cikin gajeriyar ciyawa, ba su da labari shaho na jewa a sama. Farat ɗaya, uwarsu ta kira su ta buɗe fukafukanta. ’Yan tsaki suka ruga wajenta, nan da nan ta ɓoye su a ƙarƙashin fukafukanta. Shahon ya fasa kawo musu hari.a Menene darasin wannan? Biyayya tana ceton rai!
2 Wannan darasin yana da muhimmanci musamman ga Kiristoci a yau, domin Shaiɗan yana iyakar ƙoƙarinsa ya yi farautar mutanen Allah. (Ru’ya ta Yohanna 12:9, 12, 17) Nufinsa shi ne ya halaka ruhaniyarmu don mu yi hasarar tagomashin Jehovah da begen rai madawwami. (1 Bitrus 5:8) Amma, idan muka matsa kusa da Allah kuma muka yi biyayya da sauri ga ja-gorar Kalmarsa da ƙungiyarsa, tabbatacce zai kāre mu. Mai Zabura ya rubuta: “Za shi rufe ka da jawarkinsa, a ƙarƙashin fukafukansa za ka sami kāriya.”—Zabura 91:4.
Al’umma Marar Biyayya ta Zama Abinci
3. Menene sakamakon rashin biyayya a kai a kai na Isra’ila?
3 Sa’ad da al’ummar Isra’ila take wa Jehovah biyayya, ta amfana daga kulawarsa a kai a kai. Duk da haka, sau da yawa, mutanen suka bar Mahaliccinsu suka juya wa allolin itatuwa da na duwatsu—“al’amuran banza waɗanda ba su da iko su amfane [su], ko su cece [su].” (1 Samu’ila 12:21) Bayan ƙarnuka na tawaye, ridda ta rinjaye duk al’ummar da har ya kai ba za ta iya farfaɗowa ba. Shi ya sa Yesu ya furta baƙin cikinsa: “Ya Urushalima, Urushalima, wanda ki ke kisan annabawa, kina jejjefe waɗanda an aiko a gareki! so nawa ina so in tattara ’ya’yanki, kamar yadda kaza ta kan tattara ’yan tsakinta ƙarƙashin fukafukanta, amma ba ku yarda ba! Ga shi, an bar muku gidanku kango.”—Matta 23:37, 38.
4. Ta yaya yasar da Urushalima da Jehovah ya yi ya bayyana a shekara ta 70 A.Z.?
4 Yasar da Isra’ila da ta bauɗe da Jehovah ya yi ta bayyana a hanya ta baƙin ciki a shekara ta 70 A.Z. A wannan shekara sojojin Roma, suna riƙe da mizanansu ta yin biki da sifar gaggafa, suka sauƙo wa Urushalima suka halaka ta. Birnin tana cike maƙil da masu bikin Ƙetarewa. Hadayunsu masu yawa sun kasa samo musu tagomashin Allah. Wannan ya tuna wa Sarki Saul marar biyayya kalmomin Samu’ila: “Ubangiji yana murna dayawa da [kyauta] na ƙonawa da [hadayu] kuma, kamar yadda ya ke murna da biyayya ga muryar Ubangiji? Ka lura, biyayya ta fi hadaya, jin magana kuma ya fi kitsen raguna.”—1 Samu’ila 15:22.
5. Wace irin biyayya ce Jehovah yake bukata, kuma ta yaya muka sani cewa irin wannan biyayya tana yiwuwa?
5 Duk da nacewarsa game da biyayya, Jehovah ya san kasawar mutane ajizai. (Zabura 130:3, 4) Yana bukatar zuciya mai gaskiya da kuma biyayya bisa bangaskiya, ƙauna, da tsoron ɓata masa rai. (Kubawar Shari’a 10:12, 13; Misalai 16:6; Ishaya 43:10; Mikah 6:8; Romawa 6:17) ‘Taron shaidu mai girma kafin Kiristoci,’ da suka riƙe amincinsu a lokacin gwaji, har mutuwarsu, sun nuna cewa ana iya yin irin wannan biyayya. (Ibraniyawa 11:36, 37; 12:1) Waɗannan suna faranta wa Jehovah rai da gaske! (Misalai 27:11) Wasu suna da aminci da farko amma suka kasa ci gaba cikin tafarkin biyayya. Ɗaya cikin waɗannan Sarki Jehoash ne na Yahuda ta dā.
Tarayya da Miyagu Ya Ɓata Wani Sarki
6, 7. Wane irin sarki ne Jehoash sa’ad da Jehoiada yake da rai?
6 Sarki Jehoash ya ƙetare rijiya da baya sa’ad da yake jariri. Lokacin da Jehoash ya kai shekara bakwai, Babban Firist Jehoiada da gaba gaɗi ya fito da shi daga inda yake ɓoye ya naɗa shi sarki. Domin Jehoiada mai jin tsoron Allah ya zama kamar uban Jehoash kuma mashawarcinsa, saurayin “ya yi abin da ke daidai a gaban Ubangiji dukan kwanakin ran Jehoiada [firist].”—2 Labarbaru 22:10–23:1, 11; 24:1, 2.
7 Abubuwa masu kyau da Jehoash ya yi ya haɗa da gyara haikalin Jehovah—abin da “Jehoash ya yi nufi.” Ya tuna wa Babban Firist Jehoiada a tara harajin haikali daga Yahuda da Urushalima, yadda ‘Musa ya ba da umurni,’ don aikin. Babu shakka, Jehoiada ya ci nasara a ƙarfafa saurayin ya yi nazari kuma ya yi biyayya da Dokar Allah. Ta haka, aka gama aiki a haikalin da kwanonin haikalin da sauri.—2 Labarbaru 24:4, 6, 13, 14; Kubawar Shari’a 17:18.
8. (a) Menene musamman ya sa Jehoash ya fāɗi a ruhaniya? (b) Menene rashin biyayyar sarki ya kai shi ga yi?
8 Abin baƙin ciki, biyayyar Jehoash ga Jehovah bai daɗe ba. Me ya sa? Kalmar Allah ta gaya mana: “Bayan mutuwar Jehoiada, sarakunan Yahuda suka zo suka yi sujjada ga sarki. Sarki kuwa ya kasa kunne garesu. Sai suka bar gidan Ubangiji, Allah na ubanninsu, suka bauta ma Asherim, da gumaka: fushi kuma ya faɗo ma Yahuda da Urushalima sabili da wannan laifi nasu.” Munanan tasiri na sarakunan Yahuda ya sa sarkin bai saurari annabawan Allah ba, ɗaya cikinsu Zechariah ne ɗan Jehoiada, wanda da gaba gaɗi ya tsauta wa Jehoash da mutanensa don rashin biyayyarsu. Maimakon ya tuba, Jehoash ya sa aka jejjefi Zechariah da duwatsu har aka kashe shi. Lallai Jehoash ya rikiɗa ya zama mutum ne marar biyayya da tausayi—duk wannan domin ya yi tarayya da miyagu ne!—2 Labarbaru 24:17-22; 1 Korinthiyawa 15:33.
9. Ta yaya ƙarshen Jehoash da sarakunan ya nuna wautar rashin biyayya?
9 Da yake sun bar Jehovah, yaya Jehoash da abokansa miyagu suka ji? Rundunan Suriyawa—“mutane kima” kawai—suka kawo wa Yahuda hari “suka halaka dukan sarakunan jama’a daga cikin mutane.” Rundunan suka tilasta wa sarkin ya ba da kayansa da kuma zinariya da azurfa na alfarwa ta sujjada. Ko da Jehoash ya tsira, an ƙyale shi raunanne, da ciwo. Bayan haka, wasu cikin bayinsa suka haɗa baki suka kashe shi. (2 Labarbaru 24:23-25; 2 Sarakuna 12:17, 18) Kalmomin Jehovah ga Isra’ila sun kasance gaskiya: “Idan ba ka saurara ga muryar Ubangiji Allahnka ba, da za ka kiyaye dukan dokokinsa da farillansa . . . la’anoni duka za su auko maka, su tarshe ka kuma”!—Kubawar Shari’a 28:15.
Biyayya ta Ceci Wani Sakatare
10, 11. (a) Me ya sa yake da kyau mu yi bimbini a kan gargaɗin Jehovah ga Baruch? (b) Wane gargaɗi Jehovah ya ba wa Baruch?
10 Wani lokaci kana sanyin gwiwa ne domin ba mutane da yawa ne ka sadu da su ba a hidimar Kirista suke son bisharar? Wani lokaci kana ɗan kishin masu arziki da salon rayuwarsu? Idan haka ne, ka yi tunanin Baruch, sakataren Irmiya, da gargaɗi mai kyau da Jehovah ya yi masa.
11 Baruch na bakin rubuta saƙon annabci sa’ad da Jehovah ya mai da hankali gare shi. Me ya sa? Domin Baruch ya soma baƙin ciki game da yanayinsa yana son abu mafi kyau da gatarsa ta musamman a hidimar Allah. Da ya lura cewa Baruch ya canja halinsa, Jehovah ya yi masa gargaɗi: “Kana fa biɗa ma kanka manyan abu? kada ka biɗe su: gama, ga shi, zan jawo mugunta a bisa dukan masu-rai, . . . amma zan ba ka naka rai ganima gareka ke nan, dukan wuraren da ka tafi.”—Irmiya 36:4; 45:5.
12. Me ya sa za mu guji biɗa wa kanmu “manyan abu” a wannan zamani?
12 Ka lura cewa a kalmominsa ga Baruch Jehovah ya damu sosai da wannan mutum nagari, wanda ya bauta masa cikin aminci da gaba gaɗi tare da Irmiya? Hakanan ma yau, Jehovah ya damu sosai game da waɗanda aka jarabe su su biɗi abin da suke tunani ya fi kyau a wannan zamani. Abin farin ciki, kamar Baruch, da yawa cikin irin wannan mutane sun saurari gyara da ’yan’uwa da suka manyanta a ruhaniya suka yi musu. (Luka 15:4-7) Hakika, bari dukanmu mu fahimci cewa waɗanda suke biɗa wa kansu “manyan abu” a wannan zamani ba su da saurar rayuwa a nan gaba. Ba kawai cewa irin waɗannan ba za su samu farin ciki na gaske ba, mafi muni za su shuɗe da wannan duniya da dukan sha’awoyinta na son kai.—Matta 6:19, 20; 1 Yohanna 2:15-17.
13. Wane darasi ne game da tawali’u labarin Baruch ya koya mana?
13 Labarin Baruch ya kuma koya mana darasi mai kyau game da tawali’u. Ka lura cewa Jehovah bai yi wa Baruch gargaɗi da kansa ba amma ya yi haka ne ta bakin Irmiya, wanda wataƙila Baruch ya san ajizancinsa da halayensa sosai. (Irmiya 45:1, 2) Har ila, fahariya bai sha kan Baruch ba; cikin tawali’u ya gane gargaɗin—daga Jehovah ne. (2 Labarbaru 26:3, 4, 16; Misalai 18:12; 19:20) Saboda haka, idan mun ‘iske kanmu a cikin kowanne laifi’ kuma aka yi mana gargaɗi daga Kalmar Allah, bari mu yi koyi da manyantar Baruch, fahimi na ruhaniya, da tawali’u.—Galatiyawa 6:1.
14. Me ya sa yake da kyau mu yi biyayya ga waɗanda suke ja-gora tsakaninmu?
14 Irin wannan halin tawali’u a wajenmu zai taimaki waɗanda suke ba da gargaɗi. Ibraniyawa 13:17 ta ce: “Ku yi biyayya da waɗanda ke shugabannanku, ku sarayadda kanku garesu: gama suna yin tsaro sabili da rayukanku, kamar waɗanda za su amsa tambaya; su yi shi da farinciki, ba da baƙinciki ba: gama wannan marar-amfani ne gareku.” Sau da yawa dattawa suna yin addu’a sosai ga Jehovah, suna addu’a don ƙarfin zuciya, hikima, da kissa da suke bukata don su cika wannan fannin aiki mai wuya na kiwo! Bari mu “shaida irin waɗannan fa.”—1 Korinthiyawa 16:18.
15. (a) Ta yaya Irmiya ya nuna yana da tabbaci a game da Baruch? (b) Ta yaya aka saka wa Baruch don ya yi biyayya cikin tawali’u?
15 An ga cewa Baruch ya gyara tunaninsa, domin Irmiya ya ba shi aiki da ya fi wuya—ya je haikali ya karanta saƙon hukunci da Irmiya ya gaya masa ya rubuta. Baruch ya yi biyayya ne? E, ya yi “dukan abin da annabi Irmiya ya umurce shi.” Har ma, ya karanta saƙon ga sarakunan Urushalima, wanda babu shakka ya bukaci gaba gaɗi. (Irmiya 36:1-6, 8, 14, 15) Sa’ad da birnin ya faɗā hannun Babiloniyawa shekara 18 bayan haka, ka yi tunanin godiya da Baruch zai yi don ya tsira domin ya yi biyayya ga kashedin da Jehovah ya yi masa ya daina biɗan “manyan abu” wa kansa!—Irmiya 39:1, 2, 11, 12; 43:6.
Biyayya Lokacin Hari ta Ceci Rayuka
16. Ta yaya Jehovah ya nuna wa Yahudawa a Urushalima juyayi lokacin da Babiloniyawa suka kai musu hari a shekara ta 607 K.Z.?
16 Sa’ad da ƙarshen Urushalima ya zo a shekara ta 607 K.Z., Allah ya nuna wa waɗanda suka yi biyayya juyayi. Lokacin da hari yake da tsanani, Jehovah ya gaya wa Yahudawa: “Ga shi, a gabanku na sa hanyar rai da hanyar mutuwa. Wanda ya zauna cikin birnin nan mutuwa za ya yi ta bakin takobi, da yunwa, da annoba: amma wanda ya fita ya fāɗa cikin hannun Chaldiyawa da ke kewaye ku da yaƙi, shi za ya yi rai, za ya tsira da ransa.” (Irmiya 21:8, 9) Ko da mazaunan Urushalima sun cancanci a halaka su, Jehovah ya nuna wa waɗanda suke yi masa biyayya juyayi, har a lokaci na ƙarshe.b
17. (a) A waɗanne hanyoyi biyu aka gwada biyayyar Irmiya sa’ad da Jehovah ya umurce shi ya gaya wa Yahudawan da aka kewaye su su “ridda zuwa Chaldiyawa”? (b) Ta yaya za mu amfana daga misalin Irmiya na yin biyayya da gaba gaɗi?
17 Gaya wa Yahudawa su ba da kansu babu shakka ya gwada biyayyar Irmiya. Dalili ɗaya shi ne, yana da himma don sunan Allah. Ba ya son magabta da za su ce sun yi nasara da taimakon gumaka marasa rai su zargi sunan. (Irmiya 50:2, 11; Makoki 2:16) Ƙari ga haka, Irmiya ya san cewa gaya wa mutane su ba da kansu, yana saka rayuwarsa cikin kasada, don mutane da yawa za su ce maganarsa ta da zaune tsaye ne. Duk da haka, bai ji tsoro ba, amma cikin biyayya ya faɗi hukuncin Jehovah. (Irmiya 38:4, 17, 18) Kamar Irmiya, mu ma muna sanar da saƙo da ba a so. Wannan saƙon ne da aka tsani Yesu dominsa. (Ishaya 53:3; Matta 24:9) Saboda haka, kada mu ji ‘tsoron mutane,’ amma kamar Irmiya, bari da gaba gaɗi mu yi biyayya ga Jehovah, mu dogara a gare shi sosai.—Misalai 29:25.
Biyayya a Lokacin Farmakin Gog
18. Wane gwaji na biyayya bayin Jehovah za su fuskanta a nan gaba?
18 Jim kaɗan, za a halaka mugun tsarin Shaiɗan a “ƙunci mai-girma.” (Matta 24:21) Babu shakka kafin kuma a lokacin, mutanen Allah za su fuskanci gwaji na bangaskiyarsu da biyayyarsu. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa Shaiɗan, a matsayinsa na “Gog na ƙasar magog,” zai kai wa bayin Jehovah farmaki, ya shirya runduna da aka kwatanta da “babbar rundunar yaƙi . . . kamar hadari garin a rufe ƙasan.” (Ezekiel 38:2, 14-16) Da yake ba su da yawa kuma ba su da makami, mutanen Allah za su nemi mafaka a “jawarkin” Jehovah, wanda yake miƙa don ya kāre masu biyayya.
19, 20. (a) Me ya sa biyayya wajen Isra’ila take da muhimmanci sa’ad da suke a Jar teku? (b) Ta yaya yin bimbini da addu’a a kan labarin Jar Teku zai amfane mu a yau?
19 Wannan yanayin ya tuna mana Fitowar Isra’ila daga ƙasar Masar. Bayan ya bugi Masar da annoba goma, Jehovah ya ja-goranci mutanensa, ba gajeriyar hanya zuwa Ƙasar Alkawari ba, amma zuwa Jar Teku, inda zai yi wuya su tsira idan aka kai musu farmaki. A ganin soja, wannan tafiya tana da lahani. Idan kana wajen, za ka yi biyayyar maganar Jehovah ta bakin Musa ka tafi Jar Teku da cikakken aminci, da sanin cewa hanyar Ƙasar Alkawari dabam take?—Fitowa 14:1-4.
20 Yadda muka karanta a Fitowa sura ta 14, mun ga yadda Jehovah ya ceci mutanensa a nuna iko na ban mamaki. Irin wannan labari na ƙarfafa bangaskiyarmu sa’ad da muka ɗauki lokaci mu yi nazari kuma mu yi bimbini a kansu! (2 Bitrus 2:9) Bangaskiya mai ƙarfi na ƙarfafa mu mu yi wa Jehovah biyayya, ko lokacin da farillansa ta saɓa da ra’ayin mutane. (Misalai 3:5, 6) Ka tambayi kanka, ‘Ina ƙoƙari na gina bangaskiya ta ta wurin nazarin Littafi Mai Tsarki sosai, addu’a, yin bimbini, da kuma cuɗanya kullum da mutanen Allah?—Ibraniyawa 10:24, 25; 12:1-3.
Biyayya na Kawo Bege
21. Wace albarka, a yanzu da kuma nan gaba, suke ga waɗanda suka yi wa Jehovah biyayya?
21 Waɗanda suka mai da yi wa Jehovah biyayya hanyar rayuwarsu suna ganin cikar Misalai 1:33 da ta ce: “Amma dukan wanda ya saurara [cikin biyayya] gareni za ya zauna lafiya, za ya zauna da rai a kwance, ba tsoron masifa ba.” Wannan kalmomi na ban ƙarfafa za su cika a ranar ramako na Jehovah mai zuwa! Yesu ya gaya wa almajiransa: “Sa’anda waɗannan al’amura sun soma faruwa, ku duba bisa, ku tada kanku; gama fansarku ta kusa.” (Luka 21:28) Hakika, sai waɗanda suka yi wa Allah biyayya kawai za su kasance da tabbaci su yi biyayya ga waɗannan kalmomi.—Matta 7:21.
22. (a) Wane dalilin tabbaci mutanen Jehovah suke da shi? (b) Waɗanne abubuwa za a tattauna a talifi na gaba?
22 Wani dalili na tabbaci shi ne cewa “Ubangiji Yahweh ba za ya yi kome ba, sai shi bayyana asirinsa ga bayinsa annabawa.” (Amos 3:7) A yau, Jehovah ba ya hure annabawa yadda ya yi dā; maimako, ya ba ajin bawa mai aminci umurni su ba da abinci na ruhaniya a kan lokaci wa iyalinsa. (Matta 24:45-47) Saboda haka, yana da muhimmanci mu kasance da biyayya ga wannan “bawan”! Yadda talifi na gaba zai nuna, irin wannan biyayya tana nuna halinmu game da Yesu, ubangijin “bawan.” Shi ne Wanda ‘biyayyar al’ummai ta nufa.’—Farawa 49:10.
[Hasiya]
a Ko da yake sau da yawa ana nuna ba ta da ƙarfin zuciya, “Kaza tana faɗa har mutuwa don ta kāre ’yan tsakinta,” in ji wani littafi game da dabbobi.
b Irmiya 38:19 ya bayyana cewa Yahudawa da yawa da sun “ridda zuwa” hannun Chaldiyawa ba a kashe su ba amma an kwashe su zuwa bauta. Ko sun ba da kansu a yin biyayya da kalmomin Irmiya, ba a gaya mana ba. Duk da haka, tsirarsu ta tabbatar da abin da annabin ya faɗa.
Ka Tuna?
• Menene sakamakon rashin biyayyar Isra’ila a kai a kai?
• Ta yaya abokane suka shafi rayuwar Sarki Jehoash, na farko da na baya?
• Waɗanne darussa za mu koya daga Baruch?
• Me ya sa mutanen Jehovah masu biyayya ba su da dalilin tsoro yayin da ƙarshen zamanin nan ya yi kusa?
[Hoto a shafi na 21]
Lokacin ja-goran Jehoida, saurayi Jehoash ya yi wa Jehovah biyayya
[Hoto a shafi na 23]
Tarayya da miyagu ya sa Jehoash ya kashe annabin Allah
[Hoto a shafi na 24]
Da za ka yi wa Jehovah biyayya ka ga nunin ikonsa na ban mamaki?