Ku Koyar Da Yaranku
Jehoash Ya Bar Bauta wa Jehobah Domin Mugayen Abokane
LOKACI ne mai tsanani a Urushalima, birnin da aka kafa haikalin Allah. An kashe Sarki Ahaziah. Yana da wuya a yi tunanin abin da Athaliah mahaifiyar Ahaziah ta yi. Ta sa an kashe ’ya’yan Ahaziah, wato, jikokinta! Ka san dalilin da ya sa?—a Saboda ta yi sarauta maimakon ɗaya daga cikin ’ya’yan.
Amma, an ɓoye Jehoash ɗaya daga cikin jikokin Athaliah, kuma kakarsa ba ta san da haka ba. Za ka so ka san yadda aka ɓoye shi?— Jaririn yana da gwaggo mai suna Jehosheba, ita ce ta ɓoye shi a haikalin Allah. Hakan ya yiwu saboda mai gidanta ne Jehoiada Babban Firist. Tare da maigidanta suka ɓoye Jehoash.
Sun ɓoye Jehoash har na shekara shida a haikali. A nan ne aka koya masa dukan abubuwa game da Jehobah da dokokinsa. Daga baya, sa’ad da Jehoash ya kai shekara bakwai da haihuwa, Jehoiada ya yi ƙoƙari ya naɗa Jehoash ya zama sarki. Za ka so ka san yadda Jehoiada ya yi hakan da kuma abin da ya faru da muguwar Sarauniya Athaliah kakar Jehoash?—
A ɓoye Jehoiada ya kira dukan masu tsaron na musamman da sarakuna a Urushalima suke da su. Ya gaya musu yadda shi da matarsa suka ɓoye ɗan Sarki Ahaziah. Sai Jehoiada ya kai Jehoash wajen masu tsaron , kuma suka fahimci cewa shi ne ainihi ya kamata ya yi sarauta. Sai suka yi wani shiri.
Jehoiada ya fito da Jehoash ya naɗa shi ya zama sarki. Sai mutane suka “yi tāfi, suka ce Ran sarki shi daɗe!” Masu tsaron suna kewaye Jehoash don su kāre shi. Sa’ad da Athaliah ta ji ana murna, ta fito a guje ta nemi ta hana. Amma Jehoiada ya ba da umurni cewa masu tsaron su kashe Athaliah.—2 Sar. 11:1-16.
Kana gani Jehoash ya ci gaba da sauraran Jehoiada kuma ya yi abin da ya dace?— E, ya ci gaba har sai bayan mutuwar Jehoiada. Jehoash ya sa mutane suka ba da kuɗi don a gyara haikalin Allah, wanda mahaifinsa Ahaziah da kakansa Jehoram ba su kula da wurin ba. Amma bari mu ga abin da ya faru sa’ad da Babban Firist Jehoiada ya rasu.—2 Sar. 12:1-16.
A lokacin Jehoash yana da kusan shekara 40 da haihuwa. Maimakon ya ci gaba da tarayya da mutanen da suke bauta wa Jehobah, Jehoash ya kafa abokantaka da mutanen da suke bauta wa allolin ƙarya. Zakariya ɗan Jehoiada shi ne firist ɗin Jehobah a lokacin. Menene ka ke ganin Zakariya ya yi sa’ad da ya ji mugun abubuwan da Jehoash yake yi yanzu?—
Zakariya ya gaya wa Jehoash: ‘Domin ka rabu da Ubangiji, shi kuma ya yashe ka.’ Waɗannan kalaman sun ba Jehoash haushi sosai har ya ba da umurni cewa a jefi Zakariya har ya mutu. Ka tuna—an ceci Jehoash daga hannun matar da take son ta kashe shi, amma yanzu shi ma ya zama mai kisa! —2 Laba. 24:1-3, 15-22.
Akwai darussa da za mu iya koya daga wannan labarin?— Ba za mu taɓa so mu zama kamar Athaliah wacce take mai ƙiyayya da azzaluma. Maimakon haka, mu ƙaunaci ’yan’uwanmu masu bi kuma har da maƙiyanmu, kamar yadda Yesu ya koya mana. (Matta 5:44; Yohanna 13:34, 35) Ka tuna, idan muka fara yin abu mai kyau kamar Jehoash, ya kamata mu ci gaba da yin abokane da waɗanda suke ƙaunar Jehobah kuma suna ƙarfafa mu mu bauta masa.
[Hasiya]
a Idan kana karanta wa yara, wannan alamar fid da ma’ana tana nufin ka dakata, ka yi masu tambaya.
Tambayoyi:
○ Ta yaya aka ceci Jehoash, kuma daga hannun wanene?
○ Yaya ne Jehoash ya zama ainihin sarki, kuma wane abu mai kyau ya yi?
○ Me ya sa Jehoash ya zama mugu, kuma wanene ya kashe?
○ Wane darussa ne za mu koya daga wannan labari na Littafi Mai Tsarki?
[Hotunan da ke shafi na 27]
An ceci Jehoash