Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w03 3/1 pp. 25-30
  • Ka Dogara Ga Jehovah Da Dukan Zuciyarka

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Dogara Ga Jehovah Da Dukan Zuciyarka
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Nagarin Misali na Joshua da Kaleb
  • Abin da Ya Sa Za Mu Dogara ga Jehovah da Zuciya Ɗaya
  • Dauda Ya Dogara ga Jehovah
  • An Kunita Dogarar Hezekiya
  • Menene Yake Nufi a Dogara ga Jehovah?
  • Ka Bi Misalin Bulus
  • Riƙe Amana Yana da Muhimmanci Don Rayuwa ta Farin Ciki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Za Ku Iya Yarda da ’Yan’uwanku
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • ’Yan Leken Asiri
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • “Ya Jehobah, . . . a Gare Ka Na Dogara”
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2017
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
w03 3/1 pp. 25-30

Ka Dogara Ga Jehovah Da Dukan Zuciyarka

“Waɗanda sun san sunanka za su dogara gare ka.”—ZABURA 9:10.

1, 2. Menene wasu abubuwa da mutane suke dogara da su domin samun kwanciyar rai?

AYAU, abubuwa da yawa suna ta da mana hankali, daidai ne a nemi wani abu ko kuma wanda za a dogara domin samun kwanciyar rai. Wasu suna jin cewa ta wurin samun arziki za su sami kwanciyar rai, amma arziki mafaka ne marar tabbas. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Shi wanda ya dogara ga wadatarsa za ya fāɗi.” (Misalai 11:28) Wasu suna dogara ga shugabannai na mutane, amma mafi kirki cikin waɗannan yakan yi kuskure. Kuma a ƙarshe duka za su mutu. Cikin hikima Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada ku dogara ga sarakuna, ko kuwa ɗan adam, wanda babu taimako gareshi.” (Zabura 146:3) Waɗannan hurarrun kalmomi sun kuma yi mana gargaɗi a kan kada mu dogara ga ƙoƙarce-ƙoƙarcenmu. Mu kanmu ‘ ’yan Adam’ ne.

2 Annabi Ishaya ya ga laifin shugabannan al’ummar Isra’ila a zamaninsa domin sun dogara ga “mafakan ƙarya.” (Ishaya 28:15-17) A neman kwanciyar rai da suke yi, sun yi abokantaka ta siyasa da ƙasashe maƙwabta. Irin wannan abokantaka ba abar dogara ba ce—ƙarya ce. Haka nan ma, a yau shugabannai da yawa na addini suna dangantaka da shugabannan siyasa. Abutar nan ma za ta zama “ƙarya.” (Ru’ya ta Yohanna 17:16, 17) Ba za su kawo kwanciyar rai na dindindin ba.

Nagarin Misali na Joshua da Kaleb

3, 4. Ta yaya rahoto da Joshua da Kaleb suka ba da ya yi dabam da na sauran goma masu leƙen asiri?

3 To, daga ina ya kamata mu nemi kwanciyar rai? A wurin da Joshua da Kaleb a zamanin Musa suka nema. Ba da daɗewa ba bayan ’yantar da Isra’ila daga ƙasar Masar, al’ummar tana shirye domin ta shiga ƙasar Kan’ana, Ƙasar Alkawari. An tura mutane 12 su je su leƙi asirin ƙasar, bayan kwanaki 40 suka dawo su ba da rahotonsu. Biyu ne kawai cikinsu, Joshua da Kaleb, suka yi maganar kirki game da begen nasarar Isra’ila a Kan’ana. Wasun sun amince cewa ƙasar tana da kyau amma suka ce: “Mazaunan ƙasan ƙarfafa ne, birane kuma masu ganuwa, manya ƙwarai . . . Ba mu da iko mu hau mu yi yaƙi da mutanen nan ba: gama sun fi mu ƙarfi.”—Litafin Lissafi 13:27, 28, 31.

4 Isra’ilawa suka saurari masu leƙen asiri goma kuma suka tsorata, har suka soma yi wa Musa gunaguni. A ƙarshe, Joshua da Kaleb, cikin juyayi suka ce: “Ƙasa wadda muka ratsa domin mu gewaya, kyakkyawar ƙasa ce ƙwarai. Idan Ubangiji ya ji daɗinmu, sai shi kawo mu ciki, shi ba mu ita; ƙasa mai-zuba da madara da zuma. Sai dai kada ku tayar ma Ubangiji, kada kuwa ku ji tsoron mutanen ƙasan.” (Litafin Lissafi 14:6-9) Duk da haka, Isra’ilawa suka ƙi su saurara, kuma domin haka, ba a yarda musu su shiga Ƙasar Alkawarin a wannan lokacin ba.

5. Me ya sa Joshua da Kaleb suka ba da kyakkyawan rahoto?

5 Me ya sa Joshua da Kaleb suka ba da kyakkyawan rahoto, sa’ad da goman suka ba da mummunan rahoto? Dukansu 12 sun ga birane masu ƙarfi da al’ummai da sun kahu. Mutane goman gaskiya suka faɗa da suka ce Isra’ila ba ta da ƙarfi ta ci ƙasar a yaƙi. Joshua da Kaleb sun san da haka su ma. Amma, mutane goman sun ɗauki abubuwa bisa ra’ayin ’yan Adam. Sa’an nan kuma Joshua da Kaleb sun dogara ga Jehovah. Sun ga ikonsa mai girma a Masar, a Jar Teku, da kuma a ƙarƙashin Dutsen Sinai. Domin wannan, har bayan shekaru da yawa ma labarin ayyukan nan sun motsa Rahab a Jericho ta kasadar da ranta domin mutanen Jehovah! (Joshua 2:1-24; 6:22-25) Joshua da Kaleb, shaidun ayyukan da Jehovah ya yi, sun tabbata cewa Allah zai ci gaba da yin yaƙi domin mutanensa. Bayan shekara 40, an kunita dogararsu yayin da sabuwar tsara ta Isra’ilawa, ƙarƙashin shugabancin Joshua, suka shiga ƙasar Kan’ana kuma suka ci ƙasar.

Abin da Ya Sa Za Mu Dogara ga Jehovah da Zuciya Ɗaya

6. Me ya sa Kiristoci a yau suke cikin matsi, kuma ga wa ya kamata su dogara?

6 A cikin wannan “miyagun zamanun” kamar Isra’ilawa, muna fuskantar magabta da suka fi mu ƙarfi. (2 Timothawus 3:1) Muna fuskantar matsi a ɗabi’a, a ruhaniya, da kuma wasu fasaloli, har ma a jiki. Idan da namu iko ne, ba za mu iya shan kan waɗannan matsi ba, domin suna fitowa daga tushe mai girma, Shaiɗan Iblis. (Afisawa 6:12; 1 Yohanna 5:19) To, a ina za mu sami taimako? Wani mai aminci a zamanin dā, ya faɗi cikin addu’a ga Jehovah: “Waɗanda sun san sunanka za su dogara gareka.” (Zabura 9:10) Idan mun san Jehovah kuma mun fahimci abin da sunansa ke nufi, za mu dogara a gare shi da zuciya ɗaya kamar yadda Joshua da Kaleb suka yi.—Yohanna 17:3.

7, 8. (a) Ta yaya halitta ta ba mu dalilin dogara ga Jehovah? (b) Waɗanne dalilai Littafi Mai Tsarki ya bayar domin dogara ga Jehovah?

7 Me ya sa za mu dogara ga Jehovah? Joshua da Kaleb sun yi haka domin sun ga tabbacin ikonsa. Mu ma haka. Alal misali, dubi ayyukan halitta na Jehovah, haɗe da sararin samaniya, da biliyoyin dammai na taurari. Yawan ikoki da ake gani da Jehovah yake sarrafa su ya nuna cewa da gaske shi ne, Mai Iko Duka. Sa’ad da muke bimbini kan al’ajabin halitta, za mu yarda da Ayuba, da ya ce game da Jehovah: “Wa ke hana shi? Wa za ya ce masa, Me ka ke yi?” (Ayuba 9:12) Hakika, idan Jehovah yana wajenmu, ba mu da dalilin tsoron kowa a dukan sararin samaniya.—Romawa 8:31.

8 Ka kuma yi la’akari da Kalmar Jehovah, Littafi Mai Tsarki. Wannan tushen hikima marar ƙarewa yana cike da iko ƙwarai a taimakonmu mu sha kan munanan ayyuka kuma mu gyara rayuwarmu ta jitu da nufin Jehovah. (Ibraniyawa 4:12) Daga cikin Littafi Mai Tsarki ne muka san sunan Jehovah kuma ga manufar sunan. (Fitowa 3:14) Mun fahimci cewa Jehovah zai iya zama abin da ya zaɓa ya zama—Uba mai ƙauna, Alƙali mai adalci, Mayaƙi mai nasara—domin ya cika nufe-nufensa. Kuma muna ganin yadda maganarsa take cika kullum. Yayin da muke nazarinsa cikin Kalmar Allah, muna masu cewa yadda mai Zabura ya ce: “Ina dogara ga maganarka.”—Zabura 119:42; Ishaya 40:8.

9. Ta yaya fansa da tashin Yesu daga matattu suka ƙarfafa dogararmu ga Jehovah?

9 Fansa ita ce kuma wani dalili na dogara ga Jehovah. (Matta 20:28) Abu ne mai ban sha’awa ƙwarai da Allah ya aiko da Ɗansa ya mutu domin ya fanshe mu! Fansar da gaske kuwa mai ci ce. Tana yin kafarar zunuban dukan mutanen da suka tuba kuma suka juya ga Jehovah da zuciyar kirki. (Yohanna 3:16; Ibraniyawa 6:10; 1 Yohanna 4:16, 19) Wani sashe na biyan wannan fansar ta wurin tashin Yesu ne daga matattu. Mu’ujizar nan da ɗarurruwan mutane suka gani, dalili ne na dogara ga Jehovah. Tabbaci ne cewa ba za mu sha kunya ba domin begenmu.—Ayukan Manzanni 17:31; Romawa 5:5; 1 Korinthiyawa 15:3-8.

10. Waɗanne dalilai na kanmu ne muke da su domin mu dogara ga Jehovah?

10 Waɗannan kalilan ne kawai cikin dalilai da ya sa za mu iya kuma ya kamata mu dogara ƙwarai ga Jehovah. Da akwai wasu da yawa, wasu ma na kanmu ne. Alal misali, a wasu lokatai, muna fuskantar yanayi masu wuya a rayuwarmu. Da yake muna biɗan ja-gorar Jehovah a yadda za mu bi da su, mukan shaida yadda ja-gorar take da taimako. (Yaƙub 1:5-8) Idan muka dangana ga Jehovah cikin harkoki na yau da kullum kuma muna shaida sakamakon haka, dogararmu gare shi za ta ƙarfafa.

Dauda Ya Dogara ga Jehovah

11. Duk da wane irin yanayi ne Dauda ya dogara ga Jehovah?

11 Dauda a Isra’ila ta dā ya dogara ga Jehovah. Dauda ya fuskanci barazanar Sarki Saul, wanda yake nema ya kashe shi, da kuma jaruman sojojin Filistiya da suke neman su ci Isra’ila. Duk da haka, ya tsira kuma ya yi nasara. Me ya sa? Dauda da kansa ya yi bayani: “Ubangiji ne haskena da cetona kuma; tsoron wa zan ji? Ubangiji shi ne ƙarfin raina; zan ji tsoron wanene?” (Zabura 27:1) Mu ma za mu yi nasara idan muka dogara ga Jehovah.

12, 13. Ta yaya Dauda ya nuna cewa ya kamata mu dogara ga Jehovah ko ma masu hamayya sun yi amfani da harshensu makamai gāba da mu?

12 A wani lokaci Dauda ya yi addu’a: “Ya Allah, ka ji muryata cikin kawo ƙarata: Ka tsare raina daga tsoron maƙiyi. Ka suturce ni daga shawarar masu-aika mugunta; daga hayaniyar masu-aika zamba: Waɗanda sun wasa harshensu kamar takobi, sun harɗa kibawunsu, watau maganganu masu-zafi: Domin su harbi kamili daga cikin maɓoya.” (Zabura 64:1-4) Ba mu san abin da ya sa Dauda ya rubuta waɗannan kalmomi ba. Amma, mun sani cewa a yau, masu hamayya ma ‘suna wasa harshensu’ haka nan, maganarsu ta kan kasance makamin yaƙi. Suna ‘harbin’ Kiristoci marasa laifi, suna amfani da furci ko kuma rubutu kamar ‘kibiyoyi’ na yi mana sharri. Idan muka dogara ga Jehovah babu jijjiga, me zai faru?

13 Dauda ya ci gaba da cewa: “Allah za ya barce su; ba sanannen ciki za a yi musu rauni da kibiya. Hakanan za a sa su su yi tuntuɓe, harshen kansu yana gāba da su: . . . Adali za ya yi murna cikin Ubangiji, ya dogara gareshi kuma.” (Zabura 64:7-10) Hakika, ko da yake magabta suna wasa harshensu dominmu, a ƙarshe ‘harshensu yakan koma kansu.’ A ƙarshe Jehovah yana mai da al’amura su yi kyau saboda waɗanda suka dogara gare shi su yi murna dominsa.

An Kunita Dogarar Hezekiya

14. (a) A lokacin da yake fuskantar wane yanayi ne mai wuya Hezekiya ya dogara ga Jehovah? (b) Ta yaya Hezekiya ya nuna cewa bai gaskata da ƙaryan Assuriyawa ba?

14 Sarki Hezekiya wani da aka kunita dogararsa ga Jehovah ne. A lokacin sarautar Hezekiya, runduna mai girma ta Assuriya tana wa Urushalima barazana. Rundunar ta ci al’ummai da yawa. Ta ma ci biranen Yahuda Urushalima ce kawai ta tsira, kuma Sennacherib yana barazanar cewa zai ci wannan birnin ma. Ta bakin Rabshakeh—ya nuna cewa—dogara ga Masar domin taimako ruɗu ne. Amma kuma ya ce: “Kada Allahnka da ka ke dogara gareshi ya ruɗe ka, da cewa, Ba za a bada Urushalima a cikin hannun sarkin Assyria ba.” (Ishaya 37:10) Amma, Hezekiya ya sani cewa Jehovah ba yaudararsu yake yi ba. Saboda haka, ya yi addu’a yana cewa: “Ya Ubangiji Allahnmu, ka cece mu daga hannun [Assuriya], domin dukan mulkoki duniya su sani kai ne Ubangiji kai kaɗai.” (Ishaya 37:20) Jehovah ya saurari addu’ar Hezekiya. A cikin dare ɗaya mala’ika guda ya kashe sojojin Assuriya 185,000. An ceci Urushalima, kuma Sennacherib ya bar ƙasar Isra’ila bai sake dawowa ba har abada. Dukan waɗanda suka ji game da wannan aukuwa sun ji game da ɗaukakar Jehovah.

15. Menene kawai zai shirya mu domin yanayi mai wuya da za mu iske kanmu ciki a wannan duniya?

15 A yau, kamar Hezekiya, muna cikin yanayi irin na yaƙi. A yanayinmu, yaƙin na ruhaniya ne. Amma, mu masu yaƙi na ruhaniya muna bukatar mu koyi dabarun tsira. Muna bukatar mu yi tsammanin farmaki kuma mu shirya kanmu domin mu iya tsaya gāba da su. (Afisawa 6:11, 12, 17) A duniya marar kan gado, yanayi yana iya canjawa farat ɗaya. Tarzoma tana iya tasowa babu labari. Ƙasashe da suka ba da ’yancin addini suna iya hanawa. Idan muka shirya kanmu kamar yadda Hezekiya ya yi ta wajen gina dogara marar girgiza ga Jehovah ne, za mu iya mu kasance a shirye mu fuskanci kome da zai faru.

Menene Yake Nufi a Dogara ga Jehovah?

16, 17. Ta yaya za mu nuna cewa muna dogara ga Jehovah?

16 Dogara ga Jehovah ba batun magana ba ne kawai. Ta shafi zuciyarmu kuma tana bayyana a ayyukanmu. Idan muka dogara ga Jehovah, za mu tabbata da Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki sosai. Za mu karanta shi kullum, mu yi bimbini a kansa, kuma mu yarda ya ja-goranci rayuwarmu. (Zabura 119:105) Dogara ga Jehovah ya ƙunshi tabbata da ikon ruhu mai tsarki. Ta wurin taimakon ruhu mai tsarki, za mu iya koyon ’ya’ya da ke faranta wa Jehovah rai, kuma za mu iya kawar da mugun hali da ke manne mana. (1 Korinthiyawa 6:11; Galatiyawa 5:22-24) Saboda haka, ta wurin taimakon ruhu mai tsarki, mutane da yawa sun sami taimako su bar shan taba ko kuma shan miyagun ƙwayoyi. Wasu sun bar hanyoyin lalata. Hakika, idan muka dogara ga Jehovah, muna aiki ta wurin ƙarfinsa ne, ba namu ba.—Afisawa 3:14-18.

17 Ƙari ga haka, dogara ga Jehovah yana nufin dogara ga waɗanda ya amince da su. Alal misali, Jehovah ya shirya “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” su lura da abubuwan duniya na Mulkin. (Matta 24:45-47) Ba ma ƙoƙarin mu nemi ’yancin kanmu, kuma ba ma yin banza da naɗinsu, domin mun amince da tsarin Jehovah. Ban da haka, dattawa da suke hidima a ikilisiya, kuma in ji Bulus, an naɗa su ne da ruhu mai tsarki. (Ayukan Manzanni 20:28) Ta wurin ba da haɗin kanmu ga tsari na cikin ikilisiya, mu ma muna nuna cewa muna dogara ga Jehovah.—Ibraniyawa 13:17.

Ka Bi Misalin Bulus

18. Ta yaya Kiristoci a yau suke bin misalin Bulus, amma ga menene ba sa dogara?

18 Manzo Bulus ya fuskanci matsi da yawa a hidimarsa, kamar yadda muke fuskanta. A zamaninsa, ana ƙaryata Kiristanci a gaban masu iko, kuma a wasu lokatai ya yi ƙoƙarin ya gyara ƙaryar ko kuma kafa aikin wa’azin bisa doka. (Ayukan Manzanni 28:19-22; Filibbiyawa 1:7) A yau, Kiristoci suna bin misalinsa. A duk inda ya yiwu, muna taimakon wasu su waye game da aikinmu, muna amfani da dukan hanyoyi da suka yiwu. Kuma muna aiki domin mu yi kāriya kuma mu kafa bisharar. Amma, ba ma sa dogararmu duka duka ga ƙoƙarce-ƙoƙarcen nan domin ba mu gaskata cewa nasara ta dangana a shari’a daga kotu ko kuma samun farin jini. Maimako, mun dogara ga Jehovah. Mun tuna da ƙarfafarsa ga Isra’ila ta dā: “Cikin komawa da hutu za ku tsira; da natsuwa da dogara ƙarfinku za ya tabbata.”—Ishaya 30:15.

19. Yayin da ake tsananta musu, ta yaya aka kunita dogarar ’yan’uwanmu ga Jehovah?

19 A wasu lokatai cikin tarihinmu na zamani, an hana aikinmu a Gabashi da Yammacin Turai, a wuraren Asiya da Afirka, da kuma a ƙasashen Amirka ta Kudu da ta Arewa. Wannan yana nufi ne cewa dogararmu ga Jehovah ba daidai ba ce? A’a. Ko da yake wani lokaci yana ƙyale tsanani na ƙwarai domin nasa nufi mai kyau, Jehovah yana ƙarfafa waɗanda suke jimre wa tsananin nan. Cikinsa, Kiristoci da yawa sun yi suna mai kyau game da riƙe bangaskiyarsu da kuma dogara ga Allah.

20. Ko da za mu amfana daga ’yanci, a wace hanya ce ba za mu taɓa karya amincinmu ba?

20 A wata sassa, a yawancin ƙasashe muna da izini na aikinmu, kuma a wasu lokatai muna samun farin jini ta hanyar wasa labarai. Muna godiya domin wannan kuma mun fahimci cewa yana taimako a cika nufin Jehovah. Ta wurin albarkarsa ce muke yin amfani da ƙarin ’yanci ba domin mu gabatar da salon rayuwa irin tamu ba, amma domin mu bauta wa Jehovah sosai kuma a fili. Amma, domin kawai hukumomi su ba mu daraja, ba za mu karya ƙa’ida na riƙe amincinmu ba, ko rage aikinmu na wa’azi, ko kuma raunana hidimarmu ga Jehovah. Mu talakawan Mulkin Almasihu ne kuma a kafe a wajen ikon mallaka na Jehovah muke. Begenmu ba domin wannan zamani ba, amma na sabuwar duniya, inda Mulkin Almasihu na samaniya zai kasance shi ne kaɗai gwamnatin da za ta yi sarautar wannan duniyar. Babu bom bom ko makamai, ko kuma wani farmaki na nukiliya da zai girgiza wannan gwamnatin ko kuma ya sa ta faɗi. Babu mai cinta kuma za ta cika nufin Jehovah dominta.—Daniel 2:44; Ibraniyawa 12:28; Ru’ya ta Yohanna 6:2.

21. Wane tafarki za mu ƙudura aniyar bi?

21 Bulus ya ce: “Mu ba mu cikin masu-noƙewa zuwa halaka ba; amma cikin waɗanda su ke da bangaskiya zuwa ceton rai.” (Ibraniyawa 10:39) Bari dukanmu mu bauta wa Jehovah da aminci har matuƙa. Muna da kyakkyawan dalili na dogara ga Jehovah da zuciya ɗaya a yanzu har kuma da nan gaba.—Zabura 37:3; 125:1.

Me Ka Koya?

• Me ya sa Joshua da Kaleb suka ba da rahoto mai kyau?

• Wane dalilai ne sun sa ya kamata mu dogara ga Jehovah da zuciya ɗaya?

• Menene yake nufi a dogara ga Jehovah?

• A dogara ga Jehovah, muna shirye mu ɗauki wane mataki?

[Hoto a shafi na 27]

Me ya sa Joshua da Kaleb suka ba da rahoto mai kyau?

[Hotuna a shafi na 28]

Halitta tana ba mu dalili mai girma na dogara ga Jehovah

[Inda aka Dauko]

Duka sifofi uku: Anglo-Australian Observatory ne suka bayar kuma David Malin ya ɗauki hoton

[Hoto a shafi na 30]

Dogara ga Jehovah yana nufin tabbata da waɗanda shi ya tabbata da su

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba