Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w03 11/1 pp. 4-7
  • Riƙe Amana Yana da Muhimmanci Don Rayuwa ta Farin Ciki

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Riƙe Amana Yana da Muhimmanci Don Rayuwa ta Farin Ciki
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Dogara ga Jehovah da Dukan Zuciyarka
  • Ka Dogara ga Jehovah Kuma Ka Yi Farin Ciki
  • Mutane da Za Mu Iya Amince da Su
  • Kada Ka Yarda Kasawa na Wasu Lokatai Su Sa Ka Sanyin Gwiwa
  • Za a Iya Amince da Ni?
  • Za Ku Iya Yarda da ’Yan’uwanku
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Ka Dogara Ga Jehovah Da Dukan Zuciyarka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ka Nuna Cewa Kai Amintacce Ne
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Me Zan Yi Don Iyayena Su Yarda da Ni?
    Tambayoyin Matasa
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
w03 11/1 pp. 4-7

Riƙe Amana Yana da Muhimmanci Don Rayuwa ta Farin Ciki

DAFI na abinci bai da daɗi ko kaɗan. Wanda dafi na abinci yake damunsa yana bukatar ya mai da hankali da irin abinci da yake ci. Amma daina cin abinci gabaki ɗaya domin guje wa dafi na abinci ba shawarar kirki ba ce. Yin haka zai daɗa kawo matsaloli ne maimakon maganta yanayin. Idan mutum bai ci abinci ba na dogon lokaci zai mutu.

Haka nan ma, idan aka ci amanar mutum abin baƙin ciki ne. Idan ana cin amanarmu kowanne lokaci zai iya sa mu soma tunanin waɗanda za mu zaɓa su zama abokanmu. Amma, idan muka guji mutane gabaki ɗaya saboda an ci amanarmu ba zai magance matsalar ba. Me ya sa? Saboda idan ba ma amince da wasu, zai hana mu yin farin ciki. Domin mu yi rayuwa mai gamsarwa, muna bukatar dangantaka da ke bisa riƙe amana.

“Amincewa tana sa yin cuɗanya da mutane yau da kullum ya kasance da sauƙi,” in ji littafin nan Jugend 2002. “Kowa yana sha’awar ya sami mai riƙon amana,” in ji rahoton jaridar Neue Zürcher Zeitung. “Amincewa tana kyautata rayuwa” har ma tana da “muhimminci don samun ceto.” Jaridar ta ci gaba, idan ba tare da amincewa ba, “mutum ba zai iya jure da rayuwa ba.”

Tun da muna da bukata ta musamman na amince da wani, wa za mu amince da shi da ba zai ci amanarmu ba?

Ka Dogara ga Jehovah da Dukan Zuciyarka

“Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka,” in ji Littafi Mai Tsarki. (Misalai 3:5) Hakika, sau da sau Kalmar Allah ta aririce mu mu dogara ga Mahaliccinmu, Jehovah Allah.

Me ya sa za mu dogara ga Allah? Da farko, domin Jehovah, Allah ne mai tsarki. Annabi Ishaya ya rubuta: “Mai-tsarki, Mai-tsarki, Mai-tsarki ne, Ubangiji.” (Ishaya 6:3) Ra’ayi na kasance da tsarki bai ba ka sha’awa ba? Hakika, ya kamata ka yi sha’awarta saboda tsarkakar Jehovah tana nufin cewa yana da tsabta, ba ya mugunta, matabbaci ne sarai. Ba zai taɓa ɓatanci ko zalunci ba, kuma ba ya yiwuwa ya ci amanarmu.

Ban da haka, za mu iya dogara ga Allah domin iyawarsa da sha’awarsa na son goyon bayan waɗanda suke bauta masa. Alal misali, ikonsa mafifici na motsa shi ya aikata. Kamiltacciyar shari’arsa da hikima suna ja-gorar ayyukansa. Kuma ƙaunarsa da ba ta biyunta ce take motsa shi ya aikata. Manzo Yohanna ya rubuta: “Allah ƙauna ne.” (1 Yohanna 4:8) Ƙaunar Allah tana shafan dukan abin da yake yi. Tsarkaka ta Jehovah da kuma wasu halaye na musamman sun sa ya zama Uba da ya dace, wanda za mu iya dogara gare shi sarai. Babu wani abu ko kuma wani da ya cancanci mu dogara gare shi idan ba Jehovah ba.

Ka Dogara ga Jehovah Kuma Ka Yi Farin Ciki

Wani dalili mai kyau da ke sa mu dogara ga Jehovah shi ne domin ya fahimce mu fiye da yadda wani zai iya. Ya sani cewa kowanne mutum yana bukatar dangantaka mai kyau, mai jurewa, tabbatacce da Mahalicci. Waɗanda suke da irin dangantakar nan sun fi samun kwanciyar rai. “Mai-albarka ne mutum wanda ya maida Ubangiji abin dogararsa,” in ji Sarki Dauda. (Zabura 40:4) Miliyoyi a yau suna furta kalmomin Dauda da zuciya ɗaya.

Ga wasu misalai. Doris ta yi zama a Amirka, Helas, Jamhuriyar Dominican, da kuma Jamus. Ta ce: “Ina farin ciki na dogara ga Jehovah. Ya san yadda yake kula da ni a zahiri, a ruhaniya, da kuma a jiye-jiye. Shi ne aboki mafi kyau da mutum zai iya samu.” Wolfgang, wani lauya, ya bayyana: “Abu ne mai daɗi ka dangana ga wanda yake sonka sosai, wanda zai iya—kuma da zai yi—abu mafi kyau dominka!” Ham, wanda aka haife shi a Asiya da yanzu yana zama a Turai, ya ce: “Na tabbata cewa Jehovah yana kula da dukan al’amari, kuma ba ya kuskure, domin haka ina farin cikin cewa na dogara gare shi.”

Alhali, kowannenmu na bukatar mu amince ba da Mahaliccinmu kawai ba amma da mutane ma. Shi ya sa, Jehovah shi aboki da ya ƙware ne mai hikima, yana ba da shawara game da irin mutane da ya kamata mu amince da su. Ta wurin karanta Littafi Mai Tsarki sosai, za mu iya lura da gargaɗinsa a wannan batun.

Mutane da Za Mu Iya Amince da Su

“Kada ku dogara ga sarakuna, ko kuwa ɗan adam, wanda babu taimako gareshi,” in ji mai Zabura. (Zabura 146:3) Wannan huraren furci ya taimake mu mu fahimta cewa mutane da yawa ba su cancanci mu amince da su ba. Ko waɗanda ma ake ɗaukansu “sarakuna” na wannan duniyar, kamar su gwanaye a fannonin ilimi ko ayyuka na musamman, ba za mu amince da su haka nan kawai ba. Sau da yawa ja-gorarsu na kasawa, kuma idan muka dogara da irin waɗannan “sarakuna” ba zai daɗe ba za mu sha kunya.

Amma, bai kamata wannan ya sa mu ƙi amince da dukan mutane ba. Alhali, a bayyane yake muna bukatar mu yi zaɓe a waɗanda za mu amince da su. Wane mizani ya kamata mu yi amfani da shi? Wani misali na al’ummar Isra’ila ta dā zai iya taimakonmu. Lokacin da aka bukaci a naɗa wasu mutane su ɗauki hakki masu nauyi a Isra’ila, an gaya wa Musa ya “tanaji waɗansu masu-iyawa, masu-tsoron Allah, amintattu, masu-ƙin rishu’a.” (Fitowa 18:21) Me za mu iya koya daga wannan?

Waɗannan mutane ne da suka nuna halaye na ibada kafin a naɗa su su ɗauki hakki na riƙe amana. Sun riga sun tabbatar da cewa suna tsoron Allah; suna daraja Mahalicci kuma suna tsoron su baƙanta masa rai. A bayyane yake cewa kowanne cikin waɗannan mutane sun yi iyakacin ƙoƙarinsu su bi mizanan Allah. Sun ƙi ha’inci, da ke nuna suna da ɗabi’a da zai hana su daga ɓata ikonsu. Ba za su ci amana ba domin riban kansu ko kuma domin danginsu ko abokai ba.

Ba zai yi kyau mu a yau mu yi amfani da mizanan nan a zaɓan waɗanda za mu iya amince da su ba? Mun san mutane da halayensu yake nuna suna tsoron Allah? Suna ƙoƙari ne su kasance da halaye da sun yi daidai da mizanansa? Suna da gaba gaɗi su guji yin abubuwan da ba daidai ba ne? Suna yarda wa gaskiya ta mallaki yanayin domin nasu amfani ko kuma su sami abin da suke so? Hakika, maza da mata da suke da irin halayen nan sun cancanci mu amince da su.

Kada Ka Yarda Kasawa na Wasu Lokatai Su Sa Ka Sanyin Gwiwa

Idan muna shawarar wanda za mu iya amince da shi, dole mu yi haƙuri, tun da yake da sannu sannu ake amince da mutum. Abar hikima ita ce mu soma amince da mutum a hankali, bi da bi. Ta yaya? To dai, muna iya lura da mutumin na ɗan lokaci, muna lura da yadda yake aikatawa a wasu yanayi. Ana iya tabbata da mutumin ne a ƙananan al’amura? Alal misali, yana mayar da abin da ya ara kuma shi wanda ya saba da makara ne kowane lokaci? Idan haka ne, to za mu iya shawarta mu amince da shi a al’amura masu muhimmanci ma. Wannan ya yi daidai da ƙa’idar nan: “Wanda ya ke da aminci cikin ƙanƙanin abu mai-aminci ne cikin mai-yawa.” (Luka 16:10) Idan muna zaɓe kuma muna haƙuri zai iya taimake mu mu guje wa shan kunya.

Idan wani ya ba mu kunya kuma fa? Ɗaliban Littafi Mai Tsarki za su iya tuna cewa a daren da aka tsare Yesu Kristi, manzanninsa suka ba shi kunya. Yahuda Iskariyoti ya ci amanarsa, kuma sauran suka tsere don tsoro. Har Bitrus ma ya yi musun Yesu sau uku. Amma Yesu ya fahimci cewa Yahuda ne kawai ya aikata da ganga. Da aka ba Yesu kunya haka a lokaci na musamman bai hana shi sake tabbatar da amincewarsa wurin sauran manzanninsa 11 ba ’yan makonni daga baya. (Matta 26:45-47, 56, 69-75; 28:16-20) Haka nan ma, idan muna ganin wani ya ci amanarmu, zai yi kyau mu bincika ko da gaske ne halin cin amanar ko kuma raunana ce kawai ta jiki.

Za a Iya Amince da Ni?

Mutumin da yake son ya yi zaɓe game da wanda zai iya amince da shi zai dace ya yi wa kansa tambaya: ‘Za a iya amince da ni kuwa? Waɗanne mizanai na amincewa ya kamata na yi kuma na yi tsammaninsa daga wasu?’

Hakika wanda za a iya amince da shi ko yaushe yana faɗin gaskiya. (Afisawa 4:25) Ba ya canja maganarsa dangane da wanda yake sauraronsa don ya sami ribar kansa ba. Wanda ake iya amince da shi, sa’ad da ya yi alkawari yana iyakacin ƙoƙarinsa ya cika alkawarinsa. (Matta 5:37) Idan wani ya gaya masa maganar asiri, mutumin yakan rufe asirin kuma ba ya gulmansa. Wanda za a iya amince da shi yana riƙe aminci ga abuyar aurensa. Ba ya kallon hotunan tsirarrun mutane, ba ya dulmaya cikin wasiƙar jaki ba, kuma ba ya kwarkwasa. (Matta 5:27, 28) Wanda muke amince da shi yana ƙoƙari domin ya ciyar da kansa da kuma iyalinsa kuma ba ya neman arzikin dare ɗaya. (1 Timothawus 5:8) Tuna da irin mizanan nan na Nassosi zai taimake mu mu iya sanin mutane da za mu amince da su. Ban da haka, idan muka bi mizanan nan zai sa wasu su amince da mu.

Zai zama abin farin ciki ne yin rayuwa cikin duniya da dukan mutane za a iya amince da su, inda shan kunya don cin amana zai zama abin dā! Wannan mafarki ne kawai? Ba ga mutane da suke gaskata da alkawuran Littafi Mai Tsarki ba, domin Kalmar Allah ta annabta zuwan “sabuwar duniya” da ba za a ga ruɗu ba, ƙarya, da kuma zamba, ba za a yi baƙin ciki, ciwo, har mutuwa kuma ba! (2 Bitrus 3:13; Zabura 37:11, 29; Ru’ya ta Yohanna 21:3-5) Ba abin da ya cancanta ne a ƙara binciken wannan zaton ba? Shaidun Jehovah za su yi farin cikin yi maka tanadin ƙarin koyarwa game da wannan da kuma wasu muhimman darussa.

[Hoto a shafi na 4]

Idan ba ma amince da wasu, zai hana mu yin farin ciki

[Hoto a shafi na 5]

Ya fi cancanta mu dogara ga Jehovah

[Hotuna a shafi na 7]

Dukanmu na bukatar dangantaka da ke bisa riƙe amana

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba