Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w03 4/1 pp. 21-26
  • Tawali’u Yana Da Muhimmanci Ƙwarai Ga Kirista

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Tawali’u Yana Da Muhimmanci Ƙwarai Ga Kirista
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “Da Tamani Mai-Girma a Gaban Allah”
  • Tawali’u Yana Jawowa Kuma Yana Wartsakarwa
  • Ya Fi Kowa Tawali’u a Zamaninsa
  • Tankiya da Kuma Tawali’u
  • Ka Biɗi Tawali’u
  • Tawali’u​—Yaya Yake Amfanar Mu?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Ka “Nuna Iyakacin Tawali’u Ga Dukan Mutane”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Mai Sauƙin Kai Jarumi Ne
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • “Wanene A Cikinku Mai-hikima Ne, Mai Fahimi?”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
w03 4/1 pp. 21-26

Tawali’u Yana Da Muhimmanci Ƙwarai Ga Kirista

“Ku yafa tawali’u.”—KOLOSSIYAWA 3:12.

1. Menene ya sa tawali’u ya kasance hali mai ban sha’awa?

IDAN mutum mai tawali’u ne, kasancewa tare da shi yana da daɗi. Duk da haka, mai hikima Sarki Sulemanu ya lura cewa: “Harshe mai taushi kuma ya kan karya ƙashi.” (Misalai 25:15) Tawali’u hali ne mai kyau da ya haɗa daɗi da kuma ƙarfi.

2, 3. Wace nasaba ce da akwai tsakanin tawali’u da ruhu mai tsarki, kuma menene za mu bincika a wannan talifin?

2 Manzo Bulus ya haɗa tawali’u a cikin jerinsa na ‘ ’yar ruhu,’ da yake cikin Galatiyawa 5:22, 23. Kalmar Helenanci da aka fassara “tawali’u” a cikin aya ta 23 na Litafi Mai-Tsarki sau da yawa ana fassara ta “taushi” a wasu fassarar Littafi Mai Tsarki. Hakika, yana da wuya a sami kalmar da ta yi daidai da kalmar Helenanci a yawancin harsuna domin kalmar ainihi tana kwatanta, ba taushi na waje ba ne ko kuma tawali’u, amma taushi ko kuma tawali’u na ciki; ba yadda halin mutum yake ba, amma yanayin zuciyarsa.

3 Domin mu sami cikakken fahimi na muhimmancin tawali’u, bari mu bincika misalai huɗu na Littafi Mai Tsarki. (Romawa 15:4) Idan muka yi haka za mu fahimci fiye da wannan halin, za mu koyi yadda za a koya da kuma yadda za a nuna shi a cuɗanyarmu.

“Da Tamani Mai-Girma a Gaban Allah”

4. Ta yaya muka sani cewa Jehovah yana ɗaukan tawali’u da tamani?

4 Tun da tawali’u yana cikin ’yar ruhun Allah, daidai ne mu ga cewa yana da nasaba da halaye na ban sha’awa na Allah. Manzo Bitrus ya rubuta cewa “ruhu mai-ladabi mai-lafiya” yana da “tamani mai-girma a gaban Allah.” (1 Bitrus 3:4) Hakika, tawali’u hali ne na Allah; Jehovah yana ɗaukan shi da tamani ƙwarai. Babu shakka, wannan kansa isashen dalili ne da dukan bayin Allah ya kamata su koyi tawali’u. Amma, ta yaya Allah maɗaukakin sarki, Mai Iko bisa dukan halitta, yake nuna tawali’u?

5. Domin tawali’un Jehovah wane bege muka samu?

5 Sa’ad da mata da miji na fari, Adamu da Hauwa’u suka taka dokar Allah kada su ci itacen sanin nagarta da mugunta, sun yi haka ne da gangan. (Farawa 2:16, 17) Wannan ƙin biyayya da gangan ya kawo zunubi, mutuwa, da kuma warewa daga Allah a gare su da kuma ’ya’yansu. (Romawa 5:12) Ko da yake Jehovah ba shi da laifi wajen yanke musu hukunci, bai share iyalin ’yan Adam kawai ba gabaki ɗaya da cewa bai yiwuwa a fanshe su ba. (Zabura 130:3) Maimakon haka, da son ransa ba tare da tilastawa ba—a nuna tawali’u—Jehovah ya yi tanadin abin da mutane masu zunubi za su zo wurinsa domin su sami tagomashi. Hakika, ta wurin kyautar hadaya ta fansa ta Ɗansa, Yesu Kristi, Jehovah ya sa ya yiwu a zo gaban kursiyinsa mai girma ba tare da tsoro ba.—Romawa 6:23; Ibraniyawa 4:14-16; 1 Yohanna 4:9, 10, 18.

6. Ta yaya tawali’u ya bayyana cikin cuɗanyar Allah da Kayinu?

6 Da daɗewa kafin Yesu ya zo duniya, Jehovah ya nuna tawali’unsa sa’ad da Kayinu da Habila, ’ya’yan Adamu, suka ba da hadayarsu ga Allah. Da ya fahimci yanayin zuciyarsu, Jehovah ya ƙi hadayar Kayinu amma “ya kula” da Habila da kuma hadayarsa. Domin Allah ya dubi Habila da idon rahama da kuma hadayarsa, wannan ta jawo ɓacin rai ga Kayinu. “Kayinu fa ya ji haushi ƙwarai, gabansa kuwa ya faɗi,” in ji Littafi Mai Tsarki. Menene Jehovah ya yi? Ya yi fushi ne domin halin Kayinu marar kyau? A’a. Da taushin harshe, ya tambayi Kayinu abin da ya sa ya yi fushi. Har Jehovah ma ya yi wa Kayinu bayanin yadda zai sami “amsa.” (Farawa 4:3-7) Hakika, Jehovah yana cike da tawali’u.—Fitowa 34:6.

Tawali’u Yana Jawowa Kuma Yana Wartsakarwa

7, 8. (a) Ta yaya muka kai ga fahimtar tawali’un Jehovah? (b) Menene kalmomin Matta 11:27-29 suka bayyana game da Jehovah da kuma Yesu?

7 Hanya ɗaya na fahimtar halayen Jehovah da babu na biyunta, ita ce ta wurin yin nazarin rayuwa da kuma hidimar Yesu Kristi. (Yohanna 1:18; 14:6-9) Sa’ad da yake Galili a shekara ta biyu na aikinsa na wa’azi, Yesu ya yi ayyuka masu ban al’ajabi da yawa a Korasinu, Baitsaida, Kafarnahum, da kuma wuraren da suke kusa. Duk da haka, mutanen suna da fahariya kuma ba sa so, saboda haka, suka ƙi su ba da gaskiya. Menene Yesu ya yi? Ko da yake ya tunasar da su sakamakon rashin imaninsu, tausayi ya motsa shi domin yanayin ruhaniya na ‘amha’arets, talakawa da suke tsakaninsu.—Matta 9:35, 36; 11:20-24.

8 Ayyukan Yesu da suka biyo baya sun nuna cewa Yesu ya ‘san Uban’ kuma ya yi koyi da shi. Ga talakawan, Yesu ya gayyace su: “Ku zo gareni, dukanku da ku ke wahala, masu-nauyin kaya kuma, ni kuwa in ba ku hutawa. Ku ɗauka ma kanku karkiyata, ku koya daga wurina; gama ni mai-tawali’u ne, mai-ƙasƙantar zuciya: za ku sami hutawa ga rayukanku.” Hakika waɗannan kalmomi sun ba da ta’aziyya da kuma wartsakewa ga waɗanda suke da nauyin kaya kuma ake zaluntarsu! Sun ma wartsakar da mu a yau. Idan muna yafa tawali’u da gaske, to, za mu kasance tsakanin waɗanda “Ɗan ya nufa shi bayyana” musu Ubansa.—Matta 11:27-29.

9. Wane hali ne yake da nasaba da tawali’u, kuma ta yaya ne Yesu ya kasance abin koyi mai kyau a wannan?

9 “Ƙasƙantar zuciya” tana da nasaba ta kusa da tawali’u. Amma fahariya kuwa tana kai wa ga ɗaga kai, sau da yawa tana sa mutane su yi ƙeta. (Misalai 16:18, 19) Yesu ya nuna tawali’u a cikin dukan hidimarsa. Har lokacin da ya shiga Urushalima a kan jaki kwana shida kafin ya mutu aka jinjina masa Sarkin Yahudawa, Yesu ya bambanta ƙwarai da sarakunan duniya. Ya cika annabcin Zakariya na Almasihu. “Ki duba, ga Sarkinki yana zuwa gareki, mai-tawali’u ne, yana tafiya bisa kan jaki, a kan aholaki kuma ɗan jaki.” (Matta 21:5; Zechariah 9:9) Annabi mai aminci Daniel ya gani a cikin wahayi Jehovah ya ba wa Ɗansa iko. Duk da haka, a annabci na farko ya kwatanta Yesu da “ƙasƙantattun mutane.” Tawali’u da kuma ƙasƙantar zuciya suna da nasaba ta kusa.—Daniel 4:17; 7:13, 14.

10. Me ya sa tawali’u na Kiristoci ba ya nufin raunana?

10 Tawali’u mai daɗa rai da Jehovah da Yesu suka nuna ya taimaka mana mu matsa kusa da su. (Yaƙub 4:8) Hakika, tawali’u ba ya nufin raunana. Ko kaɗan! Jehovah, Allah maɗaukakin sarki, yana nuna ƙarfi mai yawa da kuma iko. Fushinsa yana faɗuwa a kan marasa adalci. (Ishaya 30:27; 40:26) Yesu ma ya nuna aniya ba zai shirka ba, har a lokacin da Shaiɗan Iblis ya kai masa hari. Bai ƙyale haramtaccen kasuwanci na shugabannin addini na zamaninsa ba. (Matta 4:1-11; 21:12, 13; Yohanna 2:13-17) Duk da haka, ya nuna tawali’u wajen bi da kasawar almajiransa, kuma cikin haƙuri ya ɗauki raunanarsu. (Matta 20:20-28) Wani manazarin Littafi Mai Tsarki ya kwatanta tawali’u a wannan hanyar: “A ƙarƙashin tawali’u da ƙarfi irin na ƙarfe.” Ya kamata mu nuna irin wannan hali na Kristi—tawali’u.

Ya Fi Kowa Tawali’u a Zamaninsa

11, 12. Idan aka yi la’akari da yadda aka rene shi, menene ya sa tawali’un Musa ya yi fice?

11 Misali na uku da za mu bincika shi ne Musa. Littafi Mai Tsarki ya kwatanta shi da “mai-tawali’u ne ƙwarai, gaba da kowane mutum da ke zaune a bisa fuskar duniya.” (Litafin Lissafi 12:3) Allah ne ya sa aka rubuta wannan kwatanci. Tawali’un Musa da ya yi fice ya sa ya bi ja-gorar Jehovah.

12 Yadda aka reni Musa ba a hanyar da aka saba ba ce. Jehovah ya tabbata cewa an kāre wannan ɗan Yahudawa masu aminci a lokacin maƙirci da kisa. Musa ya kasance da uwarsa a lokacin da yake yaro, ita kuma ta koyar da shi game da Allah Jehovah. Daga baya, an ɗauki Musa zuwa wurin da ya bambanta ƙwarai. “Aka sanar ma Musa da dukan hikimar Masarawa,” in ji Istifanus Kirista da aka fara kashe shi domin addininsa. “[Musa] ya kasance mai-iko cikin zantattukansa da ayyukansa.” (Ayukan Manzanni 7:22) Bangaskiyarsa ta bayyana sa’ad da ya ga rashin gaskiyar da shugabannin bayin Fir’auna suke yi wa ’yan’uwansa. Domin ya kashe Bamasare da ya gani yana dūkan Bayahude, dole ne Musa ya gudu ya bar ƙasar Masar zuwa ƙasar Midiya.—Fitowa 1:15, 16; 2:1-15; Ibraniyawa 11:24, 25.

13. Yaya shekaru 40 na zama a Midiya ya shafi Musa?

13 Sa’ad da yake ɗan shekara 40, dole ne Musa ya yi wa kansa tanadi a cikin daji. A Midiya ya sadu da ’ya’ya mata guda bakwai na Reuel ya taimake su jawo ruwa wa garken ubansu mai girma. Da suka isa gida ’yammatan suka yi wa babansu bayani cewa “wani, Ba-masare” ya cece su daga hannun makiyaya da suke matsa musu. Reuel ya gayyace shi, Musa ya zauna da iyalin. Wahala da ya sha ba ta sa ya yi ɓacin rai ba; ko kuma ta hana shi gyara hanyar rayuwarsa ta jitu da sabon mazauninsa ba. Muradinsa ya yi nufin Allah bai jijjiga ba. A cikin shekaru 40, lokacin da yake kula da tumakin Reuel, ya auri Zipporah, kuma ya yi renon ’ya’ya maza, Musa ya koyi kuma ya kyautata wannan hali da aka zo ga kwatanta shi da shi. Hakika, ta cikin wahala, Musa ya koyi tawali’u.—Fitowa 2:16-22; Ayukan Manzanni 7:29, 30.

14. Ka kwatanta abin da ya faru a lokacin shugabancin Musa a Isra’ila da ya nuna tawali’unsa.

14 Bayan Jehovah ya naɗa shi shugaban al’ummar Isra’ila, halin Musa na tawali’u har ila ya bayyana. Wani saurayi ya kawo wa Musa rahoto cewa Eldad da kuma Medad suna ayyukan annabawa a cikin zango—ko da yake ba sa wurin sa’ad da Jehovah ya zubo da ruhunsa bisa dattawa 70 da za su taimaki Musa. Joshua ya ce: “Ya ubangijina Musa, ka hana su!” Musa ya amsa cikin tawali’u: “Kana jin kishi domina? Da ma dukan jama’an Ubangiji annabawa ne, Ubangiji kuwa ya sa ruhunsa a bisansu!” (Litafin Lissafi 11:26-29) Tawali’u ya kame wannan yanayi mai wuya.

15. Ko da yake Musa ajizi ne, me ya sa misalinsa abin da za a bi ne?

15 A wani lokaci kuma tawali’un Musa ya kasance kamar ba shi da shi. A Meribah, kusa da Kadesh, ya ƙyale ɗaukaka Jehovah, Mai Yin Mu’ujiza. (Litafin Lissafi 20:1, 9-13) Ko da yake Musa ajizi ne, bangaskiyarsa marar jijjiga ta tallafa masa a dukan rayuwarsa, kuma tawali’unsa da ya yi fice ya kan ba mu sha’awa har a yau.—Ibraniyawa 11:23-28.

Tankiya da Kuma Tawali’u

16, 17. Wane gargaɗi muka samu daga labarin Nabal da Abigail?

16 Wani misalin gargaɗi kuma ya kasance a lokacin Dauda, ba da daɗewa ba bayan annabin Allah Sama’ila ya mutu. Ta ƙunshi ma’aurata ne, Nabal da matarsa Abigail. Su biyun sun bambanta ƙwarai! Abigail mace ce “mai-fahimi,” mijinta kuma mutum “mai-tankiya ne mai-munanan ayyuka.” Nabal ya ƙi ya amsa roƙon mutanen Dauda waɗanda suka taimake shi wajen gadin garkensa mai girma daga ɓarayi. Da fushi irin na adalci, Dauda da mutanensa suka sha ɗamara da takubbansu suka nufi wajen Nabal.—1 Samu’ila 25:2-13.

17 Sa’ad da abin da ya faru ya faɗi a kunnen Abigail, ta yi hanzari ta shirya gurasa, ruwan inabi, nama, da kuma waina ta ɓaure ta fita ta tari Dauda. “Ya ubangijina, laifin nan a kaina ya ke,” ta roƙe shi. “Ina roƙonka kuma ka bar baiwarka ta yi magana a kunnenka, ka ji maganar baiwarka.” Zuciyar Dauda ta yi sanyi domin roƙon Abigail cikin tawali’u. Bayan ya saurari bayanin Abigail, Dauda ya ce: “Mai-albarka ne Ubangiji Allah na Isra’ila, wanda ya aiko ki yau garin ki tarbe ni! Mai-albarka ce hikimarki, mai-albarka ce ke kuma da kin hana ni yau daga alhakin jini.” (1 Samu’ila 25:18, 24, 32, 33) Tankiyar Nabal ta kai shi ga mutuwarsa. Halaye masu kyau na Abigail a ƙarshe ya kai ta ga farin cikin zama matar Dauda. Tawali’unta tafarki ne ga dukan waɗanda suke bauta wa Jehovah a yau.—1 Samu’ila 25:36-42.

Ka Biɗi Tawali’u

18, 19. (a) Waɗanne canji za su bayyana sa’ad da muka yafa wa kanmu tawali’u? (b) Menene zai taimake mu mu bincika kanmu da kyau?

18 To, tawali’u ya zama dole. Ya fi kasancewa da laushin hali kawai; hali ne mai wartsakar da wasu. A dā wataƙila muna da tankiya da kuma ƙeta. Da muka koyi gaskiyar Littafi Mai Tsarki, mun canju mun zama masu daɗaɗa wa wasu zuciya kuma masu jituwa. Bulus ya yi maganar wannan canji sa’ad da ya aririci ’yan’uwa Kiristoci: “Ku yafa zuciya ta tausayi, nasiha, tawali’u, ladabi, jimrewa.” (Kolossiyawa 3:12) Littafi Mai Tsarki ya kwatanta wannan canjin da canjuwar dabbar daji—kirkice, damisa, zaki, da kuma kumurci—zuwa dabba ta gida kamar su—ɗan rago, ɗan akuya, ɗan maraƙi, da kuma saniya. (Ishaya 11:6-9; 65:25) Irin wannan canjin hali yana sa masu lura su yi mamaki idan suka gani. Amma mu muna yaba wa ruhun Allah domin irin wannan canji, domin wannan ya ƙunshi ’yar ruhunsa na tawali’u.

19 Wannan yana nufi ne cewa daga mun yi canji da ake bukata kuma muka keɓe kanmu ga Jehovah, ba ma bukatar mu yi aiki domin mu kasance masu tawali’u? Ko kaɗan. Sababbin tufafi suna bukatar a kula da su domin su kasance da tsabta da kuma kyaun gani. Bincika Kalmar Allah da kuma bimbini a kan misalai da ke ciki za su taimake mu mu sake duba kuma mu kula da kanmu. Menene madubin Kalmar Allah ta bayyana game da kai?—Yaƙub 1:23-25.

20. Ta yaya za mu ci nasara wajen nuna tawali’u?

20 Ainihi mutane suna da zuciya dabam dabam. Wasu bayin Allah yana da sauƙi a gare su su nuna tawali’u fiye da wasu. Duk da haka, dukan Kiristoci suna bukatar su koyi ’yar ruhun Allah, haɗe da tawali’u. Bulus cikin ƙauna ya yi wa Timothawus gargaɗi: “Ka bi adalci, ibada, bangaskiya, ƙauna, haƙuri, tawali’u.” (1 Timothawus 6:11) Kalmar nan “bi” ta nuna cewa ana bukatar ƙoƙari. Wata fassarar Littafi Mai Tsarki ta ce ‘ka kafa zuciyarka bisa.’ (New Testament in Modern English, na J. B. Phillips) Idan ka yi ƙoƙari ka yi bimbini a kan misalai daga Kalmar Allah, za su iya zama kamar jikinka, kamar an dasa a cikinka. Za su mulmule ka kuma su yi maka ja-gora.—Yaƙub 1:21.

21. (a) Me ya sa za mu bi tawali’u? (b) Menene za a yi zancensa a talifi na gaba?

21 Yadda muke bi da wasu mutane zai nuna yadda muke yi a wannan batun. “Wanene a cikinku mai-hikima ne, mai-fahimi?” in ji tambayar almajiri Yaƙub. “Ta wurin kyakkyawan tasarrufinsa shi nuna ayyukansa cikin tawali’u na hikima.” (Yaƙub 3:13) Ta yaya za mu nuna wannan hali na Kirista a gida, a hidimar Kirista, da kuma a cikin ikilisiya? Talifi na gaba ya yi tanadin ja-gora da za ta yi taimako.

Domin Maimaitawa

• Me ka koya game da tawali’u daga misalin

• Jehovah?

• Yesu?

• Musa?

• Abigail?

• Me ya sa muke bukatar mu bi tawali’u?

[Hoto a shafi na 22]

Me ya sa Jehovah ya kula da hadayar Habila?

[Hoto a shafi na 23]

Yesu ya nuna cewa tawali’u da ƙasƙantar zuciya suna da nasaba ta kusa

[Hoto a shafi na 24]

Musa ya kafa misali mai kyau na tawali’u

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba