“Wanene A Cikinku Mai-hikima Ne, Mai Fahimi?”
“Wanene a cikinku mai-hikima ne, mai-fahimi? ta wurin kyakkyawan tasarrufinsa shi nuna ayyukansa cikin tawali’u na hikima.”—YAƘ. 3:13.
1, 2. Menene za a iya cewa game da yawancin mutanen da aka ɗauka cewa suna da hikima?
WANENE kake tunanin cewa shi ne mafi hikima? Wataƙila iyayenka ne, wani tsohon mutum, ko kuwa malamin makarantarka? Yanayinka da kuma inda ka girma zai iya yin tasiri a kan ra’ayinka na mutumin da ke da hikima. Amma bayin Allah sun fi son ra’ayin Allah.
2 Ba dukan waɗanda mutane suke ɗauka masu hikima ba ne suke da hikima a gaban Allah. Alal misali, Ayuba ya tattauna da mutanen da suke tunanin cewa suna furta kalamai masu hikima, amma ya kammala cewa: “Ban iske mai-hikima a cikinku ba.” (Ayu. 17:10) Ga waɗanda suka ƙi sanin Allah, manzo Bulus ya rubuta: “Garin kiraren kansu masu-hikima, suka zama wawaye.” (Rom. 1:22) Kuma ta bakin annabi Ishaya, Jehobah ya ce: “Kaiton waɗanda ke maida kansu masu-hikima!”—Isha. 5:21.
3, 4. Idan mutum yana son ya kasance mai hikima da gaske, me zai yi?
3 Babu shakka, muna bukatar mu san abin da zai sa mutum ya zama mai hikima sosai kuma ya sami tagomashin Allah. Misalai 9:10 ta ba mu wannan ƙarin hasken: “Tsoron Ubangiji mafarin hikima ne: Sanin Mai-tsarki kuma shi ne fahimi.” Dole ne mutum mai hikima ya ji tsoron Allah kuma ya daraja mizanansa. Amma, muna bukatar fiye da sanin cewa akwai Allah da kuma cewa yana da mizanai. Almajiri Yaƙub ya ƙarfafa mu mu yi tunani game da wannan. (Ka karanta Yaƙub 3:13.) Ka yi la’akari da furcin nan: “Ta wurin kyakkyawan tasarrufinsa [halayensa] shi nuna ayyukansa.” Kana bukatar ka nuna hikima ta gaske a ayyukanka da kuma furcinka na yau da kullum.
4 Hikima ta gaske ta ƙunshi nuna sanin ya kamata da kuma yin amfani da sani da fahimi a hanya mai kyau. Waɗanne ayyuka ne za su nuna cewa muna da irin wannan hikimar? Yaƙub ya ambata abubuwan da waɗanda ke da hikima za su yi.a Menene Yaƙub ya ce zai taimaka mana mu kasance da dangantaka mai kyau da ’yan’uwanmu masu bi, da kuma waɗanda ba masu bi ba ne?
Ayyukan da ke Nuna Cewa Mutum Yana da Hikima
5. Wane irin hali ne mutumin da ke da hikima ta gaske zai nuna?
5 Yana da muhimmanci mu sake maimaita cewa Yaƙub ya haɗa hikima da hali mai kyau. Domin tsoron Jehobah shi ne mafarin hikima, mutum mai hikima yana iya ƙoƙarinsa ya yi abubuwan da suka jitu da hanyoyin Allah da kuma mizanansa. Ba a haife mu da hikima na sama ba. Duk da haka, muna iya samun hikima ta wajen yin nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma yin bimbini. Hakan zai taimaka mana mu yi abin da Afisawa 5:1 ta ce: “Ku zama fa masu-koyi da Allah.” Idan muka ci gaba da yin koyi da halayen Jehobah, hakan zai sa mu nuna hikima a halayenmu. Hanyoyin Jehobah sun ɗara ta mutane. (Isha. 55:8, 9) Saboda haka, yayin da muka ci gaba da yin koyi da yadda Jehobah yake yin abubuwa, mutanen waje za su ga cewa mun bambanta.
6. Me ya sa tawali’u ke nuna cewa mutum na tsoron Allah, kuma menene wannan halin ya ƙunsa?
6 Yaƙub ya nuna cewa hanya ɗaya ta zama kamar Jehobah ita ce mu kasance da “tawali’u na hikima.” Ko da yake tawali’u ya ƙunshi kasancewa mai haƙuri, duk da haka Kirista zai iya kasancewa da ƙarfin hali wanda zai taimake shi ya aikata yadda ya kamata. Ko da yake ƙarfinsa bai da iyaka, Allah yana da tawali’u, kuma ba ma tsoron kusantarsa. Ɗan Allah ya nuna irin tawali’un Ubansa sosai wanda hakan ya sa ya ce: “Ku zo gareni, dukanku da ku ke wahala, masu-nauyin kaya kuma, ni kuwa in ba ku hutawa. Ku ɗauka ma kanku karkiyata, ku koya daga wurina; gama ni mai-tawali’u ne, mai-ƙasƙantar zuciya: za ku sami hutawa ga rayukanku.”—Mat. 11:28, 29; Filib. 2:5-8.
7. Me ya sa Musa misali ne mai kyau na tawali’u a gare mu?
7 Littafi Mai Tsarki ya ba mu labarin wasu mutanen da suka yi fice wajen nuna tawali’u. Ɗaya a cikinsu shi ne Musa. Ya sami gata mai yawa, duk da haka an ce shi “mai-tawali’u ne ƙwarai, gaba da kowane mutum da ke zaune a bisa fuskar duniya.” (Lit. Lis. 11:29; 12:3) Kuma ka tuna irin gaba gaɗin da Jehobah ya ba Musa don ya cika nufinsa. Jehobah ya yi farin cikin yin amfani da mutane masu tawali’u don ya cika nufinsa.
8. Ta yaya ne mutane ajizai za su iya nuna “tawali’u na hikima”?
8 Babu shakka, yana yiwuwa mutane ajizai su nuna “tawali’u na hikima.” Mu kuma fa? Ta yaya za mu iya nuna wannan halin sosai? Tawali’u yana cikin ’yar ruhu mai tsarki na Jehobah. (Gal. 5:22, 23) Muna iya roƙon Allah ya ba mu ruhunsa kuma mu yi iya ƙoƙarinmu mu nuna ’yarta, mu kuma kasance da tabbaci cewa Allah zai taimaka mana mu nuna tawali’u sosai. Wannan tabbacin da ke zabura zai motsa mu mu yi hakan: “[Allah] za shi koya ma masu-tawali’u tafarkinsa.”—Zab. 25:9.
9, 10. Wane irin ƙoƙari ne muke bukatar mu yi don mu nuna haƙuri, kuma me ya sa?
9 Duk da haka, muna bukatar mu ƙoƙarta sosai don mu nuna wannan halin sosai. Saboda al’adarmu, wasu a cikinmu suna iya ƙin nuna tawali’u. Bugu da ƙari, mutanen da muke zaune da su suna iya cewa bai kamata mu zama masu haƙuri ba, kuma su ce mutum yana bukatar “ya yaƙi wuta da wuta.” Amma, hakan yana da kyau kuwa? Idan wani abu ya kama wuta a gidanka, za ka kashe wutan ne da māi ko da ruwa? Zuba māi a kan wutan zai ƙara ɓata al’amura ne, amma idan aka zuba ruwa hakan zai iya kashe wutan. Hakazalika, Littafi Mai Tsarki ya ba mu wannan shawarar: “Mayarda magana da taushi ya kan juyadda hasala: amma magana mai-zafi ta kan tone fushi.” (Mis. 15:1, 18) Idan wani abin ban haushi ya sake tasowa a nan gaba, wataƙila a cikin ikilisiya ko kuwa a waje, za mu nuna cewa muna da hikima ta gaske idan muka mai da martani cikin haƙuri.—2 Tim. 2:24.
10 Kamar yadda aka ambata a sama, yawancin mutanen da ruhun duniya ya yi tasiri a kansu ba su da haƙuri, ba sa son zama lafiya, kuma ba su da kwanciyar hankali. Shi ya sa mutane da yawa ba su da tausayi da sauƙin kai. Yaƙub ya san da haka, shi ya sa ya yi gargaɗi sosai saboda kada wannan mugun halin ya shafi waɗanda suke cikin ikilisiya. Menene za mu iya koya daga gargaɗin da ya yi?
Halayen Mutane Marasa Hikima
11. Waɗanne halaye ne ba su jitu da hikima ta gaskiya ba?
11 Yaƙub ya rubuta dalla-dalla irin halayen da ba su jitu da hikima ta gaskiya ba. (Ka karanta Yaƙub 3:14.) Kishi da masifa halaye ne na jiki, ba na ruhaniya ba. Yi la’akari da abin da ke faruwa sa’ad da tunani marar kyau ya sha kan mutum. Rukunonin “Kiristoci” guda shida suna da iko a kan ɓangarori dabam dabam na Cocin Kabari Mai Tsarki a Urushalima, wanda ake da’awar cewa an gina shi ne a wurin da aka kashe Yesu kuma aka binne shi. Akwai rashin jituwa a tsakanin waɗannan rukunonin. A shekara ta 2006, jaridar Time ta faɗi cewa akwai lokacin da mazan da suka keɓe kansu don zama a wannan cocin “suka yi ta yin faɗa har na awoyi, . . . suna ta bugun juna da sandar riƙe kyandir.” Saboda mugun rashin jituwar da ke tsakaninsu, hakan ya sa suka ba wani Musulmi riƙon maƙullin ƙofar cocin.
12. Idan babu hikima, menene zai iya faruwa?
12 Bai kamata irin wannan mugun rashin jituwar ta faru a cikin ikilisiyar Kirista na gaskiya ba. Duk da haka, a wasu lokatai ajizanci ya sa wasu sun nace wa ra’ayoyinsu. Hakan na iya kai ga rigima da rashin jituwa. Manzo Bulus ya lura da haka a ikilisiyar da ke Koranti, shi ya sa ya rubuta: “Gama ku masu jiki ne tukuna; gama da shi ke a cikinku akwai kishi da husuma, ba masu-jiki ba ne ku, kuna tafiya cikin al’amuran mutane kuwa?” (1 Kor. 3:3) Wannan yanayin na baƙin ciki ya ɗan daɗe yana faruwa a wannan ikilisiyar ta ƙarni na farko. Saboda haka, muna bukatar mu mai da hankali domin kada irin wannan halin ya sami shiga cikin ikilisiya a yau.
13, 14. Ka ba da misalin yadda za a iya nuna hali na jiki?
13 Ta yaya ne irin wannan halin zai iya shiga cikin ikilisiya? Zai iya somawa a wasu ƙananan hanyoyi. Alal misali, sa’ad da ake son a gina Majami’ar Mulki, mutane suna iya kawo ra’ayoyi dabam dabam na yadda za a tafiyar da abubuwa. Ɗan’uwa guda yana iya yin fushi idan aka ƙi amincewa da shawararsa, wataƙila yana iya soma sukan shawarwarin da aka yi. Yana ma iya ƙin saka hannu a aikin! Duk mutumin da ya nuna irin wannan halin ya mance ne cewa, cim ma duk wani aikin da ya shafi ikilisiya ya dangana ne a kan haɗin kan ikilisiyar ba ra’ayin mutum ɗaya ba kawai. Tawali’u ne Jehobah yake so, ba rashin haɗin kai ba.—1 Tim. 6:4, 5.
14 Wani misalin kuma shi ne, dattawa a cikin wata ikilisiya sun lura cewa wani dattijo wanda ya daɗe yana hidima, a yanzu ba ya cika farillan Nassosi da suka sa ya cancanta a dā. Domin ya lura cewa an ba ɗan’uwan shawara a dā amma ya ƙi bin shawarar, mai kula da da’ira da ya ziyarce su ya yarda cewa zai sa hannu a wasiƙar da aka rubuta na sauke shi daga matsayin dattijo. Menene ya kamata ya yi? Zai amince ne da abin da dattawan suka kammala da kuma shawarar da suka ba shi daga cikin Nassi cikin sauƙin kai da tawali’u kuma ya ƙudurta cewa zai yi abin da Nassi ya ce don ya cancanta kuma ya sake yin hidima? Ko kuwa zai nuna fushi ne da kishi don ba shi da gatan da yake da shi a dā? Me ya sa ɗan’uwa zai nace cewa ya cancanci ya zama dattijo, sa’ad da dukan sauran dattawan suka ce bai cancanta ba? Zai dace mutum ya nuna tawali’u da kuma fahimi!
15. Me ya sa kake jin cewa hurarriyar shawarar da ke Yaƙub 3:15, 16 tana da muhimmanci sosai?
15 Akwai wasu hanyoyin da za a iya nuna waɗannan halayen. Amma ko da menene zai taso, dole ne mu yi iya ƙoƙarinmu don mu guje wa waɗannan halayen. (Ka karanta Yaƙub 3:15, 16.) Almajiri Yaƙub ya kira waɗannan halayen “ta duniya,” domin na jiki ne ba na ruhaniya ba. Na “jiki” ne domin suna kama ne da halayen dabbobin da ba sa tunani. Irin waɗannan halayen na “Shaiɗan” ne domin suna nuna irin halayen aljanu maƙiyan Allah. Waɗannan halaye ne da bai kamata Kirista ya nuna ba!
16. Waɗanne canje-canje ne muke bukatar mu yi, kuma ta yaya za mu iya yin su?
16 Duk wanda ke cikin ikilisiya ya kamata ya bincika kansa sosai kuma ya kawar da irin waɗannan halayen. A matsayin malamai a cikin ikilisiya, masu kula suna bukatar su kawar da mugayen halaye daga zuciyarsu. Hakan ba shi da sauƙi saboda ajizancinmu da kuma tasirin wannan duniyar. Za a iya kwatanta hakan da yin tafiya a kan hawan da ke da santsi. Idan mutum bai riƙe wani abu ba, yana iya faɗuwa. Amma fa, za mu iya yin nasara idan muka bi shawarar da ke cikin Littafi Mai Tsarki, kuma muka yi amfani da taimakonikilisiyoyin dukan duniya na Allah suke bayarwa.—Zab. 73:23, 24.
Halayen da Masu Hikima Suke Nunawa
17. Wane mataki ne masu hikima suke ɗauka sa’ad da aka jarraba su da mugun abu?
17 Ka karanta Yaƙub 3:17. Muna iya amfana ta wajen tattauna wasu halayen da suke nuna “hikima mai-fitowa daga bisa.” Kasancewa mai tsarki ya ƙunshi kasancewa da tsabta a ayyukanmu da kuma muradinmu. Muna bukatar mu ƙi abin da ba shi da kyau nan da nan. Yin hakan ya kamata ya zama kamar abin da za mu yi ba zato ba tsammani. Wataƙila wani yana son ya tsone maka ido. Za ka kawar da kanka ne nan da nan ko kuma ka tare hannun. Wannan abu ne da za ka yi nan da nan wanda ba ka bukatar ka yi wani tunani a kai. Abin da ya kamata mu yi ke nan sa’ad da aka jarraba mu mu yi abin da bai da kyau. Ya kamata ɗabi’armu mai kyau da kuma lamirinmu da Littafi Mai Tsarki ya koyar su motsa mu mu ƙi abin da ba shi da kyau. (Rom. 12:9) Littafi Mai Tsarki ya ba da misalan waɗanda suka ɗauki wannan matakin, kamar Yusufu da Yesu.—Far. 39:7-9; Mat. 4:8-10.
18. Mecece ma’anar (a) kasancewa mai son zaman lafiya? (b) kasancewa mai son yin salama?
18 Hikima ta sama tana bukatar mu kasance masu son zaman lafiya. Hakan ya ƙunshi guje wa mugun fushi, son faɗa, ko kuwa yin abubuwan da za su jawo tashin hankali. Yaƙub ya ƙara bayyana wannan batun sa’ad da ya ce: “Ana shibka ɗiyan adilci cikin salama domin masu-yin salama.” (Yaƙ. 3:18) Yi la’akari da furcin nan “yin salama.” A cikin ikilisiya, an san mu ne a matsayin masu son salama ko kuwa masu jawo tashin hankali? Muna yawan samun rashin jituwa da mutane, mu masu saurin fushi ne ko kuwa muna yawan ɓata wa wasu rai? Muna nacewa cewa mutane su karɓe mu yadda muke, ko kuwa muna iya ƙoƙarinmu mu kawar da halayen da wasu ba sa so? Mutane sun san mu a matsayin masu son yin sulhu da wasu, masu gafartawa da wuri kuma mu mance laifin da aka yi mana? Bincika kai sosai zai taimaka mana mu ga ko muna bukatar mu nuna hikima na bisa a wannan batun.
19. Ta yaya ake sanin cewa mutum yana nuna sanin ya kamata?
19 Yaƙub ya ambata sanin ya kamata a cikin kwatancin da ya bayar na abubuwan da ke nuna hikima na sama. An san mu da bin shawarar wasu idan hakan bai taka mizanan Nassi ba, kuma ba ma saurin nacewa cewa mutane su bi shawararmu? Mutane sun san cewa mu masu sauƙin hali ne kuma wanda za a iya tattauna da shi? Hakan zai tabbatar da cewa muna nuna sanin ya kamata.
20. Wane sakamako ne za mu samu idan muka nuna halaye masu kyau da muka tattauna?
20 Yanayi zai kasance mai daɗi a cikin ikilisiya idan ’yan’uwa maza da mata suka ci gaba da yin iya ƙoƙarinsu wajen nuna halaye masu kyau da Yaƙub ya rubuta! (Zab. 133:1-3) Kasancewa masu tawali’u, masu son zaman lafiya, da kuma nuna sanin ya kamata ga juna zai kyautata dangantakarmu sosai kuma hakan zai nuna cewa muna da “hikima mai-saukowa daga bisa.” A talifi na gaba za mu koyi yadda ɗaukan mutane yadda Jehobah ya ɗauke su zai taimaka mana a wannan batun.
[Hasiya]
a Wannan bayanin ya nuna cewa ainihi Yaƙub yana yin magana ne ga dattawa, ‘masu koyarwa,’ a cikin ikilisiya. (Yaƙ. 3:1) Ya kamata waɗannan mazan su kafa misali wajen nuna irin hikimar da Allah yake so, duk da haka, mu duka muna iya bin shawararsa.
Za Ka Iya Bayyanawa?
• Menene zai sai Kirista ya kasance mai hikima sosai?
• Ta yaya za mu iya nuna hikimar da Allah yake so sosai?
• Waɗanne halaye ne waɗanda ba su da “hikima mai-saukowa daga bisa” suke nuna wa?
• Waɗanne halaye ne ka ƙudurta cewa za ka ci gaba da nuna wa sosai?
[Hoto a shafi na 23]
Ta yaya ne rashin jituwa zai iya shiga tsakaninmu a yau?
[Hoto a shafi na 24]
Halin ka ne ƙin mugunta nan da nan?