Mu Ci Gaba Da Yin Alheri A Duniya Ta Ƙiyayya
“Gwargwadon alherin mutum a ke sonsa.”—MISALAI 19:22.
1. Me ya sa zai yi wuya a yi alheri?
KANA ganin kai mai alheri ne? Idan haka ne zama a duniyar yau zai yi wuya. Hakika, a cikin Littafi Mai Tsarki alheri yana cikin ‘ ’ya’yan ruhu,’ amma me ya sa yake da wuya a yi alheri har ma cikin ƙasashe da wai ake Kiristanci? (Galatiyawa 5:22) Yadda muka gani a talifi da ya gabata, za a iya samun amsar kaɗan cikin abin da manzo Yohanna ya rubuta—dukan duniya tana hannun halittar ruhu da ba ya kirki, Shaiɗan Iblis. (1 Yohanna 5:19) Yesu Kristi ya ce Shaiɗan ne “sarkin duniya.” (Yohanna 14:30) Da haka, wannan duniyar tana kama da mai sarautarsa ɗan tawaye, wanda yake da mugun hali.—Afisawa 2:2.
2. Waɗanne abubuwa za su sa ba za mu yi alheri ba?
2 Yana shafan rayuwarmu sosai sa’ad da wasu ba su yi mana alheri ba. Mai yiwuwa, maƙwabta masu ƙiyayya, baƙi da ba sa abokantaka, har abokai da waɗanda suke cikin iyali da wani lokaci suna abu da garaje ba za su yi mana alheri ba. Matsin saduwa da mutane da suke taurin kai da kuma waɗanda suke zargin juna sau da yawa yana kawo baƙin ciki. Irin wannan rashin alheri da wasu suke nunawa zai sa mu yi ƙiyayya mu kanmu, muna iya jin mu rama rashin alheri da rashin alheri. Irin wannan zai iya sa mu samu matsalolin rashin lafiya na ruhaniya da na zahiri.—Romawa 12:17.
3. Waɗanne matsaloli masu tsanani mutane da suke son su yi alheri ke fuskanta?
3 Yanayi mai wuya na duniya zai iya sa yin alheri ya yi mana wuya. Alal misali, dukan ’yan Adam sun gaji da burga na ta’addanci da kuma ayyukan ta’addanci, makamai masu yaɗa cututtuka da na nukiliya da rukuni dabam dabam da al’umma suke amfani da su. Ƙari ga haka, miliyoyin mutane suna talauci, suna rayuwa ta cin ɗan abinci, rashin isashen wurin kwanciya, tufafi, da kuma kulawa da lafiyar jiki. Yin alheri ya zama ƙalubale tun da babu begen kyautata yanayin.—Mai-Wa’azi 7:7.
4. Yaya wasu za su kammala yadda bai dace ba sa’ad da ake maganar yi wa wasu alheri?
4 Mutum zai iya kammala da sauƙi cewa yin alheri ba shi da muhimmanci kuma zai iya zama alamar kumamanci. Zai iya jin cewa an zalunta shi, musamman sa’ad da wasu suka bi da shi ba tare da yin la’akari da yadda yake ji ba. (Zabura 73:2-9) Amma, Littafi Mai Tsarki ya ba mu ja-gora da ta dace sa’ad da ya ce: “Mayarda magana da taushi ya kan juyadda hasala: amma magana mai-zafi ta kan tone fushi.” (Misalai 15:1) Taushin hali da alheri fannoni biyu ne na ’ya’yan ruhu da suke da nasaba ta kusa kuma suna taimakonmu sa’ad da muke bi da yanayi mai wuya.
5. A waɗanne wurare na rayuwa ake bukatar alheri?
5 Tun da yake nuna ’ya’yan ruhu mai tsarki na Allah yana da muhimmanci a gare mu Kiristoci, ya kamata mu bincika yadda za mu nuna ɗaya cikin waɗannan halaye—alheri. Zai yiwu a biɗi alheri a duniya ta ƙiyayya? Idan haka ne, a waɗanne wurare ne za mu nuna cewa ba ma ƙyale tasirin Shaiɗan ya sha kan alherinmu, musamman a yanayi mai wuya? Bari mu bincika yadda za mu yi alheri a cikin iyali, a wajen aiki, a makaranta, da maƙwabtanmu, a hidimarmu, da kuma tsakanin ’yan’uwa masu bi.
Alheri Cikin Iyali
6. Me ya sa alheri cikin iyali yake da muhimmanci sosai, kuma yaya za a yi shi?
6 Don mu samu albarka da ja-gorar Jehovah, ’ya’yan ruhu suna da muhimmanci kuma ana bukatar a koye su sosai. (Afisawa 4:32) Bari mu mai da hankali a bukatar waɗanda suke cikin iyali su yi wa juna alheri. A sha’ani na yau da kullum, ya kamata mata da miji su kasance da halin kulawa da yi wa juna alheri da kuma yaransu. (Afisawa 5:28-33; 6:1, 2) Ya kamata a ga irin wannan alheri a yadda waɗanda suke cikin iyali suke wa juna magana, yara suna daraja kuma yi wa iyayensu ladabi iyaye kuma suna bi da yaransu yadda ya dace. Ku yi saurin yaba musu, amma kada ku yi saurin hukunta su.
7, 8. (a) Wane irin hali za mu guje wa idan za mu nuna alheri na gaskiya a cikin iyali? (b) Ta yaya yin magana da kyau zai sa iyali ta kasance da gami mai kyau? (c) Ta yaya za ka yi alheri cikin iyalinka?
7 Yi wa waɗanda suke cikin iyalinmu alheri ya ƙunshi bin gargaɗin manzo Bulus: “Ku kawarda dukan waɗannan; fushi, hasala, ƙeta, tsegumi, alfasha daga cikin bakinku.” Kowacce rana, iyalan Kirista ya kamata su yi magana da juna da ladabi. Me ya sa? Domin idan iyalai za su yi farin ciki yin magana da kyau yana da muhimmanci. Sa’ad da jayayya ta taso, a rage fāɗan, a yi ƙoƙari a warware matsalar maimako a ci nasarar musun. Waɗanda suke cikin iyali masu farin ciki suna ƙoƙari su ɗaukaka alheri da kuma yin la’akari da juna.—Kolossiyawa 3:8, 12-14.
8 Alheri yana da kyau kuma yana sa mu so mu yi wa wasu abu mai kyau. Da haka, muna nema mu kasance da amfani ga waɗanda suke cikin iyali, muna la’akari, kuma muna taimaka musu. Yana bukatar ƙoƙarin dukan mutane su yi irin wannan alheri da yake kawo wa iyali daraja. Domin haka, ba kawai za su samu albarkar Allah ba, amma a cikin ikilisiya da kuma yankin da suke, za su ɗaukaka Jehovah Allah wanda ya fi yin alheri.—1 Bitrus 2:12.
Alheri a Wajen Aiki
9, 10. Ka kwatanta wasu matsaloli da za su iya tasowa a wajen aiki, ka faɗa yadda za a warware su a hankali.
9 Ga Kirista, wajen aiki zai iya kawo ƙalubale na yi wa abokan aiki alheri. Gasa tsakanin masu aiki zai sa wani abokin aiki da yake ha’inci ko dabara ya ɓata aikin mutumin, wannan zai ɓata sunan mutumin a gaban mai gidan aikin. (Mai-Wa’azi 4:4) Ba shi da sauƙi a yi alheri a wannan yanayi. Duk da haka, tuna cewa yin kirki abu mai kyau ne da za a yi, ya kamata bawan Jehovah ya yi iyakacin ƙoƙarinsa ya rinjayi waɗanda ba shi da sauƙi a yi tarayya da su. Nuna halin kulawa zai taimake mu mu yi haka. Wataƙila za ka nuna ka damu idan abokin aikin yana ciwo ko kuma wani cikin iyalinsa yana ciwo. Tambayar yadda wani ko iyalin yake zai kasance da tasiri mai kyau ga mutumin. Hakika, ya kamata Kiristoci su nemi su ɗaukaka haɗin kai da salama gwargwadon iyawarsu. Wani lokaci kalmomin alheri da suke nuna kulawa da damuwa za su taimaka a yanayin.
10 A wani lokaci kuma, mai gidan aiki zai nanata ra’ayoyinsa a kan ma’aikatan kuma zai so kowa ya sa hannu a wani biki na ƙasa ko kuma wanda ba na Nassi ba ne. Sa’ad da lamiri na Kirista bai ƙyale shi ya sa hannu ba, wannan zai sa mai wajen aikin ya yi masa magana. A lokacin ba zai dace ba ka bayyana dalla-dalla yadda ba zai yi kyau ba ka yi abin da mai wajen aikinka yake so. Ballantana ma, waɗanda ba sa bin imaninka na Kirista, bikin da ake yi mai yiwuwa abu mai kyau ne gare su. (1 Bitrus 2:21-23) Wataƙila za ka iya bayyana a hankali dalilin da ya sa ba ka sa hannu ba. Kada ka rama baƙar magana da aka yi maka da baƙar magana. Yana da kyau Kirista ya bi shawara mai kyau na Romawa 12:18: “Idan ya yiwu, ku zama lafiya da dukan mutane, gwargwadon iyawarku.”
Alheri a Makaranta
11. Waɗanne ƙalubale matasa suke fuskanta a yin alheri da abokan makaranta?
11 Zai iya kasance ƙalubale sosai matasa su yi wa abokan makaranta alheri. Matasa sau da yawa suna son abokan ajinsu su amince da su. Wasu yara maza suna aikata da zafin hali domin wasu ’yan makaranta su yi sha’awarsu, har su razanar da wasu a makaranta ma. (Matta 20:25) Wasu matasa suna so su burge wasu da iyawarsu, a wasan guje-guje, ko kuma wasu ayyuka. Wajen nuna iyawarsu, sau da yawa ba sa yi wa ’yan ajinsu da wasu abokan makaranta kirki, suna tunani cewa wannan zai sa su fi wasu. Ya kamata matashi Kirista ya mai da hankali kada ya yi koyi da waɗannan mutane. (Matta 20:26, 27) Manzo Bulus ya ce “ƙauna tana da yawan haƙuri, tana da nasiha” ya kuma ce ƙauna “ba ta yin fahariya, ba ta yin kumbura.” Shi ya sa, bai kamata Kirista ya bi mummunar misali na waɗanda ba sa alheri ba, amma ya manne wa gargaɗi na Nassi a sha’aninsa da abokan makaranta.—1 Korinthiyawa 13:4.
12. (a) Me ya sa zai kasance ƙalubale matasa su yi wa malamansu alheri? (b) Matasa za su dogara da wanene don taimako sa’ad da aka matsa musu kada su yi alheri?
12 Ya kamata matasa su yi wa malamansu alheri. Yaran makaranta da yawa suna jin daɗin sa malamansu su ji haushi. Suna jin suna da wayo sa’ad da suna ƙin yi wa malamansu biyayya ta yin ayyuka da suka taka dokokin makaranta. Ta wurin razanar da wasu, za su iya sa su bi su. Sa’ad da matashi Kirista ya ƙi ya bi su, shi ko ita za ta zama abin ba’a ko kuma zagi. Fuskantar irin wannan yanayi a shekarun da yake makaranta zai gwada niyyar Kirista na yin alheri. Amma ka tuna cewa yana da muhimmanci ka zama bawa mai aminci na Jehovah. Ka tabbata cewa zai goyi bayanka ta ruhunsa a waɗannan lokaci mai wuya a rayuwa.—Zabura 37:28.
Alheri ga Maƙwabta
13-15. Menene zai iya hana mu yi wa maƙwabtanmu alheri, amma yaya za a bi da waɗannan ƙalubale?
13 Ko kana zama a gida, ruga, ko wani waje, za ka iya tunanin hanyoyi da za ka yi alheri da damuwa ga zaman lafiyar maƙwabtanka. Har ila, wannan ma ba koyaushe yake da sauƙi ba.
14 Idan maƙwabtanka ba sa sonka domin ƙabilarka, ƙasarka, ko kuma addininka kuma fa? Idan suna taurin kai wani lokaci ko kuma suna banza da kai kuma fa? Da yake kai bawan Jehovah ne, yin alheri yadda zai yiwu zai kasance da amfani. Za ka kasance dabam, wanda yake yabon Jehovah da gaske—wanda yake da misali mai kyau a yin alheri. Ba ka san sa’ad da maƙwabcin zai canja halinsa domin alherinka ba. Zai iya zama mai bauta wa Jehovah.—1 Bitrus 2:12.
15 Yaya za a yi wa maƙwabta alheri? Ta hali mai kyau cikin iyali yayin da dukan waɗanda suke cikin iyali suke nuna ’ya’yan ruhu. Ƙila maƙwabtanka za su iya lura da wannan. Wasu lokatai, za ka iya yi ma maƙwabcinka abin kirki. Ka tuna cewa alheri na nufin nuna son zaman lafiyar wasu sosai.—1 Bitrus 3:8-12.
Alheri a Hidimarmu
16, 17. (a) Me ya sa alheri yake da muhimmanci a hidimarmu ta fage? (b) Ta yaya za a yi alheri a fannoni dabam dabam na hidimar fage?
16 Ya kamata muna alheri a hidimarmu ta Kirista yayin da muke ƙoƙari sosai mu sami mutane a gidajensu, wajen aikinsu, da kuma inda jama’a suke. Ya kamata mu tuna cewa muna wakiltan Jehovah, wanda koyaushe yana alheri.—Fitowa 34:6.
17 Menene ƙoƙarce-ƙoƙarcenka ka yi alheri a hidimarka ya ƙunsa? Alal misali, sa’ad da kake wa’azi na titi titi za ka iya alheri ta gajerta maganarka kuma kana la’akari sa’ad da ka je wajen mutane. Mutane suna yawa a gefen titi, saboda haka ka yi hankali kada ka tare mutane a gefen titi. Sa’ad da kake wa’azi a yankin da ake kasuwanci, ka yi alheri ta wurin gajerta maganarka, ka tuna cewa masu kanti za su biya bukatar masu ciniki.
18. Yaya basira za ta taimake mu mu yi alheri a hidimarmu?
18 A hidima ta gida gida, ka kasance da basira. Kada ka jima ainu a wani gida, musamman idan yanayin ba mai kyau ba ne. Za ka iya gane sa’ad da mutum ya gaji da kai? Wataƙila a inda kuke zama, Shaidun Jehovah suna zuwan gidajen mutane sau da yawa. Idan haka ne, ka yi la’akari sosai, kana kirki koyaushe kuma kana abubuwa da za su sa mutane su amince da kai. (Misalai 17:14) Ka yi ƙoƙari ka fahimci dalilin da ya sa maigidan ba ya son ya saurara a wannan ranar. Ka tuna, ɗaya cikin ’yan’uwanka Kirista za su iya zuwan gidan ba da daɗewa ba. Idan ka sadu da wani da yake da taurin kai, ka yi ƙoƙari ka yi alheri. Kada ka ta da muryarka ko kuma ka ɓata fuska, amma ka yi magana da kwanciyar hankali. Kirista da yake kirki ba zai so ya sa su soma musu da maigidan ba. (Matta 10:11-14) Wataƙila wata rana wannan mutumin zai saurari bisharar.
Alheri a Taron Ikilisiya
19, 20. Me ya sa ake bukatar alheri a ikilisiya, kuma yaya za a yi shi?
19 Yana da muhimmanci kuma a yi alheri ga ’yan’uwa masu bi. (Ibraniyawa 13:1) Tun da yake muna cikin ’yan’uwanci na dukan duniya, alheri yana da muhimmanci a sha’aninmu da juna.
20 Idan ikilisiya tana amfani da Majami’ar Mulki da ikilisiyoyi ɗaya, biyu, ko fiye da haka, yana da muhimmanci a bi da waɗanda suke sauran ikilisiyoyin da kyau, ana bi da su da daraja. Halin jayayya na kawo rashin haɗin kai sa’ad da ya zo ga shirya lokacin taro da kuma shara ko kuma adana ginin. Ka yi kirki da kuma la’akari ko da za a sami ra’ayi dabam dabam. A wannan hanya alheri zai ci nasara, kuma Jehovah zai albarkaci yadda kake son zaman lafiyar wasu.
Ka Ci Gaba da Yin Alheri
21, 22. Daidai da Kolossiyawa 3:12, me ya kamata mu ƙudura niyyar yi?
21 Alheri hali ne da ya shafi dukan fannonin rayuwarmu. Saboda haka, ya kamata mu sa ya zama ɓangare na musamman ta mutuntakarmu na Kirista. Yin alheri ga wasu ya kamata ya zama halinmu.
22 Bari dukanmu mu yi wa mutane alheri kowacce rana kuma kowanenmu ya yi amfani da kalmomin manzo Bulus: “Ku fa, domin ku zaɓaɓu na Allah ne, masu-tsarki, ƙaunatattu kuma, ku yafa zuciya ta tausayi, nasiha, tawali’u, ladabi, jimrewa.”—Kolossiyawa 3:12.
Ka Tuna?
• Me ya sa yake wuya Kirista ya yi alheri?
• Me ya sa yake da muhimmanci mutum ya yi alheri cikin iyalinsa?
• Me zai sa ya yi wuya a yi alheri a makaranta, wajen aiki, kuma ga maƙwabta?
• Ka bayyana yadda Kiristoci za su yi alheri a hidimarsu ta fage.
[Hoto a shafi na 11]
Idan dukan waɗanda suke cikin iyali suka yi alheri zai kawo salama da haɗin kai
[Hoto a shafi na 12]
Za ka iya yin alheri sa’ad da abokin aikinka ko wani cikin iyalinsa yana ciwo
[Hoto a shafi na 13]
Jehovah yana goyon bayan waɗanda cikin aminci suna alheri duk da ba’a
[Hoto a shafi na 14]
Taimakon maƙwabciya da take da bukata yin alheri ne