Dole Mutanen Allah Su So Alheri
“Me ne Ubangiji ya ke biɗa gareka kuma, sai aikin gaskiya, da son jinƙai, ka yi tafiya da tawali’u tare da Allahnka?”—MIKAH 6:8.
1, 2. (a) Me ya sa ba za mu yi mamaki ba cewa Jehovah ya bukaci mutanensa su yi alheri? (b) Waɗanne tambayoyi game da alheri ya kamata mu bincika?
JEHOVAH Allah ne mai alheri. (Romawa 2:4; 11:22) Babu shakka, ma’aurata na farko, Adamu da Hauwa’u sun ji daɗin alherinsa! A cikin lambu na Adnin, halittu da ake gani da suka nuna tabbacin alherin Allah sun gewaye mutane, da yake sune za su iya jin daɗin waɗannan. Kuma Allah ya ci gaba da yi wa dukan mutane alheri, har da miyagu da marasa godiya.
2 Da yake an halicce su cikin siffar Allah, mutane suna iya nuna halaye na ibada. (Farawa 1:26) Ba abin mamaki ba ne, da Jehovah yake bukatar mu yi alheri. Yadda Mikah 6:8 ta ce, dole mutanen Allah su ‘so jinƙai’ ko alheri. Amma menene alheri? Ta yaya yake da nasaba da wasu halaye na ibada? Tun da yake mutane suna iya yin alheri, me ya sa duniya ta zama wuri mai wuyan zama? Me ya sa mu Kiristoci ya kamata mu yi ƙoƙari mu yi alheri a sha’aninmu da wasu?
Menene Alheri?
3. Yaya za ka ba da ma’anar alheri?
3 Ana yin alheri ta nuna son zaman lafiyar wasu. Ana yinsa kuma ta ayyukan taimako da kuma kalmomi na sanin ya kamata. A yi alheri yana nufin a yi nagarta maimakon abu mai lahani. Mai alheri yana da halin abokantaka, tawali’u, yana tausayi, kuma yana kirki. Yana da halin karimanci, da la’akari da wasu. Manzo Bulus ya yi wa Kiristoci gargaɗi: “Ku yafa zuciya ta tausayi, nasiha, tawali’u, ladabi, jimrewa.” (Kolossiyawa 3:12) Saboda haka, alheri tufa ce ta alama na kowane Kirista na gaskiya.
4. Ta yaya Jehovah ya soma yi wa ’yan Adam alheri?
4 Jehovah Allah shi ne ya soma yin alheri. Yadda Bulus ya faɗa, sa’ad da “nasihar Allah Mai-cetonmu, da ƙaunarsa zuwa mutane, suka bayyana” ne “ya cece mu, ta wurin wankan maya-haihuwa da sabontuwar Ruhu Mai-tsarki.” (Titus 3:4, 5) Allah ya ‘wanke,’ ko tsarkake shafaffun Kiristoci da jinin Yesu, ya yi amfani da fa’idodin hadayar fansa ta Kristi dominsu. Ruhu mai tsarki ya kuma sabonta su, sun zama “sabon halitta” ’ya’yan Allah da aka haifa ta ruhu. (2 Korinthiyawa 5:17) Ban da haka, Allah ya yi alheri da kuma ƙauna wa “taro mai-girma,” da “suka wanke rigunansu, suka faranta su cikin jinin Ɗan ragon kuma.”—Ru’ya ta Yohanna 7:9, 14; 1 Yohanna 2:1, 2.
5. Me ya sa waɗanda ruhun Allah ke musu ja-gora za su yi alheri?
5 Alheri yana cikin ’ya’yan ruhu mai tsarki na Allah, ko kuma ikon aiki. Bulus ya ce: “Ɗiyan Ruhu ƙauna ne, farinciki, salama, tsawon jimrewa, nasiha, nagarta, aminci, tawali’u, kamewa: irin waɗannan babu shari’a a kansu.” (Galatiyawa 5:22, 23) Tun da haka ne, bai kamata waɗanda ruhun Allah ke musu ja-gora su yi alheri ga wasu ba?
Alheri na Gaske Ba Kumamanci Ba Ne
6. Yaushe ne alheri yake zama kumamanci, me ya sa?
6 Wasu mutane suna ɗaukan yin alheri kumamanci ne. Suna jin cewa ya kamata mutum ya yi taurin kai a wasu lokatai, don wasu su ga ƙarfin halinsa. A gaskiya kam, yana bukatar ƙoƙari sosai don a yi alheri kuma a guje ɓata alheri. Tun da yake alheri na gaske yana cikin ’ya’yan ruhun Allah, ba zai zama kumamanci ba, ƙyale munanan hali. A wata sassa, ɓata alheri kumamanci ne da ke sa mutum ya yi na’am da laifi.
7. (a) Ta yaya Eli ya yi sakaci a yin horo? (b) Me ya sa dole dattawa su guje ɓata alheri?
7 Alal misali, ka yi la’akari da Eli, babban firist na Isra’ila. Bai yi wa ’ya’yansa Hofni da Finehas da suke aiki na babban firist a mazauni horo ba. Domin ba su gamsu ba da abin da Dokar Allah ta ce a ba su, sun gaya wa ɗan atenda ya gaya wa mai yin hadayar ya ba su ɗanyen nama kafin a ƙone kitsen a kan bagadi. ’Ya’yan Eli sun yi fasikanci da mata da suke hidima a kofar mazaunin. Maimakon ya sallami Hofni da Finehas daga aiki, Eli ya ɗan yi musu magana kawai. (1 Samu’ila 2:12-29) Ba abin mamaki ba da “maganar Ubangiji kuma da wuya ce a waɗannan kwanaki”! (1 Samu’ila 3:1) Dole dattawa Kirista su mai da hankali kada su ɓata alheri wajen masu laifi da za su iya saka ruhaniyar ikilisiya cikin haɗari. Alheri na gaske ba ya ƙyale munanan kalmomi da ayyuka da suke ɓata mizanan Allah.
8. Ta yaya Yesu ya nuna alheri na gaske?
8 Yesu Kristi, wanda muke bin misalinsa bai ɓata alheri ba. Amma, shi ne ya ba da misali mafi kyau na alheri na gaske. Alal misali, “ya yi juyayi a kan [mutanen], domin suna wahala, suna watse kuma, kamar tumakin da ba su da makiyayi.” Mutane masu zuciyar kirki ba su ji tsoron zuwa wajen Yesu ba, har ma sun kai masa yaransu ƙanana. Ka yi tunanin alheri da juyayi da ya nuna sa’ad da “ya rungume su, ya sa musu albarka, ya ɗibiya musu hannuwa.” (Matta 9:36; Markus 10:13-16) Ko da Yesu yana da kirki, ya yi tsayin daka ga abin da ke na gaskiya a gaban Ubansa na samaniya. Yesu bai goyi bayan mugunta ba; da gaba gaɗi daga wurin Allah ya hukunta shugabanan addinai masu riya. Yadda yake a Matta 23:13-26, sau da yawa ya maimaita hukunci: “Kaitonku, ku marubuta da Farisawa, masu-riya!”
Alheri da Wasu Halaye na Ibada
9. Yaya alheri yake da nasaba da tsawon jimrewa da nagarta?
9 Alheri yana da nasaba da wasu halaye da ruhun Allah yake haifarsu, kamar tsawon jimrewa da nagarta. Hakika, wanda yake yin alheri yana nuna wannan hali ta tsawon jimrewa. Yana haƙuri har da mutane da ba sa kirki. Alheri yana da nasaba da nagarta yayin da ake yin sa sau da yawa ta ayyukan taimako don amfanin wasu. Wani lokaci, kalmar Helenanci da aka yi amfani da ita cikin Littafi Mai Tsarki don ‘alheri’ za a iya fassara ta “nagarta.” Wannan halin tsakanin Kiristoci na farko ya ba arna mamaki, in ji Tertullian, sun kira waɗancan mabiyan Yesu ‘mutane da yin alheri ya fi musu muhimmanci.’
10. Ta yaya alheri da ƙauna suke da nasaba?
10 Da akwai nasaba tsakanin alheri da ƙauna. Yesu ya ce game da mabiyansa: “Bisa ga wannan mutane duka za su fahimta ku ne almajiraina, idan kuna da ƙauna ga junanku.” (Yohanna 13:35) Kuma game da wannan ƙaunar Bulus ya ce: “Ƙauna tana da yawan haƙuri, tana da nasiha.” (1 Korinthiyawa 13:4) Alheri kuma yana da nasaba da ƙauna da yake an kwatanta shi sau da yawa da kalmar ‘ƙauna ta alheri.’ Wannan alheri ne da ya fito daga ƙauna ta aminci. Isimin Ibrananci da aka fassara ‘ƙauna ta alheri’ ya fi nuna juyayi. Alheri ne da ke manne wa abu har sai ya cim ma nufinsa game da abin. Jehovah ya nuna ƙauna ta alheri ko ƙauna ta aminci a hanyoyi dabam dabam. Alal misali, an ga wannan cikin ayyukansa na ceto da kuma kāriya.—Zabura 6:4; 40:11; 143:12.
11. Wane tabbaci ƙauna ta alheri na Allah ya ba mu?
11 Ƙauna ta alheri na Jehovah na jawo mutane wajensa. (Irmiya 31:3) Sa’ad da bayin Allah masu aminci suke bukatar ceto ko kuma taimako, sun sani cewa zai nuna musu ƙauna ta alheri. Sun tabbata cewa zai nuna musu ƙaunarsa ta alheri. Saboda haka, za su yi addu’a kuma su kasance da bangaskiya, yadda mai Zabura ya yi: “Amma na dogara ga jinƙanka; Zuciyata za ta yi murna cikin cetonka.” (Zabura 13:5) Tun da yake ƙaunar Allah tana da aminci, bayinsa za su iya dogara gare shi ƙwarai. Suna da wannan tabbaci cewa: “Ubangiji ba za ya yarda mutanensa ba: ba kuwa za ya yi ɓari da gādonsa ba.”—Zabura 94:14.
Me Ya Sa Zalunci Ya Yi Yawa a Duniya?
12. Yaushe ne kuma ta yaya sarauta ta zalunci ta soma?
12 Amsar wannan tambaya ta ƙunshi abin da ya faru a lambun Adnin. Ba da daɗewa ba bayan somawar tarihin mutane, wani halittar ruhu da ya zama mai son kai da girman kai ya soma wani ƙulli ya zama masaraucin duniya. Domin ƙullinsa, ya zama “mai-mulkin wannan duniya,” hakika na zalunci. (Yohanna 12:31) Aka san shi da Shaiɗan Iblis, uban hamayyar Allah da mutum. (Yohanna 8:44; Ru’ya ta Yohanna 12:9) Ƙullinsa na son kai don ya kafa sarauta daidai da na Jehovah ya bayyana jim kaɗan bayan an halicce Hauwa’u. Da haka, muguwar sarauta ta soma sa’ad da Adamu ya zaɓi hanyar ’yancin kai daga sarautar Allah, ya ƙi da alherinsa gabaki ɗaya. (Farawa 3:1-6) Maimakon su samu ’yanci na gaske, Adamu da Hauwa’u sun kasance cikin tasiri na son kai da fahariya na Iblis, sun zama talakawan sarautarsa.
13-15. (a) Menene wasu sakamakon ƙin sarautar Jehovah ta adalci? (b) Me ya sa duniya ta zama matsanancin wuri?
13 Bari mu yi la’akari da wasu cikin sakamakon. An kori Adamu da Hauwa’u daga gefen duniya da aljanna ce. Yanayinsu ya canja daga zama a lambu mai kyau da ke da tsiro da ’ya’yan itace masu kyau zuwa yanayi mai wuya waje da lambun Adnin. Allah ya ce wa Adamu: “Don ka lura da muryar matarka, har ka ci kuma daga cikin itacen, wanda na dokace ka, cewa, ba za ka ci shi ba; sabili da kai an la’anta ƙasa; da wahala za ka ci daga cikinta duk muddar ranka; Ƙayayuwa da sarƙaƙiya za ta haifa maka.” La’ana da aka yi wa ƙasa tana nufin cewa yin noma a ciki zai yi wuya sosai. Sakamakon ƙasa da aka la’anta da ƙayoyinta da sarƙaƙƙiya sun shafi zuriyar Adamu sosai har da baban Nuhu, Lamech, ya yi maganar ‘aikinsu da wahalar hannuwansu, da ya fito daga ƙasa wadda Ubangiji ya la’anta.’—Farawa 3:17-19; 5:29.
14 Adamu da Hauwa’u sun yi musanyar kwanciyar hankali da wahala. Allah ya ce wa Hauwa’u: “Zan yawaita baƙincikinki ƙwarai da juna biyunki; da baƙinciki za ki haifi ’ya’ya; nufinki kuma za ya komo wurin mijinki, za shi kuwa shugabance ki.” Bayan haka, Kayinu ɗan fari na Adamu da Hauwa’u, ya yi zalunci ya kashe ɗan’uwansa Habila.—Farawa 3:16; 4:8.
15 “Duniya duka kuwa tana kwance cikin Shaiɗan,” in ji manzo Yohanna. (1 Yohanna 5:19) Domin shi sarkinta ne, duniya a yau tana nuna mugun halaye da ya haɗa da son kai da girman kai. Ba abin mamaki ba ne da tsananci da zalunci sun cika duniya! Amma ba haka zai kasance har abada ba. Jehovah zai tabbata cewa alheri da juyayi, za su kasance a Mulkinsa maimakon tsananci da zalunci.
Za a Yi Alheri Sosai a Mulkin Allah
16. Me ya sa za a yi alheri a sarautar Allah ta wurin Kristi Yesu, kuma wannan ya sa mu kasance da hakkin yin menene?
16 Jehovah da Sarkin da ya zaɓa na Mulkinsa, Kristi Yesu, suna bukata a san da talakawansu ta wurin alherinsu. (Mikah 6:8) Yesu Kristi ya nuna mana yadda alheri zai kasance a sarautar da Ubansa ya danƙa masa. (Ibraniyawa 1:3) Za a lura da wannan a kalmomin Yesu da ya fallasa shugabanan addinin ƙarya, da suka zalunta mutanen da kaya masu nauyi. Ya ce: “Ku zo gareni, dukanku da ku ke wahala, masu-nauyin kaya kuma, ni kuwa in ba ku hutawa. Ku ɗauka ma kanku karkiyata, ku koya daga wurina; gama ni mai-tawali’u ne, mai-ƙasƙantar zuciya: za ku sami hutawa ga rayukanku. Gama karkiyata mai-sauƙi ce, kayana kuma marar-nauyi.” (Matta 11:28-30) Dukan masu sarautar duniya, da suke bin addini ko waɗanda ba sa bi, suna nauyaya mutane da dokoki marasa iyaka da kuma ayyuka da ba sa nuna halin godiya. Amma, abin da Yesu yake bukata daga wajen mabiyansa yana gamsar da bukatunsu kuma za su iya yi. Babu shakka, karkiyarsa tana wartsakewa kuma mai sauƙi ce! Ba mu motsa mu zama kamarsa a yin alheri ga wasu ba ne?—Yohanna 13:15.
17, 18. Me ya sa za mu tabbata cewa waɗanda za su yi sarauta da Kristi a sama da kuma wakilansa a duniya za su yi alheri?
17 Kalmomin Yesu ga manzanninsa ya taƙaita yadda Mulkin Allah zai bambanta sosai da na mutum. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Maƙagara kuma ta tashi a tsakaninsu [almajiransa], ko wanene a ke maishe shi babba a cikinsu. Shi kuwa ya ce musu, Sarakunan Al’ummai suna da sarauta bisansu; su kuma waɗanda suna da hukunci bisansu, ana ce da su Masu-kyautawa. Amma ku ba haka za ku yi ba: amma shi wanda shi ke babba a cikinku, shi zama kamar auta; wanda shi ke magabci kuma shi zama kamar wanda ya ke bauta. Gama wanene ya fi girma mai-zama wurin abinci, ko kuwa mai-hidima? ba shi ne ba wanda ya ke zaune wurin abinci? Amma ni ina nan a cikinku kamar mai-hidima.”—Luka 22:24-27.
18 ’Yan Adam masu sarauta suna nema su kafa nasu girma ta yin ‘sarauta bisa’ mutane da kuma neman laƙabi mai girma, suna gaskata cewa irin wannan laƙabi yana sa su fi waɗanda suke ƙarƙashin sarautarsu. Amma Yesu ya ce girma ta gaske tana zuwa daga yi wa wasu hidima—yin ƙwazo da kuma nacewa a ƙoƙarin yi wa wasu hidima. Dukan waɗanda za su yi sarauta da Kristi a sama ko kuma waɗanda za su wakilce shi a duniya dole su yi ƙoƙari su bi misalinsa na tawali’u da kuma alheri.
19, 20. (a) Ta yaya Yesu ya nuna yawan alherin Jehovah? (b) Ta yaya za mu yi koyi da Jehovah a yin alheri?
19 Bari mu duba wasu gargaɗi masu kyau da Yesu ya ba da. Da yake nuna yawan alherin Jehovah, Yesu ya ce: ‘Idan kuwa kuna ƙaunar masu-ƙaunarku, wane abin godiya ke gareku? gama har da masu-zunubi suna ƙaunar masu-ƙaunarsu. Idan kuma kuna yin nagarta ga waɗanda su ke yi muku nagarta, wane abin godiya ke gareku? gama har da masu zunubi suna yin wannan. Idan kuwa kuna bada rance ga waɗanda ku ke sa zuciya za ku samu a garesu, wane abin godiya ke gareku? har da masu-zunubi suna bada rance ga masu-zunubi, domin su samu kuma misalin abin da suka bayar. Amma ku yi ƙaunar magabtanku, ku yi musu nagarta, ku bada rance, kada ku fidda zuciya daɗai; ladarku kuwa mai-girma ce, za ku zama ’ya’yan Maɗaukaki, gama shi mai-alheri ne ga marasa-godiya da miyagu. Ku zama masu-jinƙai, kamar yadda Ubanku mai-jinƙai ne.’—Luka 6:32-36.
20 Alheri na ibada ba ya son kai. Ba ya neman lada. Jehovah cikin alheri “ya kan sa ranatasa ta fito ma miyagu da nagargaru, ya kan aiko da ruwa bisa masu-adalci da marasa-adalci.” (Matta 5:43-45; Ayukan Manzanni 14:16, 17) Ta yin koyi da Ubanmu na samaniya, ba kawai mu guje yi wa marasa godiya lahani ba amma muna yi musu nagarta, har waɗanda suka nuna cewa su magabtanmu ne. Ta yin alheri, muna nuna wa Jehovah da Yesu cewa muna son mu yi rayuwa a Mulkin Allah, sa’ad da alheri da wasu halaye na ibada za su kasance cikin dukan dangantaka da ’yan Adam suka ƙulla.
Me Ya Sa Za Mu Yi Alheri?
21, 22. Me ya sa ya kamata mu yi alheri?
21 Ga Kirista na gaskiya, yin alheri yana da muhimmanci sosai. Tabbaci ne cewa muna da ruhun Allah. Ƙari ga haka, sa’ad da muka yi alheri na gaske, muna yin koyi ne da Jehovah Allah da Kristi Yesu. Alheri farilla ce ga waɗanda za su zama talakawan Mulkin Allah. Saboda haka, dole ne mu so alheri kuma mu koyi yinsa.
22 A waɗanne hanyoyi ne za mu yi alheri a rayuwarmu ta yau da kullum? Talifi na gaba zai tattauna wannan batu.
Yaya Za Ka Amsa?
• Menene alheri?
• Me ya sa duniya wuri ne na zalunci da ƙiyayya?
• Ta yaya muka sani cewa alheri zai kasance a sarautar Allah?
• Me ya sa yin alheri yake da muhimmanci ga waɗanda suke son su yi rayuwa a Mulkin Allah?
[Hoto a shafi na 6]
Dattawa Kirista suna ƙoƙari su yi alheri a bi da garken
[Hoto a shafi na 8]
Jehovah zai nuna wa bayinsa ƙauna ta alheri a lokacin wahala
[Hotuna a shafi na 9]
Cikin alheri Jehovah yana sa rana ta haskaka kuma ya aiko da ruwan sama a kan dukan mutane