Jehovah Ya Bayyana Ɗaukakarsa Ga Masu Tawali’u
“Kana da tsoron Ubangiji, ka yi tawali’u, za ka arzuta, ka ɗaukaka, ka sami tsawon rai.”—KARIN MAGANA 22:4.
1, 2. (a) Ta yaya ne littafin Ayyukan Manzanni ya nuna cewa Istifanas mutum ne “da ke cike da bangaskiya da Ruhu Mai Tsarki”? (b) Wane tabbaci ne ya nuna cewa Istifanas yana da tawali’u?
ISTIFANAS mutum ne “da ke cike da bangaskiya da Ruhu Mai Tsarki.” Kuma yana “cike da alheri da iko.” A matsayinsa na ɗaya daga cikin almajiran Yesu na farko, yana ta yin manyan mu’ujizai da al’ajabi a cikin mutane. A wani lokaci, waɗansu mutane suka tayar masa da mahawara, “amma ba su da iko su tsaya ma hikima da Ruhu wanda ya ke magana da shi.” (Ayyukan Manzanni 6:5, 8-10) Lallai Istifanas ɗalibi ne na gaske na Kalmar Allah, kuma ya kāre ta a gaban shugabannin addini na Yahudawa na kwanakinsa. Tabbacinsa da ke rubuce a Ayyukan Manzanni sura 7, ya nuna yana son yadda manufar Allah take bayyana sosai.
2 Ba kamar shugabannin addinai waɗanda iliminsu yake sa su ji cewa sun fi talakawa ba, Istifanas mai tawali’u ne. (Matiyu 23:2-7; Yahaya 7:49) Ko da yake yana da ilimin Nassosi, ya yi farin ciki sosai da aka ba shi aikin “sha’anin abinci” domin manzannin su nace da ‘yin addu’a da kuma koyar da magana.’ Domin Istifanas ya yi suna mai kyau a tsakanin ’yan’uwan ya sa aka zaɓe shi ya zama ɗaya daga cikin mutane bakwai waɗanda ake yaba musu domin su kula da raba abinci kowace rana. Ya karɓi wannan aikin cikin sauƙin kai.—Ayyukan Manzanni 6:1-6.
3. Wane alherin Allah na musamman ne Istifanas ya shaida?
3 Jehovah ya lura da tawali’u, da aminci, da kuma ruhaniyar Istifanas. Sa’ad da Istifanas yake yi wa abokan gāba shugabannin Yahudawa wa’azi a Majalisa, masu yin adawa da shi “suka ga fuska tasa kamar fuskar mala’ika take.” (Ayyukan Manzanni 6:15) Fuskarsa ta mai ɗauke da saƙon Allah ne, da kuma salama da ke zuwa daga wurin Allah mai ɗaukaka, Jehovah. Bayan ya ba da shaida da gaba gaɗi ga ’yan Majalisar, Istifanas ya shaida wani alherin Allah na musamman. “Amma Istifanas, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya zuba ido sama, ya ga ɗaukakar Allah, da kuma Yesu tsaye dama ga Allah.” (Ayyukan Manzanni 7:55) Ga Istifanas, wannan wahayin ya ƙara tabbatar da matsayin Yesu na Ɗan Allah da kuma Almasihu. Wannan ya ƙarfafa Istifanas kuma ya ƙara tabbatar masa cewa yana da tagomashin Jehovah.
4. Su waye ne Jehovah yake bayyana wa ɗaukakarsa?
4 Kamar yadda wahayin da Istifanas ya gani ya nuna, Jehovah yana bayyana ɗaukakarsa da manufarsa wa mutane masu tsoron Allah da suke da tawali’u kuma suna nuna godiya wa dangantakarsu da shi. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kana da tsoron Ubangiji, ka yi tawali’u, za ka arzuta, ka ɗaukaka, ka sami tsawon rai.” (Karin Magana 22:4) Saboda haka, wajibi ne mu fahimci abin da tawali’u na gaskiya yake nufi, yadda za mu iya gina wannan hali mai muhimmanci, da kuma yadda za mu amfana idan muka bayyana shi a dukan fasaloli na rayuwa.
Tawali’u—Halin da Allah Yake Nunawa
5, 6. (a) Menene tawali’u? (b) Ta yaya ne Jehovah ya nuna tawali’u? (c) Yaya ne tawali’un da Jehovah ya nuna ya kamata ya shafe mu?
5 Mutane na iya mamakin cewa Jehovah Allah, wanda shi ne mafi girma da ɗaukaka a sararin samaniya, shi ne kuma misali mafi girma na tawali’u. Sarki Dauda ya ce game da Jehovah: “Ya Ubangiji ka kiyaye ni, ka cece ni, na zama babban mutum saboda kana lura da ni, ikonka kuma ya kiyaye lafiyata.” (Zabura 18:35) Sa’ad da yake kwatanta cewa Jehovah mai tawali’u ne, Dauda ya yi amfani da kalmar Ibrananci da aka samo daga wani tushe da yake nufin “sunkuyar da kai.” Ban da kalmar “tawali’u,” wasu kalmomi da suke da dangantaka da wannan tushen sun haɗa da “salihanci,” da kuma “ƙasƙantar da kai.” Wato Jehovah ya nuna tawali’u da ya ƙasƙantar da kansa domin ya yi sha’ani da Dauda ajizi kuma ya yi amfani da shi a matsayin sarkin da ke wakiltarsa. Yadda rubutun sama na Zabura 18 ya nuna, Jehovah ya kāre kuma ya taimaki Dauda, “ya cetar da shi daga hannun dukan maƙiyansa, da kuma hannun Shawulu.” Haka kuma, Dauda ya sani cewa duk wani girma ko ɗaukaka da zai iya samu a matsayinsa na sarki zai kasance ne domin tawali’un Jehovah. Fahimtar wannan ya taimaki Dauda ya kasance da tawali’u.
6 Mu kuma fa? Jehovah ya zaɓi ya koya mana gaskiya, wataƙila ya ba mu gatar hidima ta musamman a cikin ƙungiyarsa ko kuwa ya yi amfani da mu a wata hanya domin ya cim ma manufarsa. Yaya ya kamata mu ji game da dukan wannan? Bai kamata mu kasance da tawali’u ba ne? Bai kamata mu yi godiya wa tawali’u da Jehovah ya nuna ba kuma mu kauce ma ɗaga kai, wanda zai iya kai mu ga halaka?—Karin Magana 16:18; 29:23.
7, 8. (a) Yaya ne Jehovah ya nuna tawali’u a sha’aninsa da Manassa? (b) A wace hanya ce Jehovah da Manassa, suka kafa misali mai kyau na tawali’u da za mu bi?
7 Ba ta wajen yin sha’ani da mutane ajizai kaɗai ne Jehovah ya nuna tawali’u ba, amma kuma ta nuna jinƙai ga talakawa har ma yakan ta da ko kuma ɗaukaka, waɗanda suka ƙasƙantar da kansu. (Zabura 113:4-7) Ka yi la’akari da misalin Sarki Manassa na Yahudiya. Ya ɓata gatarsa a matsayin sarki domin ya gabatar da ibada ta ƙarya kuma “ya aikata mugunta ƙwarai a gaban Ubangiji, yana tsokanar fushin Ubangiji.” (2 Tarihi 33:6) A ƙarshe, Jehovah ya horar da Manassa sa’ad da ya sa sarkin Assuriya ya cire shi daga kan karaga. A kurkuku, Manassa “ya roƙi jinƙan Ubangiji Allahnsa, ya ƙasƙantar da kansa sosai,” wannan ya sa Jehovah ya sake komar da shi kan mulkinsa a Urushalima, kuma Manassa “ya sani Ubangiji shi ne Allah.” (2 Tarihi 33:11-13) Hakika, a ƙarshe, tawali’u da Manassa ya nuna ya faranta wa Jehovah rai, domin haka ya nuna tawali’u ta hanyar gafarta masa kuma ya mai da shi sarki.
8 Gafartawa da son rai na Jehovah da kuma halin tuba na Manassa ya nuna mana muhimman darussa na tawali’u. Ya kamata mu tuna a kowane lokaci cewa yadda muke bi da waɗanda suka yi mana laifi da kuma halin da muka nuna sa’ad da muka yi zunubi zai iya shafan yadda Jehovah yake bi da mu. Idan muka gafarta wa wasu laifin da suka yi mana da son rai kuma muka yarda da laifinmu cikin tawali’u, sa’an nan za mu iya samun jinƙan Jehovah.—Matiyu 5:23, 24; 6:12.
An Bayyana Ɗaukakar Allah ga Masu Tawali’u
9. Tawali’u alama ce ta kumamanci? Ka ba da bayani.
9 Bai kamata mu ɗauka cewa tawali’u da sauran halayen alama na kumamanci ne ko kuma don haka mu amince da abin da ba shi da kyau. Nassosi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehovah yana da tawali’u, duk da haka, yana nuna fushi na adalci da ikonsa mai ban mamaki sa’ad da yanayi ya sa ya yi hakan. Saboda tawali’unsa, Jehovah yana nuna wa masu kaɗaici tagomashi, ko kuwa kulawa na musamman, amma yana nisanta kansa daga masu girman kai. (Zabura 138:6) Ta yaya ne Jehovah yake nuna kulawa ta musamman ga bayinsa masu tawali’u?
10. Yadda aka nuna a 1 Korantiyawa 2:6-10, menene Jehovah ya bayyana wa masu tawali’u?
10 A lokacin da ya ga dama kuma ta hanyar sadarwarsa, Jehovah ya ba da cikakken bayani ga masu tawali’u game da yadda zai cim ma manufarsa. Waɗannan manyan bayanai suna a ɓoye ga masu girma da taurin kai, da suka manne wa hikima ko tunanin mutane. (1 Korantiyawa 2:6-10) Domin suna da cikakken fahimi na manufar Jehovah, masu tawali’u sun motsa su ɗaukaka Jehovah don suna godiya ga ɗaukakarsa sosai.
11. A ƙarni na farko, ta yaya ne wasu suka nuna rashin tawali’u, kuma ta yaya ne wannan ya kasance da lahani a gare su?
11 A ƙarni na farko mutane da yawa har wasu da suke ikirarin cewa su Kiristoci ne sun nuna rashin tawali’u, kuma sun yi sanyin gwiwa domin abin da manzo Bulus ya bayyana musu game da manufar Allah. Bulus ya zama “manzo ne ga al’ummai,” ba domin ƙasar da ya fito ba, ilimi, shekarunsa, ko kuwa shekaru da yawa na ayyuka masu kyau. (Romawa 11:13) Sau da yawa, mutane marasa ruhaniya suna ɗaukan cewa waɗannan abubuwa ne suke nuna wanda Jehovah zai yi amfani da shi. (1 Korantiyawa 1:26-29; 3:1; Kolosiyawa 2:18) Amma, Bulus shi ne zaɓaɓɓen Jehovah, domin ƙaunarsa ta alheri da manufarsa ta adalci. (1 Korantiyawa 15:8-10) Waɗanda Bulus ya kwatanta a matsayin “mafifitan manzannin” da kuma sauran ’yan adawa, sun ƙi su karɓi Bulus da mahawararsa na Nassosi. Rashin tawali’unsu ya hana su samun sani da fahimta na hanyar ɗaukaka da Jehovah yake cim ma manufarsa. Kada mu raina ko shar’anta waɗanda Jehovah ya zaɓa don ya yi amfani da su ya cika manufarsa.—2 Korantiyawa 11:4-6.
12. Ta yaya ne misalin Musa ya nuna cewa Jehovah yana nuna tagomashi ga waɗanda suke da tawali’u?
12 A wani ɓangare kuma, akwai misalai masu yawa na Littafi Mai Tsarki da suka nanata yadda mutane masu tawali’u suka sami tagomashin ganin kaɗan daga cikin ɗaukakar Allah. Musa “mai tawali’u ne ƙwarai” fiye da dukan mutane, ya ga ɗaukakar Allah kuma ya more dangantaka ta kud da kud da shi. (Littafin Ƙidaya 12:3) Wannan mutumin mai tawali’u, wanda ya yi shekara 40 talikin makiyayi, ko da yake ya yi yawancin shekarunsa kusa da hancin ƙasar da ta kutsa cikin teku na Arabiya, ya sami tagomashin Mahalicci a hanyoyi masu yawa. (Fitowa 6:12, 30) Da taimakon Jehovah, Musa ya zama kakaki da kuma shugaban shirye-shirye na al’ummar Isra’ila. Allah yana yi masa magana kuma yana amsawa. Ta wurin wahayi, ya ga ‘zatin Ubangiji.’ (Littafin Ƙidaya 12:7, 8; Fitowa 24:10, 11) Waɗanda suka yarda da wannan bawa mai tawali’u kuma wakilin Allah sun sami albarka. Haka nan ma, za mu sami albarka idan muka bi kuma muka yi biyayya ga babban annabin da ya fi Musa, Yesu, da kuma “amintaccen bawan nan mai hikima” wanda ya naɗa.—Matiyu 24:45, 46; Ayyukan Manzanni 3:22.
13. Yaya Jehovah ya bayyana ɗaukakarsa ga makiyaya masu tawali’u a ƙarni na farko?
13 A kan su wanene ‘ɗaukakar Jehovah ta haskaka’ sa’ad da mala’ika ya bayyana albishir na haihuwar “Mai Ceto . . . wanda yake shi ne Almasihu, Ubangiji”? Bai bayyana wa shugabannin addinai masu fahariya ko manyan mutane masu matsayi ba, amma makiyaya masu tawali’u masu “kwana a filin Allah, suna tsaron garken tumakinsu da dad dare.” (Luka 2:8-11) Ba a daraja irin mutanen nan domin aiki da kuma fasaharsu. Duk da haka, sune Jehovah ya lura da su kuma ya fara bayyana musu haihuwar Almasihu. Hakika, Jehovah ya bayyana ɗaukakarsa ga masu tawali’u da masu tsoron Allah.
14. Ta yaya Allah yake saka wa waɗanda suke da tawali’u?
14 Menene waɗannan misalai suka koya mana? Suna nuna mana cewa Jehovah yana da tagomashi kuma yana bayyana sani da fahimta na manufarsa ga masu tawali’u. Yana zaɓan waɗanda ba su kai kome ba a idon mutane ya yi amfani da su wajen sanar da manufarsa mai ɗaukaka ga wasu. Wannan zai motsa mu mu nemi ja-gora daga wurin Allah, Kalmarsa ta annabci, da kuma ƙungiyarsa. Muna da tabbacin cewa Jehovah zai ci gaba da sanar da bayinsa masu tawali’u game da bayyanar manufarsa mai ɗaukaka. Annabi Amos ya ce: “Hakika Ubangiji ba yakan aikata kome ba, sai da sanin bayinsa annabawa.”—Amos 3:7.
Ka Koyi Tawali’u Kuma Ka Sami Tagomashin Allah
15. Me ya sa ya kamata mu kasance masu tawali’u, yaya aka taƙaita wannan a batun sarkin Isra’ila Shawulu?
15 Domin morar alherin Allah mai daɗewa, dole ne mu ci gaba da zama masu tawali’u. Domin mutum yana da tawali’u a wani lokaci a rayuwarsa, wannan ba ya nufin cewa zai ci gaba da kasancewa mai tawali’u. Yana da sauƙi mutum ya yi rashin tawali’u kuma ya fara fahariya da kuma ɗaga kai, wanda zai iya kai ga girman kai da bala’i. Abin da Shawulu, sarkin Isra’ila na farko da aka shafe ya yi ke nan. Sa’ad da aka zaɓe shi, ya ji cewa shi ‘ba wani abu ba ne.’ (1 Sama’ila 15:17) Amma, bayan ya yi sarauta na shekaru biyu kaɗai, sai ya fara ɗaga kai. Ya raina shirye-shiryen Jehovah na yin hadaya ta wurin annabi Sama’ila, sai ya fara ƙirƙiro hujjar da ta sa ya yi hakan. (1 Sama’ila 13:1, 8-14) Wannan aukuwa ita ce ta bayyana rashin tawali’unsa. Sakamakon hakan shi ne, ya rasa ruhun Allah da tagomashinsa, wadda ta kai shi ga mutuwar kunya. (1 Sama’ila 15:3-19, 26; 28:6; 31:4) Darasin a bayyana yake: Dole ne mu yi ƙoƙari mu kasance masu tawali’u da kuma biyayya, mu kuma kauce wa girman kai, mu kauce wa duk wani hali na girman kai da zai iya jawo mana rashin tagomashin Jehovah.
16. Ta yaya ne yin bimbini a kan dangantakarmu da Jehovah da ’yan’uwanmu zai taimaka mana mu nuna tawali’u?
16 Tawali’u inganci ne na ibada da ya kamata mu ke da shi. (Kolosiyawa 3:10, 12) Tun da shike ya shafi yanayin zuciyarmu—yadda muka ɗauki kanmu da kuma wasu—kasancewa da tawali’u na bukatar ƙoƙari sosai. Yin tunani da bimbini a kan dangantakarmu da Jehovah da ’yan’uwanmu zai taimaka mana mu kasance da tawali’u. Dukan ’yan Adam ajizai kamar ciyawa suke a gaban Allah da ke girma a ƙanƙanin lokaci, kuma su bushe. Mutane kamar ƙananan ƙwari suke. (Ishaya 40:6, 7, 22) Kana ganin ɗan ganyen ciyawa yana da dalilin yin fahariya domin ya fi sauran ciyayin tsawo? Kana ganin ƙaramin ƙwaro yana da dalilin yin fahariya domin ya fi sauran tsalle? Kasancewa da irin wannan tunanin wauta ce. Da haka, manzo Bulus ya tuna wa ’yan’uwansa Kiristoci: “Wa ya fifita ka da sauran? Me kuma kake da shi, wanda ba karɓa ka yi ba? Da ya ke karɓa ka yi, don me kake fariya, kamar ba karɓa ka yi ba?” (1 Korantiyawa 4:7) Yin bimbini a kan irin waɗannan ayoyi na Littafi Mai Tsarki za su taimaka mana mu nuna tawali’u.
17. Menene ya taimaki Daniyel ya nuna sauƙin kai, kuma menene zai taimake mu mu yi hakan?
17 Allah ya kira annabi Daniyel Ba’ibrane ‘mutumin da ake so ƙwarai’ domin ya “ƙasƙantar” da kansa ta wurin tawali’unsa. (Daniyel 10:11, 12) Menene ya taimaki Daniyel ya nuna tawali’u? Na farko, ya dogara sosai ga Jehovah, da kuma yin addu’a a gare shi kowane lokaci. (Daniyel 6:10, 11) Bugu da ƙari, ɗalibin Kalmar Allah ne da ya taimake shi ya mai da hankali ga manufar ɗaukakar Allah. Ya ga nasa kasawa, ba na mutanensa kaɗai ba. Kuma yana marmarin ɗaukaka adalcin Allah, ba na kansa ba. (Daniyel 9:2, 5, 7) Muna iya koyo daga misali na musamman na Daniyel kuwa don mu yi ƙoƙarin nuna tawali’u a fasaloli na rayuwanmu?
18. Wane ɗaukaka ne ke jiran waɗanda suka nuna tawali’u a yau?
18 “Kana da tsoron Ubangiji, ka yi tawali’u, za ka arzuta, ka ɗaukaka, ka sami tsawon rai,” in ji Karin Magana 22:4. Hakika, Jehovah yana nuna tagomashi ga masu sauƙin kai, kuma sakamakon shi ne ɗaukaka da rai. Bayan ya kusan daina yin ibada ga Allah amma daga baya sai Jehovah ya daidaita tunaninsa, marubucin zabura Asaph ya faɗi cewa: “Shawararka, tana bi da ni, daga ƙarshe kuma za ka karɓe ni da daraja.” (Zabura 73:24) Ta yaya wannan ya shafe mu a yau? Wane ɗaukaka ne ke jiran waɗanda suka nuna tawali’u? Ban da more tagomashi da dangantaka da Jehovah, za su ci gaba da sauraron cikar hurarriyar kalmar Sarki Dauda: “Amma masu ladabi za su zauna lafiya a ƙasar, su ji daɗin cikakkiyar salama.” Hakika nan gaba zai zama mai ɗaukaka!—Zabura 37:11.
Ka Tuna?
• Ta yaya Istifanas ya zama misalin mutum mai tawali’u wanda Jehovah ya bayyana masa Ɗaukakarsa?
• A waɗanne hanyoyi ne Jehovah ya nuna tawali’u?
• Waɗanne misalai ne suka nuna cewa Jehovah ya bayyana ɗaukakarsa ga masu tawali’u?
• Ta yaya ne misalin Daniyel zai taimaka mana mu kasance masu tawali’u?
[Akwati a shafi na 22]
Mai Tabbaci Sosai Amma Mai Tawali’u
A taron gunduma na Ɗaliban Littafi Mai Tsarki (da aka san su da Shaidun Jehovah a yau) na shekarar 1919 a Cedar Point, Ohio, Amirka, J. F. Rutherford ɗan shekara 50 wanda shi ne mai kula da aikin, da murna yana kwasan akwatunan mutane kuma ya raka su zuwa dakunansu. A rana ta ƙarshe na taron gundumar, ya ƙarfafa mutane 7,000 da wannan furci: “Ku jakadun Sarkin sarakuna da Ubangijin iyayengiji ne, masu sanar da mutane . . . ɗaukakar mulkin Ubangijinmu.” Ko da yake ɗan’uwa Rutherford mutum ne mai tabbaci sosai, an kuma san shi da yin magana da ƙarfi kuma bai taka ƙa’idar abin da ya sani cewa gaskiya ne, ya ƙasƙantar da kansa a gaban Allah, yakan nuna wannan in yana yin addu’a a ibadar safiya a Bethel.
[Hoto a shafi na 19]
Istifanas, mai ilimin Nassosi, cikin tawali’u ya rarraba abinci
[Hoto a shafi na 20]
Ƙasƙantar da kai da Manassa ya nuna ya faranta wa Jehovah rai
[Hoto a shafi na 22]
Menene ya sa Daniyel ‘mutumin da ake so ƙwarai’ ne?