Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w05 11/1 pp. 14-19
  • Ka Koyi Tawali’u Na Gaske

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Koyi Tawali’u Na Gaske
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Misali Mafi Kyau na Tawali’u
  • Abin da Ya Sa Yesu ya Kasance da Tawali’u
  • Abin da Ya Sa Yake da Wuya a Kasance da Tawali’u
  • Koya da Kuma Nuna Tawali’u na Gaske
  • Tawali’u na Magance Matsaloli
  • Jehovah Ya Bayyana Ɗaukakarsa Ga Masu Tawali’u
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Jehobah Yana Daraja Bayinsa Masu Saukin Kai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
  • Yesu Ya Kafa Misali Na Tawali’u
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • ‘Ku Yafa Zuciya ta Tawali’u’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
w05 11/1 pp. 14-19

Ka Koyi Tawali’u Na Gaske

“Kakan ceci masu tawali’u.”—2 SAMA’ILA 22:28.

1, 2. Wane irin hali ne sarakunan duniya da yawa suke da shi?

DALAR Masar ta nuna sarakunan ƙasar a dā. Waɗansu sarakuna kuma da suka yi suna sune Sennakerib na Assuriya, Iskandari Mai Girma na Helas, da Yuliyas Kaisar na Roma. Sarakunan nan suna da abu iri ɗaya. Ba sa cikin masu tawali’u a tarihi.—Matiyu 20:25, 26.

2 Kana tsammanin wani cikin sarakunan da aka ambata a sama zai je ya nemi talakawa da ke bukatar ta’aziyya a mulkinsa? Da ƙyar! Ba za su kuma je gidajen waɗanda suka karai a zuci su ƙarfafa su ba. Halinsu game da ’yan adam masu tawali’u ya bambanta da na Jehobah Allah, Sarki mafi girma na sararin samaniya!

Misali Mafi Kyau na Tawali’u

3. Ta yaya Sarki Mafi Girma yake bi da talakawansa ’yan adam?

3 Girman Jehobah da ɗaukakarsa sun fi gaban bincikawa, duk da haka idonsa “yana kai da komowa ko’ina a duniya don ya nuna ikonsa ga dukan waɗanda suka dogara gare shi da zuciya ɗaya.” (2 Tarihi 16:9) Menene Jehobah yake yi sa’ad da ya iske masu tawali’u da suke bauta masa sun karai a zuci domin gwaji dabam dabam? Yana “tare” da irin waɗannan ta ruhunsa mai tsarki domin ya “farfaɗo da ruhun masu tawali’u, [ya] kuma farfaɗo da zukatan masu tuba.” (Ishaya 57:15) Da haka, masu bauta masa da suka farfaɗo suna shirye su soma bauta masa da farin ciki. Allah ne mai tawali’u da gaske!

4, 5. (a) Yaya mai zabura yake ji game da yadda Allah yake sarauta? (b) Yadda Allah yake “duba ƙasa” ya taimaki “masu tawali’u” yana nufin menene?

4 Babu wani a sararin samaniya da ya ƙasƙantar da kansa kamar Ubangiji Mai Ikon Mallaka domin ya taimaki ’yan adam masu zunubi. Shi ya sa mai zabura ya rubuta: “Ubangiji ke mulkin dukan sauran al’umma, ɗaukakarsa tana bisa kan sammai. Ba wani kamar Ubangiji Allahnmu. Yana zaune a can ƙwanƙolin sama, amma ya duba ƙasa, ya dubi sammai da duniya. Yakan ɗaga talakawa daga ƙura, yakan ɗaga matalauta daga cikin azabarsu.”—Zabura 113:4-7.

5 Ka lura da furcin nan “duba ƙasa.” Idan ɗan adam ya dubi ƙasa, wannan ba shi da ma’ana ta kirki, wato ‘yana nuna ya fi wani talaka ko kuma fakiri.’ Ba za a kwatanta Jehobah Allah wanda yake da tsarki kuma ba ya “girmankai,” da irin wannan halin ba. (Markus 7:22, 23) Amma “duba ƙasa” na nufin mutum ya ƙasƙantar da kansa ga wanda yake ƙasa da shi ko kuma ya rage matsayinsa ko kuma ɗaukakarsa sa’ad da yake sha’ani da matalauta. Shi ya sa wasu Littattafai Masu Tsarki suka fassara Zabura 113:6 cewa Allah ya ƙasƙantar da kansa. Wannan ya kwatanta halin Allahnmu mai tawali’u da kyau, yana kula da bukatun ’yan adam ajizai masu bauta masa!—2 Sama’ila 22:36.

Abin da Ya Sa Yesu ya Kasance da Tawali’u

6. Wane tawali’u ne mafi girma Jehobah ya nuna?

6 Allah ya fi nuna tawali’u da ƙauna sa’ad da ya aiko da Ɗan farinsa ƙaunatacce a haife shi a duniya kuma a yi renonsa kamar ɗan adam don ceton mutane. (Yahaya 3:16) Yesu ya koya mana gaskiya game da Ubansa na samaniya kuma ya ba da ransa kamiltacce domin ya ɗauke “zunubin duniya.” (Yahaya 1:29; 18:37) Da yake ya nuna halin Ubansa sarai har da tawali’unsa, Yesu yana shirye ya yi abin da Allah ya ce ya yi. Wannan ne misali na tawali’u da ƙauna mafi kyau da ɗaya cikin halittun Allah ya taɓa nunawa. Ba dukan mutane ba ne suka daraja tawali’un Yesu, magabtansa sun ma ɗauke shi “talaka talak.” (Daniyel 4:17) Duk da haka, manzo Bulus ya fahimci cewa ya kamata ’yan’uwansa masu bi su yi koyi da Yesu kuma su kasance da tawali’u a yadda suke bi da juna.—1 Korantiyawa 11:1; Filibiyawa 2:3, 4.

7, 8. (a) Ta yaya Yesu ya koyi tawali’u? (b) Wane roƙo ne Yesu ya yi wa waɗanda za su zama almajiransa?

7 Bulus ya nanata misalin Yesu na musamman, ya rubuta: “Ku ɗauki halin Almasihu Yesu, Wanda, ko da yake ya kasance cikin surar Allah, bai yi ma tunanin zama daidai da Allah ba, sai ma ya mai da kansa baya matuƙa ta ɗaukar surar bawa, da kuma kasancewa da kamannin ɗan adam. Da ya bayyana da siffar mutum, sai ya ƙasƙantar da kansa ta yin biyayya, har wadda ta kai shi ga mutuwa, mutuwar ma [a kan gungume azaba].”—Filibiyawa 2:5-8, NW.

8 Wasu suna iya mamaki, ‘Ta yaya Yesu ya koyi tawali’u?’ Ya amfana don ya kasance da dangantaka ta kud da kud da Ubansa na samaniya na shekaru aru aru, a lokacin shi ne “mai tsara fasalin” halittar dukan abubuwa. (Karin Magana 8:30) Bayan tawayen da aka yi a Aidan, Ɗan Fari na Allah ya ga yadda Ubansa cikin tawali’u ya yi sha’ani da ’yan adam masu zunubi. Shi ya sa sa’ad da Yesu yake duniya ya nuna tawali’un Ubansa kuma ya yi wannan roƙo: “Ku shiga bautata, ku kuma koya a gare ni, domin ni mai tawali’u ne, marar girmankai, za ku kuwa sami kwanciyar rai.”—Matiyu 11:29; Yahaya 14:9.

9. (a) Menene Yesu yake so game da yara? (b) Yesu ya koyar da wane darasi ta yin amfani da ɗan yaro?

9 Domin Yesu mai tawali’u ne da gaske, yara ba sa jin tsoronsa. Maimakon haka, sun matsa kusa da shi. Shi kuma yana son yara kuma ya mai da musu hankali. (Markus 10:13-16) Menene Yesu yake so game da yara? Babu shakka suna da halaye masu kyau da wasu cikin almajiransa manya ba koyaushe suke nunawa ba. Hakika, yara sun san manya sun fi su. Za ka ga wannan ta tambayoyi masu yawa da suke yi. Hakika, idan aka gwada su da manya da yawa, yara suna son a koyar da su kuma ba sa fahariya yadda manya suke yi. A wani lokaci, Yesu ya fito da wani ɗan yaro kuma ya ce wa mabiyansa: “In ba kun juyo kun zama kamar ƙananan yara ba, har abada ba za ku shiga Mulkin Sama ba.” Ya ci gaba: “Duk wanda ya ƙasƙantar da kansa kamar ɗan yaron nan, ai, shi ne mafi girma a Mulkin Sama.” (Matiyu 18:3, 4) Yesu ya faɗi ƙa’idar: “Duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Mai ƙasƙantar da kansa kuma, ɗaukaka shi za a yi.”—Luka 14:11; 18:14; Matiyu 23:12.

10. Waɗanne tambayoyi ne za mu bincika?

10 Wannan gaskiyar ta sa aka yi tambayoyi masu muhimmanci. Begenmu na samun rai madawwami ya dangana ga tawali’u na gaske, amma me ya sa Kiristoci wani lokaci suke iske shi da wuya su kasance da tawali’u? Me ya sa ƙalubale ne mu kasance da tawali’u sa’ad da muke fuskantar gwaji? Kuma me zai taimake mu mu yi nasara wajen kasancewa da tawali’u na gaske?—Yakubu 4:6, 10.

Abin da Ya Sa Yake da Wuya a Kasance da Tawali’u

11. Me ya sa ba abin mamaki ba ne cewa muna fama mu kasance masu tawali’u?

11 Idan kana fama ka kasance mai tawali’u, kuna da yawa. A shekara ta 1920 wannan jaridar ta tattauna gargaɗin Littafi Mai Tsarki a kan abin da ya sa ake bukatar a kasance da tawali’u, tana cewa: “Da yake mun ga yadda Ubangiji ya ɗauki kasancewa da tawali’u da muhimmanci, ya kamata ya ƙarfafa dukan almajirai na gaske su koyi wannan halin.” Sai jaridar ta yi wannan kalami na gaskiya: “Duk da wannan gargaɗi na Nassi, ajizancin ’yan adam ya sa yake wa mutanen Ubangiji da suka ƙuduri aniyar bin hanyar Ubangiji wuya ainun su kasance da tawali’u fiye da wani hali.” Wannan ya nanata dalili ɗaya da ya sa Kiristoci na gaske suke bukata su yi fama don su kasance da tawali’u, wato, yanayinmu na zunubi ta sha’awar ɗaukaka da ba ta dace ba. Wannan haka ne domin mu zuriyar Adamu da Hauwa’u ne, ma’aurata masu zunubi da suka faɗa wa sha’awa ta sonkai.—Romawa 5:12.

12, 13. (a) Ta yaya duniya ta zama tangarɗa ga Kiristoci wajen kasancewa da tawali’u? (b) Waye ke sa fama da muke yi mu kasance da tawali’u yake da wuya ƙwarai?

12 Wani dalili da ya sa muke iske shi da wuya mu kasance da tawali’u shi ne cewa duniya da ke ƙarfafa mutane su yi ƙoƙari su fi wasu ta kewaye mu. Wannan duniya ta fi son gamsar da “sha’awa irin ta halin mutuntaka, da sha’awar ido, da kuma alfarmar banza.” (1 Yahaya 2:16) Maimakon irin waɗannan sha’awoyi na duniya ya rinjaye su, ya kamata almajiran Yesu su sa idonsu ya zama lafiyayye kuma su mai da hankali ga yin nufin Allah.—Matiyu 6:22-24, 31-33; 1 Yahaya 2:17.

13 Dalili na uku da ya sa kasancewa da tawali’u yake da wuya shi ne cewa Shaiɗan Iblis wanda ya soma girman kai ne sarkin wannan duniya. (2 Korantiyawa 4:4; 1 Timoti 3:6) Shaiɗan yana gabatar da mugun halayensa. Alal misali, ya nemi Yesu ya bauta masa kuma ya ba shi “dukan mulkokin duniya da ɗaukakarsu.” Da yake Yesu mai tawali’u ne, ya ƙi abin da Iblis ya ba shi babu ɓata lokaci. (Matiyu 4:8, 10) Hakanan ma, Shaiɗan yana ƙoƙarin ya jarabi Kiristoci su nemo wa kansu ɗaukaka. Maimakon haka, Kiristoci masu tawali’u suna ƙoƙari su bi misalin Yesu, suna yabon Allah suna ɗaukaka shi kuma.—Markus 10:17, 18.

Koya da Kuma Nuna Tawali’u na Gaske

14. Menene “tawali’un ƙarya”?

14 A wasiƙar da ya rubuta wa Kolosiyawa, manzo Bulus ya yi gargaɗi game da nuna tawali’u don a burge mutane. Bulus ya ce wannan “tawali’un ƙarya” ne. Waɗanda suke nuna kamar suna da tawali’u ba masu ruhaniya ba ne. Maimakon haka, suna “kumbura” kansu da fahariya. (Kolosiyawa 2:18, 23) Yesu ya nuna misalin irin wannan tawali’un ƙarya. Ya hukunta Farisawa don suna tsayawa a kan hanya don mutane su ga suna addu’a da kuma yadda suke turɓune fuska idan suna azumi don mutane su lura da su. Akasarin haka, don addu’o’inmu su kasance da muhimmanci a gaban Allah, ya kamata mu yi su cikin tawali’u.—Matiyu 6:5, 6, 16.

15. (a) Menene za mu iya yi don mu zama masu tawali’u? (b) Waɗanne misalai masu kyau game da tawali’u muke da shi?

15 Kiristoci za su sami taimako su kasance da tawali’u ta wajen mai da hankali ga Jehobah Allah da Yesu Kristi waɗanda misalan tawali’u ne mafi kyau. Yin haka ta ƙunshi yin nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai da kuma littattafan nazari da “amintaccen bawan nan mai hikima” ya yi tanadinsu. (Matiyu 24:45) Yana da muhimmanci dattawa Kirista su yi irin wannan nazari ‘don kada zuciyarsu ta kumbura, har su ga sun fi ’yan’uwansu.’ (Maimaitawar Shari’a 17:19, 20; 1 Bitrus 5:1-3) Ka yi tunanin misalai da yawa na waɗanda aka albarkace su don tawali’unsu, kamar su Rut, Hannatu, Alisabatu, da wasu da yawa. (Rut 1:16, 17; 1 Sama’ila 1:11, 20; Luka 1:41-43) Ka kuma yi tunanin misalan mutane sanannu da yawa da suka kasance da tawali’u a hidimar Jehobah, kamar su Dauda, Yosiya, Yahaya mai Baftisma, da manzo Bulus. (2 Tarihi 34:1, 2, 19, 26-28; Zabura 131:1; Yahaya 1:26, 27; 3:26-30; Ayyukan Manzanni 21:20-26; 1 Korantiyawa 15:9) Misalan tawali’u da yawa da muke gani cikin ikilisiyar Kirista a zamani kuma fa? Yin bimbini a kan waɗannan misalan zai taimaki Kiristoci na gaskiya su kasance da ‘tawali’u ga juna.’—1 Bitrus 5:5.

16. Ta yaya hidima ta Kirista ke taimakon mu mu kasance da tawali’u?

16 Zuwa hidimar fage a kai a kai zai taimake mu mu kasance masu tawali’u. Tawali’u zai sa mu yi wa’azi da kyau sa’ad da muka sadu da baƙi a wa’azin gida gida da kuma wasu wurare. Wannan yana da muhimmanci sa’ad da masu gida don wariya ko kuma taurin kai suka ƙi sauraron saƙon Mulki da farko. Sau da yawa ana tahumar imaninmu, kasancewa da tawali’u ne zai taimaki Kirista ya ci gaba da amsa tambayoyi cikin “tawali’u da bangirma.” (1 Bitrus 3:15) Bayin Allah masu tawali’u sun ƙaura zuwa sababbin yankuna kuma sun taimaki mutane daga al’adu da kuma salon rayuwa dabam dabam. Don su masu tawali’u ne irin waɗannan masu hidima suna iya jimrewa da aiki mai wuya na koyon sabon yare domin su taimaki waɗanda suke wa wa’azi da kyau. Wannan abin yabo ne!—Matiyu 28:19, 20.

17. Waɗanne ayyuka ne na Kirista suke bukatar a kasance da tawali’u?

17 Da yake su masu tawali’u ne, mutane da yawa suna yin ayyukansu ta Kirista, suna sa bukatun wasu gaba da nasu. Alal misali, sai da tawali’u uba Kirista zai keɓe lokaci daga nasa ayyuka ya shirya kuma ya gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki da yaransa. Tawali’u na taimakon yara su girmama iyayensu ajizai kuma su yi musu biyayya. (Afisawa 6:1-4) Mata waɗanda mazansu marasa bi ne sau da yawa suna fuskantar yanayi da ke bukatar su kasance da tawali’u yayin da suke ƙoƙari su shawo kan abokan aurensu ta “tsarkakakken halin[su] da kuma ladabin[su].” (1 Bitrus 3:1, 2) Muna bukatar tawali’u da ƙauna na sadaukar da kai sa’ad da muke kula da bukatun masu ciwo da iyaye tsofaffi.—1 Timoti 5:4.

Tawali’u na Magance Matsaloli

18. Ta yaya tawali’u zai taimake mu mu magance matsaloli?

18 Dukan bayin Allah ajizai ne. (Yakubu 3:2) Wani lokaci, jayayya takan taso tsakanin Kiristoci biyu. Wani yana iya kasancewa da dalili na ƙara game da wani. Ana iya magance irin wannan yanayi ta yin amfani da wannan gargaɗin: “Kuna jure wa juna, in kuma wani yana da ƙara game da wani, sai su yafe wa juna. Kamar yadda Ubangiji ya yafe muku, ku kuma ku yafe.” (Kolosiyawa 3:13) Hakika, bin wannan gargaɗin ba shi da sauƙi amma tawali’u zai taimaki mutum ya yi amfani da shi.

19. Menene ya kamata mu tuna sa’ad da muke wa wanda ya yi mana laifi magana?

19 Wani lokaci Kirista zai ji cewa dalili na ƙara yana da tsanani ainun da ba za a iya ƙyalewa ba. A wannan yanayin tawali’u zai taimake shi ya je wajen wanda yake gani ya yi masa laifi domin su sulhunta. (Matiyu 18:15) Dalilin da ya sa matsaloli ke ci gaba tsakanin Kiristoci shi ne cewa wani ko mutanen suna fahariya ainun da ba za su yarda da laifinsu ba. Ko kuwa wanda ya ɗauki mataki ya je ya sami ɗayan ya yi hakan ta nuna adalcin kai, ko kuma cikin halin kushewa. Akasarin haka, halin tawali’u zai taimaka sosai wajen magance matsaloli da yawa.

20, 21. Wane taimako ne mafi kyau zai sa mu kasance da tawali’u?

20 Mataki na musamman na kasancewa da tawali’u shi ne yin addu’a don taimakon Allah da ruhunsa. Amma ka tuna, Allah “yana yi wa masu tawali’u alheri [har da ruhunsa mai tsarki].” (Yakubu 4:6) Saboda haka idan kana da matsala da ɗan’uwa, ka yi wa Jehobah addu’a ya taimake ka ka yarda da naka kuskure, ƙarami ko babba. Idan an ɓata maka rai kuma mai laifin ya faɗi cikin gaskiya, “ka yafe mini,” sai ka gafarta cikin tawali’u. Idan yin haka yana maka wuya, ka nemi taimakon Jehobah don ka kawar da girman kai da ke zuciyarka.

21 Fahimtar amfanin tawali’u ya kamata ya motsa mu mu koya kuma mu ci gaba da nuna wannan hali mai tamani. Don mu yi hakan muna da misalai masu kyau, Jehobah Allah da Yesu Kristi! Kada ka manta da wannan tabbaci da Allah ya ba da: “Kana da tsoron Ubangiji, ka yi tawali’u, za ka arzuta, ka ɗaukaka, ka sami tsawon rai.”—Karin Magana 22:4.

Darussa don Bimbini

• Su waye ne misalan tawali’u mafi kyau?

• Me ya sa yake wuya a kasance da tawali’u?

• Menene zai taimake mu mu kasance da tawali’u?

• Me ya sa yake da muhimmanci a ci gaba da kasancewa da tawali’u?

[Hoto a shafi na 14]

Yesu mai tawali’u ne da gaske

[Hoto a shafi na 16]

Duniya tana ƙarfafa mutane su yi ƙoƙari su fi wasu

[Inda aka Dauko]

WHO photo by L. Almasi/K. Hemzǒ

[Hoto a shafi na 17]

Tawali’u na taimakonmu mu je wajen baƙi lokacin da muke hidima

[Hotuna a shafi na 18]

Za a iya magance matsaloli ta wajen rufe batun cikin ƙauna

[Hotuna a shafi na 19]

Da hanyoyi da yawa da Kiristoci za su nuna tawali’u

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba