“Ku Yi Ɗamara Da Dukan Makamai Na Allah”
“Ku yi ɗamara da dukan makamai na Allah, don ku iya dage gāba da kissoshin Iblis.”—AFISAWA 6:11.
1, 2. A naka kalmomin, ka kwatanta makami na ruhaniya da ya kamata Kiristoci su yi ɗamara da shi.
ROMA tana da iko sosai a ƙarni na farko K.Z. Ƙarfin sojojin Roma ya sa tana iko da dukan duniya a lokacin. Wani ɗan tarihi ya kwatanta sojojin cewa “rukunin sojoji ne da suka fi cin nasara a dukan tarihi.” Ƙwararrun rundunar Roma ya ƙunshi sojojin da suka sami horo da koyarwa sosai, amma cin nasararsu a matsayin mayaƙa ya dangana ne a kan makamansu. Manzo Bulus ya yi amfani da makaman sojan Roma ya kwatanta makamai na ruhaniya da Kiristoci suke bukata domin su ci nasara a yaƙinsu da Iblis.
2 Mun sami kwatancin wannan makami na ruhaniya a Afisawa 6:14-17. Bulus ya rubuta: “Ku dage, gaskiya ta zama ɗamararku, adalci ya zama sulkenku, shirin kai bisharar salama ya zama kamar takalmi a ƙafafunku. Banda waɗannan kuma ku ɗauki garkuwar bangaskiya, wadda za ku iya kashe dukan kiban wutar mugun nan da ita. Ku kuma ɗauki kwalkwalin ceto, da takobin ruhu, wato Maganar Allah.” Idan muka duba a bisa ra’ayinmu na mutane, ɗamara na dukan makamai da Bulus ya kwatanta, tana kāre sojan Roma sa’ad da ya zaro takobinsa domin ya yi yaƙi da wani.
3. Me ya sa za mu yi biyayya da umurnin Yesu Kristi kuma mu bi misalinsa?
3 Ban da kayan yaƙi da horo, idan sojojin Roma na son su sami nasara, suna bukatar su yi wa shugabansu biyayya. Haka nan, dole ne Kiristoci su yi wa Yesu Kristi biyayya, wanda Littafi Mai Tsarki ya kwatanta “shugaban yaƙi na al’ummai.” (Ishaya 55:4) Kuma shi ne “shugaban ikilisiya.” (Afisawa 5:23) Yesu ya ba mu umurni game da yaƙinmu na ruhaniya kuma ya kafa mana kamiltaccen misali game da yadda za mu sha ɗamarar makamanmu na ruhaniya. (1 Bitrus 2:21) Tun da yake irin halayen Kristi sun yi daidai da ɗamararmu na makaman ruhaniya, Nassosi ya ba mu shawarar mu “ɗauki” irin wannan ra’ayi na Kristi. (1 Bitrus 4:1) Yayin da muke bincika kowane sashe na makamanmu na ruhaniya, za mu yi amfani da misalin Yesu wajen nuna muhimmanci da amfanin makaminmu na ruhaniya.
Kāre Ƙugu, Zuciya, da Ƙafafu
4. Wane matsayi ne ɗamara ke da shi wajen ɗaukan makamin soja, kuma menene wannan ke nunawa?
4 Gaskiya ta zama ɗamara. A lokacin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki, sojoji suna sanya ɗamara mai tsawo wadda ta yi faɗin inci biyu zuwa shida. Ɗamarar soja tana kāre ƙugunsa kuma tana da mariƙi, inda zai iya rataye takobinsa. Sa’ad da soja ya sha ɗamara, wannan na nuna cewa yana shirin yaƙi. Bulus ya yi amfani da ɗamarar soja domin ya nuna yadda gaskiyar da ke cikin Nassi ya kamata ya motsa rayuwarmu. A alamance, dole ne mu sha ɗamara sosai domin mu yi rayuwa cikin jituwa da gaskiya kuma mu kāre ta a kowane lokaci. (Zabura 43:3; 1 Bitrus 3:15) Saboda haka, muna bukatar mu yi nazarin Littafi Mai Tsarki sosai mu kuma yi bimbini a kan abubuwan da ke ciki. Yesu ya kiyaye dokar Allah a cikin ‘zuciyarsa.’ (Zabura 40:8) Sa’ad da ’yan adawa suka yi masa tambaya, ya mai da martani ta wurin karanta musu Nassosi da ya haddace.—Matiyu 19:3-6; 22:23-32.
5. Ka bayyana yadda shawarar Nassi za ta iya taimaka mana a lokacin gwaji.
5 Idan muka yarda gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki ya yi mana ja-gora, hakan zai kāre mu daga yin tunanin da bai da kyau kuma zai sa mu yanke shawarar da ta dace. Farillan Littafi Mai Tsarki za su ƙarfafa mu mu tsai da shawarar yin abin da ya dace sa’ad da muka fuskanci gwaji. Wato, zai kasance kamar muna ganin Mai Koyarwa Mai Girma, Jehovah, kuma za mu ji wata murya a bayanmu tana cewa: “Ga hanyan nan, ku bi ta.”—Ishaya 30:20, 21.
6. Menene ya sa zuciyarmu ta alama take son kāriya, kuma ta yaya ne adalci za ta iya kāre ta?
6 Adalci ya zama sulke. Sulken soja shi ke kāre masa zuciya. Zuciyarmu ta alama—mutum na ciki—tana bukatar muhimmiyar kāriya domin takan yi tunanin abin da ba shi da kyau. (Farawa 8:21) Saboda haka, dole ne mu sani kuma mu ƙaunaci mizanan adalci na Jehovah. (Zabura 119:97, 105) Ƙaunar adalci na sa mu ƙi tunani na duniya wanda ke sa mu ƙi ja-gorar Jehovah. Bugu da ƙari, idan muka ƙi mugunta kuma muka so nagarta, za mu guje wa tafarkin da zai iya lalata rayuwarmu. (Zabura 119:99-101; Amos 5:15) Yesu ya kafa misali mai kyau game da wannan, Nassosi ya ce haka game da shi: “Kā ƙaunaci aikin adalci, kā ƙi aikin saɓo.”—Ibraniyawa 1:9.a
7. Me ya sa sojojin Roma suke bukatar takalma masu ƙwari, kuma menene hakan ke nunawa?
7 Bisharar salama ta zama kamar takalmi a ƙafafu. A lokacin da za su tafi wajen yaƙi, sojojin Roma suna yin tafiya har na tsawon mil 20 kuma suna ɗauke da kayan yaƙi da makamai da suka kai nauyin kilo 27, saboda haka suna bukatar takalma masu ƙwari. Daidai da haka, Bulus ya yi amfani da takalmi ya kwatanta shirinmu na yin wa’azin saƙon Mulki ga duk wanda zai saurara. Wannan na da muhimmanci domin ta yaya ne mutane za su san Jehovah idan ba mu yi musu wa’azi ba?—Romawa 10:13-15.
8. Ta yaya za mu iya yin koyi da misalin Yesu na mai wa’azin bishara?
8 Wane aiki ne ya fi muhimmanci a rayuwar Yesu? Ya gaya wa Gwamnar Roma Bilatus Babunti: ‘Na shigo duniya, don in shaida gaskiya.’ Yesu ya yi wa’azi a duk inda ya sami mai sauraronsa, ya ji daɗin hidimarsa sosai har ya sa shi a gaba fiye da dukan bukatunsa. (Yahaya 4:5-34; 18:37) Idan muna ɗokin yin bishara kamar Yesu, za mu sami dama mai yawa na yi wa mutane bishara. Bugu da ƙari, idan muka duƙufa a cikin hidimarmu hakan zai taimaka mana mu kasance masu ruhaniya.—Ayyukan Manzanni 18:5.
Garkuwa, Kwalkwali, da Takobi
9. Wace irin kāriya ce babbar garkuwa take yi wa sojan Roma?
9 Garkuwar bangaskiya. Kalmar Helenanci da aka fassara “garkuwa” tana nufin babbar garkuwa wadda za ta iya kāre kusan dukan jiki. Za ta ba da kāriya daga ‘kiban wuta’ da aka ambata a Afisawa 6:16. A lokacin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki, sojoji suna amfani da kibiya da aka yi da kyauro da ƙananan ƙarafa da aka jika da dafi. Wani masani ya kwatanta wannan kibiya cewa “tana cikin makaman yaƙi mafi haɗari na dā.” Idan soja ba shi da babbar garkuwa da zai iya kāre kansa daga wannan makamin, za a iya ji masa mugun rauni ko a kashe shi.
10, 11. (a) Wace “kiban wutar” Shaiɗan ce za ta iya raunana bangaskiyarmu? (b) Ta yaya ne misalin Yesu ya nuna muhimmancin bangaskiya a lokatai masu wuya?
10 Wace irin ‘kiban wuta’ ce Shaiɗan yake amfani da ita don ya yi wa bangaskiyarmu zagon ƙasa? Yana iya jawo tsanani a cikin iyali, a wajen aiki, ko kuwa a makaranta. Sha’awar tara dukiya mai yawa da yin lalata ya halaka ruhaniyar wasu Kiristoci. Domin mu kāre kanmu daga irin wannan burga, dole ne mu “ɗauki garkuwar bangaskiya.” Ana samun bangaskiya daga yin koyi da Jehovah, yin magana da shi kullum a cikin addu’a, fahimtar yadda yake kāre mu da kuma yadda yake mana albarka.—Joshuwa 23:14; Luka 17:5; Romawa 10:17.
11 Sa’ad da yake a nan duniya, Yesu ya nuna muhimmancin kasancewa da bangaskiya mai ƙarfi a lokatai masu wuya. Ya dogara ne a kan shawarar Ubansa da kuma son yin nufin Allah. (Matiyu 26:42, 53, 54; Yahaya 6:38) Har ma sa’ad da yake cikin baƙin ciki a lambun Jathsaimani, Yesu ya ce wa Ubansa: “Ba nufina ba, sai naka.” (Matiyu 26:39) Yesu bai taɓa manta da muhimmancin riƙe aminci da kuma faranta wa Ubansa rai ba. (Karin Magana 27:11) Idan muka dogara ga Jehovah, ba za mu ƙyale sūka ko hamayya ta raunana bangaskiyarmu ba. A maimako, bangaskiyarmu za ta ƙarfafa idan muka dogara ga Allah, muka ƙaunace shi, kuma muka bi dokokinsa. (Zabura 19:7-11; 1 Yahaya 5:3) Babu dukiya ko sha’awa ta ɗan lokaci da za mu iya gwadawa da albarkar Jehovah da ke jiranmu.—Karin Magana 10:22.
12. Wane muhimmin sashe ne kwalkwali na alama yake kārewa a jikinmu, kuma me ya sa wannan kāriya yake da muhimmanci?
12 Kwalkwalin ceto. Kwalkwali yana kāre kai da ƙwaƙwalwar soja—tushen basira. An kwatanta begenmu na Kirista da kwalkwali domin yana kāre zuciyarmu. (1 Tasalonikawa 5:8) Ko da yake mun riga mun sabonta tunaninmu ta wurin tacaccen sani na Kalmar Allah, duk da haka, mu rarraunu da ajizan mutane ne. Zuciyarmu na iya ɓacewa. Makasudin zamanin nan na iya janye hankalinmu ko juya begen da Allah ya ba mu. (Romawa 7:18; 12:2) Ƙoƙarin Iblis ya zama banza sa’ad da ya so ya raba hankalin Yesu, “ya nunnuna masa dukan mulkokin duniya da ɗaukakarsu.” (Matiyu 4:8) Yesu ya ƙi abin da ya ba shi gabaki ɗaya, Bulus ya ce game da shi: “Domin farin cikin da aka sa gabansa [Yesu] ya daure wa [gungumen azaba], bai mai da shi wani abin kunya ba, yanzu kuma a zaune yake dama ga kursiyin Allah.”—Ibraniyawa 12:2.
13. Ta yaya ne za mu iya riƙe amincinmu a begen da ke nan gabanmu?
13 Irin amincin da Yesu yake da shi ba haka kawai ba ne. Idan muka sa zuciyarmu a kan abubuwan zamanin nan maimakon begen da ke gabanmu, bangaskiyarmu a alkawuran Allah za ta raunana. Da sannu sannu, muna iya rasa begenmu gabaki ɗaya. A wani ɓangare kuma, idan muka ci gaba da yin bimbini a kan alkawuran Allah, za mu ci gaba da yin murna cikin begen da ke nan gabanmu.—Romawa 12:12.
14, 15. (a) Menene takobinmu na alama, kuma ta yaya za mu iya amfani da shi? (b) Ka kwatanta yadda takobin ruhu zai iya taimaka mana mu tsayayya wa gwaji.
14 Takobin ruhu. Kalmar Allah ko saƙonsa da ke rubuce a cikin Littafi Mai Tsarki, ya yi kama da takobi mai kaifi wanda zai iya halaka addinin ƙarya kuma taimaka wa mutane masu zukatan kirki su sami ’yanci na ruhaniya. (Yahaya 8:32; Ibraniyawa 4:12) Wannan takobi na ruhu zai iya kāre mu sa’ad da muka fuskanci gwaji ko ’yan ridda da suke son su halaka bangaskiyarmu. (2 Korantiyawa 10:4, 5) Amma muna godiya cewa ‘kowane Nassi hurarre na Allah ne kuma shiryayye ne sarai domin kowane managarcin aiki’!—2 Timoti 3:16, 17.
15 Sa’ad da Shaiɗan ya jaraba shi a cikin jeji, Yesu ya yi amfani da takobin ruhu sosai domin ya kau da tunanin ƙarya da gwaji. Ga kowane gwaji na Shaiɗan, ya ce masa: “A rubuce yake.” (Matiyu 4:1-11) David, wani Mashaidin Jehovah a Spain, ya ga cewa Nassosi ya taimaka masa ya sha kan gwaji. Sa’ad da yake ɗan shekara 19, wata budurwa kyakkyawa da suke aiki tare a wani kamfanin share-share ta ce masa ya zo “su fita su more.” David ya ƙi yaudararta kuma ya gaya wa shugabansa ya sake masa wurin aiki domin kada hakan ya sake faruwa. “Na tuna misalin Yusufu,” in ji David. “Ya ƙi lalata kuma nan da nan ya bar wajen. Ni ma na yi hakan.”—Farawa 39:10-12.
16. Ka bayyana dalilin da ya sa muke bukatar koyarwa ‘domin mu fassara maganar gaskiya daidai.’
16 Yesu ya yi amfani da takobin ruhu ya taimaka wa mutane su tsira daga ikon Shaiɗan. “Koyarwata ba tawa ba ce,” in ji Yesu, “ta wanda ya aiko ni ce.” (Yahaya 7:16) Domin mu yi ƙwararriyar koyarwa irin ta Yesu, muna bukatar koyo. Game da sojojin Roma, ɗan tarihi Bayahude Josephus ya rubuta: “Kowane soja yana motsa jiki kowace rana, kuma yana yin hakan ne da ƙwazo kamar yana wajen yaƙi, hakan ya sa suke jimre wa gajiyar yaƙi.” A namu yaƙin na ruhaniya, muna bukatar yin amfani da Littafi Mai Tsarki. Bugu da ƙari, dole ne ‘mu himmantu, mu miƙa kanmu yardajje ga Allah, ma’aikaci wanda ba hanya ya kunyata, mai kuma fassarar Maganar gaskiya daidai.’ (2 Timoti 2:15) Kuma muna farin ciki ƙwarai sa’ad da muka yi amfani da Nassosi wajen amsa sahihiyar tambayar waɗanda suke son saƙon!
Ku Yi Addu’a Kullum
17, 18. (a) Wane matsayi ne addu’a ke da shi wajen yin tsayayya da Shaiɗan? (b) Ka ba da misalin da ya nuna muhimmancin addu’a.
17 Bayan mun yi la’akari da dukan makamai na ruhaniya, Bulus ya ba da wata muhimmiyar shawara. Sa’ad da suke ƙin Shaiɗan, dole ne Kiristoci su ba da kansu ga yin “addu’a da roƙo.” Sau nawa? Bulus ya rubuta: “Kullum kuna addu’a da roƙo ta ikon ruhu ba fasawa.” (Afisawa 6:18) Addu’a za ta ƙarfafa mu sa’ad da muke fuskantar gwaji, ko sanyin gwiwa. (Matiyu 26:41) Yesu “ya yi addu’o’i da roƙe-roƙe, tare da kuka mai tsanani, har da hawaye, ga wannan da ke da ikon cetonsa daga mutuwa, aka kuwa saurare shi saboda tsananin miƙa kansa.”—Ibraniyawa 5:7.
18 Milagros, wadda take kula da mijinta da yake rashin lafiya fiye da shekara 15 yanzu, ta ce: “Na kan juya wurin Jehovah cikin addu’a, sa’ad da na yi sanyin gwiwa. Babu wanda zai iya taimaka mini kamarsa. A wasu lokatai, na kan ji cewa ba zan iya ci gaba da jimrewa ba. Sau da yawa idan na yi addu’a ga Jehovah, sai in ji na sami wani sabon ƙarfi.”
19, 20. Menene muke bukata domin mu yi nasara a yaƙin da muke yi da Shaiɗan?
19 Iblis ya sani cewa yana da ƙanƙanin lokaci, kuma yana ƙara ƙoƙarce-ƙoƙarcensa domin ya ci nasara a kanmu. (Wahayin Yahaya 12:12, 17) Muna bukatar mu yi tsayayya da wannan abokin gāba mai ƙarfi kuma mu yi “faman gaske saboda bangaskiya.” (1 Timoti 6:12) Wannan na bukatan mafificin iko. (2 Korantiyawa 4:7) Muna bukatar taimakon ruhu mai tsarki na Allah, kuma sai mu yi addu’a don mu same shi. Yesu ya ce: “Ku da kuke mugaye ma kuka san yadda za ku ba ’ya’yanku kyautar kyawawan abubuwa, balle Ubanku na Sama zai ba da ruhu mai tsarki ga masu roƙonsa.”—Luka 11:13.
20 Babu shakka, yana da muhimmanci mu ɗauki dukan makamai na Jehovah. Ɗaukan waɗannan makamai na ruhaniya na bukatar mu koyi halayen da Allah ke so, kamar bangaskiya da aminci. Wannan ya bukaci cewa mu so gaskiya kamar ɗamara, kuma a shirye muke mu yi wa’azin bishara a kowane lokaci, da kuma sa begen da ke a gaba a cikin zuciyarmu. Dole mu koyi yadda ake yin amfani da takobi na ruhu sosai. Idan muka ɗauki dukan makamai na Allah, za mu ci nasara a kokawa da muke yi da mugayen ruhohi kuma wannan zai kawo ɗaukaka ga tsarkakken sunan Jehovah.—Romawa 8:37-39.
[Hasiya]
a A cikin annabcin Ishaya, an kwatanta Jehovah yana sanye da “sulken adalci.” Da haka, yana bukatar masu kula a cikin ikilisiya su nuna adalci da kuma gaskiya.—Ishaya 59:14, 15, 17.
Yaya Za Ka Amsa?
• Wanene ya kafa misali mafi kyau wajen ɗaukan makamai na ruhaniya, kuma me ya sa ya kamata mu yi la’akari da misalinsa sosai?
• Ta yaya ne za mu iya kāre hankalinmu da zuciyarmu ta alama?
• Ta yaya za mu iya zama ƙwararru a wajen sarrafa takobi na ruhu?
• Me ya sa ya kamata mu ci gaba da yin addu’a a kowane lokaci?
[Hotuna a shafi na 17]
Yin nazarin Littafi Mai Tsarki sosai zai motsa mu mu yi shelar bishara a kowane lokaci
[Hotuna a shafi na 18]
Tabbataccen begenmu na taimaka mana mu fuskanci gwaji
[Hotuna a shafi na 19]
Kuna amfani da “takobin ruhu” a hidima?