Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w07 4/1 pp. 16-20
  • Ta Yaya Za Mu Tsayayya Wa Aljanu?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ta Yaya Za Mu Tsayayya Wa Aljanu?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ta Yaya Shaiɗan da Aljanu Suka Wanzu?
  • Yaya Ikon Shaiɗan Yake?
  • Wace Kāriya Ce Muke da Ita?
  • Ta Yaya Za Ka “Tsaya” da Ƙarfi?
  • “Kuna Addu’a Kowane Loto”
  • “Ku Yi Ɗamara Da Dukan Makamai Na Allah”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Gaskiya Game da Mala’iku da Kuma Aljanu
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • “Ku Ƙarfafa Ga Ubangiji”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Ta Yaya Jehobah Yake Kāre Ka?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
w07 4/1 pp. 16-20

Ta Yaya Za Mu Tsayayya Wa Aljanu?

“Mala’iku kuma waɗanda ba su riƙe matsayi nasu ba, amma suka rabu da nasu wurin zama, [Allah] ya tsare su cikin madawaman sarƙoƙi a cikin dufu zuwa hukuncin babbar ranar.”—YAHUDA 6.

1, 2. Waɗanne tambayoyi ne aka yi game da Shaiɗan Iblis da aljanu?

MANZO Bitrus ya yi kashedi, “ku yi hankali shimfiɗe, ku yi zaman tsaro, magabcinku Shaiɗan, kamar zaki mai-ruri, yana yawo, yana neman wanda za ya cinye.” (1 Bitrus 5:8) Manzo Bulus ya ce game da aljanu: “Ba ni so fa ku yi zumunta da aljanu. Ba ku da iko ku sha ƙoƙon Ubangiji duk da na aljanu ba: ba ku da iko ku tara ci daga table na Ubangiji, da na aljanu ba.”—1 Korinthiyawa 10:20, 21.

2 Su waye ne Shaiɗan Iblis da kuma aljanu? Ta yaya suka soma wanzuwa kuma yaushe? Allah ne ya halicce su? Yaya yawan rinjayarsu wajen ’yan adam yake? Wace irin kāriya ce muke da ita dominsu?

Ta Yaya Shaiɗan da Aljanu Suka Wanzu?

3. Ta yaya mala’ikan Allah ya zama Shaiɗan Iblis?

3 Ba da daɗewa ba bayan somawar tarihin ’yan adam a lambun Adnin, wani mala’ikan Allah ya zama ɗan tawaye. Me ya sa? Domin bai gamsu da matsayinsa a tsarin Jehobah na samaniya ba. Da aka halicci Adamu da Hauwa’u, ya samu zarafi na juya biyayyarsu daga bauta wa Allah na gaskiya don su soma bauta masa. Ta wajen yin tawaye ga Allah da kuma sa mutane biyu na farko su bi tafarkin zunubi, wannan mala’ikan ya mai da kansa Shaiɗan Iblis. Da shigewar lokaci, wasu mala’iku suka bi shi yin tawaye. Ta yaya?—Farawa 3:1-6; Romawa 5:12; Ru’ya ta Yohanna 12:9.

4. Menene wasu mala’iku ’yan tawaye suka yi kafin Rigyawa na zamanin Nuhu?

4 Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa wani lokaci kafin babban Rigyawa na zamanin Nuhu, wasu mala’iku suka soma sha’awar mata da ke duniya. Don manufar da bai dace ba, “ya’yan Allah [na samaniya] suka ga yan mata na mutane kyawawa ne,” in ji Littafi Mai Tsarki, kuma “suka ɗauko wa kansu mata dukan waɗanda suka zaɓa.” Wannan jima’i ne da bai dace ba, kuma suka haifi ’ya’ya da ake kira Ƙattai. (Farawa 6:2-4) Halittu na ruhu da suka yi wa Allah rashin biyayya sun bi Shaiɗan a tawayensa ga Jehobah.

5. Menene ya sami ’yan tawayen sa’ad da Jehobah ya kawo halaka ta wurin babban Rigyawa?

5 Sa’ad da Jehobah ya kawo Rigyawa, Ƙattan da uwarsu suka mutu. Hakan ya tilasta wa mala’iku da suka yi tawaye su saki jikinsu na ’yan adam su koma lardi na ruhu. Amma ba su “riƙe matsayi nasu ba” da Allah. Maimakon haka, an saka su cikin “ramummuka [na ruhaniya] masu-dufu.”—Yahuda 6; 2 Bitrus 2:4.

6. Ta yaya aljanu suke ruɗin mutane?

6 Tun lokacin da mugayen mala’iku suka yi rashin ‘matsayinsu,’ sun zama abokan Shaiɗan kuma suna biyan bukatarsa. Tun daga lokacin, aljanun ba su da ikon canja jikinsu zuwa na ’yan adam. Amma, suna iya rinjayar maza da mata su yi lalata dabam dabam. Aljanu kuma suna ruɗin ’yan adam ta sihiri, da suka ƙunshi abubuwa kamar su dabo, yin tsafi, da masu duba. (Kubawar Shari’a 18:10-13; 2 Labarbaru 33:6) Abin da zai sami mugayen mala’iku ne zai sami Iblis, wato za a halaka su har abada. (Matta 25:41; Ru’ya ta Yohanna 20:10) Kafin lokacin, muna bukatar mu tsaya da ƙarfi mu yi tsayayya da su. Zai yi kyau idan muka bincika ikon Shaiɗan da kuma yadda za mu yi nasara wajen yin tsayayya da shi da aljanunsa.

Yaya Ikon Shaiɗan Yake?

7. Wane iko ne Shaiɗan yake da shi bisa duniya?

7 Shaiɗan ya tsegunta Jehobah a cikin tarihi. (Misalai 27:11) Kuma ya rinjayi ’yan adam da yawa. “Duniya duka kuwa tana kwance cikin Shaiɗan,” in ji 1 Yohanna 5:19. Shi ya sa Iblis ya gwada Yesu ta wajen ba shi iko da ɗaukaka na “dukan mulkokin duniya.” (Luka 4:5-7) Manzo Bulus ya ce game da Shaiɗan: “Amma dai idan bishararmu tana rufe, a rufe ta ke cikin waɗanda su ke lalacewa: a cikinsu kuwa allah na wannan zamani ya makantadda hankulan marasa-bada gaskiya, domin kada hasken bisharar darajar Kristi, wanda shi ke surar Allah, ya waye musu.” (2 Korinthiyawa 4:3, 4) Shaiɗan “maƙaryaci ne shi, da uban ƙarya kuma” amma ya mai da kansa “mala’ika na haske.” (Yohanna 8:44; 2 Korinthiyawa 11:14) Yana da iko da hanyoyin makantar da zukatan sarakunan duniya da talakawansu. Yana ruɗun ’yan adam ta hanyar labaran ƙarya da ƙage na addini .

8. Menene Littafi Mai Tsarki ya nuna game da rinjayar Shaiɗan?

8 Ƙarnuka biyar Kafin Zamaninmu, an ga ikon Shaiɗan da rinjayarsa a zamanin annabi Daniel. Sa’ad da Jehobah ya aika mala’ika ya je ya ƙarfafa Daniel, “[ruhun] sarkin mulkin Persia” ya yi tsayayya da mala’ikan. An tsayar da mala’ikan mai aminci kwana ashirin da ɗaya har sai da “Michael, ɗaya daga cikin manyan sarakuna,” ya zo ya taimake shi. Labarin kuma ya ambata “[aljan] sarkin Hellas.” (Daniel 10:12, 13, 20) A Ru’ya ta Yohanna 13:1, 2 an kira Shaiɗan “dragon” wanda yake ba wa bisa na siyasa “ikonsa da kursiyinsa da hukunci mai-girma.”

9. Kiristoci suna yaƙi da su wanene?

9 Shi ya sa manzo Bulus ya rubuta: ‘Kokawarmu ba da nama da jini ta ke ba, amma da mulkoki, da ikoki, da mahukuntan wannan zamani mai-duhu, da rundunai masu-ruhaniya na mugunta cikin sammai.’ (Afisawa 6:12) A yau, rundunar aljannu da ba a gani da ke ƙarƙashin ikon Shaiɗan Iblis, suna rinjayar sarakunan ’yan adam gabaki ɗaya, suna sa su yi mugun ayyuka kamar su kisan ƙare-dangi, ta’addanci, da kuma kisan kai. Bari yanzu mu bincika yadda za mu yi nasara wajen tsayayya wa waɗannan miyagun ruhohi.

Wace Kāriya Ce Muke da Ita?

10, 11. Ta yaya za mu tsayayya wa Shaiɗan da miyagun aljanunsa?

10 Ba za mu iya tsayayya wa Shaiɗan da miyagun aljanunsa ba da ƙarfinmu na zahiri ko kuma na hankali. Bulus ya yi gargaɗi: “Ku ƙarfafa cikin Ubangiji, cikin ƙarfin ikonsa kuma.” Muna bukatar mu je wurin Allah don kāriya. Bulus ya daɗa: “Ku yafa dukan makamai na Allah, domin ku sami ikon da za ku yi tsayayya da dabarun Shaiɗan . . . ku ɗauki dukan makamai na Allah, da za ku iya tsayayya cikin mugunyar rana, kuma bayanda an gama duka, a tsaya.”—Afisawa 6:10, 11, 13.

11 Sau biyu Bulus ya aririce Kiristoci masu bi su ‘yafa dukan makamai na Allah.’ Kalmar nan “duka” na nufin cewa tsayayya wa farmakin aljanu na bukatar yin hakan da dukan ƙarfinmu. Saboda haka, waɗanne abubuwa ne masu muhimmanci na makaman ruhaniya Kiristoci a yau suke bukata don su tsayayya wa aljanu?

Ta Yaya Za Ka “Tsaya” da Ƙarfi?

12. Ta yaya Kiristoci za su sha ɗamara da gaskiya?

12 Bulus ya ba da bayani: “Ku tsaya fa, kun rigaya kun ɗaure gindinku da gaskiya, kun yafa sulke na adalci.” (Afisawa 6:14) Makamai biyu da aka ambata a nan su ne ɗamara da sulke. Soja zai sha ɗamara don ya kāre ɗuwawunsa, da kuma ƙugunsa da zai ɗauki nauyin takobinsa. Hakanan ma, a alamance muna bukatar mu sha ɗamara sosai da gaskiyar Littafi Mai Tsarki, don mu yi rayuwa cikin jituwa da shi. Muna da tsarin karanta Littafi Mai Tsarki kullum? Dukan iyali ne suke karantawa? Muna da tsarin bincika nassosin yini kowace rana a iyalinmu? Ƙari ga haka, muna karanta bayanin da ke cikin littattafai da “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” ke tanadinsa kuwa? (Matta 24:45) Idan haka ne, muna iya ƙoƙarinmu mu bi gargaɗin Bulus. Muna da kaset na bidiyo da kuma faifai na DVD da za su ba da ja-gora na Nassi. Riƙe gaskiya gam gam zai taimake mu mu tsai da shawara mai kyau kuma ya kāre mu daga bin mugun tafarki.

13. Ta yaya za mu kāre zuciyarmu ta alama?

13 Sulke na zahiri na kāre kirji, da zuciya da kuma wasu gaɓoɓi masu muhimmanci na soja. Kirista zai iya kāre zuciyarsa ta alama, wato mutum da yake a ciki ta wajen ƙaunar adalci na Allah da kuma manne wa mizanan adalci na Jehobah. Sulke na alama yana hana mu rage muhimmancin Kalmar Allah. Yayin da muka “ƙi mugunta, [muka] ƙaunaci nagarta,” za mu guje wa “kowace hanyar mugunta.”—Amos 5:15; Zabura 119:101.

14. Menene ‘ɗaura wa sawayenmu shirin bishara ta salama’ take nufi?

14 Ana kāre ƙafafun sojojin Romawa da takalma da suka dace don doguwar tafiya na miloli da yawa a kan manyan hanyoyi na Roma da suka zagaya daular. Menene furcin nan ‘ɗaura wa sawayensu shirin bishara ta salama’ yake nufi ga Kiristoci? (Afisawa 6:15) Yana nufin cewa mun yi shirin aiki. Muna shirye mu yi wa’azin bishara ta Mulkin Allah a kowane lokaci da ya dace. (Romawa 10:13-15) Yin ƙwazo a hidima ta Kirista kāriya ce ga “dabarun” Shaiɗan.—Afisawa 6:11.

15. (a) Menene ya nuna cewa garkuwar bangaskiya tana da muhimmanci? (b) Waɗanne “dabaru” ne za su iya kasancewa da lahani ga bangaskiyarmu?

15 Bulus ya ci gaba: “Musamman kuma, ku ɗauki garkuwa ta bangaskiya, wadda za ku iya ɓice dukan jefejefe masu-wuta na Mugun da ita.” (Afisawa 6:16) An gabatar da shawarar ɗaukan garkuwa ta bangaskiya da furcin nan “musamman kuma,” hakan ya nuna cewa wannan makami yana da muhimmanci sosai. Ba za mu yi rashin bangaskiyarmu ba. Kamar garkuwa, bangaskiyarmu tana kāre mu daga “dabarun” Shaiɗan. Menene wannan yake wakilta a yau? Za su iya zama zagi, ƙarya, da rabin gaskiya da magabta da ’yan ridda suke amfani da su don su raunana bangaskiyarmu. Waɗannan “dabaru” za su iya zama gwaji na son abin duniya, da za su sa mu shagala da sayan kaya masu yawa da kuma sa mu riƙa gasa da waɗanda suke nuna arziki ta salon rayuwarsu. Wataƙila sun sayi manyan gidaje da motoci ko kuma suna nuna kayansu na ado masu tsada da tufafi da ake yayinsa. Ko menene wasu suka yi, ya kamata mu kasance da bangaskiya da take da ƙarfi don ta kawar da waɗannan “dabaru.” Ta yaya za mu samu kuma mu kasance da bangaskiya mai ƙarfi?—1 Bitrus 3:3-5; 1 Yohanna 2:15-17.

16. Menene zai taimake mu mu gina bangaskiya mai ƙarfi?

16 Za mu kusaci Allah ta wurin yin nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai da kuma yin addu’a sosai. Za mu roƙi Jehobah ya ƙarfafa bangaskiyarmu kuma mu aikata cikin jituwa da addu’o’inmu. Alal misali, muna shirya Nazarin Hasumiyar Tsaro sosai da nufin yin kalami? Bangaskiyarmu za ta yi ƙarfi idan muka yi nazarin Littafi Mai Tsarki da littattafan da ke bisa Littafi Mai Tsarki.—Ibraniyawa 10:38, 39; 11:6.

17. Ta yaya za mu “ɗauki kwalkwali na ceto”?

17 Bulus ya kammala kwatancinsa na makamai na ruhaniya da wannan gargaɗin: “Ku ɗauki kwalkwali na ceto kuma, da takobin Ruhu, watau maganar Allah.” (Afisawa 6:17) Kwalkwali na kāre kai da ƙwaƙwalwar soja, cibiyar yin shawara. Hakanan ma, begenmu na Kirista na kāre hankalinmu. (1 Tassalunikawa 5:8) Maimakon mu cika zuciyarmu da makasudi da sha’awoyi na duniya, ya kamata mu mai da hankalinmu ga begen da Allah ya ba mu, yadda Yesu ya yi.—Ibraniyawa 12:2.

18. Me ya sa ba za mu ƙyale tsarinmu na karanta Littafi Mai Tsarki kullum ba?

18 Kāriyarmu ta ƙarshe a kan rinjaya ta Shaiɗan da aljanunsa ita ce Kalmar Allah, ko saƙo da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Wannan ƙarin dalili ne da ya sa bai kamata mu yi banza da tsarin karanta Littafi Mai Tsarki a kai a kai ba. Cikakken sani na Kalmar Allah na kāre mu daga ƙaryace-ƙaryacen Shaiɗan da labarin ƙarya na aljanu da kuma furcin ƙiyayya na ’yan ridda.

“Kuna Addu’a Kowane Loto”

19, 20. (a) Menene ke jiran Shaiɗan da aljanunsa? (b) Menene zai ƙarfafa mu a ruhaniya?

19 Lokacin da za a kawar da Shaiɗan, aljanunsa da muguwar duniya ta kusa. Shaiɗan ya san cewa “sauran zarafinsa kaɗan ne.” Yana baƙin ciki kuma yana yaƙi da waɗanda “ke kiyaye umarnin Allah, suke kuma shaidar Yesu.” (Ru’ya ta Yohanna 12:12, 17) Yana da muhimmanci mu yi tsayayya da Shaiɗan da aljanunsa.

20 Ya kamata mu nuna cewa mun amince da gargaɗi mu yafa dukan makamai na Allah! Bulus ya kammala bayaninsa na makami na ruhaniya da wannan gargaɗi: “Kuna addu’a kowane loto cikin Ruhu da kowace irin addu’a da roƙo; kuna tsare wannan da iyakar naciya da roƙo saboda dukan tsarkaka.” (Afisawa 6:18) Addu’a za ta ƙarfafa mu a ruhaniya kuma ta taimake mu mu kasance a faɗake. Bari mu bi gargaɗin Bulus kuma mu ci gaba da yin addu’a, don wannan zai taimake mu mu yi tsayayya da Shaiɗan da aljanunsa.

Menene Ka Koya?

• Ta yaya Shaiɗan da aljanunsa suka wanzu?

• Yaya ikon Iblis yake?

• Wace kāriya ce muke da ita game da Shaiɗan da aljanunsa?

• Ta yaya za mu yafa dukan makamai na Allah?

[Hoto a shafi na 16]

“ ’Ya’yan Allah suka ga ’yan mata na mutane”

[Hoto a shafi na 18]

Za ka iya bayyana abubuwa shida da ke cikin makamanmu na ruhaniya?

[Hotuna a shafi na 19]

Ta yaya yin waɗannan ayyuka za su kāre mu daga Shaiɗan da aljanunsa?

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba