Ka Kusaci Allah
Mai Son Adalci
Ibraniyawa 10:26-31
KA TAƁA fuskantar mugunta, wataƙila daga wajen wani da ba a hukunta shi ba kuma bai yi nadama ba? Yana da wuya sosai a jimre irin wannan muguntar, musamman ma idan daga wajen wani ne da ya kamata ya ƙaunace ka ko kuma ya kula da kai. Za ka iya tambaya, ‘Me ya sa Allah ya ƙyale irin waɗannan abubuwa su faru?’a Gaskiyar ita ce Jehobah ya ƙi jinin kowace irin mugunta. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa Allah zai hukunta masu taurin zuciya da suka ƙi su yi abin da ya dace. Bari mu tattauna kalaman manzo Bulus da ke cikin Ibraniyawa 10:26-31.
Bulus ya rubuta: “Idan muna yin zunubi da nufin zuciyarmu bayanda mun karɓi sanin gaskiya, babu sauran wata hadaya domin zunubai.” (Aya 26) Ya dace a hukunta waɗanda suke aikata zunubin ganganci. Me ya sa? Na farko, zunubin da suke yi ba don kumamancinsu ba ne, wato irin kuskuren da muke yi don ajizancinmu. Suna yin zunubi ne a kai a kai. Na Biyu, suna yin zunubi da saninsu. Mugunta ta cika zuciyarsu saboda sun saba suna yi a kai a kai. Na uku, zunuban da suke yi ba don rashin sani ba ne. Domin sun “karɓi sanin gaskiya” game da nufin Allah da farillansa.
Ta yaya ne Allah yake ɗaukan masu zunubin ganganci da suka ƙi su tuba? Bulus ya ce: “Babu sauran wata hadaya domin zunubai.” Hadayar Kristi, wato, kyautar Allah ga ’yan adam ya rufe zunuban da muka yi saboda ajizancinmu. (1 Yohanna 2:1, 2) Amma waɗanda suke yin zunubi kuma sun ƙi tuba suna nuna cewa ba su daraja wannan kyauta mai tamani ba. A gaban Allah, sun ‘tattake Ɗan Allah . . . ƙalƙashin sawunsu, sun maida jinin [Yesu] abu mara-tsarki’. (Aya 29) Ta halayensu sun nuna cewa ba su daraja Yesu ba kuma sun mai da jininsa “abu mara-tsarki,” wato, marar tamani kamar na ɗan adam ajizi. Irin waɗannan marasa godiya ba za su amfana daga hadayar Kristi ba.
Menene sakamakon miyagu? Allah mai adalci ya yi alkawari: “Ɗaukan fansa nawa ne, ni in yi sakamako.” (Aya 30) Bari dukan waɗanda suke yin zunubi don su cuci wasu su lura. Ƙin yin biyayya ga dokar Allah zai kai ga hukunci. Sau da yawa, muguntan da suka yi yana shafan su. (Galatiyawa 6:7) A ƙarshe, za su fuskanci hukuncin Allah sa’ad da ya zo ya cire kowace irin mugunta a wannan duniyar. (Misalai 2:21, 22) Bulus ya yi gargaɗi: “Abin ban tsoro ne a fāɗa cikin hannuwan Allah mai-rai.”—Aya 31.
Sanin cewa Jehobah bai amince da zunubin ganganci ba yana da ƙarfafa musamman ga waɗanda aka yi wa mugunta. Da gaba gaɗi bari mu bar rama mugunta a hannun Allah, wanda ya ƙi jinin kowace irin mugunta.
[Hasiya]
a Don ka fahimci abin da ya sa Allah ya ƙyale wahala, ka duba shafuffuka na 106-114 a littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa.