“Sukan Bi Ɗan Ragon Inda Ya Tafi Duka”
“Su ne sukan bi Ɗan rago inda ya tafi duka.”—R. YOH. 14:4.
1. Yaya almajiran Yesu na gaskiya suka ji game da binsa?
MISALIN shekara biyu da rabi na hidimarsa, Yesu “yana koya ma mutane a cikin Kafarnahum.” Da yake a garesu suna ganin maganarsa tana da wuya, “dayawa a cikin almajiransa suka koma da baya, ba su ƙara tafiya tare da shi ba.” Sa’ad da Yesu ya tambayi manzanninsa sha biyu ko su ma suna son su tafi, Siman Bitrus ya ce: “Ubangiji, a wurin wa za mu tafi? kai ne da maganar rai na har abada. Mu kuwa mun rigaya mun bada gaskiya, kuma mun sani kai ne Mai-tsarki na Allah.” (Yoh. 6:48, 59, 60, 66-69) Almajiran Yesu na gaskiya ba su daina binsa ba. Bayan an shafa su da ruhu mai tsarki, sun ci gaba da bin umurnin Yesu.—A. M. 16:7-10.
2. (a) Wanene “bawan nan mai-aminci, mai-hikima,” ko kuma “wakili mai-aminci”? (b) Ta yaya bawan ya kafa tarihi mai kyau wajen ‘bin Ɗan rago inda ya tafi duka’?
2 Shafaffu Kiristoci na zamani kuma fa? A cikin annabcinsa game da ‘alamar zuwansa da cikar zamani,’ Yesu ya kira rukunin mabiyansa a duniya da aka shafa da ruhu, “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” ko kuma “wakili mai-aminci.” (Mat. 24:3, 45; Luk 12:42) A matsayin rukuni, bawan ya kafa tarihi mafi kyau wajen bin “Ɗan rago inda ya tafi duka.” (Karanta Ru’ya ta Yohanna 14:4, 5) Waɗanda suke cikin rukunin, budurwai ne a azanci na ruhaniya domin ba su ƙazantu ba da imani da ayyukan “Babila Babba,” daular duniya na addinin ƙarya. (R. Yoh. 17:5) Babu koyarwa ta ƙarya a “bakinsu,” kuma sun kasance “marasa-aibi” a duniyar Shaiɗan. (Yoh. 15:19) A nan gaba, shafaffu da suka rage a duniya za su “biyo” Ɗan Ragon har cikin sama.—Yoh. 13:36.
3. Me ya sa yake da muhimmanci mu amince da rukunin bawan nan?
3 Yesu ya naɗa bawan nan mai aminci mai hikima bisa “iyalin gidansa,” wato, mutane ɗai-ɗai da suke cikin rukunin bawan, su “ba su abincinsu a lotonsa.” Ya naɗa bawan nan “bisa dukan abin da ya ke da shi.” (Mat. 24:45-47) “Abin da ya ke da shi” ya haɗa da “taro mai-girma” na “waɗansu tumaki” da ke ƙaruwa. (R. Yoh. 7:9; Yoh. 10:16) Bai kamata ba ne mutane ɗai-ɗai da suke cikin shafaffu da kuma “taro mai-girma” su amince da bawan da aka naɗa ya kula da su? Da akwai dalilai da yawa da ya sa muke bukatar mu amince da rukunin bawan nan. Dalilai biyu masu muhimmanci su ne: (1) Jehobah ya amince da rukunin bawan. (2) Yesu ya amince da bawan. Bari mu bincika abin da ya nuna cewa Jehobah Allah da Yesu Kristi suna da cikakken tabbaci a bawan nan mai aminci mai hikima.
Jehobah Ya Amince da Bawan Nan
4. Me ya sa muke da tabbaci a abinci na ruhaniya da bawan nan mai aminci, mai hikima yake tanadinsa?
4 Ka yi la’akari da abin da ya sa ya yiwu bawan nan mai aminci, mai hikima yake mana tanadin abinci na ruhaniya a lotonsa. Jehobah ya ce: “Ni sanarda kai, ni koya maka cikin tafarkin da za ka bi.” Ya daɗa: “Da idona a kanka zan ba ka shawara.” (Zab. 32:8) Hakika, Jehobah yana yi wa bawan nan ja-gora. Saboda haka, muna da cikakken tabbaci a cikin basira, da fahimi da kuma ja-gora na ruhaniya da bawan nan yake mana.
5. Menene ya nuna cewa ruhun Allah yana ƙarfafa rukunin bawan nan?
5 Jehobah ya albarkaci rukunin bawan nan da ruhunsa mai tsarki. Ko da yake ba a ganin ruhun Jehobah, ana ganin aikin da yake sa waɗanda suke da shi su yi. Ka yi tunanin abin da bawan nan mai aminci, mai hikima ya cim ma ta wajen ba da shaida game da Jehobah Allah, da Ɗansa, da kuma Mulkin a dukan duniya. Masu bauta wa Jehobah suna shelar saƙon Mulki da ƙwazo a fiye da ƙasashe 230 da tsibirai. Hakan ya ba da tabbaci da ba za a iya ƙaryatawa ba cewa ruhun Allah ne yake ƙarfafa bawan nan. (Karanta Ayukan Manzanni 1:8.) Dole ne rukunin bawan nan su tsai da shawarwari da yawa masu muhimmanci domin su yi tanadin abinci na ruhaniya a lotonsa ga mutanen Jehobah a dukan duniya. Sa’ad da yake yanke shawarwarin, bawan nan yana nuna ƙauna, tawali’u, da kuma wasu fannoni na ɗiyar ruhu.—Gal. 5:22, 23.
6, 7. Yaya yawan yadda Jehobah ya amince da bawan nan mai aminci?
6 Don mu fahimci yawan yadda Jehobah ya amince da bawan nan mai aminci, ka yi tunanin alkawarin da ya yi wa waɗanda suke cikin rukunin. Manzo Bulus ya rubuta: “Ƙaho za shi yin ƙara, matattu kuma za su tashi marasa-ruɓuwa, mu kuma za mu sāke. Gama dole shi wannan mai-ruɓuwa za shi yafa rashin ruɓa, wannan mai-mutuwa kuwa shi yafa rashin mutuwa.” (1 Kor. 15:52, 53) Mabiyan Kristi shafaffu da suka bauta wa Allah da aminci kuma suka mutu da jiki mai ruɓa, za a ta da su daga matattu a matsayin halittun ruhu, da za su rayu har abada. Ba za su taɓa mutuwa ba kuma ba za a iya halaka su ba. Bugu da ƙari, an ba su jiki marar ruɓa kuma yana kiyaye kansa. Ru’ya ta Yohanna 4:4 ta kwatanta cewa waɗannan da aka ta da daga matattu suna zaune a kan kursiyi da kambi na zinariya a kansu. Ɗaukakar sarauta na jiran shafaffu Kiristoci. Akwai ƙarin tabbaci da ya nuna cewa Allah ya amince da su.
7 “Auren Ɗan rago ya zo, matatasa kuma ta shirya kanta. Aka yarda mata kuma ta yafa ma kanta linen mai-labshi, mai-walƙiya, mai-tsabta: gama linen nan mai-labshi ayuka masu-adilci na tsarkaka ne,” in ji Ru’ya ta Yohanna 19:7, 8. Jehobah ya zaɓi shafaffu Kiristoci su zama amaryar da Ɗansa zai aura a nan gaba. Rashin ruɓewa, marar mutuwa, sarauta, da kuma “auren Ɗan rago,” dukansu kyauta ne mai ban al’ajabi! Tabbaci ne mai ƙarfi da suka nuna cewa Allah ya amince da shafaffu, waɗanda suka ci gaba da bin “Ɗan rago inda ya tafi duka.”
Yesu Ya Amince da Bawan
8. Ta yaya ne Yesu ya nuna cewa yana da tabbaci a mabiyansa da aka shafa da ruhu?
8 Menene ya nuna cewa Yesu ya amince sosai da mabiyansa da aka shafa da ruhu? A darensa na ƙarshe na rayuwarsa a duniya, Yesu ya yi wa manzanninsa goma sha ɗaya masu aminci alkawari. Ya gaya musu: “Ku ne waɗanda kun lizimce ni a cikin jarabtuwana; ni ma na sanya maku mulki, kamar yadda Ubana ya sanya mani, domin ku ci, ku sha tare da ni cikin mulkina; kuma za ku zauna bisa kursiyai, kuna yin shari’a bisa kabilan Isra’ila goma sha biyu.” (Luk 22:28-30) Alkawarin da Yesu ya yi da manzanninsa goma sha ɗaya zai kai ga dukan Kiristoci shafaffu guda 144,000. (Luk 12:32; R. Yoh. 5:9, 10; 14:1) Yesu zai yi musu alkawarin da ya ƙunshi yin sarauta tare da shi inda bai gaskata da su ba?
9. Menene “dukan abin da [Kristi] ya ke da shi” ya ƙunsa?
9 Bugu da ƙari, Yesu Kristi ya naɗa bawan nan mai aminci, mai hikima “bisa dukan abin da ya ke da shi,” wato, dukan abubuwa game da Mulkin a duniya. (Mat. 24:47) Waɗannan abubuwa sun ƙunshi gine-gine na hedkwata na Shaidun Jehobah, ofishin reshe da ke ƙasashe dabam dabam, da kuma Majami’un Taro da Majami’un Mulki a dukan duniya. Wani abu kuma da hakan ya ƙunsa shi ne aikin wa’azin Mulki da almajirantarwa. Akwai wanda zai ba mutumin da bai amince da shi ba ajiya da kuma yin amfani da kayansa masu tamani?
10. Menene ya nuna cewa Yesu Kristi yana tare da mabiyansa shafaffu?
10 Jim kaɗan kafin ya koma sama, Yesu da aka ta da daga matattu ya bayyana ga almajiransa masu aminci kuma ya yi musu alkawari, yana cewa: “Ga, shi kuwa ina tare da ku kullayaumi har matuƙar zamani.” (Mat. 28:20) Yesu ya cika wannan alkawarin kuwa? A cikin shekaru 15 da suka shige, adadin ikilisiyoyin Shaidun Jehobah a dukan duniya ya ƙaru daga 70,000 zuwa fiye da 100,000, wato, an samu ƙaruwa na fiye da kashi 40. Sababbin almajirai nawa ne aka ƙara? Kusan almajirai miliyan huɗu da rabi ne aka yi wa baftisma a cikin shekaru 15 da suka shige, avirejin fiye da 800 a kowace rana. Waɗannan ƙaruwa mai yawa sun nuna sarai cewa Kristi yana yi wa mabiyansa shafaffu ja-gora a taron ikilisiyarsu kuma yana goyon bayansu a aikinsu na almajirantarwa.
Bawan nan Mai Aminci ne Kuma Mai Hikima
11, 12. Ta yaya bawan ya nuna cewa shi mai aminci ne kuma mai hikima?
11 Tun da Jehobah Allah da Yesu Kristi sun amince da bawan nan mai aminci mai hikima, bai kamata ba ne mu ma mu yi hakan? Ballantana ma, bawan nan ya nuna cewa shi mai aminci ne ta wajen yin aikin da aka sa shi. Alal misali, an yi shekaru 130 ana buga jaridar Hasumiyar Tsaro. Taron ikilisiya, manyan taro, da taron gunduma na Shaidun Jehobah suna ci gaba da ƙarfafa mu a ruhaniya.
12 Bawan nan mai aminci yana da hikima domin ya san iyakarsa, ba ya aikatawa kafin Jehobah ya ba da umurni, kuma ba ya rashin biyayya sa’ad da Allah ya ba da umurni sarai a kan wani batu. Alal misali, yayin da shugabannin addinai suka amince ko kuma suka yi na’am da halaye marar kyau na mutanen duniya, bawan nan ya yi kashedi game da tarkunan zamanin Shaiɗan. Bawan yana tanadin gargaɗi masu kyau na kan lokaci domin suna samun albarkar Jehobah Allah da kuma Yesu Kristi. Da haka, bawan ya cancanci mu amince da shi. Amma, ta yaya za mu nuna cewa mun amince da bawan nan mai aminci mai hikima?
Ku “Tafi tare da” Shafaffu Yayin da Suke Bin Ɗan Ragon
13. Bisa annabcin Zechariah, ta yaya zai yiwu mu nuna cewa mun amince da bawan nan mai aminci mai hikima?
13 Littafin Zechariah na Littafi Mai Tsarki ya ce “mutum goma” sun je wajen “Ba-yahudi,” kuma suka ce: “Za mu tafi tare da ku.” (Karanta Zechariah 8:23.) Tun da yake an kira “Ba-yahudi” “ku,” hakan yana wakiltar rukunin mutane. A zamaninmu, yana wakiltar shafaffu Kiristoci da suka rage, wato, sashen “Isra’ila na Allah.” (Gal. 6:16) “Mutum goma daga cikin dukan harsunan al’ummai” suna wakiltan taro mai girma na waɗansu tumaki. Kamar yadda shafaffu Kiristoci suke bin Yesu duk inda ya je, taro mai girma yana ‘bin’ bawan nan mai aminci kuma mai hikima. Bai kamata waɗanda suke cikin taro mai girma su ji kunyar nuna cewa suna tare da “masu-tarayya na kira basamaniya.” (Ibran. 3:1) Yesu ba ya jin kunyar kiran shafaffu, “yan-uwa.”—Ibran. 2:11.
14. Ta yaya za a tallafa wa ’yan’uwan Kristi da aminci?
14 Yesu Kristi yana ɗaukan tallafa wa ’yan’uwansa da ake yi a matsayin shi ne ake yi ma wa. (Karanta Matta 25:40.) A wace hanya ce waɗanda suke da begen zama a duniya suke tallafa wa ’yan’uwan Kristi shafaffu? Hanya ta musamman ita ce ta wajen taimakonsu a aikin wa’azin Mulki. (Mat. 24:14; Yoh. 14:12) Ko da yake adadin shafaffu a duniya ya ragu cikin shekarun da suka shige, adadin waɗansu tumaki ya ƙaru. Sa’ad da waɗanda suke da begen zama a duniya suke aikin ba da shaida, kuma suna hidima na cikakken lokaci idan ya yiwu, suna tallafa wa shafaffu ne a aikin almajirantarwa. (Mat. 28:19, 20) Ya kamata mu tuna zarafin da muke da shi na tallafa wa wannan aikin ta wajen ba da gudummawa ta kuɗi a hanyoyi dabam dabam.
15. Yaya ya kamata kowanne Kirista ya aikata ga abinci na ruhaniya na kan lokaci da bawan nan yake tanadinsa da kuma shawarwari da yake yi game da ƙungiyar?
15 A matsayinmu na Kiristoci, ta yaya kowannenmu yake ɗaukan abinci na ruhaniya na kan lokaci da bawan nan mai aminci yake bayarwa ta wajen littattafai da ke bisa Littafi Mai Tsarki da kuma taronmu dabam dabam na Kirista? Muna cin abincin kuwa kuma mu yi amfani da abin da muka koya? Yaya muke aikatawa ga shawarwari game da ƙungiya da bawan nan ya yi? Yin biyayya da yardan rai ga umurnin da aka ba da yana nuna cewa mun yi imani da tsarin da Jehobah ya kafa.—Yaƙ. 3:17.
16. Me ya sa ya kamata dukan Kiristoci su saurari ’yan’uwan Kristi?
16 Yesu ya ce: “Tumakina suna jin muryata, na kuwa san su, suna biyona kuma.” (Yoh. 10:27) Hakan gaskiya ce game da shafaffu Kiristoci. Waɗanda suke ‘tafiya tare’ da su kuma fa? Dole ne waɗannan su saurari Yesu. Kuma dole ne su saurari ’yan’uwansa. Ballantana ma, an ba su hakki na musamman na kula da lafiyar ruhaniya na mutanen Allah. Menene saurarar muryar ’yan’uwan Kristi ya ƙunsa?
17. Menene saurarar rukunin bawan nan ya ƙunsa?
17 Hukumar Mulki ce take wakiltar bawan nan mai aminci mai hikima, da take ja-gora da kuma tsara aikin wa’azin Mulki a dukan duniya. Waɗanda suke cikin Hukumar Mulki dattawa ne ƙwararru kuma shafaffu na ruhu. Ana iya kwatanta su da ‘waɗanda su ke shugabanninmu.’ (Ibran. 13:7) Sa’ad da suke kula da masu shelar Mulki kusan 7,000,000 a ikilisiyoyi fiye da 100,000 a dukan duniya, waɗannan shafaffu masu kula suna “yawaita cikin aikin Ubangiji.” (1 Kor. 15:58) Saurarar rukunin bawan nan yana nufin mu ba da cikakken haɗin kai ga Hukumar Mulki.
Waɗanda Suka Saurari Bawan Sun Samu Albarka
18, 19. (a) Ta yaya aka albarkaci waɗanda suka saurari bawan nan mai aminci kuma mai hikima? (b) Menene ya kamata ya zama ƙudurinmu?
18 Tun lokacin da aka naɗa shi, rukunin bawan nan mai aminci kuma mai hikima yana “juya mutane dayawa kuma zuwa adilci.” (Dan. 12:3) Waɗannan sun haɗa da waɗanda suke da begen tsira daga halakar wannan mugun zamani. Wannan kasancewa da adalci a gaban Allah albarka ce sosai!
19 A nan gaba, sa’ad da ‘birni mai tsarki, sabuwar Urushalima [da ta haɗa da 144,000] tana saukowa daga sama daga wurin Allah, shiryayya kamar amarya da ado domin mijinta,’ menene waɗanda suka saurari muryar bawan nan za su shaida? “Allah kuma da kansa za ya zauna tare da su,” in ji Littafi Mai Tsarki. “Za ya share dukan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙin zuciya, ko kuka, ko azaba: al’amura na fari sun shuɗe.” (R. Yoh. 21:2-4) Saboda haka, bari mu saurari Kristi da kuma amintaccen ’yan’uwansa shafaffu na ruhu.
Menene Ka Koya?
• Wane tabbaci muke da shi cewa Jehobah ya amince da bawan nan mai aminci, mai hikima?
• Menene ya nuna cewa Yesu Kristi ya tabbata da rukunin bawan nan?
• Me ya sa ya dace mu amince da wakilin nan mai aminci?
• Ta yaya za mu nuna cewa mun amince da bawan nan?
[Hotunan da ke shafi na 25]
Ka san wadda Jehobah ya zaɓa ta zama amarya ta gaba na Ɗansa?
[Hotunan da ke shafi na 26]
Yesu Kristi ya ba bawan nan mai aminci, mai hikima “abin da yake da shi”
[Hotunan da ke shafi na 27]
Sa’ad da muke yin aikin wa’azi, muna tallafa wa waɗanda aka shafa da ruhu