Wani ‘Bawa’ Da Yake Da Aminci Da Kuma Hikima
“Wanene fa bawan nan mai-aminci, mai-hikima wanda ubangijinsa ya sanya shi bisa iyalin gidansa?”—MATTA 24:45.
1, 2. Me ya sa yake da muhimmanci mu riƙa samun abinci na ruhaniya a yau a kai a kai?
RANAR talata da rana, 11 ga Nisan, shekara ta 33 A.Z., almajiran Yesu sun yi tambaya da take da ma’ana sosai a gare mu a yau. Sun yi masa tambaya: “Me ne kuma alamar zuwanka da cikar zamani?” Yesu ya ba da amsar annabci mai girma. Ya yi maganar lokacin hargitsi na yaƙe-yaƙe, yunwa, girgizar ƙasa, da cututtuka. Kuma wannan zai zama “al’amura mafarin wahala.” Yanayin zai yi muni. Lallai zato ne na ban razana!—Matta 24:3, 7, 8, 15-22; Luka 21:10, 11.
2 Tun shekara ta 1914, yawancin fannoni na annabcin Yesu sun cika. ’Yan Adam suna shan “wahala” sosai. Amma, Kiristoci na gaskiya ba sa bukatar jin tsoro. Yesu ya yi alkawari zai kiyaye su da abinci mai gina jiki na ruhaniya. Tun da yake Yesu yana sama yanzu, yaya ya shirya mu riƙa samun abinci na ruhaniya a nan duniya?
3. Wane shiri Yesu ya yi don mu sami ‘abinci a lotonsa’?
3 Yesu da kansa ya ba da amsar wannan tambaya. Da yake annabcin, ya yi tambaya: “Wanene fa bawan nan mai-aminci, mai-hikima wanda ubangijinsa ya sanya shi bisa iyalin gidansa, domin shi ba su abincinsu a lotonsa?” Sai ya ce: “Wannan bawa mai-albarka ne, wanda ubangijinsa sa’anda ya zo za ya iske shi yana yin haka. Hakika, ina ce muku, za ya sanya shi bisa dukan abin da ya ke da shi.” (Matta 24:45-47) Hakika, za a yi ‘bawa’ da aka ba wa aikin ya riƙa tanadin abinci na ruhaniya, “bawan” da yake da aminci da kuma hikima. Wannan bawan mutum ɗaya ne, rukunin mutane ko kuma wani abu dabam? Tun da yake bawan mai aminci yana tanadin abinci na ruhaniya da ake bukata sosai, muna son mu sami amsar.
Mutum Ɗaya ne ko Kuma Rukuni?
4. Ta yaya muka sani cewa “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” ba zai zama mutum ɗaya ba?
4 “Bawan nan mai-aminci, mai-hikima” ba zai zama mutum ɗaya ba. Me ya sa? Domin bawan ya soma ba da abinci na ruhaniya a can ƙarni na farko, kuma in ji Yesu, har ila bawan zai riƙa yin hakan sa’ad da Ubangijin ya zo a shekara ta 1914. Wannan da zai zama shekaru 1,900 na hidima da aminci na mutum ɗaya. Har Methuselah ma bai yi rayuwa na dogon lokaci haka ba!—Farawa 5:27.
5. Ka bayyana abin da ya sa furcin nan “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” ba ya nufin kowanne Kirista.
5 To, furcin nan “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” yana nufin kowanne Kirista ne? Gaskiya ne cewa dukan Kiristoci dole ne su kasance da aminci da kuma hikima; amma, Yesu yana nufin wani abu sa’ad da ya yi maganar “bawan nan mai-aminci, mai-hikima.” Yaya muka sani? Domin ya ce ‘ubangijin sa’anda ya zo’ zai danƙa wa bawan ‘dukan abin da yake da shi.’ Ta yaya za a danƙa wa kowane Kirista kome—bisa “dukan” abin da Ubangijin yake da shi? Ba zai yiwu ba!
6. Me ya sa ake son al’ummar Isra’ila ta zama ‘bara’ ko kuma ‘bawa’ na Allah?
6 Zai yi kyau a kammala cewa Yesu yana maganar rukunin Kiristoci, cewa sune “bawan nan mai-aminci, mai-hikima.” Zai yiwu a ce wannan yana nufin haɗaɗɗen bawa? E. Shekara ɗari bakwai kafin Kristi, Jehovah ya kira dukan al’ummar Isra’ila “shaiduna” kuma ‘barana wanda na zaɓa.’ (Ishaya 43:10) Kowanne da yake cikin al’ummar Isra’ila daga 1513 K.Z., sa’ad da aka ba da Dokar Musa, zuwa Fentakos na shekara ta 33 A.Z., yana cikin wannan rukunin baran. Yawancin Isra’ilawa ba su sa hannu a kula da harkokin al’ummar ba ko kuma gudanar da tsarin cin abinci na ruhaniya. Jehovah ya yi amfani da sarakuna, alƙalai, annabawa, firistoci, da Lawiyawa su yi waɗannan ayyuka. Duk da haka, al’ummar Isra’ila za ta wakilci ikon mallakar Jehovah kuma tana yabonsa tsakanin al’ummai. Kowanne Ba’isra’ile zai zama mashaidin Jehovah.—Kubawar Shari’a 26:19; Ishaya 43:21; Malachi 2:7; Romawa 3:1, 2.
An Sallami Wani ‘Bara’
7. Me ya sa al’ummar Isra’ila ta dā ba su cancanta su zama ‘bara’ na Allah ba?
7 Tun da yake Isra’ila ‘baran’ Allah ne ƙarnuka da daɗewa, ita ce bawan da Yesu ya yi magana game da shi? A’a, abin baƙin ciki ne cewa Isra’ila ta dā ba su kasance masu aminci ko kuma masu hikima ba. Bulus ya taƙaita yanayin sa’ad da ya yi ƙaulin kalmomin Jehovah ga al’ummar: “A wurin Al’ummai ana saɓon sunan Allah saboda ku.” (Romawa 2:24) Hakika, Isra’ila suna da tarihin tawaye na ƙin Yesu, shi ya sa Jehovah ya ƙi su.—Matta 21:42, 43.
8. Yaushe ne aka naɗa ‘baran’ da ya sake Isra’ila, kuma a wane yanayi?
8 Wannan rashin aminci na ‘baran,’ Isra’ila, ba ya nufin cewa masu bauta da suke da aminci ba za su taɓa sake samun abinci na ruhaniya ba. Kwanaki hamsin bayan tashin Yesu daga matattu, a Fentakos na shekara ta 33 A.Z., an zuba ruhu mai tsarki a kan almajiransa 120 a ɗakin gidan bene a Urushalima. A lokacin ne aka haifi sabuwar al’umma. Yadda ya dace, an yi shelar haihuwarta sa’ad da almajiran suka soma gaya wa mazaunan Urushalima game da “ayyuka masu-girma na Allah” da gaba gaɗi. (Ayukan Manzanni 2:11) Da haka, wannan sabuwar al’umma, al’umma ta ruhaniya ta zama ‘bara’ da zai yi shelar ɗaukakar Jehovah ga al’ummai kuma ya ba da abinci a lotonsa. (1 Bitrus 2:9) Daidai, daga baya aka kira ta “Isra’ila na Allah.”—Galatiyawa 6:16.
9. (a) Su wanene “bawan nan mai-aminci, mai-hikima”? (b) Su waye ne ‘iyalin gidan’?
9 Kowanne mutum da yake cikin “Isra’ila na Allah” Kirista ne da ya keɓe kansa ya yi baftisma kuma aka shafa shi da ruhu mai tsarki, yana da begen zama a sama. Saboda haka, furcin nan “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” yana nuni ga dukan waɗanda suke cikin wannan al’umma ta ruhaniya da aka shafe su da suke da rai a duniya daga shekara ta 33 A.Z., har zuwa yanzu, yadda kowanne Ba’isra’ile da yake da rai daga shekara ta 1513 K.Z., har zuwa Fentakos na shekara ta 33 A.Z., yake cikin rukunin bara kafin Kiristanci. Amma, su waye ne ‘iyalin gidan,’ da suke samun abinci na ruhaniya daga bawan? A ƙarni na farko A.Z., kowane Kirista yana da begen zuwa sama. Domin haka, iyalin gidan su ma shafaffun Kiristoci ne, da ake ɗaukansu mutane ɗaɗɗaya ba rukuni ba. Duka, har da waɗanda suke da matsayi cikin ikilisiyar, suna bukatar abinci na ruhaniya daga bawan.—1 Korinthiyawa 12:12, 19-27; Ibraniyawa 5:11-13; 2 Bitrus 3:15, 16.
“Ga Kowanne Kuma Aikinsa”
10, 11. Ta yaya muka sani cewa ba dukan waɗanda suke cikin rukunin bawa suke da aiki iri ɗaya ba?
10 Ko da yake “Isra’ila na Allah” ita ce rukunin bawan nan mai aminci kuma mai hikima da suke da aiki, kowanne yana da hakkinsa. Kalmomin Yesu da ke rubuce a Markus 13:34 ya bayyana wannan sarai. Ya ce: ‘Kamar mutum da ya ke baƙunci a cikin wata ƙasa, ya rigaya ya rabu da gidansa, ya bada iko ga bayinsa, ga kowane kuma aikinsa, ya umurci sarkin ƙofa shi yi tsaro.’ Saboda haka, kowanne cikin rukunin bawan ya samu aiki—ya ƙara iyalin gidan Kristi ta duniya. Kowanne cikin waɗannan yana wannan aikin bisa ga iyawarsa da kuma zarafi.—Matta 25:14, 15.
11 Ƙari ga haka, manzo Bitrus ya gaya wa Kiristoci shafaffu na zamaninsa: ‘Yayinda kowa ya karɓi baiko, kuna yi ma junanku hidima da shi, kamar nagargarun wakilai na alherin Allah iri iri masu-yawa.’ (1 Bitrus 4:10) Saboda haka, waɗannan shafaffu suna da hakkin su yi wa juna hidima su kuma yi amfani da kyauta da Allah ya ba su. Ƙari ga haka, kalmomin Bitrus ya nuna cewa ba dukan Kiristoci za su kasance da iyawa, hakki, ko kuma gata daidai da juna ba. Amma, kowanne cikin rukunin bawan zai iya taimako a wata hanya ga ƙaruwar al’umma ta ruhaniya. Ta yaya?
12. Ta yaya kowanne cikin rukunin bawan, namiji ko tamace, suke taimako ga ƙaruwan bawan?
12 Na farko, ana bukatar kowanne ya zama mashaidin Jehovah, yana wa’azin bishara na Mulkin. (Ishaya 43:10-12; Matta 24:14) Kafin ya hau sama, Yesu ya umurci dukan almajiransa masu aminci, maza da mata su zama masu koyarwa. Ya ce: ‘Ku tafi fa, ku almajirtadda dukan al’ummai, kuna yi musu baftisma zuwa cikin sunan Uba da na Ɗa da na Ruhu Mai-tsarki: kuna koya musu su kiyaye dukan iyakar abin da na umurce ku: ga shi kuwa ina tare da ku kullayaumi har matuƙar zamani.’—Matta 28:19, 20.
13. Wace gata duka shafaffu suka mora?
13 Sa’ad da aka sami sababbin almajirai, za a koya musu sosai su kiyaye dukan abin da Kristi ya umurci almajiransa. Da shigewar lokaci, waɗanda suka yi na’am suka cancanci su koya wa wasu. Aka yi wa waɗanda za su zama rukunin bawan a cikin al’ummai da yawa tanadin abinci na ruhaniya. Dukan shafaffu Kiristoci, maza da mata suka sa hannu a aikin almajirantarwa. (Ayukan Manzanni 2:17, 18) Wannan aikin zai ci gaba daga lokacin da bawan ya soma aikinsa har zuwa ƙarshen wannan zamani.
14. Su wanene kaɗai suke da gatar koyarwa cikin ikilisiya, kuma yaya mata shafaffu masu aminci suke ji game da hakan?
14 Sababbin shafaffu da suka yi baftisma sun zama ɓangaren bawan, ko da wanene ya koyar musu a farko sun ci gaba da samun koyarwa daga waɗanda suke cikin ikilisiya da suka cika farillai na Nassi su yi hidima ta dattawa. (1 Timothawus 3:1-7; Titus 1:6-9) Da haka waɗannan maza shafaffu suna da zarafin taimako a ƙaruwar al’ummar a hanya ta musamman. Mata Kiristoci shafaffu ba su yi tsayayya ba cewa maza Kiristoci ne kaɗai suke aikin koyarwa cikin ikilisiya. (1 Korinthiyawa 14:34, 35) Akasin haka, suna farin ciki su amfana daga aikin da maza cikin ikilisiya suke yi da ƙwazo kuma suna godiya da gata da mata suke da shi, har da kai wa mutane albishiri mai daɗi. ’Yan’uwa mata shafaffu masu himma a yau suna nuna irin wannan halin tawali’u, ko dattawan shafaffu ne ko ba shafaffu ba.
15. Menene ɗaya cikin ainihin tushen abinci na ruhaniya a ƙarni na farko, su waye ne suka yi ja-gorar ba da abincin?
15 Abinci na ruhaniya na musamman da aka bayar a ƙarni na farko ya fito daga wasiƙun manzanni da kuma wasu almajirai da suke shugabanci. Wasiƙu da suka rubuta—musamman waɗanda suke cikin hurarrun littattafai 27 na Nassosin Kirista na Helenanci—sun bazu tsakanin ikilisiyoyi kuma babu shakka sun zama tushen koyarwa da dattawa suke yi. Ta haka, wakilan bawan suka rarraba abinci na ruhaniya mai kyau ga sahihan Kiristoci. Ajin bawa na ƙarni na farko sun kasance da aminci ga aikinsu.
Yadda “Bawan” Yake Bayan Ƙarnuka 19
16, 17. Ta yaya ajin bawa suka kasance da aminci wajen cika aikinsu har zuwa shekaru na 1914?
16 Yau kuma fa? Sa’ad da bayyanuwar Yesu ya soma a shekara ta 1914, ya sami rukunin Kiristoci shafaffu da suke ba da abinci a lotonsa da aminci? Babu shakka. Ana iya gane wannan rukunin ta ’ya’ya masu kyau da suke bayarwa. (Matta 7:20) Tarihi ya nuna cewa wannan kammalawa ne da ya dace.
17 A lokacin da Yesu ya zo, misalin mutane 5,000 na iyalin gidansa sun taƙure suna yaɗa gaskiyar Littafi Mai Tsarki. Masu aikin kaɗan ne, amma bawan ya yi amfani da hanyoyi masu motsawa don a yaɗa bisharar. (Matta 9:38) Alal misali, an yi shiri a buga jawabai a kan jigon Littafi Mai Tsarki a jaridu na labarai kusan 2,000. Ta haka, masu karatu dubbai suka ji saƙon Kalmar Allah a lokaci ɗaya. Ƙari ga haka, an shirya tsarin ayyuka na sa’o’i takwas da ya haɗa da hotuna da kuma majigi mai motsi. Ta wannan nuni mai motsawa, mutane fiye da miliyan tara a nahiyoyi uku sun kalli saƙon Littafi Mai Tsarki, daga somawar Halitta zuwa ƙarshen Sarautar Kristi ta Shekara Dubu. An yi amfani da littattafai kuma. Alal misali, a shekara ta 1914 an buga kofi 50,000 na wannan jarida.
18. Yaushe ne Yesu ya ba wa bawan dukan abin da yake da shi, me ya sa?
18 Hakika, sa’ad da Ubangijin ya zo, ya iske bawansa mai aminci yana ciyar da iyalin gidansa sosai kuma yana wa’azin bishara. Hakki mai girma yanzu na jiran bawan nan. Yesu ya ce: “Hakika, ina ce muku, za ya sanya shi bisa dukan abin da ya ke da shi.” (Matta 24:47) Yesu ya yi hakan a shekara ta 1919, bayan bawan ya jimre wa lokacin gwaji. Me ya sa, “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” ya sami ƙarin hakki? Domin abin da Ubangijin yake da shi ya ƙaru. An naɗa Yesu ya soma sarauta a shekara ta 1914.
19. Ka bayyana yadda ake biyan bukatu na ruhaniya na “taro mai-girma.”
19 Menene sabon Ubangijin da aka naɗa shi yake da shi da ya ba wa bawansa mai aminci? Dukan abubuwa na ruhaniya da yake da shi a nan duniya. Alal misali, shekara ashirin bayan da aka naɗa Kristi a shekara ta 1914, aka gano “taro mai-girma” na “waɗansu tumaki.” (Ru’ya ta Yohanna 7:9; Yohanna 10:16) Waɗannan ba shafaffu ba ne da suke cikin “Isra’ila na Allah,” amma sahihan maza da mata da suke da begen zama a duniya da suke ƙaunar Jehovah kuma suna son su bauta masa yadda shafaffu suka yi. Wato, sun ce wa “bawan nan mai-aminci, mai-hikima”: “Za mu tafi tare da ku, gama mun ji labari Allah yana tare da ku.” (Zechariah 8:23) Waɗannan Kiristoci da suka yi baftisma ba da daɗewa ba suna cin abinci mai kyau na ruhaniya da iyalin gidan shafaffu suke ci, kuma rukuni biyun suna cin wannan abinci na ruhaniya tare tun lokacin. Wannan albarka ce ga waɗanda suke cikin “taro mai-girma”!
20. Yaya “taro mai-girma” suka ƙara abin da Ubangijin yake da shi?
20 Waɗanda suke cikin “taro mai-girma” da farin ciki suna bin rukunin shafaffen bawan a wa’azin bishara. Yayin da suke wa’azi, abin da Ubangiji yake da shi a duniya ya ƙaru, kuma ya daɗa hakkin “bawan nan mai-aminci, mai-hikima.” Yayin da adadin masu neman gaskiya suke ƙaruwa, ya zama wajibi a faɗaɗa wuraren da ake buga littattafai domin a ƙosar da masu bukatar littattafai na tushe daga Littafi Mai Tsarki. An kafa ofisoshin rassa na Shaidun Jehovah a ƙasashe da yawa. An aika da masu wa’azi na ƙasashen waje zuwa “iyakan duniya.” (Ayukan Manzanni 1:8) Daga misalin shafaffu dubu biyar a shekara ta 1914, masu yabon Allah sun ƙaru fiye da miliyan shida a yau, yawancinsu kuma suna cikin “taro mai-girma.” Hakika, abin da Sarkin yake da shi ya ƙaru sosai tun lokacin da aka naɗa shi a shekara ta 1914!
21. Waɗanne almara biyu ne za mu bincika a nazarinmu na gaba?
21 Dukan waɗannan sun nuna cewa bawan yana da ‘aminci da kuma hikima.’ Bayan ya yi maganar “bawan nan mai-aminci, mai-hikima,” Yesu ya faɗi almara biyu da ta nanata waɗannan halaye: almarar budurwoyi masu hikima da marasa azanci da kuma almarar talinti. (Matta 25:1-30) An ta da marmarinmu! Mecece ma’anar waɗannan almarar a gare mu a yau? Za mu bincika wannan tambaya a talifi na gaba.
Me Kake Tsammani?
• Su wanene “bawan nan mai-aminci, mai-hikima”?
• Su wanene ‘iyalin gidan’?
• Yaushe ne aka ba bawan nan mai aminci dukan abin da Ubangiji yake da shi, kuma me ya sa aka yi hakan a lokacin?
• Su wanene suka taimaka wajen ƙara abin da Ubangiji yake da shi a shekarun bayan nan, kuma ta yaya?
[Hotuna a shafi na 22]
Rukunin bawa na ƙarni na farko sun kasance da aminci ga aikinsu