Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 10/15 pp. 20-25
  • Kana Sa Hannu Wajen Sa Taron Kirista Ya Kasance Da Ban Ƙarfafa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kana Sa Hannu Wajen Sa Taron Kirista Ya Kasance Da Ban Ƙarfafa?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Taron da Aka Shirya don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Ƙarin Lokaci don Mu Furta Bangaskiyarmu
  • “Bari Mu Mika Hadaya ta Yabo ga Allah Kullayaumi”
  • Tarurruka da Ke ‘Ginawa, Gargaɗar da Kuma Ba da Ta’aziya’
  • Wurin Kwanciyar Hankali
  • Me Ya Sa Ya Kamata Mu Rika Halartan Taro don Ibada?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Ta Yaya Za Ka Amfana Daga Taron Shaidun Jehobah?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Yin Taro don Ibada
    Mulkin Allah Yana Sarauta!
  • Mu Yabi Jehobah a Cikin Ikilisiya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 10/15 pp. 20-25

Kana Sa Hannu Wajen Sa Taron Kirista Ya Kasance Da Ban Ƙarfafa?

“Lokacin da kun taru wuri ɗaya, . . . bari a yi kome domin ginawa.”—1 KOR. 14:26.

1. In ji 1 Korintiyawa sura ta 14, taron Kirista yana da wace manufa mai muhimmanci?

‘WANNAN taron yana da ban ƙarfafa!’ Ka taɓa furta hakan bayan ka halarci taro a Majami’ar Mulki? Babu shakka ka yi hakan! Taron ikilisiya tushen ƙarfafa ne, amma wannan ba abin mamaki ba ne. Ballantana ma, kamar yadda yake a zamanin Kiristoci na farko, manufa mai muhimmanci na taronmu a yau ita ce don a ƙarfafa dukan waɗanda suka halarta a ruhaniya. Ka lura da yadda manzo Bulus ya nanata wannan makasudi na taron Kirista a wasiƙarsa ta farko zuwa ga Korintiyawa. A cikin dukan sura ta 14 ya faɗa a kai a kai cewa ya kamata kowane sashe da aka gudanar a taron ikilisiya ya kasance da irin wannan makasudina ‘ƙarfafa ikilisiya.’—Karanta 1 Korintiyawa 14:3, 12, 26.a

2. (a) Mene ne ke sa taro ya kasance da ban ƙarfafa? (b) Wace tambaya ce za mu bincika?

2 Mun fahimci cewa ruhun Allah ne ke sa taro ya kasance da ban ƙarfafa. Saboda haka, muna soma kowane taron ikilisiya ta yin addu’a ga Jehobah inda muke roƙon Ubanmu na samaniya ya albarkaci taronmu ta wurin ruhunsa mai tsarki. Har ila, mun san cewa dukan waɗanda suke cikin ikilisiya suna iya sa tsarin ayyuka na taron ya kasance da ban ƙarfafa yadda ya yiwu. Saboda haka, waɗanne matakai ne ɗaɗɗayanmu za mu iya ɗauka don mu tabbata cewa taron da ake yi a Majami’ar Mulki kowane mako tushe ne na wartsakewa a ruhaniya da kuma na ban ƙarfafa?

3. Mene ne muhimmancin tarurrukan Kirista?

3 Don mu samu amsar, za mu bincika wasu fannoni na taronmu da ya kamata waɗanda suke gudanar da su su riƙa tunawa. Za mu kuma bincika yadda ikilisiyar gabaki ɗaya za ta iya sa taron ya zama lokacin ban ƙarfafa ga dukan waɗanda suka halarta. Wannan batun yana da muhimmanci sosai a gare mu domin tarurrukanmu masu tsarki ne. Hakika, halarta da kuma sa hannu a taro fannoni ne masu muhimmanci a bautarmu ga Jehobah.—Zab. 26:12; 111:1; Isha. 66:22, 23.

Taron da Aka Shirya don Nazarin Littafi Mai Tsarki

4, 5. Mene ne manufar Nazarin Hasumiyar Tsaro?

4 Dukanmu muna son mu amfana sosai daga Nazarin Hasumiyar Tsaro na mako mako. Saboda haka, don mu fahimci ainihin manufa na wannan taron, bari mu maimaita wasu gyara da aka yi ga mujallar Hasumiyar Tsaro da kuma talifofin nazari.

5 An saka bayani mai muhimmanci a bangon gaba na Hasumiyar Tsaro somawa da fitowa na nazari na farko na 15 ga Janairu, 2008. Ka lura da hakan kuwa? Ka duba bangon gaba na mujallar da ke hannunka sosai. A ƙasan hasumiyar, za ka lura cewa akwai Littafi Mai Tsarki da ke a buɗe. Wannan fanni da aka saka ya nuna dalilin da ya sa muke Nazarin Hasumiyar Tsaro. Don a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da taimakon wannan mujallar ne. Hakika, a Nazarinmu na Hasumiyar Tsaro na mako-mako ana ‘bayyana’ Kalmar Allah kuma kamar a zamanin Nehemiya na dā, ana “ba da fassararsa.”—Neh. 8:8; Isha. 54:13.

6. (a) Wane gyara aka yi ga Nazarin Hasumiyar Tsaro? (b) Me ya kamata a riƙa tunawa game da nassosi da aka ce a “karanta”?

6 Domin Littafi Mai Tsarki ne ainihin littafin da muke amfani da shi, an yi gyara ga Nazarin Hasumiyar Tsaro. An rubuta “karanta” a cikin nassosi na talifofin nazarin da yawa. An ƙarfafa dukanmu mu bi karatun waɗannan nassosi a lokacin taro, muna yin amfani da namu Littafi Mai Tsarki. (A. M. 17:11) Me ya sa? Sa’ad da muka ga shawarar Allah a cikin Littafinmu Mai Tsarki, yana shafanmu sosai. (Ibran. 4:12) Saboda haka, kafin a karanta nassosin, ya kamata wanda yake gudanar da taron ya ba dukan waɗanda suka halarta isashen lokaci su buɗe waɗannan nassosi kuma su riƙa bi sa’ad da ake karanta ayoyin.

Ƙarin Lokaci don Mu Furta Bangaskiyarmu

7. Wane zarafi ne muke da shi a lokacin da ake Nazarin Hasumiyar Tsaro?

7 Wani gyara kuma da aka yi ga nazarin Hasumiyar Tsaro shi ne yawan talifin. A shekarun bayan nan, an rage yawansu. Saboda haka, a lokacin Nazarin Hasumiyar Tsaro, an rage lokacin karanta sakin layin kuma an samu ƙarin lokaci don ba da kalami. Ƙarin mutane a cikin ikilisiya yanzu suna da zarafin furta bangaskiyarsu a fili ta wurin ba da amsa ga tambayar da aka yi, ta wurin faɗan yadda wani nassi ya shafi batun, ta wurin ba da ɗan labari da yake nuna amfanin bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki, ko kuma a wasu hanyoyi. Ya kamata a yi amfani da wasu lokaci wajen tattauna hotunan.—Karanta Zabura 22:22; 35:18; 40:9.

8, 9. Mene ne hakkin mai gudanar da Nazarin Hasumiyar Tsaro?

8 Amma, za a samu ƙarin lokaci don ba da kalamai dabam dabam idan ’yan’uwa suka ba da taƙaitaccen kalami kuma mai gudanar da taron ba ya yawan magana a lokacin Nazarin Hasumiyar Tsaron. To, me zai taimaka wa mai gudanar da nazari ya daidaita furcinsa da waɗanda ikilisiyar take ba da wa don taron ya kasance da ban ƙarfafa ga kowa?

9 Don a ba da amsar, ka yi la’akari da wannan misalin. Nazarin Hasumiyar Tsaro da aka gudanar da kyau yana kama da kwandon furanni da ke da kyaun gani. Kamar yadda babban kwandon furanni ya ƙunshi furanni iri iri masu yawa, haka Nazarin Hasumiyar Tsaro ya ƙunshi kalamai dabam dabam masu yawa. Kuma kamar yadda girma da launin furanni a cikin kwandon ya bambanta, hakan ne tsawo da yadda ake ba da kalamai a lokacin taron ya bambanta. Kuma mene ne hakkin mai gudanar da nazarin? Kalamai da yake yi a wani lokaci yana kama da ’yan shuke-shuke da aka daɗa cikin kwandon furannin. Waɗannan shuke-shuken ba sa cika yin yawa; maimakon haka, suna tallafa da kuma haɗa kan sauran. Haka nan ma, wanda yake gudanar da taron yana bukatan ya tuna cewa hakkinsa ba don ya sha kan furcin sauran ba, amma ya sa furcin yabo da ikilisiyar take ba da wa ya cika. Hakika, sa’ad da aka haɗa kalamai dabam dabam na ’yan’uwa a ikilisiya da kuma ’yan kalamai na mai gudanar da taron, suna zama kwandon kalamai masu kyau da ke sa dukan waɗanda suka halarta su yi farin ciki.

“Bari Mu Mika Hadaya ta Yabo ga Allah Kullayaumi”

10. Yaya Kiristoci na farko suka ɗauki tarurrukan ikilisiya?

10 Yadda Bulus ya kwatanta taron Kirista a 1 Korintiyawa 14:26-33 ya taimaka mana mu fahimci yadda aka gudanar da waɗannan tarurrukan a ƙarni na farko. Sa’ad da yake magana game da waɗannan ayoyin, wani masanin Littafi Mai Tsarki ya rubuta: “Abin da aka lura da shi game da hidimar Coci na farko shi ne cewa kusan kowa yana ji cewa yana da gata da hakkin ba da wani abu. Mutum ba ya halarta da niyyar kawai cewa zai saurara; ya zo ba don kawai ya karɓa ba amma don ya ba da wani abu.” Hakika, Kiristoci na ƙarni na farko sun ɗauki taron ikilisiya a matsayin zarafin furta bangaskiyarsu.—Rom. 10:10.

11. (a) Me yake sa taro ya kasance da ban ƙarfafa, kuma me ya sa? (b) Yin amfani da wace shawara ce za ta iya kyautata kalamanmu a taro? (Ka duba hasiya.)

11 Furta bangaskiyarmu a tarurruka yana daɗa ga “[ƙarfafa] ikilisiya.” Babu shakka za ka yarda cewa ko da shekaru nawa ne muka yi muna halartan taro, ya kasance abin farin ciki mu saurari kalamai da ’yan’uwanmu suke yi. Amsar da tsofaffi amintattu masu bi suke ba da yana motsa mu; kulawan dattijo mai ƙauna yana ƙarfafa mu; kuma muna murmushi sa’ad da ƙaramin yaro farat ɗaya ya yi kalami da ya nuna yana ƙaunar Jehobah. A bayane yake cewa ta wajen ba da kalamai, dukanmu muna sa hannu wajen sa taron Kirista ya kasance da ban ƙarfafa.b

12. (a) Mene ne za mu iya koya daga misalan Musa da kuma Irmiya? (b) Wane matsayi ne addu’a take da shi a yin kalamai?

12 Amma, zai iya yi wa masu jin kunya wuya sosai su yi kalami. Idan kai ma kana jin haka, zai kasance da taimako ka tuna cewa yanayinka bai fi tsanani ba. A gaskiya, bayin Allah masu aminci kamar Musa da Irmiya sun furta rashin gaba gaɗi a yin magana ga jama’a. (Fit. 4:10; Irm. 1:6) Hakika, kamar yadda Jehobah ya taimaki waɗancan bayinsa na dā su yi yabonsa ga jama’a, Allah zai taimake ka ka yi hadayar yabo. (Karanta Ibraniyawa 13:15.) Ta yaya za ka sami taimakon Jehobah don ka sha kan tsoron yin kalami? Da farko, ka shirya taron sosai. Sa’an nan, kafin ka je Majami’ar Mulkin, ka yi addu’a ga Jehobah kuma ka gaya masa ainihi cewa ya ba ka gaba gaɗin yin kalami. (Filib. 4:6) Kana roƙon abu ne da ke “daidai da nufinsa,” saboda haka za ka iya zama da gaba gaɗi cewa zai amsa addu’arka.—1 Yoh. 5:14; Mis. 15:29.

Tarurruka da Ke ‘Ginawa, Gargaɗar da Kuma Ba da Ta’aziya’

13. (a) Yaya ya kamata taronmu ya shafi waɗanda suka halarta? (b) Wace tambaya ce take da muhimmanci ga dattawa?

13 Bulus ya ambata cewa manufa mai muhimmanci na taron ikilisiya shi ne su ‘gina, gargaɗar, da kuma ta’azantar’ da waɗanda suka halarta.c (1 Kor. 14:3) Ta yaya dattawan Kiristoci a yau za su tabbata cewa sashen da suka gabatar a tarurruka ya wartsake ’yan’uwansu maza da mata kuma ya ƙarfafa su? Don mu samu amsar, bari mu yi la’akari da taron da Yesu ya gudanar jim kaɗan bayan tashinsa daga matattu.

14. (a) Waɗanne abubuwa ne suka faru kafin a yi taron da Yesu ya shirya? (b) Me ya sa manzannin suka yi farin ciki sa’ad da ‘Yesu ya zo wurinsu, ya yi zance da su’?

14 Da farko, ka lura da abubuwan da suka faru kafin su yi taron. Kafin a kashe Yesu, manzannin “suka bar shi, suka gudu” kuma kamar yadda aka annabta, suka “warwatse, kowa zuwa nasa [gida].” (Mar. 14:50; Yoh. 16:32) Sa’an nan, bayan tashinsa daga matattu, Yesu ya gayyaci manzanninsa masu raunanan zuciya su halarci taro na musamman.d Ta wajen amsa gayyatar, “almajiran goma sha ɗaya suka tafi cikin Galili, zuwa dutsen da Yesu ya umurce su.” Sa’ad da suka isa, “Yesu kuwa ya zo wurinsu, ya yi zance da su.” (Mat. 28:10, 16, 18) Babu shakka manzannin sun yi farin ciki sa’ad da Yesu ya ɗauki wannan matakin! Mene ne Yesu ya tattauna da su?

15. (a) Waɗanne batutuwa ne Yesu ya yi la’akari da su, amma mene ne bai tattauna ba? (b) Yaya wannan taron ya shafi manzannin?

15 Yesu ya soma da yin wata sanarwa: “Dukan hukunci . . . an bayas gareni.” Sa’an nan kuma ya ba su aiki: “Ku tafi fa, ku almajirtarda.” A ƙarshe sai ya tabbatar masu cikin ƙauna: “Ga shi kuwa ina tare da ku kullayaumi.” (Mat. 28:18-20) Amma ka lura da abin da Yesu bai yi ba? Bai tsauta wa manzannin ba; kuma bai yi amfani da taron ba don ya tuhumi ra’ayinsu ko kuma ya sa su ƙara jin laifi ta wurin yin maganar rashin bangaskiyarsu na ɗan lokaci. Maimakon haka, Yesu ya ba su tabbacin ƙaunarsa da na Ubansa ta wajen ba su aiki mai girma. Yaya yadda Yesu ya aikata ya shafi manzannin? Hakan ya ƙarfafa da kuma yi musu ta’aziyya sosai, har ma bayan taron suka soma “koyaswa da yin wa’azi kuma.”—A. M. 5:42.

16. Ta yaya dattawa Kirista a yau suke yin koyi da misalin Yesu sa’ad da suke gudanar da taron da ke kawo wartsakewa?

16 Ta wurin yin koyi da Yesu, dattawa a yau suna ɗaukan taro a matsayin zarafi na ƙarfafa ’yan’uwa masu bi game da ƙaunar Jehobah ga mutanensa. (Rom. 8:38, 39) Shi ya sa, sa’ad da dattawa suke gudanar da sashen taro, suna mai da hankali ga halaye masu kyau na ’yan’uwansu ba kasawarsu ba. Ba sa tuhumar muradin ’yan’uwansu. Maimakon haka, furcinsu yana nuna cewa suna ɗaukan ’yan’uwansu masu bi a matsayin mutane da suke ƙaunar Jehobah kuma suna son su yi abin da yake da kyau. (1 Tas. 4:1, 9-12) Gaskiya ne cewa a wani lokaci dattawa suna bukatar su ba dukan ikilisiyar shawara, amma idan mutane kalilan suna bukatan a yi musu gyara, ya fi kyau a ba da irin wannan shawarar a ɓoye ga waɗanda ya shafa kaɗai. (Gal. 6:1; 2 Tim. 2:24-26) Sa’ad da suke magana ga dukan ikilisiya, ya kamata dattawa su yaba wa ’yan’uwan duk lokacin da ya dace. (Isha. 32:2) Suna ƙoƙari su yi magana a hanyar da a ƙarshen taron, dukan waɗanda suka halarta za su wartsake da kuma ƙarfafa.—Mat. 11:28; A. M. 15:32.

Wurin Kwanciyar Hankali

17. (a) Me ya sa yanzu ya fi muhimmanci taronmu ya zama wurin kwanciyar hankali? (b) Mene ne za ka iya yi don ka sa tarurruka su kasance da ban ƙarfafa? (Ka duba akwatin nan “Hanyoyi Goma da Za Ka Sa Taro Ya Kasance da Ban Ƙarfafa a Gare ka da Kuma Wasu.”)

17 Yayin da duniyar Shaiɗan take daɗa zama da zalunci, muna bukatar mu tabbata cewa taronmu na Kirista wuri ne da ake samun kwanciyar hankali, wato, tushen ta’aziyya ga kowa. (1 Tas. 5:11) Wata ’yar’uwa da ita da mijinta suka jimre wa gwaji mai tsanani wasu shekaru da suka shige ta tuna: ‘Kasancewa a Majami’ar Mulki yana kamar muna hannun Jehobah mai kula. A sa’o’in da muke wurin, kewaye da ’yan’uwanmu Kiristoci, mun ji cewa mun iya zuba nawayarmu a kan Jehobah, kuma mun samu natsuwa a zuci.’ (Zab. 55:22) Bari dukan waɗanda suka halarci taronmu su samu irin wannan ƙarfafa da ta’aziyya. Don a tabbata cewa hakan ya faru, bari mu ci gaba da yin iya ƙoƙarinmu wajen sa taron Kirista ya kasance da ban ƙarfafa.

[Hasiya]

a An annabta cewa za a daina wasu fannoni na taron Kirista na ƙarni na farko. Alal misali, mun daina “zance da harsuna” ko kuma yin “annabci.” (1 Kor. 13:8; 14:5) Ko da hakan gaskiya ne, umurnin Bulus ya taimaka mana mu fahimci yadda ya kamata a gudanar da taron Kirista a yau.

b Don samun shawarwari a kan yadda za mu kyautata kalamanmu a taro, ka duba Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Satumba, 2003, shafuffuka na 19-22 na Turanci.

c Game da bambancin da ke tsakanin “ƙarfafa” da “ta’aziya” ƙamus na Vine’s Expository Dictionary of Old and New Testament Words ya bayyana cewa kalmar nan “ta’aziya” da aka fassara da yaren Helenanci tana nufin “yawan ƙauna fiye da [ƙarfafa.]”—Gwada Yohanna 11:19.

d Wannan zai iya zama yanayin da Bulus ya yi maganarsa daga baya sa’ad da ya ce Yesu “ya bayyana ga waɗansu ’yan’uwa, sun yi ɗari biyar.”—1 Kor. 15:6.

Yaya Za Ka Amsa?

• Yaya muhimmancin tarurrukan Kirista?

• Me ya sa kalamai da ake ba da a taro suke “[ƙarfafa] ikilisiya”?

• Mene ne za mu iya koya daga taron da Yesu ya yi da mabiyansa?

[Akwati/Hotuna da ke shafi na 22, 23]

HANYOYI GOMA DA ZA KA SA TARO YA KASANCE DA BAN ƘARFAFA A GARE KA DA KUMA WASU

Ka shirya tun da wuri. Sa’ad da ka yi nazarin abin da za a tattauna a Majami’ar Mulki tun da wuri, za ka ji daɗin taron kuma zai shafe ka sosai.

Ka riƙa halarta a kai a kai. Tun da halartan taro yana ƙarfafa kowa da ke wajen, kasancewarka a wajen yana da muhimmanci.

Ka isa a kan lokaci. Idan ka zauna kafin tsarin ayyukan ya soma, za ka haɗu da sauran ku rera waƙar buɗewa da addu’a, waɗanda sashe ne na bautarmu ga Jehobah.

Ka zo a shirye. Ka zo da Littafinka Mai Tsarki da littattafai da za a yi amfani da su a taron don ka bi abin da ake tattaunawa kuma ka fahimce shi da kyau.

Ka guji abubuwa da suke raba hankali. Alal misali, ka karanta saƙon wayar selula naka bayan taron ba a lokacin taron ba. Ta hakan za ka saka al’amura na kanka a wurin da ya dace.

Ka yi kalami. Sa’ad da mutane da yawa suka yi kalami, mutane da yawa suna samun ƙarfafa daga furcin bangaskiya dabam dabam.

Ka yi furci a taƙaice. Wannan yana ba mutane da yawa zarafin yin kalami.

Ka yi aikin makaranta. A matsayin ɗaliban Makarantar Hidima ta Allah ko kuma waɗanda suke aiki a Taron Hidima, ka shirya da kyau, ka riƙa maimaitawa tun da wuri, kuma ka yi ƙoƙari ka yi aikinka.

Ka yaba wa ’yan’uwa. Ka gaya wa waɗanda suke da aiki a taro ko kuma waɗanda suka yi kalamai yadda aka ji daɗin ƙoƙarce-ƙoƙarcensu.

Ka yi tarayya. Gaisuwa da kyau da kuma tattaunawa mai ban ƙarfafa kafin taron da kuma bayan haka yana daɗa ga farin ciki da kuma amfani da ake samu don halarta.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba