Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 2/12 p. 1
  • Ka Yi Shiri Yanzu don Yin Wa’azi Sosai

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Yi Shiri Yanzu don Yin Wa’azi Sosai
  • Hidimarmu Ta Mulki—2012
  • Makamantan Littattafai
  • Yadda Za Ku Kasance da Farin Ciki a Lokacin Tuna da Mutuwar Yesu!
    Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Za Ku Iya Yin Hidimar Majagaba na Ɗan Lokaci?
    Hidimarmu Ta Mulki—2013
  • Babban Zarafi na Yabon Jehobah
    Hidimarmu Ta Mulki—2013
  • Za Ka Iya Yin Hidimar Majagaba na Ɗan Lokaci a Watan Maris da Afrilu?
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
Dubi Ƙari
Hidimarmu Ta Mulki—2012
km 2/12 p. 1

Ka Yi Shiri Yanzu don Yin Wa’azi Sosai

1. Me ya sa lokacin Tuna Rasuwar Yesu yake da muhimmanci, kuma yaya za mu iya yin shiri don hakan?

1 Muna samun zarafin yin “babbar godiya ga Ubangiji” a kowane lokacin Tuna Rasuwar Yesu. (Zab. 109:30) Shin za ku nuna godiya ga Wanda ya yi tanadin fansa ta wajen yin wa’azi sosai a watan Maris? Yanzu ne za ku soma yin shiri.—Mis. 21:5.

2. Yaya kai da kuma wasu ’yan’uwa suka ji sa’ad da aka rage sa’o’in da majagaba na ɗan lokaci za su ba da a watan Afrilu da ya shige?

2 Hidimar Majagaba na Ɗan Lokaci: A shekarar da ta shige, ’yan’uwa sun yi farin ciki sosai sa’ad da suka ji cewa an rage sa’o’in da ake ba da a hidimar majagaba na ɗan lokaci a watan Afrilu. Wani ɗan’uwa ya ce: “Ina makarantar sakandare, saboda haka, ban samu damar yin hidimar majagaba na kullum ba. Zan cika fam na sa’o’i 30, amma zan yi ƙoƙari don na samu sa’o’i 50 a watan Afrilu.” Wata ’yar’uwa da ke aiki na cikakken lokaci ta ce: “Babu shakka, zan iya samun sa’o’i talatin!” Sa’ad da aka yi wannan sanarwa, wata ’yar’uwa tsohuwa da majagaba ce a dā ta ce: “Ina jiran wannan zarafin da daɗewa! Jehobah ya san cewa na fi yin farin ciki a lokacin da nake hidimar majagaba!” Wasu ’yan’uwa da ba su iya yin hidimar majagaba na ɗan lokaci ba sun kafa maƙasudai na ƙara sa’o’in da suke wa’azi.

3. Waɗanne dalilai ne muke da su na tsai da shawarar yin hidimar majagaba na ɗan lokaci a watannin Maris da Afrilu da kuma Mayu?

3 Watan Maris zai zama lokaci mai kyau na yin hidimar majagaba na ɗan lokaci domin za mu samu zarafin ba da sa’o’i 30 ko kuma 50. Ban da haka ma, a ranar Asabar, 17 ga Maris za mu fara yin kamfen na musamman na gayyatar mutane zuwa taron Tuna Rasuwar Yesu da za mu yi a ranar 5 ga watan Afrilu. Mutane da yawa za su yi farin cikin yin wa’azi sosai kuma hakan zai sa su so ba da sa’o’i 50 a yin hidimar majagaba na ɗan lokaci a watannin Afrilu da Mayu.

4. Ta yaya za mu ƙara yin wa’azi sosai, kuma da wane sakamako?

4 Sa’ad da kuke Bauta ta Iyali da yamma na gaba, kuna iya tattauna yadda kowanne a cikin iyalin zai iya yin wa’azi sosai a lokacin Tuna Rasuwar Yesu. (Mis. 15:22) Ku yi addu’a don Jehobah ya taimake ku. (1 Yoh. 3:22) Yayin da kuka yi wa’azi sosai, hakan zai sa ku ƙara yabon Jehobah kuma ku ƙara yin farin ciki.—2 Kor. 9:6.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba