Yadda Za Ku Kasance da Farin Ciki a Lokacin Tuna da Mutuwar Yesu!
1. Mene ne zai taimaka mana mu yi farin ciki sosai a wannan lokacin Tuna da Mutuwar Yesu?
1 Za ku so ku yi farin ciki sosai a watannin Maris da Afrilu da kuma Mayu? Wani abu da zai taimaka muku ku cim ma hakan shi ne ƙara ƙwazo a yin wa’azi, ko kuma idan zai yiwu, yin hidimar majagaba na ɗan lokaci. Ta yaya hakan zai sa ku ƙara yin farin ciki?
2. Ta yaya ƙara ƙwazo a yin wa’azi yake sa mu kasance da farin ciki sosai?
2 Ku Yi Abin da Zai Sa Ku Farin Ciki Sosai: Jehobah ya halicce mu a hanyar da idan muka bauta masa kuma muka yi abin da yake bukata a gare mu, za mu yi farin ciki kuma mu sami gamsuwa a rayuwa. (Mat. 5:3) Ƙari ga haka, Allah ya halicce mu a hanyar da idan muka taimaka wa mutane, za mu yi farin ciki. (A. M. 20:35) A taƙaice, yin wa’azi yana ba mu damar bauta wa Allah da kuma taimaka wa mutane. Saboda haka, za mu daɗa yin farin ciki idan muka ƙara ƙwazo a yin wa’azi. Ƙari ga haka, yayin da muka ƙara ƙwazo a yin wa’azi, za mu daɗa ƙwarewa. Idan muka ƙware sosai, za mu kasance da gaba gaɗi yayin da muka fita wa’azi. A sakamakon haka, za mu riƙa yi wa dukan mutane wa’azi iya gwargwado kuma mu soma nazari da mutane da yawa. Dukan waɗannan abubuwan za su sa mu ƙara jin daɗin yin wa’azi.
3. Me ya sa watannin Maris da Afrilu watanni ne da suka dace da yin hidimar majagaba na ɗan lokaci?
3 Watannin Maris da Afrilu watanni ne masu kyau na yin hidimar majagaba na ɗan lokaci, domin za mu sami damar yin awoyi 30 ko kuma 50 a wata. Ƙari ga haka, somawa daga ranar Asabar, 22 ga Maris zuwa ranar Litinin, 14 ga Afrilu, za mu yi kamfen na gayyatar mutane su halarci taron Tuna da Mutuwar Yesu. Ikilisiyoyi a faɗin duniya za su yi farin ciki sosai yayin da dukan masu shela za su yi wa’azi da “zuciya ɗaya” a dukan yankunansu.—Zaf. 3:9.
4. Idan muna so mu yi hidimar majagaba na ɗan lokaci, mene ne ya kamata mu yi?
4 Ku Shirya Tun Yanzu: Ku sake bincika yanayinku idan ba ku yi hakan ba tukun don ku ga ko zai yiwu ku ƙara ƙwazo a yin wa’azi na wata ɗaya ko fiye da hakan. Ku yi addu’a ga Jehobah don ya taimake ku a wannan batun. (Yaƙ. 1:5) Ku tattauna batun da iyalinku da kuma wasu a cikin ikilisiyarku. (Mis. 15:22) Wataƙila za ku ga cewa ku ma za ku iya more farin cikin da ake samu daga yin hidimar majagaba na ɗan lokaci, ko da kuna rashin lafiya ko kuna aiki na cikakken lokaci.
5. Mene ne zai faru idan muka yi wa’azi da ƙwazo a wannan lokacin Tuna da Mutuwar Yesu?
5 Jehobah yana so bayinsa su yi farin ciki. (Zab. 32:11) Idan muka yi wa’azi da ƙwazo sosai a wannan lokacin Tuna da Mutuwar Yesu, za mu yi farin ciki sosai kuma za mu faranta wa Ubanmu na sama rai.—Mis. 23:24; 27:11.