Ku Taimaka ma Waɗanda Ba Sa So Su Yi Nazarin Littafin Nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
1. Shin kowa ne zai so a yi nazarin littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? da shi da farko? Ka bayyana.
1 Wajibi ne mutum ya fahimci koyarwar Littafi Mai Tsarki idan yana so ya bauta wa Jehobah. Amma wasu suna bin addinin da ba ruwansa da Kiristanci, saboda haka ba sa ɗaukan Littafi Mai Tsarki a matsayin Kalmar Allah. Wasu kuma ba su gaskata da Allah ba kuma ba sa ɗaukan Littafi Mai Tsarki da muhimmanci. Waɗanne littattafanmu ne sun taimaka ma waɗanda ba su so a yi nazarin littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? da su ba? Bayanan da ke gaba daga masu shela a ƙasashe 20 ne a kan yadda za mu taimaka ma irin mutanen nan.
2. Idan wani ya ce bai yi imani da Allah ba, me ya kamata mu bincika kuma don me?
2 Waɗanda Ba Su Ba da Gaskiya ga Allah Ba: Idan wani ya ce bai yi imani da Allah ba, zai dace mu binciki dalilin hakan. Shin domin ya gaskata da ra’ayin bayyanau ne? Rashin adalci da ake shaidawa a duniya ne ko munafuncin mabiyan addinai ne suka sa ya daina yin imani da Allah? Ya fito daga ƙasar da galibin mutane ba su yi imani da Allah ba ne? Wataƙila bai musanta wanzuwar Allah ba, amma a ganinsa ba ya bukatar yin imani da Shi. Masu shela da yawa sun gano cewa yin tambayar nan “Ra’ayinka ke nan tun tashiwarka?” yana sa mutumin ya bayyana ra’ayinsa. Sai ku saurara kuma kada ku katse shi. Idan muka fahimci dalilin da ya sa mutumin bai gaskata da Allah ba, za mu san yadda za mu ba shi amsa da irin littafin da za mu ba shi.—Mis. 18:13.
3. Ta yaya za mu nuna cewa muna daraja mutane kuma muna ɗaukan imaninsu da muhimmanci?
3 Yayin da kuke ba da amsa, ku lura don kada ku sa mutumin ya ji kamar ana masa sūki. Ga wata shawara daga ofishin reshe a Amirka: “Yana da muhimmanci mu tuna cewa mutane suna da ’yancin yin imani da abin da suka ga dama. Maimakon yin jayayya, zai fi kyau mu yi tambayoyin da za su sa mutane su yi tunani kuma su tsai da shawara da kansu.” Bayan wani mai kula mai ziyara ya saurari maigida, sai ya soma magana da cewa, “Idan muka bincika zancen a wata hanya dabam fa?”
4. Ta yaya za mu iya taimaka wa mabiya addinin Buddah?
4 Zancen wanzuwar Allah baƙon zance ne a wurin mabiya addinin Buddah da yawa. Wasu masu shela a Birtaniya suna amfani da ƙasidar nan Lasting Peace and Happiness—How to Find Them wajen tattaunawa da irin waɗannan mutanen. Bayan sun gabatar da ƙasidar, sukan tattauna sashen nan “Is There Really a Most High Creator?” da kuma “A Guidebook for the Blessing of All Mankind.” Daga baya, suna iya gabatar da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? kuma su ce wa maigidan: “Ko da yake ba ka yi imani da Allah ba, za ka amfana idan ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki domin yana ɗauke da bayanai masu amfani.” Wani majagaba a Amirka da ke wa’azi a yankin ’yan Chana ya ce: “Mutane da yawa a yankinmu suna son karatu. Saboda haka, sukan karance duk littafin da muka ba su kafin mu dawo. Amma yana musu wuya su fahimci batun nazari da mutane. Nakan ba su ƙasidar nan Albishiri Daga Allah! a farkon haɗuwarmu domin an tsara ƙasidar a hanyar da za ta ƙarfafa tattaunawa.” Wani mai kula da da’ira a Amirka da ke hidima a yankin ’yan Chana ya ruwaito cewa yana yiwuwa a gabatar da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? sa’ad da aka fara haɗuwa da wani. Amma zai fi dacewa a soma da nazarin babi na 2, wanda ya yi bayani a kan Littafi Mai Tsarki, maimakon babi na 1 da ya tattauna batun Allah.
5. Me ya sa haƙuri yake da muhimmanci?
5 Yana da muhimmanci mu kasance da haƙuri domin a hankali ne mutane suke ba da gaskiya ga Allah. Mai yiwuwa mutane ba za su yarda cewa akwai Mahalicci nan da nan bayan muka tattauna da su ba. Amma a kwana a tashi, zai iya yarda cewa ƙila akwai Mahalicci, ko kuma yana iya cewa ya fahimci dalilin da ya sa wani zai gaskata da hakan.
6. Me ya sa wasu ba sa sha’awar Littafi Mai Tsarki?
6 Waɗanda Ba Sa Sha’awar Littafi Mai Tsarki ko Suna Shakkarsa: Amma, sau da yawa waɗanda suka yi imani da wanzuwar Allah suna banza da Littafi Mai Tsarki domin ba su gaskata cewa Kalmar Allah ne ba. Wataƙila yana da zama a ƙasar da Kiristanci ba addinin ƙasar ba ne, kuma ana yi wa Littafi Mai Tsarki kallon littafin Kiristoci ne kawai. Ko kuma yana zama a ƙasar da ake Kiristanci a baki ne kawai, saboda haka, yana iya ɗauka cewa Littafi Mai Tsarki ba shi da amfani a gare shi. Ta yaya za mu iya taimaka ma waɗannan mutanen su soma sha’awar Littafi Mai Tsarki kuma daga baya su yarda a yi nazarin littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? da su?
7. Me ya kamata a yi don a taimaka wa mutane su soma sha’awar Littafi Mai Tsarki?
7 Ofishin reshe da ke ƙasar Girka ya rubuto cewa: “Hanya mafi kyau na taimaka wa mutanen da ba sa son Littafi Mai Tsarki ita ce karanta musu abin da ke ciki kai tsaye. Masu shela da yawa sun lura cewa Kalmar Allah tana taɓa zuciyar mutane fiye da abin da suka faɗa da baki. (Ibran. 4:12) Ganin sunan Allah a cikin Littafi Mai Tsarki ya taimaki mutane da yawa su yi sha’awar abin da ke cikinsa.” Ofishin reshe da ke Indiya ya rubuto cewa: “Koyarwa ta gaskiya game da rayuwa da mutuwa da kuma alkawarin Allah da ke Littafi Mai Tsarki cewa a nan gaba za a daina nuna bambanci a duniya suna sa mabiya addinin Hindu su soma sha’awar Littafi Mai Tsarki.” Ambata matsaloli da ke damun mutane yana ba masu shela zarafin nuna abin da Littafi Mai Tsarki ya ce Mulkin Allah zai yi don ya warware matsalolin ’yan Adam.
8. Me za mu iya gaya ma waɗanda suke da ra’ayin da bai dace ba game da Littafi Mai Tsarki domin ’yan Kiristendam?
8 Idan wani yana da ra’ayin da bai dace ba game da Littafi Mai Tsarki domin ’yan Kiristendam, ku taimaka masa ya san cewa rayuwar Kiristendom da kuma koyarwarsu ba su jitu da koyarwar Littafi Mai Tsarki ba. Ofishin reshe da ke Indiya ya rubuto cewa: “A wasu lokatai, muna bukatar taimaka wa mutane su fahimci cewa Allah bai danƙa ma waɗannan cocin hakkin koyar da Littafi Mai Tsarki ba.” Ofishin ya daɗa da cewa sau da yawa mabiya addinin Hindu suna farin ciki idan aka nuna musu sashe na 4 a cikin ƙasidar nan Minene Ma’anar Rai? Ina Yadda Zaka Same Shi?, wadda ya bayyana yadda coci suka yi ƙoƙarin dagula da kuma halaka Kalmar Allah. Wani majagaba a Brazil yakan gaya wa mutane cewa: “Ka ɗan bincika abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki mana. Mutane da yawa suna hakan da ra’ayi mai kyau, ba tare da ji kamar sai sun bi wani addini ba. Za ka yi mamakin abubuwan da za ka koya daga Littafi Mai Tsarki.”
9. Me ya sa ba za mu fid da rai ba idan da farko wani bai yi sha’awar koyarwar Littafi Mai Tsarki ba?
9 Jehobah yana ganin zuciyar kowane mutum. (1 Sam. 16:7; Mis. 21:2) Yana jawo masu zuciyar kirki don su zo su bauta masa. (Yoh. 6:44) Irin waɗannan mutane ba su taɓa koya game da Allah ba ko kuma ba su da Littafi Mai Tsarki. Wa’azi da muke yi yana ba su dama “su tsira, kuma su kawo ga sanin gaskiya.” (1 Tim. 2:4) Saboda haka, idan a farko wasu ba su yi sha’awar sanin koyarwar Littafi Mai Tsarki ba, kada ku fid da rai! Ku yi amfani da wasu littattafai da kuke da su a yarenku don ku sa su soma sha’awarsa. Daga baya, za ku iya soma nazari da su a cikin ainihin littafin da muke amfani da shi don nazari, wato, Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
[Akwati a shafi na 4]
Idan maigidan ya ce bai gaskata da Allah ba, ku gwada wannan:
• Ku tambaye shi, “Ra’ayinka ke nan tun tashiwarka?” don ku san dalilin.
• Idan ya gaskata da ra’ayin bayyanau, abubuwan da ke gaba za su taimaka:
Jerin talifofin nan “Was It Designed?” a cikin mujallar Awake!
Bidiyon nan The Wonders of Creation Reveal God’s Glory
Ƙasidun nan A Satisfying Life—How to Attain It, sashe na 4; Was Life Created?; da kuma The Origin of Life—Five Questions Worth Asking
• Idan rashin adalci da kuma wahala ne suka sa ya daina yin imani da Allah, littattafan da ke gaba za su taimaka:
Littafin nan Is There a Creator Who Cares About You?, babi na 10
Ƙasidun nan Allah Yana Kula da Mu Kuwa da Gaske?, sashe na 6, da kuma Minene Ma’anar Rai?, Ina Yadda Zaka Same Shi?, sashe na 6
• Ku soma nazarin littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? muddin maigidan ya soma amince cewa akwai Allah. Zai dace ku soma da babi na 2 ko kuma wani babi da ya dace da shi.
[Akwati a shafi na 5]
Ku gwada wannan idan maigidan bai gaskata da Littafi Mai Tsarki ba:
• Ku tattauna babi na 17 da 18 na littafin nan Life—How Did It Get Here? By Evolution or by Creation?
• Ku yi amfani da bayanin da ke shafi na 22 a littafin nan Reasoning From the Scriptures don yin wa’azi ga mabiya addinin Hindu
• Don Yahudawa, ku yi amfani da ƙasidar nan Will There Ever Be a World Without War?, shafuffuka na 3-11.
• Ku tattauna amfanin bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Littattafan da za ku iya yin amfani da su wajen taimaka wa mutane su ga muhimmancin Littafi Mai Tsarki su ne:
Jerin talifofin nan “Help for the Family” a cikin mujallar Awake!
Bidiyon nan The Bible—Its Power in Your Life
Ƙasidun nan Albishiri Daga Allah!, darasi na 9 da 11; Littafi Don Dukan Mutane, shafuffuka na 22-26; da kuma A Satisfying Life—How to Attain It, sashe na 2
Don mabiya addinin Buddah, ku yi amfani da bayanin da ke shafi na 21 a littafin nan Reasoning From the Scriptures. (Ko kuma ƙasidar nan The Pathway to Peace and Happiness, shafuffuka na 3-7.)
Don Musulmai, ku yi amfani da ƙasidar nan Cikakken Imani—Zai Sa Ka Yi Farin Ciki a Rayuwa, sashe na 3.
Idan kuna wa’azi a yankin da ba a son Littafi Mai Tsarki, zai fi kyau kada ku ambata cewa abin da kuke faɗa daga Littafi Mai Tsarki ne, har sai kun ziyarce su sau da yawa.
• Ku bayyana yadda annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki suka cika. Kuna iya yin amfani da abubuwan da ke gaba:
Bidiyon nan The Bible—Accurate History, Reliable Prophecy
Ƙasidar nan Littafi Don Dukan Mutane, shafuffuka na 27-29
• Ku soma nazarin littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? muddin mutumin ya nemi ya san koyarwar Littafi Mai Tsarki a kan batutuwa dabam-dabam.
[Akwati a shafi na 6]
Idan maigidan ya ce: “Ban gaskata da Allah ba,” kuna iya cewa:
• “Bari in ɗan bayyana maka abin da ya sa na soma gaskata cewa akwai Mahalicci.” Sai ku bayyana abin da ke shafuffuka na 84-86 a littafin nan Reasoning from the Scriptures, ko kuma ku gaya masa cewa akwai littafin da kuka ji daɗin karantawa kuma za ku so ku kawo masa.
• “Amma idan akwai Allah, wane irin hali za ka so ya kasance da shi?” Yawancin mutane suna iya cewa za su so Allah mai ƙauna, mai son adalci, mai jin ƙai kuma marar son kai. Ku nuna masa daga Littafi Mai Tsarki cewa Allah yana da irin waɗannan halayen. (Kuna iya yin amfani da babi na 1 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? kuma ku soma da sakin layi na 6.)
Idan maigidan ya ce: “Ban gaskata da Littafi Mai Tsarki ba,” kuna iya cewa:
• “Mutane da yawa suna da irin wannan ra’ayin. Wasu suna ganin kamar Littafi Mai Tsarki bai jitu da kimiyya ba ko kuma ƙa’idodinsa ba su da amfani. Ka taɓa karanta Littafi Mai Tsarki? [Ku bari ya ba da amsa. Sai ku nuna masa gabatarwa da ke shafi na 3 a ƙasidar nan Littafi Don Dukan Mutane, sa’an nan ku ba shi ƙasidar.] Mutane da yawa suna shafa wa Littafi Mai Tsarki kashin kaza domin addinai ba sa faɗin gaskiya game da koyarwarsa. Zan sake dawowa don mu tattauna wani misali daga shafuffuka na 4 da 5.”
• “Mutane da yawa suna da irin wannan ra’ayin. Bari in nuna maka wani abu da ya burge ni game da Littafi Mai Tsarki. [Karanta Ayuba 26:7 ko Ishaya 40:22, da ya nuna cewa Littafi Mai Tsarki ya jitu da kimiyya.] Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da shawarwari da za su amfane iyalai. Zan sake dawowa don in nuna maka wani misali.”
• “Na yi farin ciki da ka gaya mini hakan. Idan da gaske ne cewa Allah ya rubuta littafi don ’yan Adam, me kake ganin zai ƙunsa?” Sai ka nuna wa mutumin wani abu daga Littafi Mai Tsarki da ya jitu da abin da ya faɗa.