Tsarin Ayyuka na Makon 23 ga Disamba
MAKON 23 GA DISAMBA
Waƙa ta 127 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
jl Darasi na 23-25 (minti 30)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Ru’ya ta Yohanna 7-14 (minti 10)
Na 1: Ru’ya ta Yohanna 9:1-21 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Yadda Kiristoci na Gaskiya Za Su Nuna Halin Karɓan Baƙi—Ibran. 13:2 (minti 5)
Na 3: Iblis Shi Ne Mai Mulkin Duniya—td 22B (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 124
Minti 10: Littattafan da Za A Ba Mutane a Watan Janairu da Fabrairu. Tattaunawa. Ku ɗan tattauna wasu talifofi a cikin ƙasidun da za a ba mutane, sa’an nan ka sa a yi gwaji guda biyu don a nuna yadda za a iya ba da ƙasidun.
Minti 20: “Ku Taimaka ma Waɗanda Ba Sa So Su Yi Nazarin Littafin Nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?” Tambayoyi ana ba da amsoshi. Ka sa a nuna yadda za a iya yin amfani da ɗaya cikin gabatarwa da ke shafi na 6.
Waƙa ta 46 da Addu’a