Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb16 Maris p. 2
  • Ku Marabci Bakin da Suka Hallara

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Marabci Bakin da Suka Hallara
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu (2016)
  • Makamantan Littattafai
  • Ku Marabce Su!
    Hidimarmu Ta Mulki—2013
  • Za a Ba da Shaida Sosai
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • Ku Marabce Su da Kyau
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2017
  • Za a Soma Kamfen na Gayyatar Mutane Zuwa Taron Tuna Rasuwar Yesu a Ranar 17 ga Maris
    Hidimarmu Ta Mulki—2012
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu (2016)
mwb16 Maris p. 2

RAYUWAR KIRISTA

Ku Marabci Baƙin da Suka Zo

A ranar 23 ga Maris, muna sa rai cewa mutane wajen miliyan 12 ko kuma fiye da hakan za su halarci taron Tuna da mutuwar Yesu. Babu shakka, za su amfana sosai daga jawabin da za a yi da zai nuna yadda Jehobah ya yi mana tanadin fansa da kuma albarkar da fansar za ta kawo mana a nan gaba! (Ish 11:​6-9; 35:​5, 6; 65:​21-23; Yoh 3:16) Amma, ba mai jawabin ba ne kaɗai zai taimaka wa mahalartan ba. Dukanmu muna da hakkin marabtar baƙin da suka halarci taron. (Ro 15:⁠7) Ga wasu shawarar da za mu iya bi.

Wani Mashaidin Jehobah yana marabtar bakin da suka halarci Taron Tuna da Mutuwar Yesu; wani Mashaidin Jehobah ya sa bakin da suka halarci Taron Tunawa da Mutuwar Yesu su yi amfani da nasa Littafi Mai Tsarki
  • Maimakon ka zauna a wurin zamanka kana jiran a soma taron, zai dace ka gai da baƙin da suke shigowa, kuma ka yi haka da fara’a

  • Maimakon mai da hankali ga mutanen da ka gayyata kawai, zai dace ka marabci mutanen da suka halarci taron domin an ba su takardar gayyata. Ka ce sababbi su zauna da kai. Ka sa su yi amfani da naka Littafi Mai Tsarki da kuma littafin waƙa

  • Bayan jawabin, ka amsa tambayoyin da suke da shi. Amma idan babu isashen lokaci domin wata ikilisiya tana son ta yi amfani da majami’ar, ku shirya yadda za ku sake haɗuwa bayan ‘yan kwanaki kaɗan don ka amsa tambayoyinsa. Idan ba ka san adireshinsa ko kuma lambar wayarsa ba, za ka iya ce masa: “Zan so mu tattauna abubuwan da ka lura a taron. A ina za mu iya sake haɗuwa?”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba