Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb21 Mayu p. 11
  • Yin Koyarwa da Himma

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yin Koyarwa da Himma
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Yi Magana da Kuzari
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Yin Tambayoyi
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
  • Ka Ratsa Zukatan Mutane
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
  • Ka Amince da Taimakon Jehobah ta Wurin Yin Addu’a
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
mwb21 Mayu p. 11
Wani dan’uwa yana murmushi da kuma motsa jiki yayin da yake nazari da wani dattijo.

KU YI WA’AZI DA KWAZO | YADDA ZA KA DAƊA JIN DAƊIN WA’AZI

Yin Koyarwa da Himma

Idan muna da himma, hakan zai iya shafan mutane. Zai sa mutane su saurari abin da muke cewa. Ƙari ga haka, yana nuna cewa muna daraja saƙonmu. Ko da yaya al’adarmu ko halinmu yake, za mu iya kasancewa da himma. (Ro 12:11) Ta yaya za mu yi hakan?

Da farko, ka yi tunani a kan muhimmancin saƙon da kake so ka idar. An ba ka babban aiki na kai wa mutane “labari mai daɗi.” (Ro 10:15) Na biyu, ka yi tunani a kan yadda wa’azinka zai kyautata rayuwar mutane. Suna bukatar su ji abin da kake so ka faɗa. (Ro 10:​13, 14) A ƙarshe, ka yi magana da himma kuma yanayin fuskarka da yadda kake motsa hannayenka su yi daidai da abin da kake faɗa.

KU KALLI BIDIYON NAN ZA KU JI DAƊIN ALMAJIRTARWA IDAN KUN INGANTA YADDA KUKE WA’AZI​—KU RIƘA KOYARWA DA HIMMA, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Wani hoto daga bidiyon nan ‘Za Ku Ji Dadin Almajirtarwa Idan Kun Inganta Yadda Kuke Wa’azi​— Ku Rika Koyarwa da Himma.’ Anita ta karaya bayan Rose ta ce ba ta da lokacin yin nazari.

    Me ya sa Anita ta daina kasancewa da himmar yin nazari da Rose?

  • Wani hoto daga bidiyon nan ‘Za Ku Ji Dadin Almajirtarwa Idan Kun Inganta Yadda Kuke Wa’azi​—Ku Rika Koyarwa da Himma.’ Rose ba ta jin dadin nazarin Littafi Mai Tsarki.

    Me ya taimaka wa Anita ta soma kasancewa da himma?

  • Wani hoto daga bidiyon nan ‘Za Ku Ji Dadin Almajirtarwa Idan Kun Inganta Yadda Kuke Wa’azi​— Ku Rika Koyarwa da Himma.’ Rose da Anita suna tattaunawa bayan sun gama nazarin Littafi Mai Tsarki.

    Idan muna da himma, hakan zai iya shafan mutane

    Me ya sa ya dace mu mai da hankali ga halaye masu kyau na masu sauraronmu?

  • Ta yaya himmar da muke da ita take shafan ɗalibanmu da kuma wasu?

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba