TALIFIN NAZARI NA 17
WAƘA TA 99 Miliyoyin ꞌYanꞌuwa
Ba Za Mu Taɓa Zama Mu Kaɗai Ba
“Zan . . . taimake ka.”—ISHA. 41:10.
ABIN DA ZA MU KOYA
Za mu ga hanyoyi huɗu da Jehobah yake kula da mu.
1-2. (a) Me ya tabbatar mana cewa ba za mu yi fama da matsalolinmu mu kaɗai ba? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?
IDAN muka sami kanmu a cikin wani yanayi mai wuya sosai, za mu ji kamar mun ɓata ne a cikin wani dajin Allah da babu mafita. Amma gaskiyar ita ce, ba mu kaɗai ba ne. Jehobah yana tare da mu. Yana ganin komen da muke fama da shi kuma ya yi alkawarin taimaka mana. Jehobah ya yi wa bayinsa alkawari cewa: “Zan . . . taimake” ku.—Isha. 41:10.
2 A wannan talifin, za mu tattauna yadda Jehobah yake taimaka mana ta wajen (1) yi mana ja-goranci, (2) yi mana tanadin abubuwan da muke bukata, (3) kāre mu, da kuma (4) ƙarfafa mu. Jehobah ya tabbatar mana cewa, ko da wace irin matsala ce muke fuskanta, ba zai taɓa yin watsi da mu ko ya manta da mu ba. Don haka, ba za mu taɓa zama mu kaɗai ba.
JEHOBAH YANA MANA JA-GORANCI
3-4. Ta yaya Jehobah yake yi mana ja-goranci? (Zabura 48:14)
3 Karanta Zabura 48:14. Jehobah ya san cewa ba za mu iya yi wa kanmu ja-goranci ba. Shi ne kaɗai zai iya yi mana ja-goranci. Ta yaya yake yi wa bayinsa ja-goranci a yau? Hanya ɗaya da yake yin hakan ita ce ta Littafi Mai Tsarki. (Zab. 119:105) Jehobah yana amfani da Kalmarsa wajen taimaka mana mu iya tsai da shawarwari masu kyau, mu kasance da halayen da za su sa mu ji daɗin rayuwa yanzu, kuma mu sa ran yin rayuwa har abada.a Alal misali, yana koya mana cewa mu riƙa gafarta wa mutane, da faɗin gaskiya a kome da muke yi, da kuma mu ƙaunaci mutane da zuciya ɗaya. (Zab. 37:8; Ibran. 13:18; 1 Bit. 1:22) Idan mun kasance da irin halayen nan, za mu zama iyayen kirki, da maꞌauratan kirki, da kuma abokan kirki.
4 Ƙari ga haka, Jehobah ya sa an rubuta labaran mutanen da suka sha wahala kamar yadda muke sha a yau. (1 Kor. 10:13; Yak. 5:17) Idan muka karanta irin labaran nan kuma muka koyi darasi, za mu amfana a hanyoyi biyu. Na ɗaya, za mu ga cewa wasu mutane ma sun yi fama da irin matsalolin da muke fuskanta a yau kuma Jehobah ya taimaka musu su jimre. (1 Bit. 5:9) Na biyu, za mu ga abubuwan da za su taimaka mana mu iya jimre matsalolinmu.—Rom. 15:4.
5. Su waye ne Jehobah yake amfani da su wajen yi mana ja-goranci?
5 Wata hanya kuma da Jehobah yake yi mana ja-goranci ita ce ta wurin ꞌyanꞌuwanmu.b Alal misali, masu kula da daꞌira suna ziyartar ikilisiyoyi kowane lokaci don su ƙarfafa mu. Jawabansu sukan sa bangaskiyarmu ta ƙara ƙarfi kuma mu kasance da haɗin kai. (A. M. 15:40–16:5) Dattawa ma suna taimaka wa kowannenmu ya ci gaba da kusantar Jehobah. (1 Bit. 5:2, 3) Iyaye suna koya wa yaransu su ƙaunaci Jehobah, da yadda za su yanke shawarwari masu kyau da kuma kasance da halaye masu kyau. (K. Mag. 22:6) Kuma ꞌyanꞌuwa mata da suka manyanta suna taimaka wa ꞌyanꞌuwa mata da suke tasowa ta wajen halayensu masu kyau, da ba su shawarwarin da suka dace da kuma ƙarfafa su.—Tit. 2:3-5.
6. Me ya kamata mu yi don mu amfana daga ja-gorancin Jehobah?
6 Jehobah ya ba mu kome da muke bukata da za su taimaka mana mu tsai da shawarwari masu kyau kuma mu yi rayuwa mai inganci. Me ya kamata mu yi don mu amfana daga ja-gorancin Jehobah? Karin Magana 3:5, 6 sun ce: “Dogara ga Yahweh da dukan zuciyarka, kada ka dogara ga ganewarka.” Idan muka yi haka, ‘shi kuwa zai daidaita hanyoyinmu.’ Wato, zai taimaka mana mu guji matsaloli da yawa kuma mu yi farin ciki. Muna matuƙar godiya don yadda Jehobah ya san mu ciki da waje, da yadda ya nuna yana ƙaunarmu ta wajen ba mu shawarwarin da muke bukata!—Zab. 32:8.
JEHOBAH YANA MANA TANADIN ABUBUWAN DA MUKE BUKATA
7. Waɗanne abubuwa ne Jehobah yake taimaka mana mu iya samuwa? (Filibiyawa 4:19)
7 Karanta Filibiyawa 4:19. Ban da yi mana ja-goranci, Jehobah yana taimaka mana mu iya samun abubuwan da muke bukata na yau da kullum, kamar abinci da kayan sakawa da kuma wurin kwana. (Mat. 6:33; 2 Tas. 3:12) Ko da yake ba laifi ba ne mu yi tunani a kan abubuwan biyan bukatunmu. Jehobah ba ya so mu damu sosai game da abubuwan nan. (Mat. 6:25) Me ya sa? Domin Ubanmu ba zai taɓa yin watsi da bayinsa masu aminci ba, musamman a lokacin da suke cikin damuwa. (Mat. 6:8; Ibran. 13:5) Muna da tabbaci cewa zai cika wannan alkawarin da ya yi mana.
8. Ta yaya Jehobah ya taimaka wa Dauda?
8 Ka yi tunani game da yadda Jehobah ya taimaka wa Dauda. A duk shekarun da ya yi yana guje-guje domin Sarki Shawulu yana so ya kashe shi, Jehobah ya tanada wa shi da mutanensa abin da suke bukata. Bayan da Dauda ya yi tunani a kan yadda Jehobah ya kula da shi a lokacin, sai ya ce: “Dā dai ni yaro ne, yanzu kam na tsufa, amma ban taɓa ganin Yahweh ya yashe mai adalci ba, ko kuwa a ga ꞌyaꞌyansa suna roƙon abinci.” (Zab. 37:25) Kamar Dauda, mai yiwuwa kai ma ka ga yadda Jehobah yake taimaka wa bayinsa masu aminci.
9. Ta yaya Jehobah yake taimaka wa bayinsa idan balaꞌi ya auku? (Ka kuma duba hotunan.)
9 Jehobah yana taimaka wa bayinsa idan balaꞌi ya auku. Alal misali, a lokacin da aka yi yunwa sosai a Urushalima a ƙarni da farko, Kiristoci daga wurare dabam-dabam sun tura musu abubuwan da suke bukata. (A. M. 11:27-30; Rom. 15:25, 26) Bayin Allah ma a yau suna taimaka wa ꞌyanꞌuwansu maza da matan da suke da bukata. Idan balaꞌi ya auku, Jehobah yakan sa bayinsa su taimaka wa ꞌyanꞌuwan da balaꞌin ya shafa. Sukan kai musu abubuwa kamar su abinci, da ruwan sha, da riguna, da magunguna da dai sauransu. ꞌYanꞌuwanmu masu gine-gine sukan gyara gidaje ko Majamiꞌun Mulkin da suka lalace. Kuma ꞌyanꞌuwa ba sa ɓata lokaci wajen yin amfani da Littafi Mai Tsarki su ƙarfafa mutanen da balaꞌin ya shafa.c
Ta yaya Jehobah yake ƙarfafa mu idan balaꞌi ya auku? (Ka duba sakin layi na 9)e
10-11. Mene ne muka koya daga labarin Borys?
10 Ban da haka ma, Jehobah yana tanada wa mutanen da ba su soma bauta masa ba abubuwan da suke bukata hannu sake. Mu ma, zai dace mu nemi hanyoyin taimaka ma waɗanda ba sa bauta wa Jehobah. (Gal. 6:10) Yin hakan zai iya ba mu damar yi musu waꞌazi. Ga labarin wani mutum mai suna Borys da ke zama a Yukiren, shi principal ne a wata makaranta. Ko da yake shi ba Mashaidin Jehobah ba ne, yana yi wa ɗalibansa da Shaidu ne alheri, kuma yana daraja abin da suka yi imani da shi. Saꞌad da aka soma yaƙi kuma ya so ya gudu zuwa inda ba a tashin hankali, ꞌyanꞌuwanmu sun taimaka masa. Daga baya, Borys ya halarci Taron Tunawa da Mutuwar Yesu. Da ya tuna da dukan abubuwan da ꞌyanꞌuwa suka yi masa, ya ce: “Shaidun Jehobah sun kula da ni sosai. Kuma ina matuƙar godiya don hakan.”
11 Mu ma za mu iya yin koyi da Ubanmu na sama mai tausayi ta wajen yi wa mutane alheri, ko da imaninmu ɗaya ne ko aꞌa. (Luk. 6:31, 36) Fatanmu shi ne, ƙaunar da muke nuna musu zai taimaka musu su so su koya game da Jehobah kuma su bauta masa. (1 Bit. 2:12) Amma ko da sun zaɓi su bauta wa Jehobah ne ko aꞌa, za mu yi farin ciki don bayarwa tana sa mutum farin ciki.—A. M. 20:35.
JEHOBAH YANA KĀRE MU
12. Wane kāriya ne Jehobah ya yi alkawari cewa zai yi wa bayinsa? (Zabura 91:1, 2, 14)
12 Karanta Zabura 91:1, 2, 14. A yau, Jehobah ya yi alkawari cewa zai kāre bayinsa daga duk wani abin da zai ɓata dagantakarsu da shi. Ba zai taɓa barin Shaiɗan ya hana bayinsa bauta masa a hanyar da yake so ba. (Yoh. 17:15) Kuma a lokacin ƙunci mai girma, muna da tabbacin cewa Jehobah zai taimaka mana mu riƙe bangaskiyarmu kuma zai cece mu.—R. Yar. 7:9, 14.
13. A waɗanne hanyoyi ne Jehobah yake kāre kowannenmu?
13 Ta yaya Jehobah yake kāre kowannenmu? Jehobah ya ba mu Littafi Mai Tsarki don mu iya sanin abin da ya dace da abin da bai dace ba. (Ibran. 5:14) Idan muka bi abin da ke Littafi Mai Tsarki, za mu ci gaba da kusantarsa. Za mu yanke shawarwarin da za su taimaka mana mu yi farin ciki kuma mu yi rayuwa mai inganci. (Zab. 91:4) Ƙari ga haka, Jehobah yana amfani da ikilisiya wajen kāre kowannenmu. (Isha. 32:1, 2) ꞌYanꞌuwanmu a ikilisiya suna ƙaunar Jehobah kuma suna yi masa biyayya. Don haka, kasancewa a taro, da waꞌazi da kuma shakatawa da su zai taimaka mana mu guji yin abin da bai dace ba.—K. Mag. 13:20.
14. (a) Me ya sa Jehobah ba ya kāre mu daga dukan matsalolinmu? (b) Mene ne Zabura 9:10 ta tabbatar mana? (Ka kuma duba ƙarin bayani.)
14 A wasu lokuta a dā, Jehobah yakan kāre bayinsa don kada a kashe su ko kuma a ji musu rauni. Amma ba ya yin hakan a kowane lokaci. A wasu lokuta, tsautsayi yakan sami kowannenmu. (M. Wa. 9:11) Ban da haka ma, Jehobah ya ƙyale a tsananta da kuma kashe wasu cikin bayinsa don ya nuna cewa Shaiɗan maƙaryaci ne. (Ayu. 2:4-6; Mat. 24:9) Haka ma yake a yau. Ko da yake Jehobah ba zai cire dukan matsalolin da muke fama da su ba, muna da tabbaci cewa ba zai taɓa yin watsi da bayinsa masu aminci ba.d—Zab. 9:10.
JEHOBAH YANA ƘARFAFA MU
15. Ta yaya adduꞌa, da Kalmar Allah da kuma ꞌyanꞌuwanmu suke ƙarfafa mu? (2 Korintiyawa 1:3, 4)
15 Karanta 2 Korintiyawa 1:3, 4. A wasu lokuta, mukan yi fama da baƙin ciki, da yawan damuwa da kuma matsaloli dabam-dabam. Wataƙila kana cikin wani yanayi yanzu da ya sa kana ganin kamar babu wanda zai taimake ka. Anya, akwai wanda ya san yanayin da kake ciki kuwa? E, Jehobah ya sani. Ba sani game da yanayin kawai yake yi ba, “yana yi mana taꞌaziyya a cikin dukan wahalarmu.” Ta yaya yake yin hakan? Idan muka yi adduꞌa ga Jehobah da dukan zuciyarmu, yakan ba mu “salama iri wadda ta wuce dukan ganewar ɗanꞌadam.” (Filib. 4:6, 7) Mukan kuma sami ƙarfafa saꞌad da muke karanta Littafi Mai Tsarki. A ciki, Jehobah ya gaya mana irin ƙaunar da yake mana, da yadda za mu zama masu hikima kuma ya ba mu bege a nan gaba. Ƙari ga haka, mukan sami ƙarfafa a taronmu. A wurin, mukan kasance da ꞌyanꞌuwanmu da suke ƙaunar mu kuma muna koyan abubuwa masu ban ƙarfafa daga Littafi Mai Tsarki.
16. Mene ne muka koya daga labarin Nathan da Priscilla?
16 Don mu ga yadda Jehobah yake ƙarfafa mu ta wurin Kalmarsa, bari mu ga abin da ya faru da Nathan da matarsa Priscilla, da suke zama a Amurka. Shekaru da yawa da suka wuce, sun ƙaura zuwa inda ake bukatar masu shela. Nathan ya ce: “Mun kasance da tabbaci cewa Jehobah zai taimaka abubuwa su tafi sumul.” Amma da suka isa wurin, sun soma rashin lafiya da kuma ƙarancin kuɗi. A ƙarshe sun koma gida, kuma sun ci gaba da fama da matsalolin kuɗi. Nathan ya daɗa da cewa: “Na yi mamakin abin da ya sa Allah bai albarkace mu kamar yadda muka zata ba. Har ma na fara tunani ko na ya wani laifi ne.” Amma da shigewar lokaci, Nathan da Priscilla sun gano cewa Jehobah bai yi watsi da su a lokacin da suke da bukata ba. Nathan ya ci gaba da cewa: “A lokacin nan da muke fama da matsaloli, Littafi Mai Tsarki ya zama kamar abokin da yake ƙarfafa da kuma taimaka mana. Mai da hankali a kan yadda Jehobah ya sa mu jimre, maimakon a kan matsalolinmu, ya taimaka mana mu tabbata cewa Jehobah zai kasance tare da mu a nan gaba yayin da muke fuskantar matsaloli.”
17. Ta yaya ꞌyarꞌuwa Helga ta sami ƙarfafa? (Ka kuma duba hoton.)
17 Jehobah yana kuma ƙarfafa mu ta wurin ꞌyanꞌuwanmu maza da mata. Labarin ꞌyarꞌuwa Helga daga Hungary ya nuna hakan. Ta yi shekaru da yawa tana fama da matsalolin da suka sa ta cikin damuwa mai tsanani. Amma da ta tuna da yadda Jehobah ya taimaka mata ta wurin ꞌyanꞌuwa a ikilisiya. Ta ce: “Jehobah yana taimaka min a duk lokacin da ya ga cewa matsalolin sun kusa su fi ƙarfi na. Kamar lokacin da nake kula da yarona da bai da lafiya, da fama a wurin aiki, da dai sauransu. A kowace rana cikin shekaru 30 da suka shige, Jehobah ya ci gaba da cika alkawarin ƙarfafa ni da ya yi. Yana yawan yin hakan ta wurin kalmomin ꞌyanꞌuwa masu ban ƙarfafa. Nakan sami saƙo ta waya, ko a kati ko kuma wasu su zo su ƙarfafa ni a daidai lokacin da na fi bukata.”
Ta yaya Jehobah zai iya amfani da kai wajen ƙarfafa mutane? (Ka duba sakin layi na 17)
18. Ta yaya za mu iya ƙarfafa mutane?
18 Mu ma za mu iya ƙarfafa mutane kamar yadda Jehobah yake yi. Ta yaya za mu iya yin hakan? Ta wajen saurarar su da kyau, da yi musu maganganu masu sanyaya zuciya da taimaka musu wajen yin wasu ayyuka, da dai sauransu. (K. Mag. 3:27) Idan maƙwabtanmu suna fama don wani nasu ya mutu ko rashin lafiya ko kuma yawan damuwa, mukan ziyarce su, mu saurare su kuma mu ƙarfafa su daga Littafi Mai Tsarki. Mukan yi hakan ga kowa har ga waɗanda ba su soma bauta wa Jehobah ba. Idan muna koyi da Jehobah, “Allah wanda yake yi mana kowace irin taꞌaziyya,” za mu taimaka wa ꞌyanꞌuwanmu. Ban da haka ma, yin hakan zai iya taimaka ma waɗanda ba sa bauta wa Jehobah su so su bauta masa.—Mat. 5:16.
JEHOBAH ZAI CI GABA DA TAIMAKA MANA
19. Mene ne Jehobah yake yi mana, kuma ta yaya za mu yi koyi da shi?
19 Jehobah ya damu da waɗanda suke ƙaunar sa. Ba ya watsi da mu idan muna fama da matsaloli. Kamar yadda iyaye suke kula da yaransu, haka ma Jehobah yake kula da bayinsa masu aminci. Yana yi mana ja-goranci, da tanada mana abubuwan da muke bukata, da kāre mu, da kuma ƙarfafa mu. Muna koyi da Jehobah idan muna taimaka da kuma ƙarfafa mutane a lokacin da suke fama da matsaloli. Duk da cewa za mu iya fama da matsaloli da kuma ƙalubale a wannan duniyar, muna da tabbaci cewa Jehobah yana tare da mu. Ya yi wa kowannenmu alkawari cewa: “Kada fa ka ji tsoro, gama ina tare da kai.” (Isha. 41:10) Saboda haka, muna da tabbaci cewa ba za mu taɓa zama mu kaɗai ba.
WAƘA TA 100 Mu Riƙa Marabtar Baƙi
a Ka duba talifin nan mai jigo “Ka Tsai Da Shawarwari Da Ke Ɗaukaka Allah” da ke Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Afrilu, 2011.
b Ka duba talifin nan mai jigo, “Ku Ci gaba da Bin Ja-gorancin Jehobah” da ke Hasumiyar Tsaro ta Fabrairu 2024, sakin layi na 11-14.
c Za ka iya samun misalin hakan na kwana-kwanan nan a jw.org/ha ta wurin rubuta “agaji” a wurin da aka rubuta “bincika.”
d Ka duba “Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu” da ke Hasumiyar Tsaro ta Fabrairu 2017.
e BAYANI A KAN HOTO: ꞌYanꞌuwanmu da balaꞌi ya shafa a Malawi suna samun abinci, da ƙarfafa, da dai sauransu daga wurin ƙugiyar Jehobah.