Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w25 Yuni pp. 14-19
  • Ka Kasance da Sauƙin Kai Idan Akwai Abubuwan da Ba Ka Sani Ba

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Kasance da Sauƙin Kai Idan Akwai Abubuwan da Ba Ka Sani Ba
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • BA MU SAN LOKACIN DA ƘARSHEN ZAMANIN NAN ZAI ZO BA
  • BA MU SAN ABIN DA JEHOBAH ZAI YI A KOWANE LOKACI BA
  • BA MU SAN ABIN DA ZAI FARU GOBE BA
  • JEHOBAH YA SAN MU FIYE DA YADDA MUKE TSAMMANI
  • Ku Tsai da Shawarwari da Za Su Nuna Kun Dogara Ga Jehobah
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
  • Ka Tuna Cewa Jehobah “Allah Mai Rai” Ne
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Me Muka Sani Game da Yadda Jehobah Zai Shariꞌanta Mutane a Nan Gaba?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Shawara ta Karshe da Maza Masu Aminci Suka Bayar
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
w25 Yuni pp. 14-19

TALIFIN NAZARI NA 26

WAƘA TA 123 Mu Riƙa Bin Ja-gorancin Jehobah

Ka Kasance da Sauƙin Kai Idan Akwai Abubuwan da Ba Ka Sani Ba

“Ina misalin zurfin yawan hikimar Allah! Zurfin saninsa kuma marar iyaka ne! Hukunce-hukuncensa sun fi gaban bincike, hanyoyin alꞌamuransa sun wuce gaban ganewa!”—ROM. 11:33.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga cewa ko da yake ba mu san dukan abubuwan da za su faru a nan gaba ba, za mu iya jimre matsaloli idan muka mai da hankali ga abubuwan da muka sani, kuma muka dogara ga Jehobah.

1. Yaya Jehobah ya halicce mu, kuma me ya sa?

JEHOBAH ya halicce mu yadda za mu iya yin tunani, mu koyi sabbin abubuwa, kuma mu iya yin amfani da abubuwan da muka koya. Me ya sa ya halicce mu a hanya mai ban mamaki haka? Yana so ne mu zaɓi bauta masa da kanmu don abubuwa da muka sani game da shi.—K. Mag. 2:​1-5; Rom. 12:1.

2. (a) Me ya kamata mu riƙa tunawa game da kanmu? (Romawa 11:​33, 34) (Ka kuma duba hoton.) (b) Me ya sa yake da muhimmanci mu riƙa tuna cewa ba mu san kome da kome ba?

2 Ko da yake Jehobah ya halicce mu yadda za mu iya koyan abubuwa da dama, ya kamata mu riƙa tuna cewa akwai abubuwa da yawa da ba mu sani ba. (Karanta Romawa 11:​33, 34.) Alal misali, Jehobah ya yi wa Ayuba tambayoyi da suka sa ya gane cewa akwai abubuwa da yawa da bai sani ba. Abin da ya faru ya taimaka wa Ayuba ya gane cewa yana bukatar ya zama da sauƙin kai, kuma ya canja tunaninsa. (Ayu. 42:​3-6) Mu ma za mu amfana idan muka gane cewa ba mu san kome da kome ba. Sanin hakan zai sa mu kasance da sauƙin kai, kuma mu dogara ga Jehobah da tabbacin cewa zai gaya mana abin da muke bukatar mu sani don mu iya tsai da shawarwarin da suka dace.—K. Mag. 2:6.

Haske yana haskakawa daga sararin sama zuwa inda Ayuba yake, yayin da Jehobah yake masa magana. Elihu da abokan ƙarya na Ayuba guda uku suna gefe suna kallo.

Sanin cewa akwai wasu abubuwa da ba mu sani ba zai amfane mu kamar yadda ya amfani Ayuba (Ka duba sakin layi na 2)


3. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

3 A wannan talifin, za mu tattauna wasu abubuwan da ba mu sani ba, da abin da ya sa rashin sanin abubuwan nan zai iya sa rayuwa ta yi mana wuya. Za mu kuma ga dalilin da ya sa ya dace da ba mu san wasu abubuwa ba. Tattauna batutuwan nan za su sa mu kasance da tabbaci cewa Jehobah, wanda shi ne “Mai cikakken sani” zai gaya mana dukan abubuwan da muke bukata mu sani.—Ayu. 37:16.

BA MU SAN LOKACIN DA ƘARSHEN ZAMANIN NAN ZAI ZO BA

4. Bisa ga Matiyu 24:​36, wane abu ne ba mu sani ba?

4 Karanta Matiyu 24:36. Ba mu san lokacin da ƙarshen zamanin nan zai zo ba. Ko Yesu ma da kansa lokacin da yake duniya, bai san rana “ko a ƙarfe nawa ne wannan zai faru” ba.a Daga baya ya gaya wa manzanninsa cewa, Jehobah ne yake da ikon sanin lokutan da wasu abubuwa za su faru. (A. M. 1:​6, 7) Jehobah ya riga ya saka lokacin da zai kawo ƙarshen wannan zamanin, amma sanin wannan ranar ya fi ƙarfinmu.

5. Da yake ba mu san lokacin da ƙarshen zai zo ba, ta yaya hakan zai iya shafanmu?

5 Ba mu san har tsawon wane lokaci ne za mu ci gaba da jira kafin ƙarshen zamanin nan ya zo ba. Hakan zai iya sa mu sanyin gwiwa, musamman idan mun daɗe muna jiran ranar Jehobah. Ban da haka ma, za mu iya yin sanyin gwiwa idan mutane ko ꞌyan iyalinmu suka yi mana baꞌa cewa, ko da yake mun daɗe muna jira, har ila ƙarshen bai zo ba. (2 Bit. 3:​3, 4) Za mu iya ganin cewa, da a ce mun san ainihin ranar da ƙarshen zai zo, da zai yi mana sauƙi mu ci gaba da jira kuma mu jimre ko da mutane suna yi mana baꞌa.

6. Me ya sa ya dace da ba mu san yaushe ƙarshen zai zo ba?

6 Gaskiyar ita ce, da yake Jehobah bai gaya mana ranar da ƙarshen zai zo ba, hakan ya ba mu damar dogara gare shi, kuma mu bauta masa da dukan zuciyarmu don muna ƙaunar sa. Ba sai ƙarshen ya zo kafin mu bauta wa Jehobah ba. Muna so mu bauta masa daga yanzu har abada. Saboda haka, maimakon mu mai da hankali a kan yaushe ne ranar Jehobah za ta zo, zai dace mu mai da hankali a kan abubuwa masu kyau da za su faru bayan ranar ta zo. Yin hakan zai sa mu ƙara kusantar Jehobah, mu dogara gare shi, kuma mu yi kome da za mu iya don mu faranta masa rai.—2 Bit. 3:​11, 12.

7. Mene ne muka sani?

7 Zai fi mana alheri mu riƙa tunani a kan abubuwan da muka sani. Alal misali, mun san cewa tun daga 1914 ne muka shiga kwanakin ƙarshe. A Littafi Mai Tsarki, akwai annabce-annabce da suka nuna cewa mun shiga kwanakin ƙarshe a 1914. Kuma Littafi Mai Tsarki ya gaya mana abubuwa da yawa game da yadda duniya za ta kasance bayan wannan lokacin. Da yake muna ganin cikar waɗannan annabce-annabcen, muna da tabbaci cewa “babbar ranar Yahweh ta yi kusa.” (Zaf. 1:14) Wani abu kuma da muka sani shi ne aikin da Jehobah yake so mu yi, wato gaya wa mutane “labari mai daɗi na mulkin sama.” (Mat. 24:14) A yau, muna shelar labari mai daɗin nan a ƙasashe wajen 240, a cikin yaruka fiye da 1,000. Ba ma bukatar mu san ranar da ƙarshe zai zo don mu yi waꞌazi da ƙwazo.

BA MU SAN ABIN DA JEHOBAH ZAI YI A KOWANE LOKACI BA

8. Mene ne furucin nan “aikin Allah” yake nufi? (Mai-Waꞌazi 11:5)

8 Ba a kowane lokaci ne muke sanin “aikin Allah ba.” (Karanta Mai-Waꞌazi 11:5.) Furucin nan “aikin Allah” yana nufin abubuwan da Jehobah yake sa su faru da kuma waɗanda yake ƙyale su faru don su cim ma nufinsa. Ba za mu iya sanin dalilin da ya sa Jehobah yake ƙyale wasu abubuwa su faru ba, ko yadda zai taimaka mana ba. (Zab. 37:5) Kamar yadda masana ba su gama gane yadda jariri yake girma a cikin mamarsa ba, haka ma, ba za mu iya gama gane yadda Jehobah yake yin abubuwa ba.

9. Da yake ba ma sanin abin da Jehobah zai yi a kowane lokaci, ta yaya hakan zai shafi tunaninmu?

9 Rashin sanin yadda Jehobah zai taimaka mana zai iya sa mu yi jinkirin tsai da wasu shawarwari. Alal misali, za mu iya yin jinkirin yin wasu sadaukarwa don mu iya faɗaɗa hidimarmu ga Jehobah, ko kuma mu yi jinkirin ƙaura zuwa inda ake bukatar masu shela. Ban da haka ma, za mu iya ɗauka cewa Jehobah bai amince da mu ba idan mun kafa wani maƙasudi a ibadarmu, amma mun gagara cimmawa, ko muna fita waꞌazi a kowane lokaci amma ba mu da ɗalibi ko guda, ko kuma muna aikin gine-gine na ƙungiyarmu amma muna fuskantar kalubale.

10. Da yake ba mu san ainihin abin da Jehobah zai yi a kowane lokaci ba, waɗanne halaye masu muhimmanci ne hakan zai sa mu kasance da su?

10 Rashin sanin yadda Jehobah zai yi abubuwa dalla-dalla a kowane lokaci, zai sa mu kasance da halaye kamar su sanin kasawarmu, da sauƙin kai. Kuma hakan zai taimaka mana mu tuna cewa Jehobah ya san abin da muka fi so. (Isha. 55:​8, 9) Ƙari ga haka, hakan zai taimaka mana mu ƙara dogara ga Jehobah da tabbaci cewa zai yi kome daidai, a hanya mafi dacewa. Don haka, idan muka yi nasara a waꞌazi ko kuma a wani aikin gine-gine na ƙungiyarmu, zai dace mu miƙa yabo ga Jehobah da yake shi ne ya taimaka mana. (Zab. 127:1; 1 Kor. 3:7) Kuma idan abubuwa ba su faru yadda muka zata ba, zai dace mu tuna cewa Jehobah yana ganin kome da kome da suke faruwa. (Isha. 26:12) Za mu yi iya ƙoƙarinmu da fatan cewa Jehobah zai ci gaba da taimaka mana. Kuma ko da bai yi hakan a hanya mai ban mamaki kamar yadda ya yi a wasu lokuta a dā ba, muna da tabbaci cewa zai ba mu ja-gorancin da muke bukata.—A. M. 16:​6-10.

11. Waɗanne abubuwa ne muka sani da za su taimaka mana?

11 Mun san cewa Jehobah yana ƙaunar mu a kowane lokaci, shi mai adalci ne, kuma hikimarsa babu iyaka. Mun san cewa yana daraja kome da muke masa, da kuma kome da muke yi wa ꞌyanꞌuwanmu. Kuma mun san cewa a kowane lokaci, yana saka wa masu bauta masa da aminci.—Ibran. 11:6.

BA MU SAN ABIN DA ZAI FARU GOBE BA

12. Bisa ga Yakub 4:​13, 14, mene ne ba mu sani ba?

12 Karanta Yakub 4:​13, 14. Gaskiyar ita ce, ba ma iya sanin abin da zai faru da mu gobe. A wannan duniyar da muke ciki, abubuwa da yawa da ba mu yi zaton su ba za su iya faruwa da mu. (M. Wa. 9:11) Saboda haka, ba za mu iya sanin ko za mu cim ma abin da muke so mu yi ba. Kuma ba mu san ko za mu kasance da rai har mu yi abin da muke so mu yi ba.

13. Yaya muke ji a wasu lokuta da yake ba mu san dukan abubuwa da za su faru a nan gaba ba?

13 Rashin sanin abin da zai faru nan gaba zai iya sa jimrewa ya yi mana wuya. Me ya sa muka ce hakan? Da yake ba mu san abin da zai iya faruwa a nan gaba ba, hakan zai iya sa mu cikin yawan damuwa. Kuma yawan damuwa zai iya sa mu daina farin ciki. Rayuwarmu za ta iya canjawa nan da nan a hanyar da ba mu yi tsammani ba, kuma munanan abubuwa za su iya faruwa da mu. Ƙari ga haka, idan abubuwa suka faru yadda ba mu yi tsammani ba, hakan zai iya sa mu sanyin gwiwa ba kaɗan ba.—K. Mag. 13:12.

14. Mene ne muke bukatar mu sani, kuma mene ne muke bukatar mu yi don mu yi farin ciki? (Ka kuma duba hotunan.)

14 Ko da a wane irin yanayi ne muka sami kanmu, za mu iya nuna cewa muna bauta wa Jehobah ne don muna ƙaunar sa. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa ba zai dace mu yi tsammanin cewa Jehobah zai kāre mu daga dukan matsaloli da muke ciki ba. Kuma ya nuna cewa Jehobah bai riga ya ƙaddara dukan abubuwan da suke faruwa a rayuwarmu ba. Jehobah ya san cewa ba sanin abin da zai faru a nan gaba ne zai sa mu farin ciki ba. A maimakon haka, yin biyayya da kuma bin ja-gorancinsa ne za su sa mu yi farin ciki. (Irm. 10:23) Idan mun nemi ja-gorancinsa a duk lokacin da muke so mu tsai da wata shawara, ba za mu damu sosai game da abin da zai faru a nan gaba ba. Raꞌayinmu zai zo ɗaya da na Yakub, wanda ya ce: “Idan Allah ya yarda, idan kuma muna cikin masu rai, za mu yi kaza da kaza.”—Yak. 4:15.

Hotuna: Na 1. Wani mutum da ɗansa suna shirya jakar gaggawa. Suna saka Littafi Mai Tsarki da wasu abubuwan da za su bukata a cikin jakar. Na 2. Mutumin da matarsa da ɗansu suna cikin wani tanti yayin da ake tabka ruwan sama. Suna amfani da wasu abubuwa da ke cikin jakar da suka ɗauko.

Neman taimakon Jehobah, da bin ja-gorancinsa zai kāre mu (Ka duba sakin layi na 14-15)b


15. Mene ne muka sani game da nan gaba?

15 Ko da yake ba mu san abin da zai faru gobe ba, mun san cewa Jehobah ya yi mana alkawarin rayuwa har abada a sama ko kuma a duniya. Mun san cewa Jehobah ba ya ƙarya, kuma babu abin da zai hana shi cika alkawuransa. (Tit. 1:2) Shi kaɗai ne zai iya “bayyana ƙarshen abu, tun daga farkonsa.” Dukan abubuwan da ya ce za su faru a dā, sun faru daidai yadda ya faɗe su. Saboda da haka, dukan abubuwan da ya ce za su faru a nan gaba, za su faru. (Isha. 46:10) Mun san cewa babu abin da zai hana Jehobah ci gaba da nuna mana ƙauna. (Rom. 8:​35-39) Zai ba mu hikima da ƙarfin da muke bukata don mu iya jimre kowace irin matsala. Muna da tabbaci cewa Jehobah zai taimaka mana kuma ya yi mana albarka.—Irm. 17:​7, 8.

JEHOBAH YA SAN MU FIYE DA YADDA MUKE TSAMMANI

16. Mene ne Jehobah ya sani game da mu, kuma yaya kake ji don hakan? (Zabura 139:​1-6)

16 Karanta Zabura 139:​1-6. Mahaliccinmu ya san kome da kome game da mu. Ya san yadda muke ji da kuma tunanin da muke yi. Ya san abin da muke faɗa, da abin da ke cikin zuciyarmu. Ya san kome da muke yi, da dalilin da ya sa muke yinsa. Sarki Dauda ya ce Jehobah yana so ya taimaka mana a koyaushe, kuma babu abin da zai hana shi yin hakan. A gaskiya, abin alfahari ne sanin cewa Allah Maɗaukaki, Mai Iko Duka, Wanda ya halicci kome, ya damu da mu haka. Shi ya sa Dauda ya ce: “Irin sanin nan” ya fi ganewarsa.—Zab. 139:6.

17. Me ya sa mai yiwuwa zai yi mana wuya mu yarda cewa Jehobah ya san mu sosai?

17 Mai yiwuwa yadda aka rene mu, da alꞌadarmu da kuma abubuwan da muka yi imani da su kafin mu soma bauta wa Jehobah, za su iya sa ya yi mana wuya mu yarda cewa Jehobah Allah ne mai ƙauna, kuma ya damu da mu. Kamar yadda Dauda ya ji a wasu lokuta, mu ma za mu iya ji kamar Jehobah ba zai so kome ya haɗa mu da shi ba, domin zunuban da muka yi a dā. (Zab. 38:​18, 21) Ban da haka ma, mutum da ke fama da halin lalata, da ke iya ƙoƙarin yin canje-canje don ya yi rayuwar da Jehobah yake so, zai iya yin tunani cewa, ‘Idan Jehobah ya san ni sosai, to me ya sa yake so in daina abubuwan da suka zama min jiki?’

18. Me ya sa zai dace mu tuna cewa Jehobah ya san mu ciki da waje? (Ka kuma duba hotunan.)

18 Gaskiyar ita ce, Jehobah ya san mu fiye da yadda muka san kanmu, kuma yana ganin wasu halayenmu masu kyau da ba mu san da su ba. Ko da yake yana ganin kurakurenmu, ya san cewa muna so mu yi abin da yake so. Don haka, yana ƙaunar mu. (Rom. 7:15) Idan muka gane cewa Jehobah ya san mu ciki da waje, hakan zai ƙarfafa mu kuma ya sa mu ci gaba da bauta masa da farin ciki da kuma aminci.

Hotuna: Na 1. Wani ɗanꞌuwa da yake cikin damuwa yana kallon waje ta wundo yayin da ake ruwan sama kuma wuri ya yi duhu. Na 2. A aljanna ɗanꞌuwan yana hawan kan dutse tare da abokansa, yana kallon yadda wurin yake da kyau.

Jehobah yana taimaka mana mu ƙara gaskata da alkawuran da ya yi da za su faru a sabuwar duniya. Hakan yana taimaka mana mu jimre matsaloli dabam-dabam da muke fuskanta a yau (Ka duba sakin layi na 18-19)c


19. Mene ne muka sani game da Jehobah?

19 Babu shakka, mun san cewa Jehobah yana ƙaunar mu. (1 Yoh. 4:8) Mun san cewa kome da ya ce mu yi, da kome da ya ce mu guje wa, ya yi hakan ne don yana ƙaunar mu kuma yana so mu yi rayuwa mafi inganci. Mun san cewa Jehobah yana so mu yi rayuwa har abada. Shi ya sa ya turo Ɗansa don ya zo ya mutu a madadinmu. Yadda Yesu ya mutu ya tabbatar mana cewa ko da yake mu masu zunubi ne, za mu iya bauta wa Allah yadda yake so. (Rom. 7:​24, 25) Kuma mun san cewa “Allah ya fi zuciyarmu ya kuma san dukan kome.” (1 Yoh. 3:​19, 20) Jehobah ya san kome da kome game da mu, kuma yana da tabbaci cewa za mu iya bauta masa yadda yake so.

20. Me zai taimaka mana mu rage yawan damuwa a kan abubuwan da ba mu sani ba?

20 Babu komen da ya kamata mu sani da Jehobah ya ɓoye mana. Saboda haka, bai kamata mu damu a kan abin da ba mu sani ba. A maimakon haka, zai dace mu mai da hankali a kan abubuwan da suka fi muhimmanci. Idan muka yi hakan, muna nuna cewa mun dogara ga Jehobah, Wanda shi ne “mai cikakken sani.” (Ayu. 36:4) Ko da yake akwai wasu abubuwa da ba mu sani yanzu ba, mun san cewa Jehobah zai ci gaba da koya mana sabbin abubuwa har abada. Hakan abin farin ciki ne domin za mu ci gaba da koyan sabbin abubuwa game da Mahaliccinmu.—M. Wa. 3:11.

MECE CE AMSARKA . . .

  • Me ya sa ya dace da ba mu san lokacin da ƙarshen zamanin nan zai zo ba?

  • Me ya sa ba sanin abin da zai faru a nan gaba ne zai sa mu farin ciki ba?

  • Me ya sa zai dace mu riƙa tuna cewa Jehobah ya san mu ciki da waje?

WAƘA TA 104 Allah Yana Ba Mu Ruhunsa Mai Tsarki

a Yesu ne zai ja-goranci yaƙin Armageddon. Saboda haka, za mu iya ce yanzu ya san ranar da za a yi wannan yaƙin da kuma lokacin da zai yi nasara kwata-kwata a kan Shaiɗan da magoya bayansa.—R. Yar. 6:2; 19:​11-16.

b BAYANI A KAN HOTUNA: Wani mutum da ɗansa suna sassaka abubuwa a cikin jakar gaggawarsu. Hakan zai sa su kasance a shirye ko da wani abu ya faru.

c BAYANI A KAN HOTO: Wani ɗanꞌuwa da yake cikin damuwa yana tunani game da irin rayuwar da zai more a cikin aljanna.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba