Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w25 Agusta pp. 2-7
  • Yadda Jehobah Yake Taimaka Mana Mu Jimre

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Jehobah Yake Taimaka Mana Mu Jimre
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ADDUꞌA
  • KALMAR ALLAH
  • ꞌYANꞌUWA A IKILISIYA
  • BEGENMU
  • Ka Tuna Cewa Jehobah “Allah Mai Rai” Ne
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Ka Kasance da Sauƙin Kai Idan Akwai Abubuwan da Ba Ka Sani Ba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Wasiƙa da Za Ta Taimake Mu Mu Jimre har Karshe
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Jehobah “Yakan Warkar da Masu Fid da Zuciya”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
w25 Agusta pp. 2-7

TALIFIN NAZARI NA 32

WAƘA TA 38 Zai Ƙarfafa Ka

Yadda Jehobah Yake Taimaka Mana Mu Jimre

“Allah mai alheri duka . . . zai mai da ku cikakku, zai kafa ku, zai kuma ƙarfafa ku.”—1 BIT. 5:10.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga abubuwan da Jehobah ya tanadar mana da za su taimaka mana mu jimre, da kuma abin da muke bukatar mu yi don mu amfana daga kowannensu.

1. Me ya sa muke bukatar mu jimre, kuma waye ne zai taimaka mana? (1 Bitrus 5:10)

A WANNAN kwanakin ƙarshe da ake shan wahala sosai, bayin Jehobah suna bukatar su kasance da jimiri. Wasu suna fama da ciwo mai tsanani. Wasu kuma suna shan wahala domin wani nasu ya mutu. Ƙari ga haka, wasu suna fama da tsanantawa, daga mambobin iyalinsu ko kuma daga hukumomin gwamnati. (Mat. 10:​18, 36, 37) Ka tabbata cewa komin wahalar da kake fama da ita, Jehobah zai iya taimaka maka ka jimre.—Karanta 1 Bitrus 5:10.

2. Idan aka ce Kirista ya jimre, mene ne ake nufi?

2 Jimrewa tana nufin kasancewa da aminci ga Jehobah da bauta masa da farin ciki, ko da muna fama da matsaloli ko ana tsananta mana, ko kuma an jarabce mu mu yi zunubi. Ba za mu iya jimrewa idan Jehobah bai taimaka mana ba. Shi ne yake ba mu “cikakken ikon da ya fi duka” don mu iya yin hakan. (2 Kor. 4:7) A wannan talifin, za mu tattauna abubuwa huɗu da Jehobah ya tanadar da za su taimaka mana mu iya jimrewa. Za mu kuma ga abin da muke bukatar mu yi don mu amfana daga kowannensu.

ADDUꞌA

3. Me ya sa adduꞌa abu ne mai ban mamaki?

3 Jehobah ya tanadar mana da wani abu mai ban mamaki da zai taimaka mana mu jimre. Ko da yake mu ajizai ne, ya ba mu gatan yi masa magana kuma yana sauraron mu. (Ibran. 4:16) Ka ɗan yi tunani: Za mu iya yin adduꞌa ga Jehobah a kowane lokaci kuma a kan kowane irin batu. Yakan saurare mu ko da wani yare ne muka yi amfani da shi, da duk inda muke, ko da muna nan mu kaɗai ko muna cikin kurkuku. (Yona 2:​1, 2; A. M. 16:​25, 26) Idan muna cikin damuwa sosai kuma muka rasa yadda za mu gaya masa yadda muke ji, Jehobah yana iya gane abin da muke so mu gaya masa. (Rom. 8:​26, 27) A gaskiya, adduꞌa abu ne mai ban mamaki!

4. Me ya sa za mu iya cewa idan muka roƙi Jehobah ya taimaka mana mu jimre, zai yi hakan?

4 A Littafi Mai Tsarki, Jehobah ya tabbatar mana cewa, “idan mun roƙi kome bisa ga nufinsa, zai saurare mu.” (1 Yoh. 5:14) Shin, za mu iya roƙan Jehobah ya taimaka mana mu jimre? Ƙwarai kuwa! Yin hakan ya jitu da nufinsa. Me ya sa za mu iya ce hakan? Jehobah ya ce idan muka jimre, zai iya ba da amsa ga mai yi masa reni, wato Shaiɗan Iblis. (K. Mag. 27:11) Ban da haka ma, Littafi Mai Tsarki ya ce, Jehobah yana marmari “ya ƙarfafa waɗanda suka dogara gare shi da zuciya ɗaya.” (2 Tar. 16:9) Saboda haka, za mu iya kasancewa da tabbaci cewa, Jehobah yana so ya taimaka mana kuma zai ba mu ƙarfin da muke bukata don mu iya jimrewa.—Isha. 30:18; 41:10; Luk. 11:13.

5. Ta yaya yin adduꞌa zai sa mu kasance da kwanciyar hankali? (Ishaya 26:3)

5 Littafi Mai Tsarki ya ce idan mun gaya wa Jehobah abubuwan da ke damun mu, ‘zai ba mu salama irin wadda ta wuce dukan ganewar ɗan Adam, za ta kuma tsare zukatanmu da tunaninmu cikin Almasihu Yesu.’ (Filib. 4:7) Hakan abin godiya ne sosai. Mutanen da ba sa bauta wa Jehobah ma suna fama da matsaloli dabam-dabam, kuma suna gwada abubuwa dabam-dabam don su kasance da kwanciyar hankali, ko su mance da wahalar da suke ciki. Alal misali, wasu suna iya ƙoƙarinsu su daina tunani a kan kome da kome don su kasance da kwanciyar hankali. Idan mutum ba ya tunani a kan kome, zai iya yi wa aljannu sauƙi su rinjaye shi, kuma hakan na da haɗari sosai. (Ka duba Matiyu 12:​43-45.) Ballantana ma, kwanciyar hankalin da za mu samu daga wurin Jehobah idan muka roƙe shi, ta fi kowace irin kwanciyar hankalin da za mu iya ba wa kanmu. Idan muka yi adduꞌa ga Jehobah, muna nuna cewa mun dogara gare shi gabaki ɗaya, kuma zai ba mu “cikakkiyar salama.” (Karanta Ishaya 26:3.) Hanya ɗaya da Jehobah yake yin hakan, ita ce ta wajen taimaka mana mu tuna Nassosi masu ban ƙarfafa da muka karanta. Nassosin nan suna kwantar mana da hankali, domin suna tuna mana cewa Jehobah yana ƙaunar mu kuma yana so ya taimaka mana.—Zab. 62:​1, 2.

6. Waɗanne abubuwa ne kuma za ka iya yin adduꞌa a kai? (Ka kuma duba hoton.)

6 Abin da za ka iya yi. Yayin da kake cikin damuwa, ka gaya wa Jehobah yadda kake ji. Ka “danƙa wa Yahweh damuwarka” kuma ka roƙe shi ya ba ka kwanciyar hankali. (Zab. 55:22) Ka roƙe shi ya taimaka maka ka san abin da za ka yi. (K. Mag. 2:​10, 11) Ƙari ga haka, kada ka manta ka gode wa Jehobah yayin da kake adduꞌa. (Filib. 4:6) Ka yi tunani a kan yadda Jehobah yake taimaka maka kowace rana don ka iya jimrewa, sai ka yi masa godiya don taimako da abubuwa masu kyau da yake ba ka. Kada ka bar matsalolin da kake fama da su su sa ka manta da hanyoyin da Jehobah yake taimaka maka.—Zab. 16:​5, 6.

Wani ɗanꞌuwa yana zaune a gidansa, yana adduꞌa, a lokacin da ake sanyi. Ya buɗe Littafi Mai Tsarki ya ajiye a cinyarsa, kuma akwai kwalban magani a kan teburin da ke gefensa.

Idan kana adduꞌa kana magana da Jehobah ne. Idan kuma kana karanta Kalmarsa, Jehobah yana magana da kai ne (Ka duba sakin layi na 6)b


KALMAR ALLAH

7. Ta yaya yin nazarin Littafi Mai Tsarki zai taimaka mana mu jimre?

7 Jehobah ya ba mu Kalmarsa don ya taimaka mana mu iya jimrewa. Littafi Mai Tsarki na ɗauke da ayoyi da yawa da suka tabbatar mana cewa Jehobah zai taimaka mana. Bari mu yi laꞌakari da ɗaya daga cikinsu. Matiyu 6:8 ta ce: “Ubanku ya san abin da kuke bukata kafin ma ku roƙe shi.” Yesu ne ya yi maganar nan, kuma babu wanda ya san Jehobah kamar sa. Saboda haka, muna da tabbacin cewa a duk yanayin da muke ciki, Jehobah ya san abin da muke bukata kuma zai taimaka mana. Littafi Mai Tsarki na ɗauke da alkawura da yawa da Jehobah ya yi da za su taimaka mana mu jimre matsalolinmu.—Zab. 94:19.

8. (a) Wace shawara ce Littafi Mai Tsarki ya ba mu da za ta taimaka mana mu jimre? (b) Me zai taimaka mana mu tuna da shawarwarin Littafi Mai Tsarki a lokacin da muke bukata?

8 Littafi Mai Tsarki na ɗauke da shawarwarin da za su taimaka mana mu jimre yanayoyi masu wuya. Shawarwarin nan za su taimaka mana mu sami hikimar da muke bukata don yin zaɓi masu kyau. (K. Mag. 2:​6, 7) Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ce kada mu damu domin gobe, a maimakon haka, mu dogara ga Jehobah kowace rana. (Mat. 6:34) Idan muna karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana kuma muna yin tunani a kan abin da muka karanta, hakan zai sa ya yi mana sauƙi mu tuna da abin da ke Littafi Mai Tsarki a lokacin da muke so mu yanke wata shawara, ko idan muna so mu san yadda za mu iya jimre wata matsala.

9. Ta yaya labaran da ke Littafi Mai Tsarki suke tabbatar mana cewa Jehobah zai taimaka mana?

9 Littafi Mai Tsarki na kuma ɗauke da labaran mutane kamar mu, da suka dogara ga Jehobah kuma ya taimaka musu. (Ibran. 11:​32-34; Yak. 5:17) Idan muka yi tunani a kan labaran nan, hakan zai sa mu tabbata cewa mu ma Jehobah zai taimaka mana, domin shi ne “wurin ɓuyanmu da ƙarfinmu, taimakonmu na kurkusa lokacin wahala.” (Zab. 46:1) Yayin da muke tunani a kan yadda bayin Jehobah suka nuna bangaskiya kuma suka ci-gaba da jimrewa, hakan zai sa mu yi koyi da su.—Yak. 5:​10, 11.

10. Me za ka yi don ka amfana sosai daga Littafi Mai Tsarki?

10 Abin da za ka iya yi. Ka karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana, kuma ka rubuta ayoyin da suka taimaka maka sosai. ꞌYanꞌuwa da yawa suna karanta Nassosi da bayyanen da ke littafin Tattauna Kalmar Allah Kowace Rana da safe, hakan yana sa su sami abin da za su riƙa yin tunani a kai a ranar. Abin da ya taimaka ma wata ꞌyarꞌuwa mai suna Mariea ke nan, lokacin da take kula da iyayenta. Dukansu biyu sun kamu da cutar kansa kuma yanayinsu sai ƙara muni yake yi. ꞌYarꞌuwa Marie ta ce, “Kowace safe, ina karanta Nassin da ke littafin Tattauna Kalmar Allah Kowace Rana, kuma in yi tunani a kan abin da na koya. Hakan ya taimaka min in riƙa yin tunani game da Jehobah kullum, da kuma abubuwa masu kyau da yake koya mana, maimakon yin tunani a kan matsalolin da nake fama da su kawai.”—Zab. 61:2.

ꞌYANꞌUWA A IKILISIYA

11. Me ya sa sanin cewa ba mu kaɗai ba ne muke fama da matsaloli yake ƙarfafa mu?

11 Jehobah ya ba mu ꞌyanꞌuwa a faɗin duniya da za su taimaka mana mu iya jimrewa. Sanin cewa ꞌyanꞌuwanmu “masu bi koꞌina a duniya, su ma suna shan wahala haka” yana ƙarfafa mu mu jimre. (1 Bit. 5:9) ꞌYanꞌuwan nan suna fama da irin matsalolin da mu ma muke fama da su kuma suna jimrewa. Saboda haka, mu ma za mu iya jimrewa!—A. M. 14:22.

12. Ta yaya ꞌyanꞌuwanmu za su iya taimaka mana, kuma ta yaya mu ma za mu taimaka musu? (2 Korintiyawa 1:​3, 4)

12 ꞌYanꞌuwanmu za su iya taimaka mana mu jimre ta abubuwan da suke faɗa, da abubuwan da suke yi. Manzo Bulus ma ya shaida hakan. A wasiƙun da ya rubuta, ya ambata sunayen mutanen da suka taimaka masa lokacin da aka tsare shi a kurkuku, kuma ya gode musu. ꞌYanꞌuwan nan sun ƙarfafa shi da kalamansu kuma sun tanadar masa da abin da yake bukata. (Filib. 2:​25, 29, 30; Kol. 4:​10, 11) A yau, idan muna fama da matsaloli, ꞌyanꞌuwanmu maza da mata suna taimaka mana mu iya jimrewa; kuma mu ma za mu iya taimaka musu a lokacin da suke cikin damuwa.—Karanta 2 Korintiyawa 1:​3, 4.

13. Mene ne ya taimaka ma wata ꞌyarꞌuwa mai suna Maya ta iya jimrewa?

13 ꞌYanꞌuwa maza da mata sun ƙarfafa wata ꞌyarꞌuwa mai suna Maya da ke ƙasar Rasha. A 2020, jamiꞌan tsaro sun shiga gidanta ba zato ba tsammani, suka yi bincike kuma suka kai ta kotu don imaninta. ꞌYarꞌuwa Maya ta ce: “A lokacin na damu, na gaji, kuma na yi baƙin ciki. Amma ꞌyanꞌuwa maza da mata sun kira ni a waya. Wasu sun tura mini saƙonnin tes, wasu kuma sun rubuta wasiƙu. Sun gaya min cewa suna ƙauna ta sosai. Na daɗe da sanin cewa ꞌyanꞌuwa suna ƙauna ta kuma mu kamar iyali ne, amma abin da suka yi ya daɗa tabbatar min da hakan.”

14. Me za mu yi don mu amfana daga taimakon da ꞌyanꞌuwanmu suke mana? (Ka kuma duba hoton.)

14 Abin da za ka iya yi. Yayin da kake jimre wata matsala, yana da muhimmanci ka kasance tare da ꞌyanꞌuwa maza da mata, kuma ku riƙa tattaunawa. Kada ka yi jinkirin neman taimako daga wurin dattawa. Kowannensu “kamar mafaka daga iska” ne, “kamar wurin ɓuya daga ruwan ƙanƙara.” (Isha. 32:2) Ka kuma tuna cewa ꞌyanꞌuwanmu Kiristoci ma suna fama da matsaloli. Saboda haka, zai dace kai ma ka riƙa nuna musu alheri. Yin hakan zai sa ka farin ciki, kuma zai taimaka maka ka iya jimre naka matsalolin.—A. M. 20:35.

Ɗanꞌuwan zaune a gidansa a lokacin damuna tare da wani ɗanꞌuwa da matarsa da yaransu mata biyu. Suna taɗi suna dariya. Akwai sanda da kwalaban magungunansa a gefensa. Ɗaya daga cikin yaran tana nuna masa hoton Aljanna da ta zana.

Ka kasance tare da ꞌyanꞌuwa maza da mata (Ka duba sakin layi na 14)c


BEGENMU

15. Ta yaya begen da Yesu yake da shi ya taimaka masa, kuma ta yaya begen da muke da shi yake taimaka mana? (Ibraniyawa 12:2)

15 Begen da Jehobah ya ba mu yana taimaka mana mu jimre. (Rom. 15:13) Ka tuna cewa, begen da Yesu yake da shi ne ya taimaka masa ya iya jimre kwanakinsa masu wuya na ƙarshe a duniya. (Karanta Ibraniyawa 12:2.) Yesu ya san cewa idan ya riƙe aminci, hakan zai ɗaukaka Jehobah kuma zai nuna cewa dukan abin da Shaiɗan ya faɗa game da Jehobah ƙarya ne. Yesu kuma ya mai da hankali ga albarkun da zai samu, wato lokacin da zai koma wurin Ubansa a sama, da lokacin da za a naɗa shi sarki, da kuma lokacin da zai soma sarauta tare da shafaffu. Haka ma, begen da muke da shi na yin rayuwa a sabuwar duniya har abada yana taimaka mana mu jimre duk wata matsala da duniyar Shaiɗan take sa mu fuskanta.

16. Ta yaya kasancewa da bege ya taimaka ma wata ꞌyarꞌuwa ta jimre, kuma mene ne ka koya daga abin da ta faɗa?

16 Bari mu yi laꞌakari da yadda begen yin rayuwa a sabuwar duniya ya taimaka ma wata ꞌyarꞌuwa mai suna Anna a ƙasar Rasha. An kama mijinta an sa shi a cikin kurkuku kafin a kai shi kotu. ꞌYarꞌuwa Anna ta ce: “Na yi adduꞌa da kuma bimbini a kan begen da Jehobah ya ba mu, hakan ya taimaka mini kada in yi sanyin gwiwa. Na fahimci cewa komin nisan dare, gari zai waye. Jehobah zai kawar da maƙiyansa kuma zai albarkace mu.”

17. Ta yaya za mu nuna cewa muna godiya don alkawuran da Jehobah ya yi mana game da nan gaba? (Ka kuma duba hoton.)

17 Abin da za ka iya yi. Ka yi tunani a kan alkawarin da Jehobah ya yi maka game da nan gaba. Ka yi tunanin yadda rayuwa za ta kasance a sabuwar duniya, inda za ka kasance da dukan abokanka da iyalinka, kuma kowa da kowa zai yi farin ciki. Idan muka gwada matsalolin da muke fama da su a yau da albarkun da za mu more a nan gaba, za mu ga cewa wannan “ꞌyar wahalar da muke sha ba za ta daɗe ba.” (2 Kor. 4:17) Ƙari ga haka, ka yi iya ƙoƙarinka wajen gaya wa mutane alkawuran da Jehobah ya yi game da nan gaba. Ka yi tunanin irin fama da mutanen da ba sa bauta wa Jehobah suke yi. Su ma suna fama da matsaloli dabam-dabam, amma ba su san game da alkawura masu kyau da Jehobah ya yi ba. Saboda haka, ko da abu kaɗan ne ka gaya musu, hakan zai ƙarfafa su kuma zai sa su so ƙara sani game da Mulkin Allah da kuma alkawuran da Jehobah ya yi.

Ɗanꞌuwan yana zaune a gidansa a lokacin rani, yana tunani a kan hoton Aljanna da ke wayarsa. A gefensa, akwai kwalaban magunguna da kuma wani abin da yake riƙewa ya yi tafiya.

Ka yi tunani a kan alkawura masu kyau da Jehobah ya yi maka (Ka duba sakin layi na 17)d


18. Me ya sa muke da tabbaci cewa Jehobah zai cika alkawuransa?

18 Bayan da Ayuba ya yi fama da matsaloli dabam-dabam kuma ya riƙe amincinsa, ya gaya wa Jehobah cewa: “Na sani ka iya yin kome, abin da ka yi niyya, ba a iya hana ka.” (Ayu. 42:2) Ayuba ya koyi cewa ba abin da zai iya hana Jehobah cika alkawuransa. Mu ma a yau, idan muka tuna cewa Jehobah zai cika alkawuransa, kuma ya cire matsalolin da muke fama da su, hakan zai taimaka mana mu jimre. Alal misali, a ce wata mata ta daɗe tana rashin lafiya, kuma ta je wurin likitoci dabam-dabam, duk da haka, babu wanda ya iya warkar da ita. Hakan zai sa ta sanyin gwiwa ba kaɗan ba. Amma idan ta haɗu da wani likitan da ya ƙware kuma ya gaya mata dalilin da ya sa take rashin lafiya da kuma irin jinyar da zai yi mata, hakan zai sa ta farin ciki sosai ko da zai ɗau lokaci kafin ta sami sauƙi. Zai yi mata sauƙi ta ci-gaba da jimrewa da yake ta san a ƙarshe za ta warke. Haka ma, mu ma za mu ci-gaba da jimrewa domin mun tabbata cewa Allah zai cika alkawarin Aljanna da ya yi.

19. Waɗanne abubuwa ne za su taimaka mana mu iya jimrewa?

19 Kamar yadda muka tattauna, Jehobah yana taimaka mana mu jimre matsalolinmu ta wajen adduꞌa, da Kalmarsa, da ꞌyanꞌuwanmu, da kuma begenmu. Idan muka yi amfani da waɗannan tanadodin, Jehobah zai taimaka mana ko da wace irin matsala ce muke ciki. Kuma za mu iya jimrewa zuwa lokacin da za a kawar da wahalolin da muke sha da kuma duniyar Shaiɗan.—Filib. 4:​13, NWT.

TA YAYA JEHOBAH YAKE TAIMAKA MANA MU JIMRE TA WAJEN . . .

  • adduꞌa da Kalmarsa?

  • ꞌyanꞌuwanmu?

  • begenmu?

WAƘA TA 33 Mu Miƙa Dukan Damuwarmu ga Jehobah

a An canja wasu sunaye a wannan talifin.

b BAYANI A KAN HOTO: Wani ɗanꞌuwa da ke fama da matsaloli ya yi shekaru da shekaru yana jimrewa da aminci.

c BAYANI A KAN HOTO: Wani ɗanꞌuwa da ke fama da matsaloli ya yi shekaru da shekaru yana jimrewa da aminci.

d BAYANI A KAN HOTO: Wani ɗanꞌuwa da ke fama da matsaloli ya yi shekaru da shekaru yana jimrewa da aminci.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba