TALIFIN NAZARI NA 47
WAƘA TA 38 Zai Ƙarfafa Ka
“ Kai Mai Daraja Ne Sosai”!
“ Kai mai daraja ne sosai.”—DAN. 9:23.
ABIN DA ZA MU KOYA
Wannan talifin zai taimaka wa waɗanda suke ganin kamar ba su da daraja su fahimci cewa Jehobah yana ɗaukan su da muhimmanci.
1-2. Me zai taimaka mana mu san cewa muna da daraja sosai a gun Jehobah?
JEHOBAH yana ɗaukan dukan bayinsa da muhimmanci sosai. Amma wasu suna ganin cewa ba su da daraja a gunsa. Mai yiwuwa suna jin hakan ne don yadda aka wulaƙanta su. Shin, hakan ya taɓa faruwa da kai? Idan haka ne, mene ne zai taimaka maka ka san cewa kana da daraja sosai a gun Jehobah?
2 Wani abin da zai taimaka maka shi ne, karanta labaran Littafi Mai Tsarki da suka nuna yadda Jehobah yake son a riƙa bi da mutane. Yesu ya daraja mutane kuma ya yi musu alheri, saꞌad da yake duniya. Ta haka, ya nuna cewa shi da Ubansa suna daraja mutanen da suke ganin cewa su ba kome ba ne. (Yoh. 5:19; Ibran. 1:3) A wannan talifin, za mu tattauna: (1) yadda Yesu ya taimaka wa mutane su san cewa suna da daraja sosai a gun Jehobah, (2) yadda za mu tabbatar wa kanmu cewa muna da daraja sosai a gun Jehobah.—Hag. 2:7.
YADDA YESU YA TAIMAKA WA MUTANE SU SAN CEWA SUNA DA DARAJA SOSAI A GUN JEHOBAH
3. Ta yaya Yesu ya bi da mutanen Galili da suka zo neman taimakonsa?
3 A lokacin da Yesu yake waꞌazi a Galili, mutane da yawa sun zo wurinsa don su saurare shi kuma ya warkar da su. Yesu ya ce “suna kama da tumakin da aka fere fatarsu kuma suna hawa da sauka don ba su da makiyayi.” (Mat. 9:36) Shugabannin addinansu suna ganin su ba kome ba ne, har ma sun kira su “laꞌanannu.” (Yoh. 7:47-49) Amma Yesu ya nuna musu cewa suna da muhimmanci ta wajen koyar da su da kuma warkar da su daga cututtukansu. (Mat. 9:35) Ƙari ga haka, don ya iya taimaka wa mutane da yawa, ya koya wa almajiransa yadda za su yi waꞌazi. Kuma ya ba su ikon warkar da marar lafiya.—Mat. 10:5-8.
4. Mene ne muka koya daga yadda Yesu ya bi da masu sauraronsa?
4 Yadda Yesu ya yi wa masu sauraronsa alheri kuma ya daraja su, ya nuna cewa shi da Ubansa suna daraja mutanen da wasu suke wulaƙantawa. Idan kana bauta wa Jehobah, kuma kana ganin kai ba kome ba ne a gunsa, ka yi tunani a kan yadda Yesu ya bi da masu sauraronsa. Yin hakan zai taimaka maka ka ga cewa kana da daraja sosai a gun Jehobah.
5. Ka bayyana yanayin da matar da Yesu ya haɗu da ita a Galili take ciki.
5 Ba tarin jamaꞌa ne kawai Yesu ya koyar da su ba, amma ya mai da hankali a kan mutane ɗaɗɗaya. Alal misali, saꞌad da yake waꞌazi a Galili, Yesu ya haɗu da wata mata da ta yi shekaru 12 tana fama da yoyon jini. (Mar. 5:25) Dokar da Allah ya bayar ta hannun Musa ta hana macen da take fama da irin cutar nan zuwa kusa da mutane. Kuma duk wanda ya taɓa ta, zai zama marar tsabta. Mai yiwuwa hakan ya sa a yawancin lokuta takan zauna ita kaɗai. Ƙari ga haka, ba za ta yin bukukuwa ko ta je wurin bauta tare da mutane ba. (L. Fir. 15:19, 25) Babu shakka, hakan zai sa ta ji kamar ba mai ƙaunar ta.—Mar. 5:26.
6. Mene ne matar ta yi don ta warke?
6 Matar ta so Yesu ya warkar da ita. Amma ba ta je wurinsa kai tsaye ba. Me ya sa? Wataƙila tana kunya ne don yanayin da take ciki. Ko kuma tana tsoron cewa Yesu zai kore ta don bai kamata ta shigo cikin jamaꞌa ba. Saboda haka, ta taɓa mayafinsa ne kawai da tabbaci cewa hakan zai warkar da ita. (Mar. 5:27, 28) Kuma abin da ya faru ke nan. Bayan hakan, sai Yesu ya ce, ‘waye ne ya taɓa ni?’ Sai ta gaya masa gaskiya cewa ita ce. Mene ne Yesu ya yi da ya ji hakan?
7. Yaya Yesu ya bi da wannan matar da take fama? (Markus 5:34)
7 Yesu ya daraja ta kuma ya yi mata magana cikin alheri. Ya lura cewa matar tana “cikin tsoro da rawar jiki.” (Mar. 5:33) Hakan ya sa ya yi mata magana da alheri kuma ya ƙarfafa ta. Ƙari ga haka, ya kira ta “ꞌyata.” Yesu ya yi amfani da wannan kalmar don ya nuna cewa yana ƙaunar ta kuma yana so ya kwantar mata da hankali. (Karanta Markus 5:34.) A wannan karon ne kaɗai, Yesu ya kira mace ‘ꞌyata,’ a Littafi Mai Tsarki. Mai yiwuwa ya yi amfani da wannan kalmar ne don ya ga cewa matar ta ji tsoro sosai. Babu shakka, matar ta yi farin ciki sosai don yadda Yesu ya yi mata magana! Da a ce Yesu bai yi mata magana haka ba, da wataƙila za ta tafi tana baƙin ciki duk da cewa ta warke. A maimakon haka, Yesu ya nuna mata cewa tana da daraja sosai a gun Jehobah, Ubanmu na sama mai ƙauna.
8. Waɗanne ƙalubale ne wata ꞌyarꞌuwa a Brazil ta yi fama da su?
8 A yau ma, wasu bayin Jehobah suna fama da cututtuka da ke ci musu tuwo a ƙwarya. Alal misali, akwai wata ꞌyarꞌuwa majagaba da ke zama a Brazil, mai suna Maria.a An haife ta ba ta da kafa da kuma hannun hagu. Ta ce: “A yawancin lokuta, ana cin zali na a makaranta don yadda nake. Kuma ana kira na da wasu irin sunayen da suke sa ni baƙin ciki sosai. A wasu lokuta, har a gida ma ana nuna min cewa ni ba kome ba ne.”
9. Mene ne ya taimaka wa Maria ta san cewa, tana da daraja sosai a gun Jehobah?
9 Mene ne ya taimaka wa ꞌYarꞌuwa Maria? Saꞌad da ta zama Mashaidiya, ꞌyanꞌuwa a ikilisiya sun ƙarfafa ta kuma sun taimaka mata ta riƙa ganin kanta yadda Jehobah yake ganin ta. Ta ce: “ꞌYanꞌuwa maza da mata da yawa sun taimaka mini. Ina gode wa Jehobah don yadda ya taimaka min in kasance a cikin iyalinsa.” ꞌYanꞌuwa mata da maza sun taimaka wa Maria ta san cewa tana da daraja sosai gun Jehobah.
10. Wace matsala ce Maryamu Magdalin take fama da ita, kuma yaya hakan ya sa ta ji? (Ka kuma duba hotunan.)
10 Bari mu yi laꞌakari kuma da yadda Yesu ya taimaka wa Maryamu Magdalin. Tana fama da aljannu bakwai a jikinta! (Luk. 8:2) Mai yiwuwa aljannun sun sa tana yin wasu irin abubuwa. Kuma wataƙila hakan ya sa mutane sun guje ta. Babu shakka a wannan lokacin, za ta damu sosai kuma ta ga kamar babu wanda yake ƙaunarta, ko yake so ya taimaka mata. Amma Yesu ya cire aljannun daga jikinta kuma ta zama ɗaya daga cikin mabiyansa. A waɗanne hanyoyi ne kuma Yesu ya taimaka wa Maryamu Magdalin ta fahimci cewa tana da daraja sosai a gun Jehobah?
Ta yaya Yesu ya nuna wa Maryamu Magdalin cewa tana da daraja sosai a gun Jehobah? (Ka duba sakin layi na 10-11)
11. Ta yaya Yesu ya nuna wa Maryamu Magdalin cewa tana da daraja sosai a gun Jehobah? (Ka kuma duba hotunan.)
11 Yesu ya ba wa Maryamu Magdalin damar bin sa zuwa waꞌazi a wurare dabam-dabam.b Hakan ya sa ta ci-gaba da amfana sosai daga abubuwan da Yesu yake koya wa mutane. Ƙari ga haka, tana cikin waɗanda suka fara haɗuwa da Yesu kuma suka yi magana da shi bayan ya tashi daga mutuwa. Kuma Yesu ya ce mata ta je ta gaya wa sauran almajiran cewa ya tashi daga mutuwa. Waɗannan abubuwan da Yesu ya yi sun taimaka mata ta ga cewa tana da daraja sosai a gun Jehobah!—Yoh. 20:11-18.
12. Me ya sa Lidia ta ga kamar ba ta da amfani?
12 Kamar Maryamu Magdalin, mutane da yawa a yau suna ganin kamar babu wanda yake ƙaunar su. Abin da ya faru da wata ꞌyarꞌuwa daga ƙasar Sifen mai suna Lidia ke nan. Lokacin da mahaifiyarta take da cikinta, ta yi ƙoƙari ta cire cikin. Kuma tun tana ƙarama mahaifiyarta tana wulaƙanta ta. ꞌYarꞌuwa Lidia ta ce: “Buri na a rayuwa shi ne mutane su amince da ni kuma su ƙaunace ni. Na ga kamar babu wanda zai taɓa ƙauna ta domin mahaifiyata ta tabbatar min cewa ba ni da amfani.”
13. Me ya taimaka wa Lidia ta san cewa tana da daraja sosai a gun Jehobah?
13 Saꞌad da Lidia ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki, abubuwa sun canja a rayuwarta. Yin adduꞌa, da karanta Littafi Mai Tsarki, da kuma yadda ꞌyanꞌuwa suke nuna mata alheri sun taimaka mata ta fahimci cewa tana da daraja sosai a gun Jehobah. Ta ce: “Mijina yana yawan gaya mini yadda yake ƙauna ta. A kowane lokaci yana tuna mini da halaye na masu kyau. Wasu ꞌyanꞌuwa ma suna tuna mini da hakan.” Kamar Lidia, akwai wani a ikilisiyarku da ke bukatar taimako don ya fahimci cewa yana da daraja sosai a gun Jehobah? Za ka iya taimaka masa ta abubuwan da kake faɗa da kuma abubuwan da kake yi.
KA RIƘA GANIN KANKA YADDA JEHOBAH YAKE GANIN KA
14. Ta yaya 1 Samaꞌila 16:7 ta taimaka mana mu ga yadda Jehobah yake ɗaukan mutane? (Ka kuma duba akwatin nan “Me Ya Sa Jehobah Yake Daraja Bayinsa?”)
14 Ka tuna cewa Jehobah ba ya ganin ka kamar yadda mutane a duniya suke yi. (Karanta 1 Samaꞌila 16:7.) Mutane da yawa a duniya suna ɗaukan mutum da daraja idan yana da kyau, ko kuɗi, ko kuma ya yi karatu sosai. Amma ba haka Jehobah yake yi ba. (Isha. 55:8, 9) Saboda haka, ka yi ƙoƙari ka riƙa ganin kanka yadda Jehobah yake ganin ka, ba kamar yadda mutane a duniya suke yi ba. Za ka iya karanta labaran mutane a Littafi Mai Tsarki da a wasu lokuta sun ga kamar ba su da daraja a gun Jehobah. Kamar su Iliya, da Naomi, da kuma Hannatu. Za ka kuma iya rubuta abubuwan da suka faru a rayuwarka da suka tabbatar maka cewa Jehobah yana ƙaunar ka kuma yana ɗaukan ka da daraja. Ƙari ga haka, za ka iya yin bincike a littattafanmu a kan abubuwan da suka nuna cewa Jehobah ya damu da kai kuma yana ɗaukan ka da daraja.c
15. Me ya sa Jehobah ya ce annabi Daniyel mutum “mai daraja ne sosai” a gunsa? (Daniyel 9:23)
15 Ka tuna cewa riƙe amincinka yana sa ka zama da daraja sosai a gun Jehobah. Akwai lokacin da annabi Daniyel ya yi sanyin gwiwa sosai. Mai yiwuwa a lokacin ya kusan shekaru 100. (Dan. 9:20, 21) Ta yaya Jehobah ya ƙarfafa shi? Ya tura malaꞌikansa wato Jibraꞌilu ya gaya masa cewa shi “mai daraja ne sosai” da kuma cewa an amsa adduꞌarsa. (Karanta Daniyel 9:23.) Me ya sa Jehobah ya daraja Daniyel sosai? Domin Daniyel mutum ne mai aminci kuma yana son adalci. (Ezek. 14:14) Jehobah ya sa an rubuta labarin nan a cikin Littafi Mai Tsarki don ya ƙarfafa mu. (Rom. 15:4) Saboda haka, idan kana bauta wa Jehobah da aminci, kuma kana son adalci, kana da daraja sosai a gunsa. Kuma kamar yadda ya amsa adduꞌar da Daniyel ya yi, zai amsa adduꞌarka kai ma.—Mik. 6:8; Ibran. 6:10.
16. Mene ne zai taimaka maka ka ɗauki Jehobah a matsayin Uba mai ƙauna?
16 Ka ɗauki Jehobah a matsayin Uba wanda yake ƙaunar ka. Yana so ya taimaka maka. Ba ya kuma neman kurakuranka. (Zab. 130:3; Mat. 7:11; Luk. 12:6, 7) Sanin hakan ya taimaka wa mutane da yawa da suke ganin kamar ba su da wani amfani. Ka yi laꞌakari da labarin ꞌyanꞌuwa Michelle daga ƙasar Sifen. Ta ga kamar ba ta da amfani kuma ba mai ƙaunar ta don mijinta ya yi shekaru yana zagin ta. Ta ce: “A wasu lokuta, ina ji kamar ba ni da amfani. Idan hakan ya faru abin da ke taimaka mini shi ne, nakan ga kaina a matsayin jaririya a hannun Jehobah kuma yana kāre ni.” (Zab. 28:9) Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Lauren, daga Afrika ta Kudu takan tuna wa kanta cewa, “Da yake Jehobah ya jawo ni wurinsa, ya taimaka mini in yi shekaru ina bauta masa, kuma yana amfani da ni wajen koyar da mutane, babu shakka yana ɗauka na da daraja da kuma muhimmanci.”—Hos. 11:4.
17. Mene ne zai taimaka maka ka kasance da tabbaci cewa Jehobah ya amince da kai? (Zabura 5:12) (Ka kuma duba hoton.)
17 Ka kasance da tabbaci cewa Jehobah ya amince da kai. (Karanta Zabura 5:12.) Dauda ya kwatanta amincewar Jehobah da garkuwa da ke kāre masu aminci. Sanin cewa Jehobah ya amince da mu zai kāre mu idan mun soma gani kamar ba mu da amfani. Ta yaya za ka san cewa Jehobah ya amince da kai? Kamar yadda muka gani, Jehobah ya tabbatar mana da hakan ta wurin Kalmarsa. Ƙari ga haka, yana amfani da dattawa, da abokanmu, da kuma wasu wajen tuna mana cewa muna da daraja sosai a gunsa. Me ya kamata ka yi idan mutane suna faɗan abubuwa masu kyau game da kai?
Sanin cewa Jehobah ya amince da mu zai taimaka mana mu daina ganin kamar mu ba kome ba ne (Ka duba sakin layi na 17)
18. Me ya sa zai dace mu amince da abubuwa masu kyau da ꞌyanꞌuwa suke faɗa game da mu?
18 Idan waɗanda suka san ka kuma suke ƙaunar ka suka yaba maka, kada ka ga kamar ba gaskiya ba ne. Mai yiwuwa Jehobah yana amfani da su wajen taimaka maka ka kasance da tabbaci cewa ya amince da kai. ꞌYarꞌuwa Michelle, da aka ambata ɗazu ta ce: “A sannu a hankali, ina koyan yadda zan amince da abubuwa masu kyau da ꞌyanꞌuwa suke faɗa game da ni. Hakan ba ya yi min sauƙi, amma na san cewa abin da Jehobah yake so mu yi ke nan.” Dattawa kuma sun taimaka wa ꞌyarꞌuwa Michelle ta ga cewa Jehobah yana ƙaunar ta. A yanzu, ita majagaba ce, kuma tana aiki a Bethel daga gidanta.
19. Me ya sa zai dace mu kasance da tabbaci cewa muna da daraja sosai a gun Jehobah?
19 Yesu ya tuna mana cewa muna da muhimmanci sosai a wurin Ubanmu na sama. (Luk. 12:24) Don haka, muna da tabbaci cewa Jehobah yana daraja mu. Kada mu taɓa mantawa da hakan! Kuma mu yi iya ƙoƙarinmu wajen taimaka wa mutane su san cewa suna da daraja sosai a gun Jehobah!
WAƘA TA 139 Rayuwa a Cikin Aljanna
a An canja wasu sunayen.
b Maryamu Magdalin tana cikin matan da suka bi Yesu zuwa wurare dabam-dabam. Matan sun yi amfani da kuɗinsu wajen kula da Yesu da manzaninsa.—Mat. 27:55, 56; Luk. 8:1-3.
c Alal misali, ka duba babi na 24 na littafin nan Ka Kusaci Jehobah.