Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
Littattafan Hausa (1987-2026)
Fita
Shiga Ciki
Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Maraba.
Wannan kayan bincike ne da ya kunshi wallafe-wallafen Shaidun Jehobah a harsuna dabam-dabam.
Idan kana so ka saukar da wallafe-wallafe, ka shiga jw.org/ha jw.org.
Sanarwa
Sabon harshe da aka ƙara: Betsileo
  • Yau

Asabar, 25 ga Oktoba

Saꞌan nan Shafan . . . ya karanta wa sarki.—2 Tar. 34:18.

Saꞌad da Sarki Josiya ya kai shekaru 26, ya soma gyara haikalin Jehobah. Saꞌad da ake aikin, an “sami Littafin Koyarwar Yahweh, wanda aka bayar ta bakin Musa.” Da aka karanta wa sarkin littafin, nan da nan ya bi abin da aka rubuta a ciki. (2 Tar. 34:​14, 19-21) Za ka so ka riƙa karanta Littafi Mai Tsarki a kullum? Idan kana ƙoƙarin yin hakan, shin kana jin daɗin sa? Shin kana mai da hankali ga ayoyin da za su taimaka maka? Saꞌad da Josiya yake wajen shekara 39, ya yi wani kuskuren da ya yi ajalinsa. Maimako ya nemi nufin Jehobah, ya dogara ga kansa. (2 Tar. 35:​20-25) Wannan ya koya mana cewa komen tsufanmu ko kuma yawan shekaru da muka yi muna nazarin Littafi Mai Tsarki, dole ne mu ci-gaba da neman nufin Jehobah. Hakan yana nufin cewa za mu riƙa roƙan sa ya yi mana ja-goranci, da yin nazarin Kalmarsa, da kuma bin shawarar Kiristoci da suka manyanta. Hakan zai taimaka mana mu guji yin kuskure mai tsanani, kuma ya taimaka mana mu yi farin ciki a rayuwa.—Yak. 1:25. w23.09 12 sakin layi na 15-16

Tattauna Kalmar Allah Kowace Rana—2025

Lahadi, 26 ga Oktoba

Allah yana ƙin mai girman kai, amma yana yin alheri ga mai sauƙin kai.—Yak. 4:6.

Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da mata da yawa da suka ƙaunaci Jehobah sosai kuma suka bauta masa. Matan sun nuna “natsuwa” da “aminci cikin kome.” (1 Tim. 3:11) Ƙari ga haka, ꞌyan mata Kiristoci za su iya bin misalin mata a ikilisiyarsu da suke ƙaunar Jehobah. ꞌYan mata, ku yi tunanin mata da kuka sani da ke da halaye masu kyau da za ku iya yin koyi da su. Ku lura da halayensu, saꞌan nan ku yi tunanin yadda ku ma za ku bi halinsu. Idan muna so mu zama Kiristoci da suka manyanta, muna bukatar sauƙin kai. Idan mace tana da sauƙin kai, za ta kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah da kuma mutane. Alal misali, macen da take ƙaunar Jehobah za ta bi abin da ke 1 Korintiyawa 11:3. A wurin, Jehobah ya nuna waɗanda yake so su yi ja-goranci a ikilisiya da kuma wanda zai yi hakan a iyali. Akwai hanyoyi da Jehobah yake so dukanmu mu bi abin da ya faɗa a ayar nan a ikilisiya da kuma a iyali. w23.12 18-19 sakin layi na 3-5

Tattauna Kalmar Allah Kowace Rana—2025

Litinin, 27 ga Oktoba

Maza su ƙaunaci matansu kamar yadda suke ƙaunar jikinsu.—Afis. 5:28.

Jehobah yana so maigida ya ƙaunaci matarsa, ya biya bukatunta, ya zama abokinta kuma ya taimaka mata ta bauta masa da kyau. Zama mai hankali, da daraja mata, da zama wanda za a iya yarda da shi, za su taimaka maka ka zama miji nagari. Bayan ka yi aure, za ku iya haifan yara. Wane darasi ne za ka iya koya daga wurin Jehobah game da zama uba nagari? (Afis. 6:4) Jehobah ya gaya wa ɗansa Yesu a gaban jamaꞌa cewa yana ƙaunar sa kuma ya amince da shi. (Mat. 3:17) Idan kana da yara, ka riƙa tabbatar musu da cewa kana ƙaunar su. Ka riƙa yaba musu don abubuwa masu kyau da suke yi. Ubanni da suke yin koyi da Jehobah suna taimaka wa yaransu su zama Kiristocin da suka manyanta. Za ka iya yin shirin zama uba nagari ta wajen kula da ꞌyan iyalinku da ꞌyanꞌuwa a ikilisiya. Ka riƙa gaya musu cewa kana ƙaunar su kuma suna da muhimmanci a gare ka.—Yoh. 15:9. w23.12 28-29 sakin layi na 17-18

Tattauna Kalmar Allah Kowace Rana—2025
Maraba.
Wannan kayan bincike ne da ya kunshi wallafe-wallafen Shaidun Jehobah a harsuna dabam-dabam.
Idan kana so ka saukar da wallafe-wallafe, ka shiga jw.org/ha jw.org.
  • Hausa
  • Raba
  • Wadda ka fi so
  • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
  • Ka'idojin Amfani
  • Tsarin Tsare Sirri
  • Saitin Tsare Sirri
  • JW.ORG
  • Shiga Ciki
Raba