Lahadi, 26 ga Oktoba
Allah yana ƙin mai girman kai, amma yana yin alheri ga mai sauƙin kai.—Yak. 4:6.
Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da mata da yawa da suka ƙaunaci Jehobah sosai kuma suka bauta masa. Matan sun nuna “natsuwa” da “aminci cikin kome.” (1 Tim. 3:11) Ƙari ga haka, ꞌyan mata Kiristoci za su iya bin misalin mata a ikilisiyarsu da suke ƙaunar Jehobah. ꞌYan mata, ku yi tunanin mata da kuka sani da ke da halaye masu kyau da za ku iya yin koyi da su. Ku lura da halayensu, saꞌan nan ku yi tunanin yadda ku ma za ku bi halinsu. Idan muna so mu zama Kiristoci da suka manyanta, muna bukatar sauƙin kai. Idan mace tana da sauƙin kai, za ta kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah da kuma mutane. Alal misali, macen da take ƙaunar Jehobah za ta bi abin da ke 1 Korintiyawa 11:3. A wurin, Jehobah ya nuna waɗanda yake so su yi ja-goranci a ikilisiya da kuma wanda zai yi hakan a iyali. Akwai hanyoyi da Jehobah yake so dukanmu mu bi abin da ya faɗa a ayar nan a ikilisiya da kuma a iyali. w23.12 18-19 sakin layi na 3-5
Litinin, 27 ga Oktoba
Maza su ƙaunaci matansu kamar yadda suke ƙaunar jikinsu.—Afis. 5:28.
Jehobah yana so maigida ya ƙaunaci matarsa, ya biya bukatunta, ya zama abokinta kuma ya taimaka mata ta bauta masa da kyau. Zama mai hankali, da daraja mata, da zama wanda za a iya yarda da shi, za su taimaka maka ka zama miji nagari. Bayan ka yi aure, za ku iya haifan yara. Wane darasi ne za ka iya koya daga wurin Jehobah game da zama uba nagari? (Afis. 6:4) Jehobah ya gaya wa ɗansa Yesu a gaban jamaꞌa cewa yana ƙaunar sa kuma ya amince da shi. (Mat. 3:17) Idan kana da yara, ka riƙa tabbatar musu da cewa kana ƙaunar su. Ka riƙa yaba musu don abubuwa masu kyau da suke yi. Ubanni da suke yin koyi da Jehobah suna taimaka wa yaransu su zama Kiristocin da suka manyanta. Za ka iya yin shirin zama uba nagari ta wajen kula da ꞌyan iyalinku da ꞌyanꞌuwa a ikilisiya. Ka riƙa gaya musu cewa kana ƙaunar su kuma suna da muhimmanci a gare ka.—Yoh. 15:9. w23.12 28-29 sakin layi na 17-18
Talata, 28 ga Oktoba
[Jehobah] ne tushe a zamaninmu.—Isha. 33:6.
Ko da yake mu bayin Jehobah ne, mu ma muna fuskantar matsaloli kuma muna rashin lafiya kamar yadda sauran mutane suke yi. Ƙari ga haka, muna iya fuskantar hamayya ko kuma tsanantawa daga mutanen da ba sa son ganin mu. Jehobah ba ya hana abubuwan nan faruwa da mu, amma ya yi alkawarin cewa zai taimaka mana. (Isha. 41:10) Da taimakon Jehobah, ko da mun shiga yanayi mai wuya sosai, za mu iya yin farin ciki, mu yanke shawarwari masu kyau kuma mu riƙe amincinmu. Jehobah ya yi alkawari cewa zai ba mu “salama.” (Filib. 4:6, 7) Wannan salamar tana nufin kwanciyar hankali da kuma natsuwa da muke samu don muna da dangantaka mai kyau da Allah. Wannan salamar ta “wuce dukan ganewar ɗan Adam,” wato tana taimaka mana a hanya mai ban mamaki. Ka taɓa yin adduꞌa ga Jehobah kuma ka ji hankalinka ya kwanta? Mai yiwuwa abin ya ba ka mamaki. ‘Salamar’ da Jehobah ya ba ka ne ya sa ka ji hakan. w24.01 20 sakin layi na 2; 21 sakin layi na 4