Talata, 28 ga Oktoba
[Jehobah] ne tushe a zamaninmu.—Isha. 33:6.
Ko da yake mu bayin Jehobah ne, mu ma muna fuskantar matsaloli kuma muna rashin lafiya kamar yadda sauran mutane suke yi. Ƙari ga haka, muna iya fuskantar hamayya ko kuma tsanantawa daga mutanen da ba sa son ganin mu. Jehobah ba ya hana abubuwan nan faruwa da mu, amma ya yi alkawarin cewa zai taimaka mana. (Isha. 41:10) Da taimakon Jehobah, ko da mun shiga yanayi mai wuya sosai, za mu iya yin farin ciki, mu yanke shawarwari masu kyau kuma mu riƙe amincinmu. Jehobah ya yi alkawari cewa zai ba mu “salama.” (Filib. 4:6, 7) Wannan salamar tana nufin kwanciyar hankali da kuma natsuwa da muke samu don muna da dangantaka mai kyau da Allah. Wannan salamar ta “wuce dukan ganewar ɗan Adam,” wato tana taimaka mana a hanya mai ban mamaki. Ka taɓa yin adduꞌa ga Jehobah kuma ka ji hankalinka ya kwanta? Mai yiwuwa abin ya ba ka mamaki. ‘Salamar’ da Jehobah ya ba ka ne ya sa ka ji hakan. w24.01 20 sakin layi na 2; 21 sakin layi na 4
Laraba, 29 ga Oktoba
Yabi Yahweh, ya raina! Dukan abin da ke a cikina, yabi Sunansa mai tsarki!—Zab. 103:1.
Waɗanda suke ƙaunar Jehobah suna so su yabi sunansa da dukan zuciyarsu. Sarki Dauda ya fahimci cewa yabon sunan Jehobah ɗaya yake da yabon Jehobah. Idan muka ji sunan Jehobah, mukan yi tunanin halayensa masu kyau da kuma abubuwan ban mamaki da ya yi. Dauda ya ɗauki sunan Ubansa na sama da tsarki kuma ya yabi sunan. Ya ce zai yi hakan da ‘dukan abin da ke a cikinsa,’ wato da dukan zuciyarsa. Lawiyawa ma sun ja-goranci mutane wajen yabon sunan Jehobah. Sun ce kalmomin bakinsu ba su isa su yabi Jehobah yadda ya dace ba. (Neh. 9:5) Babu shakka, yadda suka yabi Jehobah da dukan zuciyarsu kuma suka yi hakan da sauƙin kai, ya sa Jehobah farin ciki. w24.02 9 sakin layi na 6
Alhamis, 30 ga Oktoba
Babban abin shi ne duk inda muka kai, mu ci gaba daga nan.—Filib. 3:16.
Jehobah ba zai yi baƙin ciki domin ka kasa cim ma maƙasudin da ya fi ƙarfinka ba. (2 Kor. 8:12) Ka koyi darasi daga abubuwan da suka sa ka samu koma baya. Ka riƙa tunanin abubuwan da ka cim ma. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Allah ba marar adalci ba ne. Ba zai ƙyale ayyukanku da kuka yi ba.” (Ibran. 6:10) Don haka, bai kamata kai ma ka manta ba. Ka yi tunani a kan abubuwan da ka riga ka cim ma kamar ƙarfafa dangantakarka da Jehobah, da yin waꞌazi da kuma yin baftisma. Kamar yadda ka cim ma maƙasudanka a dā, haka ma za ka iya ci-gaba da yin ƙoƙari har sai ka cim ma waɗanda kake da su a yanzu. Za ka iya cim ma maƙasudinka da taimakon Jehobah. Yayin da kake ƙoƙari don ka cim ma maƙasudinka, ka riƙa tuna da yadda Jehobah yake taimaka maka da kuma albarka da yake maka, domin yin hakan zai sa ka farin ciki. (2 Kor. 4:7) Idan ba ka gaji ba, za ka samu ƙarin albarka.—Gal. 6:9. w23.05 31 sakin layi na 16-18