Laraba, 29 ga Oktoba
Yabi Yahweh, ya raina! Dukan abin da ke a cikina, yabi Sunansa mai tsarki!—Zab. 103:1.
Waɗanda suke ƙaunar Jehobah suna so su yabi sunansa da dukan zuciyarsu. Sarki Dauda ya fahimci cewa yabon sunan Jehobah ɗaya yake da yabon Jehobah. Idan muka ji sunan Jehobah, mukan yi tunanin halayensa masu kyau da kuma abubuwan ban mamaki da ya yi. Dauda ya ɗauki sunan Ubansa na sama da tsarki kuma ya yabi sunan. Ya ce zai yi hakan da ‘dukan abin da ke a cikinsa,’ wato da dukan zuciyarsa. Lawiyawa ma sun ja-goranci mutane wajen yabon sunan Jehobah. Sun ce kalmomin bakinsu ba su isa su yabi Jehobah yadda ya dace ba. (Neh. 9:5) Babu shakka, yadda suka yabi Jehobah da dukan zuciyarsu kuma suka yi hakan da sauƙin kai, ya sa Jehobah farin ciki. w24.02 9 sakin layi na 6
Alhamis, 30 ga Oktoba
Babban abin shi ne duk inda muka kai, mu ci gaba daga nan.—Filib. 3:16.
Jehobah ba zai yi baƙin ciki domin ka kasa cim ma maƙasudin da ya fi ƙarfinka ba. (2 Kor. 8:12) Ka koyi darasi daga abubuwan da suka sa ka samu koma baya. Ka riƙa tunanin abubuwan da ka cim ma. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Allah ba marar adalci ba ne. Ba zai ƙyale ayyukanku da kuka yi ba.” (Ibran. 6:10) Don haka, bai kamata kai ma ka manta ba. Ka yi tunani a kan abubuwan da ka riga ka cim ma kamar ƙarfafa dangantakarka da Jehobah, da yin waꞌazi da kuma yin baftisma. Kamar yadda ka cim ma maƙasudanka a dā, haka ma za ka iya ci-gaba da yin ƙoƙari har sai ka cim ma waɗanda kake da su a yanzu. Za ka iya cim ma maƙasudinka da taimakon Jehobah. Yayin da kake ƙoƙari don ka cim ma maƙasudinka, ka riƙa tuna da yadda Jehobah yake taimaka maka da kuma albarka da yake maka, domin yin hakan zai sa ka farin ciki. (2 Kor. 4:7) Idan ba ka gaji ba, za ka samu ƙarin albarka.—Gal. 6:9. w23.05 31 sakin layi na 16-18
Jumma’a, 31 ga Oktoba
Shi Uban yana ƙaunarku da kansa, saboda kun ƙaunace ni, kun kuma ba da gaskiya cewa daga wurin Allah na fito.—Yoh. 16:27.
Jehobah yana neman hanyar da zai nuna wa mutanensa cewa ya amince da su. A cikin Littafi Mai Tsarki, sau biyu Jehobah ya gaya wa Yesu cewa shi Ɗansa ne da yake ƙauna kuma Ya amince da shi. (Mat. 3:17; 17:5) Za ka so ka ji cewa Jehobah yana ƙaunar ka kuma ya amince da kai? Jehobah ba ya magana da mu daga sama, amma yana magana da mu ta wurin Kalmarsa. Idan muka karanta abubuwa masu ban ƙarfafa da Yesu ya gaya wa mabiyansa, kamar Jehobah ne yake magana da mu. Yesu yana da halaye daidai irin na Ubansa. Don haka, a duk lokacin da muka karanta yadda Yesu ya gaya wa almajiransa cewa ya amince da su, mu ɗauka cewa Jehobah ne yake magana da mu. (Yoh. 15:9, 15) Idan muna fuskantar matsaloli, hakan ba ya nufin cewa Jehobah ya daina amincewa da mu. A maimakon haka, matsaloli suna ba mu damar nuna wa Jehobah yadda muke ƙaunar sa da kuma yadda muka dogara gare shi.—Yak. 1:12. w24.03 28 sakin layi na 10-11