Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
Littattafan Hausa (1987-2026)
Fita
Shiga Ciki
Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Maraba.
Wannan kayan bincike ne da ya kunshi wallafe-wallafen Shaidun Jehobah a harsuna dabam-dabam.
Idan kana so ka saukar da wallafe-wallafe, ka shiga jw.org/ha jw.org.
  • Yau

Alhamis, 30 ga Oktoba

Babban abin shi ne duk inda muka kai, mu ci gaba daga nan.—Filib. 3:16.

Jehobah ba zai yi baƙin ciki domin ka kasa cim ma maƙasudin da ya fi ƙarfinka ba. (2 Kor. 8:12) Ka koyi darasi daga abubuwan da suka sa ka samu koma baya. Ka riƙa tunanin abubuwan da ka cim ma. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Allah ba marar adalci ba ne. Ba zai ƙyale ayyukanku da kuka yi ba.” (Ibran. 6:10) Don haka, bai kamata kai ma ka manta ba. Ka yi tunani a kan abubuwan da ka riga ka cim ma kamar ƙarfafa dangantakarka da Jehobah, da yin waꞌazi da kuma yin baftisma. Kamar yadda ka cim ma maƙasudanka a dā, haka ma za ka iya ci-gaba da yin ƙoƙari har sai ka cim ma waɗanda kake da su a yanzu. Za ka iya cim ma maƙasudinka da taimakon Jehobah. Yayin da kake ƙoƙari don ka cim ma maƙasudinka, ka riƙa tuna da yadda Jehobah yake taimaka maka da kuma albarka da yake maka, domin yin hakan zai sa ka farin ciki. (2 Kor. 4:7) Idan ba ka gaji ba, za ka samu ƙarin albarka.—Gal. 6:9. w23.05 31 sakin layi na 16-18

Tattauna Kalmar Allah Kowace Rana—2025

Jumma’a, 31 ga Oktoba

Shi Uban yana ƙaunarku da kansa, saboda kun ƙaunace ni, kun kuma ba da gaskiya cewa daga wurin Allah na fito.—Yoh. 16:27.

Jehobah yana neman hanyar da zai nuna wa mutanensa cewa ya amince da su. A cikin Littafi Mai Tsarki, sau biyu Jehobah ya gaya wa Yesu cewa shi Ɗansa ne da yake ƙauna kuma Ya amince da shi. (Mat. 3:17; 17:5) Za ka so ka ji cewa Jehobah yana ƙaunar ka kuma ya amince da kai? Jehobah ba ya magana da mu daga sama, amma yana magana da mu ta wurin Kalmarsa. Idan muka karanta abubuwa masu ban ƙarfafa da Yesu ya gaya wa mabiyansa, kamar Jehobah ne yake magana da mu. Yesu yana da halaye daidai irin na Ubansa. Don haka, a duk lokacin da muka karanta yadda Yesu ya gaya wa almajiransa cewa ya amince da su, mu ɗauka cewa Jehobah ne yake magana da mu. (Yoh. 15:​9, 15) Idan muna fuskantar matsaloli, hakan ba ya nufin cewa Jehobah ya daina amincewa da mu. A maimakon haka, matsaloli suna ba mu damar nuna wa Jehobah yadda muke ƙaunar sa da kuma yadda muka dogara gare shi.—Yak. 1:12. w24.03 28 sakin layi na 10-11

Tattauna Kalmar Allah Kowace Rana—2025

Asabar, 1 ga Nuwamba

Daga bakin yara da jarirai ka sa yabonka ya fita.—Mat. 21:16.

Idan kuna da yara, ku taimaka musu su shirya yin kalami da ya yi daidai da shekarunsu. Mai yiwuwa ba za su samu damar yin kalami sosai ba idan ana tattauna manyan batutuwa kamar matsaloli da ake samu a aure, ko batun ɗabiꞌa. Duk da haka, ba za a rasa sakin layi ɗaya ko biyu da yaro zai iya sa baƙi ba. Ƙari ga haka, ku taimaka wa yaranku su fahimci abin da ya sa wani lokaci ba za a kira su idan suka ɗaga hannu ba. Idan kuka yi musu wannan bayanin, ransu ba zai ɓace ba idan suka ɗaga hannu kuma aka kira wani. (1 Tim. 6:18) Dukanmu za mu iya yin shiri don mu yi kalaman da za su sa a yabi Jehobah kuma su ƙarfafa ꞌyanꞌuwanmu. (K. Mag. 25:11) Ko da yake za mu iya ba da labarin abin da ya taɓa faruwa da mu, zai dace mu guji yin magana da yawa game da kanmu. (K. Mag. 27:2; 2 Kor. 10:18) Maimakon haka, zai fi dacewa mu sa ꞌyanꞌuwa su mai da hankali ga Jehobah, da Kalmarsa da kuma bayinsa gabaki ɗaya.—R. Yar. 4:11. w23.04 24-25 sakin layi na 17-18

Tattauna Kalmar Allah Kowace Rana—2025
Maraba.
Wannan kayan bincike ne da ya kunshi wallafe-wallafen Shaidun Jehobah a harsuna dabam-dabam.
Idan kana so ka saukar da wallafe-wallafe, ka shiga jw.org/ha jw.org.
  • Hausa
  • Raba
  • Wadda ka fi so
  • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
  • Ka'idojin Amfani
  • Tsarin Tsare Sirri
  • Saitin Tsare Sirri
  • JW.ORG
  • Shiga Ciki
Raba