Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
Littattafan Hausa (1987-2026)
Fita
Shiga Ciki
Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Maraba.
Wannan kayan bincike ne da ya kunshi wallafe-wallafen Shaidun Jehobah a harsuna dabam-dabam.
Idan kana so ka saukar da wallafe-wallafe, ka shiga jw.org/ha jw.org.
  • Yau

Asabar, 1 ga Nuwamba

Daga bakin yara da jarirai ka sa yabonka ya fita.—Mat. 21:16.

Idan kuna da yara, ku taimaka musu su shirya yin kalami da ya yi daidai da shekarunsu. Mai yiwuwa ba za su samu damar yin kalami sosai ba idan ana tattauna manyan batutuwa kamar matsaloli da ake samu a aure, ko batun ɗabiꞌa. Duk da haka, ba za a rasa sakin layi ɗaya ko biyu da yaro zai iya sa baƙi ba. Ƙari ga haka, ku taimaka wa yaranku su fahimci abin da ya sa wani lokaci ba za a kira su idan suka ɗaga hannu ba. Idan kuka yi musu wannan bayanin, ransu ba zai ɓace ba idan suka ɗaga hannu kuma aka kira wani. (1 Tim. 6:18) Dukanmu za mu iya yin shiri don mu yi kalaman da za su sa a yabi Jehobah kuma su ƙarfafa ꞌyanꞌuwanmu. (K. Mag. 25:11) Ko da yake za mu iya ba da labarin abin da ya taɓa faruwa da mu, zai dace mu guji yin magana da yawa game da kanmu. (K. Mag. 27:2; 2 Kor. 10:18) Maimakon haka, zai fi dacewa mu sa ꞌyanꞌuwa su mai da hankali ga Jehobah, da Kalmarsa da kuma bayinsa gabaki ɗaya.—R. Yar. 4:11. w23.04 24-25 sakin layi na 17-18

Tattauna Kalmar Allah Kowace Rana—2025

Lahadi, 2 ga Nuwamba

Kada mu yi barci yadda waɗansu suke yi, sai dai mu yi zaman tsaro da shiri.—1 Tas. 5:6.

Ƙauna ma abu ne mai muhimmanci da zai taimaka mana mu zauna da shiri. (Mat. 22:​37-39) Ƙaunar da muke yi wa Allah ce take taimaka mana mu ci gaba da yin waꞌazi ko da me hakan zai jawo mana. (2 Tim. 1:​7, 8) Da yake muna ƙaunar kowa har da waɗanda ba Shaidu ba, muna yin waꞌazi har ta waya da rubuta wasiƙu. Muna ci-gaba da sa rai cewa mutanen yankinmu za su canja wata rana kuma su yi abin da ya dace. (Ezek. 18:​27, 28) Ƙari ga haka, muna ƙaunar ꞌyanꞌuwanmu maza da mata. Muna nuna irin ƙaunar nan ta wajen “ƙarfafa juna” da “gina juna.” (1 Tas. 5:11) Kamar yadda sojoji suke taimaka wa juna a yaƙi, haka mu ma muna taimaka wa juna. Ba za mu taɓa ɓata wa ꞌyanꞌuwanmu rai da gangan ba. In ma sun yi mana kuskure, ba za mu rama ba. (1 Tas. 5:​13, 15) Za mu kuma nuna cewa muna ƙaunar ꞌyanꞌuwanmu ta wajen daraja waɗanda suke ja-goranci a ikilisiya.—1 Tas. 5:12. w23.06 10 sakin layi na 6; 11 sakin layi na 10-11

Tattauna Kalmar Allah Kowace Rana—2025

Litinin, 3 ga Nuwamba

[Jehobah] ya taɓa faɗin wani abu, ya kāsa yi ne?—L. Ƙid. 23:19.

Hanya ɗaya da za mu iya ƙarfafa bangaskiyarmu ita ce ta yin bimbini, wato yin tunani mai zurfi a kan fansar Yesu. Fansar Yesu tana tabbatar mana cewa alkawuran Allah za su faru da gaske. Idan muka yi tunani sosai a kan dalilin da ya sa aka ba da fansar da kuma abin da hakan ya kunsa, za mu ƙara kasance da tabbaci cewa Allah zai sa mu rayu har abada a sabuwar duniya kamar yadda ya faɗa. Me ya sa muka ce hakan? Mene ne fansar Yesu ta ƙunsa? Yesu shi ne farkon halitta na Jehobah kuma shi ne ya fi kusa da Allah. Duk da haka, Jehobah ya turo shi duniya a matsayin kamiltaccen mutum. Da Yesu yake duniya, ya sha wahala sosai kuma ya jimre. Bayan haka, ya yi mutuwar wulaƙanci. Wannan ba ƙaramin abu ba ne Jehobah ya yi. Jehobah ba zai taɓa barin Ɗansa ya sha wahala kuma ya mutu don kawai mu ji daɗin rayuwa na ƙanƙanin lokaci ba. (Yoh. 3:16; 1 Bit. 1:​18, 19) Da yake Jehobah ya ba da fansa mafi daraja, zai tabbata cewa mun ji daɗin rayuwa har abada a sabuwar duniya. w23.04 27 sakin layi na 8-9

Tattauna Kalmar Allah Kowace Rana—2025
Maraba.
Wannan kayan bincike ne da ya kunshi wallafe-wallafen Shaidun Jehobah a harsuna dabam-dabam.
Idan kana so ka saukar da wallafe-wallafe, ka shiga jw.org/ha jw.org.
  • Hausa
  • Raba
  • Wadda ka fi so
  • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
  • Ka'idojin Amfani
  • Tsarin Tsare Sirri
  • Saitin Tsare Sirri
  • JW.ORG
  • Shiga Ciki
Raba