Lahadi, 2 ga Nuwamba
Kada mu yi barci yadda waɗansu suke yi, sai dai mu yi zaman tsaro da shiri.—1 Tas. 5:6.
Ƙauna ma abu ne mai muhimmanci da zai taimaka mana mu zauna da shiri. (Mat. 22:37-39) Ƙaunar da muke yi wa Allah ce take taimaka mana mu ci gaba da yin waꞌazi ko da me hakan zai jawo mana. (2 Tim. 1:7, 8) Da yake muna ƙaunar kowa har da waɗanda ba Shaidu ba, muna yin waꞌazi har ta waya da rubuta wasiƙu. Muna ci-gaba da sa rai cewa mutanen yankinmu za su canja wata rana kuma su yi abin da ya dace. (Ezek. 18:27, 28) Ƙari ga haka, muna ƙaunar ꞌyanꞌuwanmu maza da mata. Muna nuna irin ƙaunar nan ta wajen “ƙarfafa juna” da “gina juna.” (1 Tas. 5:11) Kamar yadda sojoji suke taimaka wa juna a yaƙi, haka mu ma muna taimaka wa juna. Ba za mu taɓa ɓata wa ꞌyanꞌuwanmu rai da gangan ba. In ma sun yi mana kuskure, ba za mu rama ba. (1 Tas. 5:13, 15) Za mu kuma nuna cewa muna ƙaunar ꞌyanꞌuwanmu ta wajen daraja waɗanda suke ja-goranci a ikilisiya.—1 Tas. 5:12. w23.06 10 sakin layi na 6; 11 sakin layi na 10-11
Litinin, 3 ga Nuwamba
[Jehobah] ya taɓa faɗin wani abu, ya kāsa yi ne?—L. Ƙid. 23:19.
Hanya ɗaya da za mu iya ƙarfafa bangaskiyarmu ita ce ta yin bimbini, wato yin tunani mai zurfi a kan fansar Yesu. Fansar Yesu tana tabbatar mana cewa alkawuran Allah za su faru da gaske. Idan muka yi tunani sosai a kan dalilin da ya sa aka ba da fansar da kuma abin da hakan ya kunsa, za mu ƙara kasance da tabbaci cewa Allah zai sa mu rayu har abada a sabuwar duniya kamar yadda ya faɗa. Me ya sa muka ce hakan? Mene ne fansar Yesu ta ƙunsa? Yesu shi ne farkon halitta na Jehobah kuma shi ne ya fi kusa da Allah. Duk da haka, Jehobah ya turo shi duniya a matsayin kamiltaccen mutum. Da Yesu yake duniya, ya sha wahala sosai kuma ya jimre. Bayan haka, ya yi mutuwar wulaƙanci. Wannan ba ƙaramin abu ba ne Jehobah ya yi. Jehobah ba zai taɓa barin Ɗansa ya sha wahala kuma ya mutu don kawai mu ji daɗin rayuwa na ƙanƙanin lokaci ba. (Yoh. 3:16; 1 Bit. 1:18, 19) Da yake Jehobah ya ba da fansa mafi daraja, zai tabbata cewa mun ji daɗin rayuwa har abada a sabuwar duniya. w23.04 27 sakin layi na 8-9
Talata, 4 ga Nuwamba
Ke mutuwa, ina ne balaꞌinki?—Hos. 13:14.
Shin Jehobah yana da niyyar ta da matattu? Babu shakka yana da niyya. Ya sa marubutan Littafi Mai Tsarki da yawa su rubuta alkawarin da ya yi game da tashin matattu a nan gaba. (Isha. 26:19; R. Yar. 20:11-13) Kuma a duk lokacin da Jehobah ya yi alkawari, yana cikawa. (Yosh. 23:14) Jehobah yana marmarin ta da waɗanda suka mutu. Ka yi laꞌakari da abin da Ayuba ya faɗa. Yana da tabbaci cewa ko da ya mutu, Jehobah zai sake ta da shi. (Ayu. 14:14, 15, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe) Jehobah yana marmarin ta da dukan bayinsa da suka mutu. Yana marmarin ta da su cikin ƙoshin lafiya da kuma farin ciki. Me zai faru da waɗanda suka mutu kuma ba su samu zarafin koya game da Jehobah ba? Su ma Ubanmu mai ƙauna yana so ya ta da su. (A. M. 24:15) Yana so su sami zarafin zama abokansa kuma su yi rayuwa har abada a duniya.—Yoh. 3:16. w23.04 9 sakin layi na 5-6