Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wt babi na 14 pp. 128-135
  • Ta Yaya Jehovah Yake Ja-Gorar Ƙungiyarsa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ta Yaya Jehovah Yake Ja-Gorar Ƙungiyarsa?
  • Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Gano Sashen da Ake Gani
  • Shiri na Tsarin Allah
  • Ka Yi Biyayya Ga Kristi Da Kuma Amintaccen Bawansa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Bari Ikilisiya Ta Ingantu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Su Wa Suke Yi wa Mutanen Allah Ja-gora a Yau?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • Wakili Mai Aminci Da Hukumarsa Ta Mulki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
Dubi Ƙari
Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
wt babi na 14 pp. 128-135

Babi Na Goma Sha Huɗu

Ta Yaya Jehovah Yake Ja-Gorar Ƙungiyarsa?

1. Wane bayani ne game da ƙungiyar Jehovah Littafi Mai Tsarki ya yi, kuma me ya sa take da muhimmanci a gare mu?

ALLAH yana da ƙungiya ne? Huraren Nassosi sun ce mana yana da ita. A cikin Kalmarsa, ya ba da tsinkaya ta sashen ƙungiyarsa ta samaniya ta ban mamaki. (Ezekiel 1:1, 4-14; Daniel 7:9, 10, 13, 14) Ko da yake ba ma iya ganin wannan sashen, yana shafar masu bauta ta gaskiya ƙwarai a yau. (2 Sarakuna 6:15-17) Ƙungiyar Jehovah ma tana da sashe da ake gani, a duniya. Littafi Mai Tsarki ya taimake mu mu fahimci yadda take da kuma yadda Jehovah ke ja-gorarta.

Gano Sashen da Ake Gani

2. Wace sabuwar ikilisiya ce Allah ya fito da ita?

2 Al’ummar Isra’ila ce ikilisiyar Allah ta shekara 1,545. (Ayukan Manzanni 7:38) Amma Isra’ila ta kasa kiyaye dokokin Allah kuma ta ƙi Ɗansa. Domin haka, Jehovah ya ƙi wannan ikilisiyar kuma ya yashe ta. Yesu ya gaya wa Yahudawa: “Ga shi, an bar muku gidanku kango.” (Matta 23:38) Sai Allah ya kafa sabuwar ikilisiya, da ya yi sabon alkawari da ita. Ikilisiyar tana ɗauke ne da mutane 144,000 da Allah ya zaɓa su haɗu da Ɗansa cikin sama.—Ru’ya ta Yohanna 14:1-4.

3. Menene ya faru a Fentakos na shekara ta 33 A.Z. da ya ba da tabbaci cewa yanzu Allah yana amfani da sabuwar ikilisiya?

3 Na farko cikin sabuwar ikilisiyar an shafe su ne da ruhu mai tsarki na Jehovah a Fentakos na shekara ta 33 A.Z. Mu karanta game da wannan aukuwa ta ban mamaki: “Sa’anda ranar Fentakos ta yi, dukansu suna tare wuri ɗaya. Ba labari, sai wani motsi kamar na hucin iska mai-ƙarfi ya fito sama, duk ya gama gida wurinda su ke zaune. Harsuna kuma mararraba da juna, kamar na wuta, suka bayyanu garesu; ya zauna bisa kowane ɗaya a cikinsu. Aka cika dukansu da Ruhu Mai-tsarki.” (Ayukan Manzanni 2:1-4) Da haka ne ruhun Allah ya ba da tabbaci cewa yanzu wannan ne rukunin mutane da Allah zai yi amfani da su ya cika nufinsa ta wajen jagabanci na Yesu Kristi a sama.

4. Su wa a yau suka zama ƙungiyar Jehovah da ake gani?

4 A yau raguwar 144,000 ce kawai take duniya. Amma a cikar annabcin Littafi Mai Tsarki, “taro mai-girma” na “waɗansu tumaki,” an kawo miliyoyinsu cikin tarayya da raguwar shafaffu. Yesu, Nagarin Makiyayi, ya haɗa waɗannan tumaki da raguwar don su zama garke ɗaya a ƙarƙashinsa ya zama Makiyayinsu ɗaya. (Ru’ya ta Yohanna 7:9; Yohanna 10:11, 16) Dukan waɗannan sun zama ikilisiya ɗaya haɗaɗɗiya, ƙungiyar Jehovah da ake gani.

Shiri na Tsarin Allah

5. Wanene yake ja-gorar ƙungiyar Allah, kuma ta yaya?

5 Furcin nan na Nassi “ikilisiyar Allah mai-rai” ya bayyana sarai wanda yake ja-gorarta. Ƙungiyar ta tsarin Allah ce, ko kuma ta sarauta ta Allah. Jehovah ya yi tanadin ja-gora wa mutanensa ta wurin Yesu, Wanda ya naɗa ya zama Shugaba da ba a gani na ikilisiyar, da kuma ta wurin Kalmarsa hurarriya, Littafi Mai Tsarki.—1 Timothawus 3:14, 15; Afisawa 1:22, 23; 2 Timothawus 3:16, 17.

6. (a) Yaya aka iya ganin ja-gora na ikilisiyar a ƙarni na farko daga sama? (b) Menene ya nuna cewa Yesu ne har ila Shugaban ikilisiya?

6 An ga irin ja-gorar nan a Fentakos. (Ayukan Manzanni 2:14-18, 32, 33) Ya bayyana yayin da mala’ikan Jehovah ya yi ja-gorar shelar bishara zuwa cikin Afirka, yayin da muryar Yesu ta umurci tuban Shawulu na Tarsus, da kuma lokacin da Bitrus ya fara aikin wa’azi tsakanin mutanen Al’ummai. (Ayukan Manzanni 8:26, 27; 9:3-7; 10:9-16, 19-22) Amma, da shigewar lokaci, ba a ƙara jin murya daga sama ba kuma, ba a ƙara ganin mala’iku ba kuma, ba a ƙara ba da kyauta ta mu’ujizai ba kuma. Duk da haka, Yesu ya yi alkawari: “Ga shi kuwa ina tare da ku kullayaumi har matuƙar zamani.” (Matta 28:20; 1 Korinthiyawa 13:8) A yau, Shaidun Jehovah suna la’akari da ja-gorar Yesu. Idan babu haka, yin shelar saƙon Mulkin da hamayya mai tsanani ba zai yiwu ba.

7. (a) Su wa suka zama “bawan nan mai-aminci, mai-hikima,” kuma me ya sa? (b) Wane aiki aka ba wa “bawan”?

7 Jim kaɗan kafin mutuwarsa, Yesu ya gaya wa almajiransa game da “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” da Ubangijinsu ya ba su hakki na musamman. “Bawan” nan yana nan lokacin da Ubangiji ya hau sama kuma zai kasance yana aiki tuƙuru a lokacin dawowar Kristi da ba a gani cikin ikon Sarauta. Irin kwatancin nan ba zai dace da mutum ɗaya ba, amma ya dace ne da ikilisiyar da aka shafe ta Kristi. Domin ya saye ta da jininsa, Yesu ya kira ta ‘bawansa.’ Ya ba waɗanda ke cikinta aiki su almajirantar kuma su ci gaba da ciyar da su, suna ba su “abincinsu [na ruhaniya] a lotonsa.”—Matta 24:45-47; 28:19; Ishaya 43:10; Luka 12:42; 1 Bitrus 4:10.

8. (a) Wane hakki ajin bawan ke da shi a yanzu? (b) Me ya sa yadda muka yi na’am da koyarwa ta wurin magudanar Allah ke da muhimmanci?

8 Da yake ajin bawan suna aikin Ubangijin da aminci a dawowarsa da ba a gani ba a shekara ta 1914, da akwai tabbaci cewa an ba ta ƙarin hakki a shekara ta 1919. Tun daga lokacin duk shekarun da suka shige sun kasance lokaci ne na yin wa’azin Mulkin a dukan duniya, kuma ana tattara taro mai girma na masu bauta wa Jehovah don su tsira daga ƙunci mai girma. (Matta 24:14, 21, 22; Ru’ya ta Yohanna 7:9, 10) Waɗannan ma suna bukatar abinci na ruhaniya, kuma aji na bawan ne ke ba su. Don a faranta wa Jehovah rai, muna bukatar mu yi na’am da koyarwa da yake tanadinsa ta wurin wannan magudanar kuma mu bi ta.

9, 10. (a) A ƙarni na farko, wane shiri ne aka yi don amsa tambayoyi game da koyarwa da kuma yin ja-gora wajen wa’azin bishara? (b) Wane shiri ne akwai a yau na tsara ayyukan mutanen Jehovah?

9 A wasu lokatai, tambayoyi sukan taso game da koyarwa ko kuma tsari. Me za a yi? Ayukan Manzanni sura 15 ta gaya mana yadda aka warware matsala game da mutane na Al’ummai da suke tuba. An kai al’amarin wa manzanni da dattawa a Urushalima, da suka yi aiki na hukumar mulki. Mutanen ba kamiltattu ba ne, amma Allah ya yi amfani da su. Sun bincika nassosi game da zancen kuma suka ga tabbacin aikin ruhu mai tsarki na Allah a buɗe fage na Al’ummai. Sai suka tsai da shawara. Allah ya albarkaci wannan shirin. (Ayukan Manzanni 15:1-29; 16:4, 5) Daga cikin rukunin nan, aka aika da wasu su yaɗa wa’azin Mulkin.

10 A zamaninmu Hukumar Mulki na ƙungiyar Jehovah da ake gani da ’yan’uwa shafaffu da ruhu ne daga ƙasashe dabam dabam suke ciki, kuma suna hedkwatar Shaidun Jehovah na dukan duniya. A ƙarƙashin shugabancin Yesu Kristi, Hukumar Mulki suna yaɗa tsarkakkiyar bauta a kowacce ƙasa, suna shirya aikin wa’azi na Shaidun Jehovah cikin dubban ikilisiyoyi. Waɗanda suke cikin Hukumar Mulkin nan suna na’am da ra’ayin manzo Bulus, da ya rubuta wa ’yan’uwa Kirista: “Ba sarauta mu ke yi bisa bangaskiyarku ba, amma mataimaka ne na farinzuciyarku: gama da bangaskiya ku ke tsayawa.”—2 Korinthiyawa 1:24.

11. (a) Ta yaya ake naɗa dattawa da bayi masu hidima? (b) Me ya sa ya kamata mu ba da haɗin kai ga waɗanda aka naɗa?

11 Shaidun Jehovah a duk duniya suna zuba ido wajen Hukumar Mulki su zaɓi ’yan’uwa da suka ƙware da su ma an ba su izinin su naɗa dattawa da bayi masu hidima su lura da ikilisiyoyi. Abin da ake bukata wajen waɗanda aka naɗa an rubuta cikin Littafi Mai Tsarki da sanin cewa waɗannan mutanen ba kamilai ba ne saboda haka sukan yi kuskure. Dattawa da suke zaɓan da kuma waɗanda suke naɗin suna ɗauke da hakki mai nauyi a gaban Allah. (1 Timothawus 3:1-10, 12, 13; Titus 1:5-9) Shi ya sa, suke yin addu’a domin ruhun Allah kuma suna biɗan ja-gora daga Kalmarsa da ya hure. (Ayukan Manzanni 6:2-4, 6; 14:23) Bari mu nuna godiyarmu ga waɗannan “kyauta ga mutane,” da suke taimakonmu duka zuwa “ɗayantuwar imani.”—Afisawa 4:8, 11-16.

12. Yaya Jehovah yake amfani da mata cikin tsarinsa?

12 Nassosi sun ce maza ne za su yi ja-gora cikin ikilisiya. Wannan ba cewa ana raina mata ba ne, domin wasu cikinsu magāda ne na Mulkin samaniya, kuma suna yin aikin wa’azi mai yawa. (Zabura 68:11) Kuma, ta wurin lura da hakkinsu na iyalin, mata suna kawo suna mai kyau ga ikilisiyar. (Titus 2:3-5) Amma koyarwa cikin ikilisiyar, maza da aka naɗa ne suke yi.—1 Timothawus 2:12, 13.

13. (a) Wane ra’ayi Littafi Mai Tsarki ya aririci dattawa su kasance da shi game da matsayinsu? (b) A wace gata ce dukanmu za mu iya sa hannu?

13 A duniya, mutumin da yake da matsayi ana ɗaukansa da muhimmanci, amma cikin ƙungiyar Allah ƙa’idar ita ce: “Wanda shi ke ƙanƙani a cikinku duka, shi ne babba.” (Luka 9:46-48; 22:24-26) Nassosi sun yi ma dattawa gargaɗi su mai da hankali kada su danka wa waɗanda gadōn Allah ne, sai dai su zama misali ga tumakin. (1 Bitrus 5:2, 3) Ba waɗanda aka zaɓa kalilan kawai ba, amma dukan Shaidun Jehovah, mata da maza suna da gatar wakilta Mai Ikon Mallakar Dukan Halitta, suna magana da tawali’u cikin sunansa kuma suna gaya wa mutane a ko’ina game da Mulkinsa.

14. Yi amfani da nassosi da aka nuna, ka tattauna tambayoyi da aka jera a ƙarshen izifin.

14 Yana da kyau mu tambayi kanmu: ‘Shin na fahimci kuma ina godiya da gaske ga yadda Jehovah yake ja-gorar ƙungiyarsa da ake gani? Halayena, maganata, da kuma ayyukata suna nuna haka?’ Yin bimbini a kan waɗannan darussa na gaba zai iya taimaka wa kowannenmu ya yi irin wannan binciken.

Idan da gaske ina biyayya ga Kristi shi Shugaban ikilisiyar, to, kamar yadda aka nuna cikin nassosi na gaba, menene zan riƙa yi? (Matta 24:14; 28:19, 20; Yohanna 13:34, 35)

Yayin da na yi na’am da tanadi na ruhaniya da ke zuwa daga ajin bawa da Hukumarta ta Mulki, wa nake ba wa daraja? (Luka 10:16)

Yaya ya kamata kowa a cikin ikilisiya, musamman dattawa su bi da wasu? (Romawa 12:10)

15. (a) Ta wurin halinmu wajen ƙungiyar Jehovah da ake gani, me muke nunawa? (b) Waɗanne zarafi muke da su na nuna cewa Iblis maƙaryaci ne kuma mu faranta wa Jehovah rai?

15 A yau Jehovah yana yi mana ja-gora ta wurin ƙungiyarsa da ake gani ƙarƙashin Kristi. Halinmu wajen wannan tsarin yana nuna yadda muke ji game da al’amarin nan na ikon mallaka. (Ibraniyawa 13:17) Shaiɗan ya nace cewa abin da muka fi so shi ne kanmu. Amma idan muka yi hidima a kowacce hanya kuma muka guje wa abubuwa da ke jawo hankali ga kanmu, za mu tabbatar da cewa Iblis maƙaryaci ne. Idan muna ƙauna kuma muna daraja waɗanda suke ja-gora a tsakaninmu amma mun ƙi ‘mu so mutane don namu riba,’ za mu faranta wa Jehovah rai. (Yahuda 16; Ibraniyawa 13:7) Ta kasance da aminci ga ƙungiyar Jehovah, muna nuna cewa Jehovah ne Allah kuma cewa muna da haɗin kai a bauta masa.—1 Korinthiyawa 15:58.

Maimaita Abin da Aka Tattauna

• Mecece ƙungiyar Jehovah da ake gani a yau? Mecece manufarta?

• Wanene Shugaban da aka naɗa na ikilisiya, kuma waɗanne tsari da ake gani suke yi mana tanadi mai kyau?

• Waɗanne halaye masu kyau ya kamata mu kasance da su wajen waɗanda suke ƙungiyar Jehovah?

[Hotuna a shafi na 133]

Jehovah yana yi mana ja-gora ta wurin ƙungiyarsa da ake gani ƙarƙashin Kristi

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba