Wakili Mai Aminci Da Hukumarsa Ta Mulki
“Ubangiji ya ce, wanene fa wakili mai-aminci, mai-azanci, wanda ubangijinsa za ya sanya shi bisa iyalin gidansa, domin shi raba musu abincinsu a lotonsa?”—LUK. 12:42.
1, 2. Wace tambaya mai muhimmanci ce Yesu ya yi sa’ad da yake ba da alamar kwanaki na ƙarshe?
SA’AD DA yake ba da alama game da kwanaki na ƙarshe, Yesu ya yi wannan tambayar: “Wanene fa bawan nan mai-aminci, mai-hikima wanda ubangijinsa ya sanya shi bisa iyalin gidansa, domin shi ba su abincinsu a lotonsa?” Yesu ya ci gaba da cewa za a ba wannan bawan lada domin amincinsa ta wajen naɗa shi bisa dukan mallakar Ubangijinsa.—Mat. 24:45-47.
2 Watanni da yawa da suka shige, Yesu ya yi irin wannan tambayar. (Karanta Luk 12:42-44.) Ya kira bawan “wakili” kuma ya kira “mallaka tasa” “iyalin gidansa.” Wakili, manaja ne ko kuma mai kula da gida wanda ke shugabantar bayi. Amma, wakili ma bawa ne. Wanene wannan bawa ko kuma wakili, kuma yaya yake tanadin ‘abinci a lotonsa’? Yana da muhimmanci dukanmu mu fahimci hanyar da ake amfani da ita a ba da abinci na ruhaniya.
3. (a) Yaya Kiristendam masu yin sharhi suka bayyana abin da Yesu ya faɗa game da “bawan nan”? (b) Wanene “wakili,” ko “bawa,” kuma su wanene “iyalin gidansa,” ko ‘mallakarsa’?
3 Kiristendam masu yin sharhi sau da yawa suna ɗaukan cewa waɗannan kalaman Yesu suna nuni ga waɗanda suke da matsayi tsakanin masu da’awar cewa su Kiristoci ne. Amma Yesu, ‘ubangiji’ a cikin kwatanci, bai faɗa ba cewa za a sami bayi masu yawa da ke ɗarikoki dabam-dabam na Kiristendam. Maimakon haka, ya faɗa sarai cewa za a sami “wakili” ko kuma “bawa” da zai naɗa bisa dukan mallakarsa. Saboda haka, kamar yadda wannan mujallar takan bayyana sau da yawa, wakilin yana wakiltar “ƙaramin garke” na almajirai shafaffu a matsayin rukuni. A Linjilar Luka, Yesu yana maganar waɗannan ne. (Luk 12:32) “Iyalin gidansa” ko ‘mallakarsa,’ na nuni ga rukuni ɗaya amma yana nanata hakkinsu a matsayin mutane ɗaɗɗaya. Hakan ya ta da tambaya mai muhimmanci, Kowanne cikin wannan rukunin bawa yana da hannu wajen tanadin abinci na ruhaniya a lotonsa? Za mu san amsar sa’ad da muka bincika abin da Nassosi ya ce sosai.
Bawan Jehobah a Dā
4. Yaya Jehobah ya kira al’ummar Isra’ila ta dā, kuma menene yake da muhimmanci mu lura da shi game da wannan al’ummar?
4 Jehobah ya yi maganar mutanensa, al’ummar Isra’ila ta dā a matsayin haɗaɗɗen rukuni. “Ku ne shaiduna [jam’i], in ji Ubangiji, barana [mufuradi] kuma wanda na zaɓa.” (Isha. 43:10) An haɗa dukan mutanen al’ummar cikin wannan rukunin bawa. Amma, yana da muhimmanci mu lura cewa firistoci ne kaɗai tare da Lawiyawa suke da hakkin koyar da al’ummar.—2 Laba. 35:3; Mal. 2:7.
5. In ji Yesu, wane canji ne za a yi?
5 Al’ummar Isra’ila ce bawan da Yesu ya yi maganarsa? A’a. Mun san hakan domin abin da Yesu ya gaya wa Yahudawa na zamaninsa: “Za a amshe muku mulkin Allah, za a bayar ga al’umma mai-fitowa da ’ya’yansa.” (Mat. 21:43) A bayane yake sarai cewa za a samu canji. Jehobah zai yi amfani da sabuwar al’umma. Duk da haka, idan ya zo ga koyarwa ta ruhaniya, aikin bawan nan na kwatancin Yesu zai yi kama da ta “bawan” Allah a Isra’ila ta dā.
Bawan Nan Mai Aminci Ya Bayyana
6. Wace sabuwar al’umma ce aka kafa a ranar Fentakos na shekara ta 33 A.Z., wanene ya zama sashenta?
6 Sabuwar al’umma, “Isra’ila na Allah” ce Isra’ilawa ta ruhaniya. (Gal. 6:16; Rom. 2:28, 29; 9:6) An kafa ta sa’ad da aka zuba ruhun Allah a ranar Fentakos na shekara ta 33 A.Z. Bayan hakan, dukan Kiristoci da aka shafa da ruhu sun zama al’ummar da yanzu ita ce rukunin bawan da Yesu Kristi, Ubangiji ya naɗa. An ba dukan waɗanda ke cikin wannan al’umma umurnin wa’azin bishara da kuma almajirantarwa. (Mat. 28:19, 20) Amma dukan waɗanda ke cikin wannan rukunin ne za su sa hannu wajen yin tanadin abinci na ruhaniya a lotonsa? Bari mu ga yadda Nassosi ya amsa wannan tambayar.
7. Da farko, menene ainihin aikin manzanni, kuma wane ƙarin hakki suka samu?
7 Sa’ad da Yesu ya zaɓi manzanninsa 12, aikinsu na musamman shi ne su yi wa mutane wa’azin bishara. (Karanta Markus 3:13-15.) Wannan aikin ya jitu da ainihin ma’anar kalmar Helenanci apostolos, da aka samo daga aikatau da ke nufin “aika.” Amma, da shigewar lokaci kuma ana son a kafa ikilisiyar Kirista, hakkin manzo ya zama ‘matsayi.’—A. M. 1:20-26; LMT.
8, 9. (a) Menene ya fi muhimmanci ga manzanni goma sha biyu? (b) Kamar yadda hukumar mulki ta tabbatar, su waye ne kuma aka ba ƙarin hakki?
8 Menene ya fi muhimmanci ga manzanni goma sha biyu? Za a samu amsar a abubuwa da suka faru bayan ranar Fentakos. Sa’ad da aka soma jayayya game da rabon gudummawar abinci a kowace rana ga mata da mazansu suka mutu, manzanni goma sha biyu suka tara almajirai kuma suka ce: “Ba ya dace ba mu bar kalmar Allah mu yi hidimar abinci.” (Karanta Ayyukan Manzanni 6:1-6.) Manzanni suka naɗa wasu ’yan’uwa maza da suka manyanta a ruhaniya don su kula da “wannan sha’ani” don manzannin su ba da kansu ga “hidimar kalman.” Jehobah ya albarkaci wannan shirin kuma “maganar Allah kuwa ta yawaita; yawan masu-bi kuma cikin Urushalima ya riɓanɓanya ƙwarai.” (A. M. 6:7) Saboda haka, manzannin ne suke da hakki na musamman na aikin ciyarwa ta ruhaniya.—A. M. 2:42.
9 Da shigewar lokaci aka ɗanka wa wasu hakki mai girma. Ikilisiyar da ke Antakiya a ƙarƙashin ja-gorar ruhu mai tsarki ne ta aika Bulus da Barnaba zuwa hidima a ƙasashen waje. Sun zama manzanni, ko da yake ba a haɗa su cikin manzanni goma sha biyu na asali. (A. M. 13:1-3; 14:14; Gal. 1:19) Hukumar mulki da ke Urushalima ce ta tabbatar da naɗinsu. (Gal. 2:7-10) Ba da daɗewa ba bayan da aka naɗa Bulus manzo, ya saka hannu wajen idar da abinci na ruhaniya. Ya rubuta wasiƙarsa ta farko da aka hure.
10. A ƙarni na farko, dukan Kiristoci ne da aka shafa da ruhu suka sa hannu wajen shirya abinci na ruhaniya? Ka ba da bayani.
10 Amma, dukan Kiristoci shafaffu ne suke sa hannu wajen kula da aikin wa’azi da kuma shirya abinci na ruhaniya? A’a. Manzo Bulus ya gaya mana: “Duka ne manzanni? duka ne annabawa? duka ne masu-koyarwa? duka ne masu-aikin ayuka na iko?” (1 Kor. 12:29) Ko da yake dukan waɗanda aka shafa da ruhu suna aikin wa’azi, ƙalilan ne kawai, maza takwas aka yi amfani da su wajen rubuta littattafai ashirin da bakwai na Nassosin Helenanci na Kirista.
Bawan Nan Mai Aminci a Zamani
11. An naɗa bawan nan ya kula da wane ‘mallaka’?
11 Kalaman Yesu da ke rubuce a Matta 24:45 sun nuna sarai cewa har ila za a samu rukunin bawan nan mai aminci mai hikima a duniya a kwanaki na ƙarshe. Ru’ya ta Yohanna 12:17 ta kira waɗannan “sauran zuriya” ta macen. A matsayin rukuni, an naɗa waɗannan bisa dukan mallakar Kristi da ke duniya. ‘Mallakar’ da aka naɗa wakili mai aminci ya kula da su su ne abubuwa na Ubangiji da ke duniya, waɗanda suka haɗa da talakawan Mulki a duniya da kayayyakin da ake amfani da su wajen yin wa’azin bishara.
12, 13. Yaya Kirista zai san cewa shi ko ita tana da begen zuwa sama?
12 Yaya Kirista zai san cewa yana ko tana da begen zuwan sama kuma yana ko tana cikin wannan Isra’ilawa ta ruhaniya da suka rage? Amsar tana cikin kalaman manzo Bulus ga waɗanda suke da begen zuwan sama tare da shi: “Iyakar waɗanda Ruhun Allah ke bishe su, waɗannan ’ya’yan Allah ne. Gama ba ku karɓi ruhun bauta da za ku sake jin tsoro ba; amma kuka karɓi ruhun ɗiyanci, inda muke kira, Abba, Uba. Ruhu da kansa tare da namu ruhu yana shaida, mu ’ya’yan Allah ne: idan ’ya’ya ne fa, magada ne kuma; magadan Allah, masu-tarayyan gādo da Kristi; in fa muna raɗaɗi tare da shi, domin kuma mu ɗaukaka tare da shi.”—Rom. 8:14-17.
13 A sauƙaƙe, an naɗa waɗannan da ruhu mai tsarki na Allah kuma sun samu “kira” zuwa sama. (Ibran. 3:1) Wannan kira daga wurin Allah ne. Kuma sun karɓi gayyatar nan da nan ba tare da shakka ba ko kuma jin tsoron zama ’ya’yan Allah. (Karanta 1 Yohanna 2:20, 21.) Saboda haka, ba su zaɓi wannan begen da kansu ba, amma Jehobah ne ya saka hatiminsa, ko ruhu mai tsarki a kansu.—2 Kor. 1:21, 22; 1 Bit. 1:3, 4.
Ra’ayin da Ya Dace
14. Yaya shafaffu suke ɗaukan kiran da aka yi musu?
14 Yaya ya kamata waɗannan shafaffu su ɗauki kansu yayin da suke jiran ladarsu ta samaniya? Sun fahimci cewa ko da yake sun samu kira mai girma, hakan kira ne kawai. Dole ne su kasance da aminci har mutuwa domin su samu wannan ladar. Suna ji kamar Bulus wanda ya ce: “’Yan’uwa, ni ban maida kaina na ruska ba tukuna: amma abu ɗaya ni ke yi, ina manta da abubuwan da ke baya, ina kutsawa zuwa ga waɗanda ke gaba, ina nace bi har zuwa ga goal, in kai ga ladan nasara na maɗaukakiyar kira ta Allah cikin Kristi Yesu.” (Filib. 3:13, 14) Dole ne shafaffu da suka rage su yi iyakar ƙoƙarinsu su yi ‘tafiya irin da ta cancanci kira da aka kiraye su da ita, da dukan tawali’u,’ suna yin hakan “da tsoro da rawan jiki.”—Afis. 4:1, 2; Filib. 2:12; 1 Tas. 2:12.
15. Yaya ya kamata Kiristoci su ɗauki waɗanda suke cin gurasa da shan inabi a lokacin Tuna Mutuwar Yesu, kuma yaya shafaffu suke ɗaukan kansu?
15 A wani ɓangare kuma, yaya ya kamata sauran Kiristoci su ɗauki mutumin da ke da’awar cewa an shafa shi da ruhu kuma ya soma cin gurasa da shan inabi a lokacin Tuna Mutuwar Kristi? Bai kamata a hukunta mutumin ba. Batun tsakanin mutumi ne da Jehobah. (Rom. 14:12) Amma, Kiristoci da aka shafa su da gaske ba sa bukata a mai da musu hankali na musamman. Ba su gaskata ba cewa zama shafaffu ya sa sun kasance da fahimi na musamman fiye da waɗanda suka manyanta da suke cikin “taro mai-girma.” (R. Yoh. 7:9) Ba sa tunanin cewa suna da ƙarin ruhu mai tsarki fiye da abokansu “waɗansu tumaki.” (Yoh. 10:16) Ba sa tunani cewa za a yi musu ladabi na musamman; kuma ba sa da’awar cewa sun fi dattawan da ke cikin ikilisiya domin suna cin gurasa da kuma shan inabi na tuna mutuwar Yesu.
16-18. (a) Dukan shafaffu suna sa hannu wajen sabon koyarwa ta ruhaniya? Ka ba da misali. (b) Me ya sa Hukumar Mulki ba ta bukatar ta tuntuɓi dukan waɗanda suke da’awar cewa su shafaffu ne?
16 Dukan waɗannan shafaffu da ke duniya suna cikin rukunin da ke bayyana sabuwar gaskiya ta ruhaniya? A’a. Ko da yake suna cikin rukuni ɗaya, ajin bawan ne ke da hakkin ciyar da iyali na ruhaniya, ba dukan mutane ɗaɗɗaya na ajin bawan ba ne suke da hakki ko kuma aiki iri ɗaya ba. (Karanta 1 Korinthiyawa 12:14-18.) Kamar yadda aka faɗa ɗazu, a ƙarni na farko, kowa ya yi aikin wa’azi mai muhimmanci. Amma adadi kaɗan ne kawai aka yi amfani da su wajen rubuta littattafai na Littafi Mai Tsarki kuma suka kula da ikilisiyar Kirista.
17 Alal misali: Nassosi takan ce “ikilisiya” tana ɗaukan wani mataki wajen yin shari’a. (Mat. 18:17) Amma, gaskiyar ita ce dattawa ne kaɗai suke ɗaukan wannan mataki a matsayin waɗanda suke wakiltar ikilisiyar. Dattawa ba sa neman ra’ayin dukan waɗanda suke cikin ikilisiya kafin su tsai da shawara. Suna yin aikin da aka ba su daidai da tsarin Allah; suna ɗaukan mataki a madadin dukan ikilisiyar.
18 Hakanan ma, a yau adadi kaɗan ne kawai cikin maza shafaffu suke da hakkin wakiltar rukunin bawan nan. Suna cikin Hukumar Mulki na Shaidun Jehobah. Waɗannan maza da aka shafa da ruhu suna kula da aikin Mulki da tsarin koyarwa ta ruhaniya. Yadda yake a ƙarni na farko, Hukumar Mulki ba ta tambayar dukan waɗanda ke cikin rukunin bawan nan kafin ta tsai da shawara. (Karanta Ayyukan Manzanni 16:4, 5.) Amma, dukan Shaidu shafaffu suna sa hannu sosai a aiki mai muhimmanci na girbi da ake yi yanzu. A matsayin rukuni, “bawan nan mai-aminci, mai hikima” jiki ɗaya ne, amma kowannensu yana da aiki dabam da yake yi.—1 Kor. 12:19-26.
19, 20. Wane ra’ayin da ya dace ne taro mai girma suke da shi game da “bawan nan mai aminci, mai-hikima” da Hukumarsa ta Mulki?
19 Yaya waɗannan bayanai ya kamata su shafi taro mai girma da suke ƙaruwa kuma suke da begen zama a duniya har abada? Da yake suna cikin abubuwan da Sarki yake da shi, suna farin cikin ba da haɗin kai ga shawarwarin da Hukumar Mulki take tsai da wa, wadda take wakiltar “bawan nan mai-aminci, mai-hikima.” Waɗanda suke cikin taro mai girma suna farin ciki game da abinci na ruhaniya da ake tanadinsa a ƙarƙashin ja-gorancin Hukumar Mulki. Amma, ko da yake suna ba bawan nan ladabi a matsayin rukuni, waɗanda suke cikin taro mai girma suna mai da hankali don kada su ɗaukaka kowanne mutum da yake da’awar cewa yana cikin rukunin wannan bawan. Babu Kirista wanda aka shafa shi da ruhun Allah da zai so ko kuma yi tsammanin cewa a ba shi ladabi na musamman.—A. M. 10:25, 26; 14:14, 15.
20 Ko muna cikin ‘mallakar’ Yesu waɗanda suke cikin shafaffu, ko kuwa muna cikin taro mai girma, bari mu ƙuduri aniya mu ba da haɗin kai sosai ga wakilin nan mai aminci da Hukumarsa ta Mulki. Bari kowanenmu ya “yi tsaro” kuma ya kasance da aminci har ƙarshe.—Mat. 24:13, 42.
Ka Tuna?
• Wanene “bawan nan mai-aminci, mai-hikima,” kuma su wanene mallaka?
• Yaya mutum zai san cewa yana da begen zuwa sama?
• Wanene yake da ainihin hakkin shirya sabon abinci na ruhaniya?
• Yaya ya kamata wanda aka shafa da ruhu ya ɗauki kansa?
[Hotunan da ke shafi na 23]
A yau, Hukumar Mulki tana wakiltar rukunin bawan nan mai aminci mai hikima. Da akwai irin wannan shirin a ƙarni na farko