Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w04 3/1 pp. 25-30
  • An Iske ‘Bawan Da Aminci’ A Lokacin Bincike!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • An Iske ‘Bawan Da Aminci’ A Lokacin Bincike!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “Mugun Bawan nan”
  • Budurwoyi Masu Hikima da Marasa Azanci
  • Almarar Talanti
  • Lokacin Bincike Ya Soma
  • An Ci Gaba da Yin Bincike
  • Wani ‘Bawa’ Da Yake Da Aminci Da Kuma Hikima
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Ka Ci Gaba da ‘Yin Tsaro!’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • “Wane ne Fa Bawan nan Mai-Aminci, Mai-Hikima?”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Kana Bin Gargadin Yesu?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
w04 3/1 pp. 25-30

An Iske ‘Bawan Da Aminci’ A Lokacin Bincike!

“Lokaci ya yi da shari’a za ta faru a kan gidan Allah.”—1 BITRUS 4:17.

1. Menene Yesu ya gani sa’ad da ya bincika “bawan”?

AFENTAKOS na shekara ta 33 A.Z., Yesu ya naɗa ‘bawa’ ya ba wa “iyalin gidansa” abinci a lotonsa. A shekara ta 1914, aka naɗa Yesu ya zama Sarki, ba da daɗewa ba lokaci ya kai da za a bincika wannan “bawan.” Ya iske cewa “bawan” ya kasance da ‘aminci da kuma hikima.’ Shi ya sa, ya naɗa shi “bisa dukan abin da ya ke da shi.” (Matta 24:45-47) Amma, akwai mugun bawa kuma, da ba shi da aminci ko kuma hikima.

“Mugun Bawan nan”

2, 3. Daga ina ne “mugun bawan nan” ya fito, kuma yaya wannan ya soma?

2 Yesu ya yi maganar mugun bawan nan, nan da nan bayan ya gama tattaunawa game da “bawan nan mai-aminci, mai-hikima.” Ya ce: “Idan mugun bawan nan ya fāɗi cikin zuciyarsa, Ubangijina yana jinkiri; har ya soma dūkan abokan bautansa, ya ci ya sha tare da masu-maye; ubangijin bawan nan za ya zo cikin rana da ba ya sa tsammani ba, cikin sa’a wadda ba ya sani ba, za ya yi masa dūka ƙwarai, ya sanya masa rabonsa tare da masu-riya: can za a yi kuka da cizun haƙora.” (Matta 24:48-51) Wannan furcin ‘mugun bawan nan’ ya jawo hankalinmu ga kalmomin Yesu da ya gabata game da bawan nan mai aminci da kuma hikima. Hakika, “mugun bawan” ya fito daga waɗanda suke cikin bawan nan mai aminci dā.a Ta yaya?

3 Kafin shekara ta 1914, waɗanda suke cikin rukunin bawa mai aminci da yawa suna da begen saduwa da Angon a sama a wannan shekara, amma begensu bai kasance hakan ba. Domin wannan da wasu abubuwa da suka taso, mutane da yawa suka yi sanyin gwiwa kuma kalilan suka yi baƙin ciki. Wasu cikin waɗannan suka soma “dūkan” ’yan’uwansu na dā da maganar baki suka kuma fara tarayya da rukunin addinan Kiristendam “masu-maye.”—Ishaya 28:1-3; 32:6.

4. Yaya Yesu ya bi da “mugun bawan” da kuma dukan waɗanda suka nuna irin wannan hali?

4 An san cewa waɗannan Kiristoci na dā sune “mugun bawan,” kuma Yesu ya yi musu horo “ƙwarai.” Ta yaya? Ya ƙi su, suka kuma yi hasarar begensu na zuwan sama. Amma, ba a halaka su nan da nan ba. Za su jimre wa lokacin kuka da cizon haƙora cikin “baƙin duhu” waje da ikilisiyar Kirista. (Matta 8:12) Tun waɗancan lokaci na farko, shafaffu kalilan sun nuna irin wannan mugun halin, suna tarayya da “mugun bawan.” Wasu cikin “waɗansu tumaki” sun yi koyi da rashin amincinsu. (Yohanna 10:16) Irin waɗannan magabtan Kristi suna fuskantar “baƙin duhu” na ruhaniya a waje.

5. Ta yaya bawan nan mai-aminci, mai-hikima ya aikata dabam da “mugun bawan”?

5 Duk da haka, an yi wa bawan nan mai-aminci, mai-hikima irin wannan gwaji na “mugun bawan.” Maimakon su yi baƙin ciki, sun yi gyara. (2 Korinthiyawa 13:11) An ƙarfafa ƙaunarsu ga Jehovah da kuma ’yan’uwansu. Saboda haka, sun zama “jigon gaskiya da ƙarfinta” a waɗannan lokacin hargitsi na “kwanaki na ƙarshe.”—1 Timothawus 3:15; 2 Timothawus 3:1.

Budurwoyi Masu Hikima da Marasa Azanci

6. (a) Ta yaya Yesu ya ba da misalin hikima na rukunin bawansa masu aminci? (b) Kafin shekara ta 1914, wane saƙo ne Kiristoci shafaffu suka yi shelarsa?

6 Bayan ya yi maganar “mugun bawan nan,” Yesu ya faɗi almara biyu don ya nuna abin da ya sa wasu Kiristoci shafaffu za su kasance da aminci da kuma hikima yayin da wasu ba za su kasance haka ba.b Don ya ba da misalin hikima, ya ce: “Sa’annan za a iske mulkin sama yana kāma da budurwoyi goma, waɗanda suka ɗauki fitilunsu, suka fita garin su tarbi ango. Biyar daga cikinsu marasa-azanci ne, biyar masu-hikima ne. Gama marasa-azancin nan, da suka ɗauki fitilunsu, ba su ɗauka duk da mai ba: amma masu-hikima suka ɗauki mai cikin santulansu tare da fitilunsu.” (Matta 25:1-4) Budurwoyi goman sun tuna mana Kiristoci shafaffu kafin shekara ta 1914. Sun yi tunanin cewa angon, Yesu Kristi, yana son ya bayyana. Shi ya sa, suka “fita” su tarbe shi, suna wa’azi da gaba gaɗi cewa “zamanan Al’ummai” za su cika a shekara ta 1914.—Luka 21:24.

7. Yaushe ne kuma me ya sa Kiristoci shafaffu “suka yi barci” ta alama?

7 Gaskiyarsu. Zamanan al’ummai sun ƙare a shekara ta 1914, kuma Mulkin Allah a ƙarƙashin Kristi Yesu ya soma sarauta. Amma wannan a sama ne. A duniya kuma, ’yan Adam suka soma shan wahalar ‘kaito’ da aka annabta. (Ru’ya ta Yohanna 12:10, 12) Lokacin gwaji ya soma. Da yake ba su fahimci abubuwa sosai ba, Kiristoci shafaffu suna jin “ango ya yi jinkiri.” Da yake sun ruɗe kuma suna fuskantar ƙiyayya daga duniya, suka rage himmarsu kuma suka kusan daina aikin wa’azi da aka tsara. Kamar budurwoyi cikin almarar, a ruhaniya “suka yi rurrumi, suka yi barci,” yadda waɗanda suke da’awa su Kiristoci ne marasa aminci suka yi bayan manzannin Yesu suka mutu.—Matta 25:5; Ru’ya ta Yohanna 11:7, 8; 12:17.

8. Me ya sa aka ji murya: “Ga ango!” kuma lokaci ya kai da Kiristoci shafaffu za su yi menene?

8 Sa’annan a shekara ta 1919 abin da ba a yi tsammaninsa ba ya faru. Mu karanta: “Da tsakiyar dare sai aka ji murya, Ga ango! Ku fito, ku tarbe shi. Sa’annan dukan waɗannan budurwai suka tashi, suka yi ta gyartan fitilunsu.” (Matta 25:6, 7) Daidai da lokacin da suka fid da rai aka ce su soma aiki! A shekara ta 1918, Yesu, “mala’ikan alkawari,” ya zo haikalin Jehovah na ruhaniya ya bincika kuma ya tsarkake ikilisiyar Allah. (Malachi 3:1) Yanzu, Kiristoci shafaffu suna bukatar su je su tarbe shi a farfajiya ta duniya na wannan haikali. Lokaci ne da za su “bada haske.”—Ishaya 60:1; Filibbiyawa 2:14, 15.

9, 10. A shekara ta 1919, me ya sa wasu Kiristoci suke da ‘hikima’ wasu kuma “marasa-azanci”?

9 Amma tsaya! Cikin almarar, wasu cikin budurwoyin suna da matsala. Yesu ya ci gaba: “Marasa-azanci suka ce ma masu-hikiman, Ku ɗibo mana daga cikin manku: gama fitilunmu suna mutuwa.” (Matta 25:8) Idan babu mai, fitilun ba za su ba da haske ba. Da haka, man fitila ya tuna mana Kalmar Allah na gaskiya da ruhunsa mai tsarki, da suke ƙarfafa masu bauta ta gaskiya su zama masu ɗauke da haske. (Zabura 119:130; Daniel 5:14) Kafin shekara ta 1919, Kiristoci shafaffu masu hikima da ƙwazo suka nemi su fahimci nufin Allah a gare su, ko da yanayinsu ya raunana na ɗan lokaci. Saboda haka, sa’ad da kiran su ba da haske ya zo, suna shirye.—2 Timothawus 4:2; Ibraniyawa 10:24, 25.

10 Amma, wasu shafaffu ba sa a shirye su yi sadaukarwa ko kuma su mazakuta kansu—ko da suna son su kasance da Angon. Saboda haka, sa’ad da ya kai lokacin da za su yi ƙwazo a aikin bishara, ba sa a shirye. (Matta 24:14) Sun ma yi ƙoƙari su rage wutar abokansu, wato, suna neman su ɗan karɓi mansu. A cikin almarar Yesu, menene budurwoyi masu hikima suka ce? Sun ce: “Wataƙila ba za ya ishe mu duk da ku ba: gwamma ku tafi wurin masu-sayarwa, ku sayo ma kanku.” (Matta 25:9) Haka nan ma, Kiristoci masu aminci a shekara ta 1919 sun ƙi su yi kome da zai rage iyawarsu na ba da haske. Aka iske su da aminci a lokacin bincike.

11. Menene ya faru wa budurwoyi marasa azanci?

11 Yesu ya kammala: “Sa’anda [budurwoyi marasa azanci] suna cikin tafiya garin saye, ango ya zo; waɗanda suna nan a shirye suka shiga tare da shi wurin anganci: aka rufe ƙofa. Daga baya kuma waɗancan budurwoyi suka zo, suka ce, Ubangiji, Ubangiji, ka buɗe mana. Amma ya amsa, ya ce, Hakika, ina ce muku, Ban san ku ba.” (Matta 25:10-12) Hakika, wasu ba su yi shiri ba don zuwan Angon. Da haka, ba a iske su da aminci ba kuma suka yi hasarar zarafi su halarci bikin aure na samaniya. Lallai abin baƙin ciki ne!

Almarar Talanti

12. (a) Menene Yesu ya yi amfani da shi ya ba da misalin aminci? (b) Wanene mutum da ya tafi “wata ƙasa”?

12 Bayan ya ba da misalin hikima, Yesu ya ci gaba da ba da misalin aminci. Ya ce: “Yana kama da mutum, da za shi wata ƙasa, ya kira bayinsa, ya damƙa musu dukiyarsa. Ga wani ya bada [talanti] biyar, ga wani kuma biyu, ga wani ɗaya; kowa ya ba shi gwargwadon iyawatasa; kāna ya yi tafiyatasa.” (Matta 25:14, 15) Yesu ne mutumin cikin almarar, wanda ya tafi “wata ƙasa” sa’ad da ya hau sama a shekara ta 33 A.Z. Amma kafin ya haura, Yesu ya ba da “dukiyarsa” ga almajiransa masu aminci. Ta yaya?

13. Yaya Yesu ya shirya babban fage na aiki kuma ya ba “bayinsa” izini su yi ciniki?

13 A lokacin hidimarsa a duniya, Yesu ya soma shirya babban fage na aiki ta wa’azin bisharar Mulki a dukan ƙasar Isra’ila. (Matta 9:35-38) Kafin ya tafi “wata ƙasa,” ya danƙa wa almajiransa masu aminci wannan fage, yana cewa: “Ku tafi fa, ku almajirtadda dukan al’ummai, kuna yi musu baftisma zuwa cikin sunan Uba da na Ɗa da na Ruhu Mai-tsarki: kuna koya musu su kiyaye dukan iyakar abin da na umurce ku.” (Matta 28:18-20) Da waɗannan kalmomi, Yesu ya ba “bayinsa” izini su yi ciniki “kowa ya ba shi gwargwadon iyawatasa,” har sai ya dawo.

14. Me ya sa ba kowa ba ne ake bukata ya yi ciniki daidai da juna?

14 Wannan furci ya nuna cewa ba dukan Kiristoci na ƙarni na farko suke da yanayi ko kuma iyawa daidai da juna ba. Wasu, kamar Bulus da Timothawus suna da zarafi su yi aikin wa’azi da koyarwa sosai. Yanayin wasu na iya rage ’yancinsu na aiki sosai. Alal misali, wasu Kiristoci bayi ne, wasu kuma suna ciwo, wasu sun tsufa, ko kuma suna da hakki na iyali. Hakika, ba dukan almajirai ba ne suke da wasu gatar ikilisiya. Shafaffu mata da wasu shafaffu maza ba su koyar ba cikin ikilisiyar. (1 Korinthiyawa 14:34; 1 Timothawus 3:1; Yaƙub 3:1) Amma, ko yaya yanayinsu yake, dukan almajiran Kristi shafaffu—maza da mata—an ce su yi ciniki, su yi amfani da zarafi da yanayinsu da kyau a hidimar Kirista. Almajiran Kristi na zamani suna hakan.

Lokacin Bincike Ya Soma

15, 16. (a) Yaushe ne lokacin yin lissafi ya kai? (b) Waɗanne sababbin zarafi na yin “ciniki” aka ba wa masu aminci?

15 Almarar ta ci gaba: “Ananan bayan da aka jima, ubangijin waɗannan bayi ya zo, ya yi lissafi da su.” (Matta 25:19) A shekara ta 1914—babu shakka da daɗewa bayan shekara ta 33 A.Z.—Kristi Yesu ya soma sarauta. A shekara ta 1918, shekara uku da rabi bayan haka, ya zo haikalin Allah na ruhaniya ya cika kalmomin Bitrus: “Lokaci ya yi da shari’a za ta faru a kan gidan Allah.” (1 Bitrus 4:17; Malachi 3:1) Lokaci ya yi da za a yi lissafi.

16 Menene bayin, ’yan’uwan Yesu shafaffu suka yi da ‘talanti’ na Sarkin? Daga shekara ta 33 A.Z., zuwa gaba, har shekaru kafin shekara ta 1914, mutane da yawa suna aiki tuƙuru suna “ciniki” da Yesu ya sa su yi. (Matta 25:16) Har lokacin yaƙin duniya na farko, sun nuna ƙwarai cewa suna son su yi wa Ubangijin hidima. Yanzu, ya dace a ba sababbi masu aminci zarafi su yi “ciniki.” Lokaci na ƙarshe na wannan zamani ya zo. Za a yi wa’azin bishara a dukan duniya. Za a girbe “amfanin duniya.” (Ru’ya ta Yohanna 14:6, 7, 14-16) Ya kamata a nemi waɗanda suke cikin rukunin alkama na ƙarshe kuma a tattara “taro mai-girma” na waɗansu tumaki.—Ru’ya ta Yohanna 7:9; Matta 13:24-30.

17. Ta yaya Kiristoci shafaffu masu aminci suka ‘shiga cikin farin zuciyar ubangijinsu’?

17 Lokacin girbi lokacin farin ciki ne. (Zabura 126:6) Saboda haka, ya dace da a shekara ta 1919 Yesu ya danƙa wa ’yan’uwansa shafaffu masu aminci ƙarin hakki, ya ce: ‘Ka yi aminci cikin matsaloli kaɗan, ni sanya ka bisa mai-yawa: ka shiga cikin farinzuciyar ubangijinka.’ (Matta 25:21, 23) Ƙari ga haka, farin cikin Ubangijin da yake shi sabon Sarki ne na Mulki Allah da aka naɗa ya wuce tsammaninmu. (Zabura 45:1, 2, 6, 7) Rukunin bawan nan mai aminci suna irin wannan farin ciki ta wurin wakiltan Sarkin da ƙara abubuwa da yake da su a duniya. (2 Korinthiyawa 5:20) Ana ganin farin cikinsu a kalmomin annabci na Ishaya 61:10: “Zan yi farinciki ƙwarai cikin Ubangiji, raina za ya yi murna cikin Allahna, gama ya sa mini tufafin ceto.”

18. Me ya sa ba a iske wasu da aminci ba a lokacin bincike, kuma da wane sakamako?

18 Abin baƙin ciki, ba a iske wasu da aminci ba a lokacin bincike. Mu karanta: “Wanda ya karɓi [talanti] guda, ya zo, ya ce, Ubangiji, na sani kai mutum marar-siyasa ne, ka kan girbi wurin da ba ka shuka ba, ka kan tattara wurin da ba ka rigaya ka watsa ba. Ni kuwa na ji tsoro, na je na ɓoye [talantin] nan naka cikin ƙasa: ga abinka.” (Matta 25:24, 25) Haka nan ma, wasu Kiristoci shafaffu ba su yi “ciniki” ba. Kafin shekara ta 1914 ba su gaya wa mutane begensu ba da ƙwazo, kuma ba sa son su soma a shekara ta 1919. Me Yesu ya yi game da rashin hankalinsu? Ya karɓi duk gatarsu. Aka ‘jefar da su cikin baƙin duhu, inda za su yi kuka da cizon haƙora.’—Matta 25:28, 30.

An Ci Gaba da Yin Bincike

19. A wace hanya ce tsarin binciken ya soma, kuma menene dukan Kiristoci shafaffu suka ƙudura niyyar yi?

19 Hakika, yawancin waɗanda za su zama shafaffu bayin Kristi a lokacin ƙarshe ba su fara bauta wa Jehovah ba sa’ad da Yesu ya soma bincikensa a shekara ta 1918. Sun yi hasarar zarafin binciken? Ko kaɗan. Tsarin binciken ya soma a shekara ta 1918 zuwa 1919, sa’ad da rukunin bawan nan mai aminci da kuma hikima suka jimre wa gwajin. An ci gaba da bincika Kiristoci shafaffu har sai da aka sa hatiminsu ya zama dindindin. (Ru’ya ta Yohanna 7:1-3) Da yake sun fahimci wannan, ’yan’uwan Kristi shafaffu sun ƙudura niyya su ci gaba da ‘yin ciniki.’ Sun ƙudura niyya su yi hikima, su kasance da mai a yalwace don hasken ya haskaka sosai. Sun sani cewa sa’ad da kowanne ya kai ƙarshen rayuwarsa cikin aminci, Yesu zai kai shi sama.—Matta 24:13; Yohanna 14:2-4; 1 Korinthiyawa 15:50, 51.

20. (a) Menene waɗansu tumaki suka ƙudura niyyar yi a yau? (b) Menene Kiristoci shafaffu suka sani?

20 Taro mai girma na waɗansu tumaki sun yi koyi da ’yan’uwansu shafaffu. Sun sani cewa iliminsu game da nufe-nufen Allah yana kawo hakki mai girma. (Ezekiel 3:17-21) Saboda haka, da taimakon Kalmar Jehovah da kuma ruhu mai tsarki, su ma sun ajiye mai a yalwace ta nazari da cuɗanya. Suna bari haskensu ya haskaka, suna sa hannu a aikin wa’azi da koyarwa da haka suna ‘yin ciniki’ tare da ’yan’uwansu shafaffu. Amma, Kiristoci shafaffu sun sani cewa talanti yana hannunsu. Dole su ba da lissafi a yadda ake gudanar da dukiyar Ubangiji a duniya. Ko da su kalilan ne, ba za su ba wa taro mai girma hakkinsu ba. Da yake sun san wannan, bawan nan mai-aminci, mai-hikima sun ci gaba da ja-gora a kula da cinikin Sarkin, suna godiya don goyon bayan taro mai girma da suka ba da kansu. Waɗannan sun san cewa ’yan’uwansu shafaffu suna da hakki kuma gata ce a gare su yi aiki a ƙarƙashin ja-gorarsu.

21. Wane gargaɗi dukan Kiristoci kafin shekara ta 1919 zuwa zamaninmu za su yi amfani da shi?

21 Da haka, ko da yake waɗannan almara biyu sun wayar da mu a kan ayyuka na shekara ta 1919 da kuma bayan haka, dukan Kiristoci na gaskiya a wannan kwanaki na ƙarshe za su yi amfani da ƙa’idodin almara biyun. A wannan hanya, ko da gargaɗin da Yesu ya bayar a ƙarshen almarar budurwoyi goma ga Kiristoci shafaffu ne kafin shekara ta 1919, har ila kowanne Kirista zai yi amfani da ƙa’idar. Saboda haka, bari dukanmu mu yi biyayya da kalmomin Yesu: “Ku yi tsaro fa, gama ba ku san rana ko sa’a ba.”—Matta 25:13.

[Hasiya]

a Haka nan ma, bayan mutuwar manzanni, “kerketai masu-zafin hali” suka fito daga dattawa shafaffu Kirista.—Ayukan Manzanni 20:29, 30.

b Don wani tattaunawa na almarar Yesu, ka duba littafin nan Worldwide Security Under the “Prince of Peace,” shafi na 5 da 6, da kuma Hasumiyar Tsaro na 1 ga Mayu, 1999, shafafi 26-30 da Shaidun Jehovah suka buga.

Za Ka Iya Bayyanawa?

• Yaushe ne Yesu ya bincika mabiyansa, kuma me ya gani?

• Me ya sa wasu Kiristoci shafaffu suka koyi halin “mugun bawan nan”?

• Ta yaya za mu nuna cewa muna da hikima ta ruhaniya?

• A yin koyi da ’yan’uwan Yesu shafaffu, a wace hanya ce za mu ci gaba da ‘yin ciniki’?

[Akwati a shafi na 28]

YAUSHE NE YESU YA ZO?

A Matta surori 24 da 25, a wurare dabam dabam an ce Yesu yana “zuwa.” Ba ya bukatar ya tashi a zahiri don ya ‘zo’ ba. Maimako, ya ‘zo’ a azanci na mai da hankalinsa wurin ’yan Adam ko kuma mabiyansa, sau da yawa don shari’a. Da haka, a shekara ta 1914 ya ‘zo’ don ya soma bayyanuwarsa na Sarki da aka naɗa. (Matta 16:28; 17:1; Ayukan Manzanni 1:11) A shekara ta 1918 ya ‘zo’ shi ne manzon alkawarin kuma ya soma shari’ar waɗanda suke da’awa suna bauta wa Jehovah. (Malachi 3:1-3; 1 Bitrus 4:17) A Armageddon zai ‘zo’ ya zartar da hukunci a kan magabtan Jehovah.—Ru’ya ta Yohanna 19:11-16.

Zuwa (ko, bayyanuwa) da aka yi maganarsa sau da yawa a Matta 24:29-44 da kuma 25:31-46 a lokacin “babban tsananin” ne. (Ru’ya ta Yohanna 7:14) A wata sassa, zuwa da aka yi maganarsa sau da yawa a Matta 24:45 zuwa 25:30 game da shari’a ce da zai yi wa waɗanda suke da’awa su almajirai ne daga shekara ta 1918 zuwa gaba. Alal misali, ba zai dace ba a ce za a saka wa bawan nan mai aminci, a yi shari’ar budurwoyi marasa azanci, da na bawa mai ƙyuya, wanda ya ɓoye talintin Ubangiji, sa’ad da Yesu ya “zo” a babban tsanani ba. Wannan yana nufin cewa a lokacin za a iske shafaffu da yawa da rashin aminci kuma ta haka za a canja su. Amma, Ru’ya ta Yohanna 7:3 ta nuna cewa dukan bayin Kristi shafaffu za a ‘hatimce’ su dindindin a lokacin.

[Hoto a shafi na 26]

“Mugun bawan” bai samu albarka a shekara ta 1919 ba

[Hoto a shafi na 27]

Budurwoyi masu hikima suna shirye sa’ad da angon ya zo

[Hoto a shafi na 29]

Bayi masu aminci sun yi “ciniki”

[Hoto a shafi na 29]

Bawa mai ƙyuya bai yi ba

[Hotuna a shafi na 30]

Shafaffu da kuma “taro mai girma” sun ci gaba da ba da haske

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba