Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w05 11/1 pp. 4-7
  • Da Wanda Zai iya Canja Duniya Kuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Da Wanda Zai iya Canja Duniya Kuwa?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ƙoƙarce-Ƙoƙarcen Kawo Canji
  • Abubuwan da Ke Hana Canji
  • Me Ya Sa Ya Ƙyale Hakan?
  • Yesu Kristi Zai Kawo Canji na Dindindin
  • “Kada Kuwa Ku Daina Yin Alheri”
  • Menene Allah ya Nufa ga Duniya?
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Ka Bi Misalin Yesu Kuma Ka Nuna Damuwa Ga Matalauta
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Albishiri Ga Talakawa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Me Ya Sa Allah Ya Halicci Mutane?
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
w05 11/1 pp. 4-7

Da Wanda Zai iya Canja Duniya Kuwa?

“Matalauta sun gaya mana cewa, fiye da kome, suna bukatar zaman lafiya da kwanciyar rai, sai kuma zarafin su kyautata rayuwarsu. Suna bukatar tsari na adalci a cikin ƙasa da kuma a duniya baki ɗaya, saboda kada iko na ƙasashe masu arziki da kamfanoni masu arziki su ɓata musu sha’ani.”

HAKA darekta ta hukumar ba da agaji ta duniya ta kwatanta bege da kuma bukatar matalauta. Hakika, kalmominta suna iya kwatanta muradin dukan mutane da suka fuskanci bala’i da kuma rashin adalci na duniya. Dukansu suna ɗokin ganin duniya da ake da zaman lafiya da kwanciyar rai. Za a taɓa samun irin wannan duniyar kuwa? Da wanda yake da iko da kuma iyawa ya canja wannan duniyar da ta kasance marar adalci?

Ƙoƙarce-Ƙoƙarcen Kawo Canji

Mutane sun yi ƙoƙari. Alal misali, Florence Nightingale, Baturiya ta ƙarni na 19, ta sadaukar da ranta ga tanadin jinya mai tsabta da tausaya wa majiyyata. A zamaninta, kafin asibiti irin na zamani, jiyya a asibiti ba kamar yadda muka sani ba ne a yau. “Nas-nas” in ji wani littafi, “ba su da ilimi, ba su da tsabta, kuma malalata ne wajen yin maye da lalata.” Shin Florence Nightingale ta yi nasara ne a ƙoƙarce-ƙoƙarcenta ta kawo canji a aikin jinya? Ta yi nasara. Hakazalika, mutane da yawa marasa sonkai sun yi nasara a wurare dabam dabam na rayuwa, yaƙi da jahilci, ilimi, magani, gine-gine, tsarin ciyar da mutane, da dai sauransu. Domin wannan, an sami canji ƙwarai a ingancin rayuwar miliyoyin mutane marasa galihu.

Duk da haka, ba za mu rufe idanunmu ga abin da ke zahiri ba: Miliyoyin mutane har ila suna wahala domin yaƙe-yaƙe, yin laifi, cututtuka, yunwa, da wasu masifu iri dabam dabam. Hukumar ba da agaji ta mutanen Ireland da ake kira Concern, ta ce “talauci yana kashe mutane 30,000 kowace rana.” Har wa yau mai da mutane bayi da masu son kawo canji suka yi ta kokawa da shi yana nan daram. “Bayi da suke raye a yau sun fi dukan mutane da aka sace daga Afirka a zamanin fataucin bayi a tekun Atilantika,” in ji littafin nan Disposable People—New Slavery in the Global Economy.

Menene ya wargaza ƙoƙarce-ƙoƙarcen da mutane suke yi na kawo cikakken canji? Shin iko ne kawai na masu arziki da masu iko, ko kuma ya ƙunshi wani abu ne?

Abubuwan da Ke Hana Canji

In ji Kalmar Allah, babban mahani ga ƙoƙarce-ƙoƙarcen mutum ya canja duniya ta zama da adalci shi ne Shaiɗan Iblis. Manzo Yahaya ya gaya mana cewa “duniya duka kuwa tana hannun Mugun.” (1 Yahaya 5:19) Hakika, a yanzu haka, Shaiɗan yana ‘yaudarar dukkan duniya.’ (Wahayin Yahaya 12:9) In ba an kawar da muguwar rinjayarsa ba, za a ci gaba da samun mutane da suka fuskanci bala’i da rashin adalci. Menene ya kawo wannan yanayi na baƙin ciki?

Iyayenmu na farko, Adamu da Hauwa’u, an ba su duniya da aka tsara ta ta zama aljanna kuma ta zama gida ga dukan ’yan adam, duniya mai “kyau ƙwarai.” (Farawa 1:31) Menene ya canja abubuwa? Shaiɗan ne ya canja. Ya ƙalubalanci ikon da Allah yake da shi na kafa dokar da mata da maza ya kamata su bi. Ya ce yadda Allah yake sarauta ba shi da adalci. Ya rinjayi Adamu da Hauwa’u su bi rayuwa ta ’yanci saboda su zaɓa wa kansu abin da yake mai kyau da marar kyau. (Farawa 3:1-6) Zunubi da ajizanci sun kasance mahani na biyu ga ƙoƙarce-ƙoƙarcen mutum ya kafa duniya mai adalci.—Romawa 5:12.

Me Ya Sa Ya Ƙyale Hakan?

‘Me ya sa Allah ya ƙyale zunubi da ajizanci su taso?’ wasu za su yi tambaya. ‘Me ya sa bai yi amfani da ikonsa marar iyaka ya kawar da ’yan tawayen ya yi wasu ba?’ Wannan kamar dai hanya ce mai sauƙi na magance matsalar. Amma kuma, yin amfani da iko ya sa an yi wata tambaya mai muhimmanci. Ba gaskiya ba ne cewa nuna iko shi ne babban matsalar matalauta da waɗanda aka yi wa danniya a duniya? Idan wani mai iko ya yi amfani da ikonsa wajen kashe duk wani mutumin da bai yarda da ra’ayinsa ba, hakan ba ya sa mutane masu zuciyar kirki su yi tambaya?

Domin ya tabbatar wa mutane masu zuciyar kirki cewa shi ba mai mugunta ba ne da ikonsa, Allah ya zaɓi ya ƙyale Shaiɗan da kuma mutane da suka yi tawaye su sami ’yanci daga dokokin Allah da kuma mizanansa’na wani ɗan lokaci kawai. Lokaci zai tabbatar da cewa yadda Allah yake sarauta shi ne kawai hanyar da ta dace. Zai nuna cewa dukan wani abin da ya hana mu domin lafiyarmu ce. Hakika, mummunan sakamako na tawaye ga sarautar Allah ya riga ya nuna cewa hakan gaskiya ne. Kuma ya nuna cewa Allah yana da kyakkyawan dalili na yin amfani da ikonsa mai girma wajen kawar da dukan mugunta sa’ad da ya zaɓi ya yi haka. Ba da jimawa ba hakan zai kasance.—Farawa 18:23-32; Maimaitawar Shari’a 32:4; Zabura 37:9, 10, 38.

Har sai Allah ya saka hannu, za mu kasance cikin tsari marar adalci, muna “nishi, na shan azaba kuma irin ta mai naƙuda.” (Romawa 8:22) Duk ƙoƙarin da muka yi mu sake abubuwa, ba za mu iya kawar da Shaiɗan ba, ko kuma mu kawar da ajizanci wanda shi ne tushen dukan wahala da muke fuskanta. Hakika magance sakamakon zunubi da muka gada daga wurin Adamu ya fi ƙarfinmu.—Zabura 49:7-9.

Yesu Kristi Zai Kawo Canji na Dindindin

Hakan yana nufi ne cewa babu wani abin da za a iya yi? A’a. An ba wani da ya fi mutum iko ƙwarai, hakkin canza abubuwa dindindin. Wanene wannan? Yesu Kristi ne. An kwatanta shi a Littafi Mai Tsarki da Shugaba da kuma Mai Ceton ’yan adam.—Ayyukan Manzanni 5:31.

A yanzu yana jiran ‘lokaci’ ne ya yi. (Wahayin Yahaya 11:18) Menene ainihi zai yi? Zai “sabunta dukkan abubuwa da Allah ya faɗa tun zamanin dā ta bakin annabawansa tsarkaka.” (Ayyukan Manzanni 3:21) Alal misali Yesu zai “ceci matalauta waɗanda suka yi kira gare shi, da waɗanda suke da bukata, da waɗanda ba a kula da su. . . . Yakan cece su daga zalunci da kama-karya.” (Zabura 72:12-16) Allah ya yi alkawarin cewa zai “hana yaƙoƙi ko’ina a duniya.” (Zabura 46:9) Ya yi alkawarin cewa: “Ba wanda zai zauna [a duniya mai tsabta] . . . har ya ƙara yin kukan yana ciwo.” Makafi, kurame, guragu, dukan waɗanda suke fama da ciwo, za su sami cikakkiyar lafiya. (Ishaya 33:24; 35:5, 6; Wahayin Yahaya 21:3, 4) Waɗanda ma suka mutu a dā za su amfana. Ya yi alkawarin zai ta da waɗanda suka fuskanci rashin adalci da danniya.—Yahaya 5:28, 29.

Canji da Yesu Kristi zai kawo ba kaɗan ba ne kawai ko kuma na ɗan lokaci. Zai kawar da dukan mahani ga samun duniya mai adalci na gaske. Zai kawar da zunubi da ajizanci zai kuma halaka Shaiɗan Iblis da dukan waɗanda suka bi tafarkinsa na tawaye. (Wahayin Yahaya 19:19, 20; 20:1-3, 10) Matsaloli da kuma wahala da Allah ya ƙyale na ɗan lokaci ba zai sake aukuwa ba, “sau ɗaya kawai zai hallaka.” (Nahum 1:9) Wannan shi ne abin da Yesu yake nufi sa’ad da ya koyar da mu mu yi addu’a domin Mulkin Allah ya zo kuma a aikata nufin Allah ‘a duniya kamar yadda ake yi a sama.’—Matiyu 6:10.

‘Amma’ za ka iya tambaya, ‘shin ba Yesu da kansa ya ce ‘kullum muna tare da gajiyayyu’ ba? Wannan bai nuna ba ne cewa rashin adalci da talauci za su dawwama?’ (Matiyu 26:11) Hakika, Yesu ya ce gajiyayyu za su kasance a kullum. Amma, abin da yake magana a kai da kuma alkawuran Kalmar Allah sun nuna cewa a kullum gajiyayyu za su kasance muddin wannan zamani ya ci gaba da wanzuwa. Ya sani cewa babu wani mutum da zai iya kawar da talauci da rashin adalci. Ya kuma sani cewa shi zai canja dukan waɗannan. Ba da daɗewa ba zai kawo sabon zamani, ‘sababbin sammai da sabuwar duniya’ inda azaba, ciwo, talauci, mutuwa ba za su kasance ba.—2 Bitrus 3:13; Wahayin Yahaya 21:1.

“Kada Kuwa Ku Daina Yin Alheri”

Wannan yana nufi ne cewa babu amfanin taimaka wa wasu? Ko kaɗan. Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu mu taimaki wasu sa’ad da suke fuskantar matsaloli da masifu. Sarki Sulemanu ya rubuta: “Ka yi wa masu bukata alheri a duk lokacin da kake iyawa.” (Karin Magana 3:27) Manzo Bulus ya aririta: “Kada kuwa ku daina yin alheri da gudunmawa.”—Ibraniyawa 13:16.

Yesu Kristi da kansa ya ƙarfafa mu mu yi iyaka ƙoƙarin mu mu taimaki wasu. Ya ba da kwatanci na Basamariye wanda ya sami mutumin da ɓarayi suka yi wa duka suka yi wa kwace. Yesu ya ce, “sai tausayi ya kama” Basamariyen, ya yi amfani da dukiyarsa ya ɗaure raunin mutumin da ɓarayi suka yi wa duka kuma ya taimake shi ya farfaɗo daga jinyarsa. (Luka 10:29-37) Wannan Basamariye mai tausayi bai canja duniya ba, amma ya canja rayuwar wani mutum ƙwarai. Muna iya yin haka.

Amma, Yesu zai yi fiye da canja rayuwar mutane kalilan. Hakika zai iya kawo canji kuma zai yi hakan ba da daɗewa ba. Sa’ad da ya yi haka, mutane da suka fuskanci rashin adalci za su kyautata rayuwarsu kuma su more zaman lafiya da kwanciyar rai.—Zabura 4:8; 37:10, 11.

Sa’ad da muke jiran wannan ya faru, kada mu yi jinkirin yin dukan abin da za mu iya, a ruhaniya ko a zahiri, “mu kyautata” wa waɗanda suka fuskanci matsaloli na wannan duniyar marar adalci.—Galatiyawa 6:10.

[Hotuna a shafi na 5]

Florence Nightingale ta kawo canji ƙwarai ga aikin nas

[Inda aka Dauko]

Courtesy National Library of Medicine

[Hotuna a shafi na 7]

Mabiyan Kristi sun yi wa wasu alheri

[Inda Aka Ɗauko Hoto da ke shafi na 4]

The Star, Johannesburg, S.A.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba