Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • bhs babi na 3 pp. 29-39
  • Me Ya Sa Allah Ya Halicci Mutane?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Me Ya Sa Allah Ya Halicci Mutane?
  • Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Karanta a Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ABOKIN GĀBAN ALLAH
  • WANE NE YAKE MULKIN DUNIYA?
  • TA YAYA ZA A HALAKA DUNIYAR SHAIƊAN?
  • SABUWAR DUNIYA TA KUSA!
  • Me Ya Sa Muke Shan Wahala Sosai?
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Wasu Sun Fi Mu Matsayi
    Ka Koya Daga Wurin Babban Malami
  • Minene Nufin Allah ga Duniya?
    Menene Allah Yake Bukata a Garemu?
  • Yaya Rayuwa Take a Lambun Adnin?
    Ka Saurari Allah Don Ka Rayu Har Abada
Dubi Ƙari
Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
bhs babi na 3 pp. 29-39

BABI NA UKU

Me Ya Sa Allah Ya Halicci Mutane?

1. Me ya sa Allah ya halicci mutane?

AKWAI dalili mai kyau da ya sa Allah ya halicci mutane. Ya halicci Adamu da Hawwa’u don su kasance cikin aljanna. Allah ya halicce su ne don su haifi yara da lura da dabbobi kuma su mai da dukan duniya aljanna.—Farawa 1:28; 2:8, 9, 15; ka duba Ƙarin bayani na 6.

2. (a) Ta yaya muka san cewa Allah zai cika nufinsa? (b) Waɗanne irin mutane ne Littafi Mai Tsarki ya ce za su zauna a duniya har abada?

2 Kana ganin zai yiwu mu yi rayuwa a aljanna kuwa? Jehobah ya ce: “Zan aikata dukan abin da na yi niyyar yi.” (Ishaya 46:9-11; 55:11) Babu shakka, Allah zai cika nufinsa kuma babu wanda zai hana shi. Jehobah ya ce da manufa mai kyau ya halicci duniya. Bai halicce ta “wofi ba.” (Ishaya 45:18) Yana son mutane su zauna a cikinta. Waɗanne irin mutane ne Allah yake so su zauna a duniya kuma na tsawon wane lokaci? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Masu-adalci [ko masu biyayya] za su gāji ƙasan, su zauna a cikinta har abada.”—Zabura 37:29; Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4.

3. Da yake mutane suna ciwo da kuma mutuwa, hakan ya sa mu yi wace tambaya?

3 Amma a yau mutane suna ciwo kuma suna mutuwa. A wurare da yawa, mutane suna tayar da hankali da kuma kashe-kashe. Hakika, wannan ba shi ne dalilin da ya sa Allah ya halicci mutane ba. To, mene ne ya jawo hakan kuma me ya sa? Littafi Mai Tsarki ne kaɗai ya ba da amsar.

ABOKIN GĀBAN ALLAH

4, 5. (a) Wane ne ya yi wa Hawwa’u magana ta bakin maciji? (b) Ta yaya mutumin kirki yakan zama ɓarawo?

4 Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa Allah yana da abokin gāba “wanda ana ce da shi Iblis da Shaiɗan.” Shaiɗan ya yi amfani da maciji don ya yi wa Hawwa’u magana a lambun Adnin. (Ru’ya ta Yohanna 12:9; Farawa 3:1) Ya yi wayo don Hawwa’u ta ga kamar macijin ne yake mata magana.—Ka duba Ƙarin bayani na 7.

5 Shin Allah ne ya halicci Shaiɗan Iblis? A’a. Wani mala’ika da ke tare da Allah a sama sa’ad da Allah ya halicci Adamu da Hawwa’u ne ya canja halinsa ya zama Iblis. (Ayuba 38:4, 7) Ta yaya hakan ya faru? Yaya mutumin kirki yakan zama ɓarawo tun da ba a haife shi da yin sata ba? Hakan na faruwa domin yana kwaɗayin kayan wani. Sai ya ci gaba da yin irin wannan tunani marar kyau, sa’ad da ya sami zarafi, sai ya yi sata kuma hakan ya sa ya zama ɓarawo.—Karanta Yaƙub 1:13-15; ka duba Ƙarin bayani na 8.

6. Ta yaya wani mala’ika ya zama abokin gāban Allah?

6 Ga abin da ya faru da wannan mala’ikan. Bayan da Allah ya halicci Adamu da Hawwa’u, ya gaya musu su haifi yara kuma su “mamaye duniya.” (Farawa 1:27, 28) Wataƙila wannan mala’ikan ya yi tunani, ‘Dukan waɗannan mutanen za su iya bauta min maimakon Jehobah!’ Da ya ci gaba da yin wannan tunanin, sai sha’awarsa ta daɗa tsanani. Wannan mala’ikan ya so mutane su bauta masa. Don haka, ya yi wa Hawwa’u ƙarya kuma ya yaudare ta. (Karanta Farawa 3:1-5.) Wannan abin da ya yi ne ya sa ya zama Shaiɗan Iblis, wato abokin gāban Allah.

7. (a) Me ya sa Adamu da Hawwa’u suka mutu? (b) Me ya sa muke tsufa da kuma mutuwa?

7 Adamu da Hawwa’u sun yi rashin biyayya ga Allah kuma suka ci ’ya’yan itacen. (Farawa 2:17; 3:6) Sun yi zunubi don haka, sun mutu kamar yadda Jehobah ya faɗa. (Farawa 3:17-19) ’Ya’yan Adamu da Hawwa’u sun gāji zunubi kuma hakan ya sa suna mutuwa. (Karanta Romawa 5:12.) Ga wani misalin da zai taimaka mana mu fahimci dalilin da ya sa ’ya’yan Adamu da Hawwa’u suka zama masu zunubi. Idan ka gasa burodi a gwangwanin da ya lanƙwashe, hakika, burodin zai kasance da alamar lanƙwasar. A lokacin da Adamu ya yi rashin biyayya, ya zama mai zunubi. Da yake mu ’ya’yan Adamu ne, dukanmu muna ɗauke da “lanƙwasa” ko kuma zunubi kamar Adamu. Kuma da yake dukanmu masu zunubi ne, muna tsufa da kuma mutuwa.—Romawa 3:23; ka duba Ƙarin bayani na 9.

8, 9. (a) Mene ne Shaiɗan ya so Adamu da Hawwa’u su gaskata da shi? (b) Me ya sa Jehobah bai halaka Shaiɗan da Adamu da kuma Hawwa’u nan da nan ba?

8 Shaiɗan ya yi tawaye a lokacin da ya ruɗi Adamu da Hawwa’u su yi wa Jehobah rashin biyayya. Ya so Adamu da Hawwa’u su yarda cewa Jehobah maƙaryaci ne da kuma mugun sarki da ba ya so su ji daɗin rayuwa. Abin da Shaiɗan ya faɗa yana nufin cewa mutane ba sa bukatar ja-gorancin Allah, don haka, Adamu da Hawwa’u za su iya tsai da shawara game da nagarta da mugunta da kansu. Me Jehobah zai yi? Zai iya halaka Adamu da Hawwa’u da kuma Shaiɗan don a daina tawayen kuma a nuna wa kowa cewa Shaiɗan maƙaryaci ne. Amma bai yi hakan ba.

9 Saboda haka, Jehobah bai halaka ’yan tawayen nan da nan ba. Maimakon haka, ya bar mutane su yi sarauta da kansu. Me ya sa? Don hakan zai sa mutane su san cewa Shaiɗan maƙaryaci ne kuma Jehobah ne ya san abin da ya fi dacewa da ’yan Adam. Za mu sami ƙarin bayani game da hakan a Babi na 11. Amma mene ne ra’ayinka game da shawarar da Adamu da Hawwa’u suka yanke? Ya dace su gaskata da abin da Shaiɗan ya faɗa kuma su yi wa Allah tawaye? Allah ya ba Adamu da Hawwa’u duk wani abu da suke bukata. Ya sa su yi rayuwa mai kyau, ya ba su wurin zama mai kyau kuma ya ba su aikin da za su ji daɗin yi. Amma Shaiɗan bai taɓa yi musu wani abu mai kyau ba. Me za ka yi da a ce kana wurin?

10. Wace shawara ce ya kamata dukanmu mu yanke?

10 Dukanmu a yau muna da shawara da ya kamata mu yanke kuma rayuwarmu ta dangana ga wannan shawarar. Za mu iya zaɓa mu yi biyayya ga Jehobah Sarkinmu kuma mu nuna cewa Shaiɗan maƙaryaci ne. Ko kuma mu zaɓi Shaiɗan a matsayin sarkinmu. (Zabura 73:28; karanta Misalai 27:11.) Mutane kaɗan ne kawai suke yi wa Allah biyayya a yau. Hakika, ba Allah ba ne yake sarautar duniya. To, waye ne yake sarautar tun da ba Allah ba?

WANE NE YAKE MULKIN DUNIYA?

Shaidan ya yi wa Yesu tayin dukan gwamnatoci ko mulkokin duniya

Shin da Shaiɗan zai yi wa Yesu alkawarin dukan mulkokin duniyar nan idan ba nasa ba ne?

11, 12. (a) Me muka koya daga gwajin da Shaiɗan ya yi wa Yesu? (b) Waɗanne ayoyi ne suka nuna cewa Shaiɗan ne yake mulki da duniya?

11 Yesu ya san wanda yake mulki da wannan duniyar. Akwai lokacin da Shaiɗan ya nuna “masa dukan mulkokin duniya da ɗaukakarsu.” Sai Shaiɗan ya yi wa Yesu alkawari cewa: ‘Dukan waɗannan zan ba ka, idan ka fāɗi, [ko rusuna] ka yi mani sujada.’ (Matta 4:8, 9, Littafi Mai Tsarki; Luka 4:5, 6) Ka tambayi kanka, ‘Da a ce waɗannan mulkokin ba na Shaiɗan ba ne, da zai ce zai ba Yesu ne?’ A’a. Dukan mulkokin wannan duniyar na Shaiɗan ne.

12 Za ka iya yin tunani: ‘Yaya za a ce Shaiɗan ne yake mulkin wannan duniyar? Ba Jehobah Maɗaukaki ba ne ya halicci sama da ƙasa?’ (Ru’ya ta Yohanna 4:11) Hakika, Allah ne ya halicci sama da ƙasa, amma Yesu ya kira Shaiɗan “mai-mulkin wannan duniya.” (Yohanna 12:31; 14:30; 16:11) Manzo Bulus ya kira Shaiɗan Iblis “allah na wannan zamani.” (2 Korintiyawa 4:3, 4) Kuma manzo Yohanna ya ce “duniya duka kuwa tana kwance cikin Shaitan.”—1 Yohanna 5:19.

TA YAYA ZA A HALAKA DUNIYAR SHAIƊAN?

13. Me ya sa muke bukatar sabuwar duniya?

13 Wannan duniyar tana daɗa lalacewa. Muna ganin yaƙe-yaƙe da cin hanci da kuma munafunci a ko’ina. ’Yan Adam ba za su iya kawar da waɗannan matsalolin ba kome ƙoƙarinsu. Amma nan ba daɗewa ba, Allah zai halaka wannan muguwar duniyar a yaƙin Armageddon kuma zai mai da ita aljanna.—Ru’ya ta Yohanna 16:14-16; ka duba Ƙarin bayani na 10.

14. Waye Allah ya zaɓa ya zama Sarki a Mulkinsa? Wane annabci ne Littafi Mai Tsarki ya yi game da Yesu?

14 Jehobah ya zaɓi Yesu Kristi ya zama Sarki a gwamnatin da ya kafa a sama. Littafi Mai Tsarki ya yi annabci shekaru da yawa cewa Yesu zai yi sarauta a matsayin “Sarkin Salama” kuma sarautarsa ba ta da iyaka. (Ishaya 9:6, 7) Yesu ya koya wa mabiyansa su yi addu’a game da mulkin suna cewa: “Mulkinka shi zo. Abin da kake so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda ake yinsa cikin sama.” (Matta 6:10) A Babi na 8, za mu koyi yadda Mulkin Allah zai sauya gwamnatocin ’yan Adam. (Karanta Daniyel 2:44.) Bayan hakan, Mulkin Allah zai sa duniya ta zama aljanna.—Ka duba Ƙarin bayani na 11.

SABUWAR DUNIYA TA KUSA!

Mutane suna waka da kade-kade kuma suna jin dadin rayuwa a aljanna

15. Mece ce “sabuwar duniya”?

15 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Muna sauraron sababbin sammai da sabuwar duniya, inda adalci yake zaune.” (2 Bitrus 3:13; Ishaya 65:17) A wani lokaci, idan Littafi Mai Tsarki ya ambaci “duniya,” yana magana ne game da mutane. (Farawa 11:1) Saboda haka, “sabuwar duniya” tana nufin dukan mutanen da suka yi wa Allah biyayya kuma ya albarkace su.

16. Wace lada ce Allah zai ba waɗanda za su zauna a aljanna a duniya, kuma me ya kamata mu yi don mu sami wannan ladar?

16 Yesu ya yi alkawari cewa waɗanda za su zauna a aljanna a duniya za su rayu “har abada.” (Markus 10:30) Me ya kamata mu yi don mu sami wannan ladar? Don Allah ka karanta Yohanna 3:16 da kuma 17:3 don ka sami amsar. Bari mu ga yadda Littafi Mai Tsarki ya kwatanta irin rayuwar da za a yi a Aljanna.

17, 18. Ta yaya muka san cewa za a kasance da salama a ko’ina a duniya kuma za mu sami tsaro?

17 Za a kawo ƙarshen mugunta da yaƙe-yaƙe da yin laifi da kuma zalunci. Ba za a sake ganin mugayen mutane a duniya ba. (Zabura 37:10, 11) Allah zai kawo ƙarshen ‘yaƙi har iyakar duniya.’ (Zabura 46:9; Ishaya 2:4) Duniya za ta cika da mutanen da suke son Allah kuma suna masa biyayya. Salama za ta kasance har abada.—Zabura 72:7.

18 Bayin Jehobah za su sami tsaro. Allah yana kāre Isra’ilawa a zamanin dā a duk lokacin da suka yi masa biyayya kuma suna samun kwanciyar hankali a sakamakon haka. (Levitikus 25:18, 19) Babu wani mutum ko wani abin da zai tsoratar da mu a Aljanna. Za mu sami tsaro a kowane lokaci.—Karanta Ishaya 32:18; Mikah 4:4.

19. Me ya sa muka tabbata cewa za a yi yalwar abinci a sabuwar duniya?

19 Za a yi yalwar abinci. Za a ‘sami hatsi mai yawa a ƙasar, . . . amfanin gona ya cika tuddai.’ (Zabura 72:16, LMT) Jehobah, “Allahnmu, za ya albarkace mu,” kuma ‘ƙasa za ta ba da amfaninta.’—Zabura 67:6.

20. Ta yaya muka san cewa duniya za ta zama aljanna?

20 Dukan duniya za ta zama aljanna. Mutane za su kasance da gidaje da gonaki masu kyau. (Karanta Ishaya 65:21-24; Ru’ya ta Yohanna 11:18.) Duniya za ta yi kyau kamar yadda lambun Adnin yake a dā. Jehobah zai riƙa biyan bukatunmu. Littafi Mai Tsarki ya ce game da Jehobah: “Kana buɗe hannunka, kana biya wa kowane mai-rai muradinsa.”—Zabura 145:16.

21. Ta yaya muka san cewa mutane da dabbobi za su kasance da salama?

21 Za a sami salama tsakanin mutane da dabbobi. Dabbobi ba za su ji wa mutane rauni ba. Yara ƙanana ba za su ji tsoron dabbobi masu lahani a yau ba.—Karanta Ishaya 11:6-9; 65:25.

22. Mene ne Yesu zai yi wa mutanen da suke ciwo?

22 Ba wanda zai yi ciwo. A lokacin da Yesu yake duniya, ya warƙar da mutane da yawa. (Matta 9:35; Markus 1:40-42; Yohanna 5:5-9) Amma a matsayinsa na Sarkin Mulkin Allah, Yesu zai warƙar da kowa. Babu wanda zai sake ce: “Ina ciwo.”—Ishaya 33:24; 35:5, 6.

23. Mene ne Allah zai yi wa mutanen da suka rasu?

23 Za a ta da mutanen da suka rasu. Allah ya yi alkawari cewa zai ta da miliyoyin mutanen da suka mutu. “Za a yi tashin matattu, na masu adalci da na marasa adalci.”—Karanta Yohanna 5:28, 29; Ayyukan Manzanni 24:15.

24. Yaya kake gani rayuwa za ta kasance a Aljanna?

24 Kowannenmu zai iya zaɓan abin da zai yi. Za mu iya koya game da Jehobah kuma mu bauta masa ko kuma mu yi abin da muka ga dama. Idan muka zaɓa mu bauta wa Jehobah, za mu ji daɗin rayuwa a nan gaba. A lokacin da wani mutum ya gaya wa Yesu ya tuna da shi sa’ad da za a ta da matattu a nan gaba, Yesu ya ce masa: Za ka kasance “tare da ni cikin Aljanna.” (Luka 23:43) Bari mu koya game da Yesu Kristi da kuma yadda zai sa nufin Allah ya cika.

TAƘAITAWA

GASKIYA TA 1: AKWAI DALILIN DA YA SA ALLAH YA HALICCE MU

“Masu-adalci za su gāji ƙasan, su zauna a cikinta har abada.”—Zabura 37:29

Me ya sa Allah ya halicci mutane?

  • Farawa 1:28

    Allah ya so iyalai su mayar da duniya aljanna kuma su kula da dabbobi.

  • Ishaya 46:9-11; 55:11

    Allah zai yi duk wani abin da ya nufa kuma babu abin da zai iya hana shi.

GASKIYA TA 2: ME YA SA RAYUWA TAKE DA WUYA?

“Duniya duka kuwa tana kwance cikin Shaitan.”—1 Yohanna 5:19

Wane ne yake mulkin wannan duniyar?

  • Yohanna 12:31

    Yesu ya kira Shaiɗan mai mulkin duniya.

  • Yaƙub 1:13-15

    Shaiɗan ya yi kwaɗayin abin da ba nasa ba.

  • Farawa 2:17; 3:1-6

    Shaiɗan ya rinjayi Hawwa’u, sai ita da mijinta Adamu suka yi tawaye da Allah, daga baya, dukansu suka mutu.

  • Romawa 3:23; 5:12

    Muna mutuwa don mun gāji zunubi daga Adamu.

  • 2 Korintiyawa 4:3, 4

    Shaiɗan yana rinjayar mutane.

GASKIYA TA 3: MULKIN ALLAH ZAI MAGANCE MATSALAR

‘Mulkinka ya zo. Abin da kake so, a yi shi, cikin duniya.’—Matta 6:10

Wane mataki ne Jehobah zai ɗauka?

  • Daniel 2:44

    Gwamnatin Allah zai sauya dukan gwamnatocin duniya.

  • Ru’ya ta Yohanna 16:14-16

    Allah zai yi amfani da yaƙin Armageddon wajen halaka wannan muguwar duniya.

  • Ishaya 9:6, 7

    Jehobah ya zaɓi Yesu ya zama Sarki a gwamnatin da ya kafa a sama. Yesu zai yi sarauta bisa duniya.

GASKIYA TA 4: MULKIN ALLAH ZAI SA DUNIYA TA ZAMA ALJANNA

“Kana buɗe hannunka, kana biya wa kowane mai-rai muradinsa.”—Zabura 145:16

Mene ne Mulkin Allah zai yi mana?

  • Zabura 46:9

    Za a kawo ƙarshen yaƙe-yaƙe da mugunta da kuma zalunci.

  • Ishaya 32:18; 65:21-24

    A sabuwar duniya, mutane za su samu gidaje masu kyau da lambuna kuma za su zauna cikin salama.

  • Zabura 72:16

    Za a yi yalwar abinci.

  • Ishaya 11:6-9

    Za a sami salama tsakanin mutane da dabbobi.

  • Ishaya 33:24; Ayyukan Manzanni 24:15

    Babu wanda zai yi ciwo kuma za a ta da waɗanda suka mutu.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba