Ka Riƙe Farin Cikinka Cikin Hidimar Jehovah
“Ku yi farinciki cikin Ubangiji kullayaumi: sai in sake cewa, Ku yi farinciki.”—FILIBBIYAWA 4:4.
1, 2. Ta yaya ne wani ɗan’uwa da iyalinsa suka iya riƙe farin cikinsu duk da hasarar kome da suka yi?
JAMES, Kirista mai shekara 70 yana zama a Saliyo, ya yi aiki sosai duk rayuwarsa. Ka yi tunanin farin cikinsa yayin da a ƙarshe ya yi ajiyar kuɗin da suka isa ya sayi gida mai ɗaki huɗu! Amma bayan da James da iyalinsa suka ƙaura zuwa gidan, aka fara yaƙin basasa a ƙasar, sai aka ƙona gidansu ƙurmus. Suka yi hasarar gidansu, amma ba su yi rashin farin cikinsu ba. Me ya sa?
2 James da iyalinsa suka sa zuciyarsu sosai, ba a kan abin da suka yi hasararsa ba, amma abin da ya rage. James ya yi bayani: “Ko a lokacin bala’i ma muna yin taronmu, mu yi karatun Littafi Mai Tsarki, mu yi addu’a tare, kuma mu raba abin da muke da shi tare da wasu. Mun iya riƙe farin cikinmu domin dangantakarmu mai kyau da Jehovah.” Ta wurin yin tunanin abubuwa masu kyau da suke da shi, wanda mafi girma cikinsu dangantakarsu ce da Jehovah, shi ya sa waɗannan Kiristoci suka ci gaba “cikin salama.” (2 Korinthiyawa 13:11) Hakika, yanayinsu na wahala ba shi da sauƙi a jimre masa. Amma ba su daina yin farin ciki wajen Jehovah ba.
3. Ta yaya wasu Kiristoci na farko suka riƙe farin cikinsu?
3 Kiristoci na farko sun fuskanci gwaji da ke kama da wanda James da iyalinsa suka fuskanta. Duk da haka, manzo Bulus ya rubuta kalmomin nan wa Kiristoci Ibraniyawa: “Da farin ciki kuka sha wason dukiyarku.” Sai Bulus ya bayyana dalilin farin cikinsu: “Kuna sane ku da kanku kuna da dukiya mafiya kyau, matabbaciya kuwa.” (Ibraniyawa 10:34; tafiyar tsutsa tamu ce.) Hakika, waɗancan Kiristoci na ƙarni na farko suna da bege mai ƙarfi. Da tabbaci suna duba gaba don samun wani abu da ba za a waso ba—“rawanin rai” wanda ba ya lalacewa a cikin Mulkin Allah na sama. (Ru’ya ta Yohanna 2:10) A yau, begenmu na Kirista—na sama ko na duniya ne—zai taimake mu mu riƙe farin cikinmu ko idan mun fuskanci wahala.
“Kuna Murna Cikin Bege”
4, 5. (a) Me ya sa shawarar Bulus ta yin “murna cikin bege” take kan lokaci wa Romawan? (b) Menene zai iya sa Kirista ya yi sakaci da begensa?
4 Manzo Bulus ya ƙarfafa wa ’yan’uwa masu bi a Roma su yi “murna cikin bege” na rai madawwami. (Romawa 12:12) Gargaɗi ne na kan lokaci ga Romawan. Shekara goma babu kaɗan bayan da Bulus ya rubuta musu, suka shiga tsanani na ƙwarai, kuma aka tsananta wasu zuwa mutuwa bisa dokar Daula Nero. Bangaskiyarsu cewa Allah zai ba su rawanin rai babu shakka ta kiyaye su cikin wahalarsu. Mu a yau kuma fa?
5 Mu Kiristoci a yau ma, za mu zaci a tsananta mana. (2 Timothawus 3:12) Ƙari ga haka, ‘lokaci da zarafi’ suna samun mu duka. (Mai-Wa’azi 9:11) Haɗari zai iya ɗaukar ran wani da muke ƙauna. Wani ciwo yana iya jawo mutuwar wani iyaye ko kuma aboki na kurkusa. Sai fa mun sa begen Mulkin ya zama abin da muka mai da hankali a kai kullum, za mu iya shan haɗari a ruhaniya idan irin gwajin nan suka auku. Zai yi kyau mu tambayi kanmu, ‘Ni ina “murna cikin bege” kuwa? Sau nawa ne nake ɗaukan lokaci don na yi bimbini a kansa? Aljanna da take zuwa gaskiya ce a gare ni? Ina tsammanin zama a wajen kuwa? Ina da marmarin ganin ƙarshen wannan tsarin abubuwa kamar yadda na yi a farkon da na koyi gaskiya?’ Wannan tambaya ta ƙarshe tana bukatar tunani sosai. Me ya sa? Domin idan muna da lafiya, muna rayuwa da kyau, muna zama a ɓangaren duniya da babu yaƙi, babu karancin abinci, ko bala’i, za mu iya—na ɗan lokaci—yi sakaci a ganin ya kyautu ƙwarai sabuwar duniya ta Allah ta zo.
6. (a) Yayin da Bulus da Sila suka sha ƙunci, a kan me suke tunani? (b) Ta yaya misalin Bulus da Sila zai ƙarfafa mu a yau?
6 Bulus ya sake yi wa Romawa gargaɗi su yi “haƙuri cikin ƙunci.” (Romawa 12:12) Bulus ba baƙon ƙunci ba ne. Akwai lokaci da ya ga wani mutum cikin wahayi ya gayyace shi ya “ƙetaro zuwa Makidoniya” ya taimaki mutane a wurin su koyi game da Jehovah. (Ayukan Manzanni 16:9) Domin haka, Bulus, tare da Luka, Sila, da Timothawus, suka tafi Turai. Menene yake jiran waɗannan masu wa’azi a ƙasashen waje masu himma? Ƙunci! Bayan sun yi wa’azi cikin birnin Filibbi na Makidoniya, aka yi wa Bulus da Sila bulala kuma aka jefa su a fursuna. A bayyane yake cewa, wasu mazauna Filibbi ba kawai sun ƙi saƙon Mulkin ba—sun yi adawa ƙwarai. Wannan aukuwan ya sa masu wa’azi na ƙasashen wajen su rasa farin cikinsu ne? A’a. Bayan an yi musu dūka kuma an jefa su a fursuna, “wajen tsakiyar dare Bulus da Sila suna addu’a suna rera waƙa ga Allah.” (Ayukan Manzanni 16:25, 26; tafiyar tsutsa tamu ce.) Babu shakka, zafin dūka bai ba Bulus da Sila farin ciki ba, amma ba abin da masu wa’azi na ƙasashen wajen nan biyu suka sa zuciyarsu a kai ba ke nan. Tunaninsu a kan Jehovah ne da kuma hanyoyin da yake amfani da shi wajen yi musu albarka. Ka ci gaba da farin ciki a ‘jimrewa cikin ƙunci,’ misalai masu kyau ne Bulus da Sila ga ’yan’uwa da suke a Filibbi da kuma wasu wurare.
7. Me ya sa addu’o’inmu ya kamata su haɗa da furcin godiya?
7 Bulus ya rubuta: “Kuna lizima cikin addu’a.” (Romawa 12:12) Kana yin addu’a lokacin da ka ke da alhini? A kan me ka ke addu’a? Wataƙila ka ambata wani abu ainihi kuma ka roƙi taimakon Jehovah. Amma kuma za ka iya haɗawa da furcin godiya domin albarkar da ka ke morewa. Idan matsaloli sun taso, ka yi bimbini a kan nagarta ta Jehovah a yadda yake bi da mu yana taimakonmu mu yi “murna cikin bege.” Dauda, wanda rayuwarsa ya cika da matsaloli, ya rubuta: “Ya Ubangiji Allahna, ayyuka masu-ban al’ajabi, waɗanda ka yi, suna dayawa, duk da tunaninka waɗanda sun nufo wajenmu: ba su lissaftuwa a gabanka; ko da ni ke so in bayyana su in bada labarinsu, sun fi gaban lissafi.” (Zabura 40:5) Idan mu, kamar Dauda muna bimbini a kai a kai game da albarkar da muke samu daga Jehovah, zai yi wuya mu yi rashin farin ciki.
Kasance da Ruhu Mai Kyau
8. Menene ke taimakon Kirista ya kasance da farin ciki yayin da yake shan tsanani?
8 Yesu ya ƙarfafa mabiyansa su kasance da ruhu mai kyau yayin da sun iske jaraba dabam dabam. Ya ce: “Masu-albarka ne ku lokacinda ana zarginku, ana tsananta maku, da ƙarya kuma ana ambatonku da kowace irin mugunta, sabili da ni.” (Matta 5:11) Wane dalili muke da shi na farin ciki cikin irin yanayin nan? Iya jimre wa adawa tabbaci ne cewa ruhun Jehovah yana tare da mu. Manzo Bitrus ya gaya wa ’yan’uwa Kirista na zamaninsa: “Idan kuna shan zargi sabili da sunan Kristi masu-albarka ne ku; domin Ruhu na daraja da Ruhu na Allah yana zaune a kanku.” (1 Bitrus 4:13, 14) Ta wurin ruhunsa, Jehovah zai taimake mu mu jimre kuma, mu riƙe farin cikinmu ya zama sakamakonsa.
9. Menene ya taimake wasu ’yan’uwa su sami dalilan yin farin ciki lokacin da suke cikin kurkuku saboda bangaskiyarsu?
9 Ko idan muna cikin yanayi mafi tsanani, za mu iya kasancewa da dalilin yin farin ciki. Wani Kirista da ake kira Adolf ya shaida wannan. Yana cikin wata ƙasa da aka hana aikin Shaidun Jehovah na shekaru da yawa. Aka kama Adolf da abokanansa kuma aka yi masu hukuncin ɗauri na dogon lokaci domin sun ƙi su shika imaninsu na Littafi Mai Tsarki. Rayuwa cikin fursuna ba shi da sauƙi, amma kamar Bulus da Sila, Adolf da abokansa suna da dalilan yin godiya ga Allah. Abin da suka gani a kurkuku, yadda suka lura ya taimaka a ƙarfafa bangaskiyarsu da kuma gina halaye na Kirista, irinsu ba da kyauta, juyayi, da kuma ƙaunar ’yan’uwanci. Alal misali, idan ɗan kurkuku ya sami wani ƙunshi daga gida, yana raba abin da ke cikinsa da ’yan’uwa masu bi, waɗanda suke ɗaukan cewa waɗannan ƙarin abubuwa daga wajen Jehovah ne, Mai ba da “kowace kyakkyawan kyauta.” Irin halin alherin nan yana kawo farin ciki wa mai bayarwar da kuma masu karɓa. Saboda haka, abin da ake son ya karya bangaskiyarsu ya sa su daɗa ƙarfi a ruhaniya!—Yaƙub 1:17; Ayukan Manzanni 20:35.
10, 11. Yaya wata ’yar’uwa ta bi da tuhuma da aka yi mata babu hutu da tsari a kurkuku na dogon lokaci da ya biyo bayansa?
10 Ella, ita ma wadda take cikin wata ƙasa da aka hana aikin Mulki da daɗewa, an tsare ta domin gaya wa wasu game da begenta na Kirista. Cikin watanni takwas, aka ta yi mata bincike ba hutu. A ƙarshe da aka kawo ta gaban alƙali, aka yi mata ɗaurin shekara goma a kurkukun da babu wasu masu bauta wa Jehovah. Shekararta 24 ne kawai a lokacin.
11 Hakika, Ella ba ta da zaton za ta ƙarasa yawancin ƙuruciyarta cikin kurkuku. Tun da ba za ta iya canja yanayinta ba, sai ta canja ra’ayinta. Daidai kuwa, ta fara ɗaukan kurkukun ya zama yankinta na yin wa’azi. Ta ce: “Da akwai aikin wa’azi da yawa da za a yi, har shekaru suna wucewa da sauri sauri.” Bayan fiye da shekara biyar, aka sake kiran Ella don a tuhume ta. Da suka ga cewa kurkuku bai karya bangaskiyarta ba, masu yi mata binciken suka ce mata: “Ba za mu iya sake ki ba; ba ki canja ba.” Ella ta faɗa da ƙarfi: “Amma ai na canja! Yanzu ina da hali mai kyau fiye da lokacin da na shiga kurkuku, kuma bangaskiyata ta fi dā ƙarfi!” Sai kuma ta daɗa: “Idan ba ku a son ku sake ni, zan zauna har sai Jehovah ya ga ya dace ya cece ni.” Tsarewa na shekara biyar da rabi bai hana Ella farin cikinta ba! Ta koya ta gamsu da kowane yanayin da ta samu kanta ciki. Za ka iya koya wani abu daga misalinta?—Ibraniyawa 13:5.
12. Menene zai iya kawo salamar zuci ga Kirista cikin yanayi masu wuya?
12 Kada ka ce ai Ella tana da wata kyauta ce ta musamman da ta sa ta fuskanci irin wannan kalubalen. Da take faɗan yadda lokacin tuhumar yake wasu watanni kafin a yanke mata hukunci, Ella ta ce: “Na tuna haƙorana suna rawa, tsoro ya kama ni kamar kanari da ya fāɗa ruwa.” Duk da haka, Ella tana da bangaskiya mai ƙarfi ga Jehovah. Ta koya ta dogara gare shi. (Misalai 3:5-7) Domin haka, Allah ya zama da gaske gare ta fiye da dā. Ta yi bayani: “Duk lokacin da na shiga ɗakin tuhuma, sai na ji wata irin salama ta sauƙo mini. . . . Idan yanayin ya zama na tsoratawa, haka ma salamar za ta ƙaru.” Jehovah ne tushen salamar. Manzo Bulus ya yi bayani: “Kada ku yi alhini cikin kowane abu; amma cikin kowane abu, ta wurin addu’a da roƙo tare da godiya, ku bar roƙe roƙenku su sanu ga Allah. Salama kuwa ta Allah, wadda ta fi gaban ganewa duka, za ta tsare zukatanku da tunaninku cikin Kristi Yesu.”—Filibbiyawa 4:6, 7.
13. Menene ke tabbatar mana cewa idan wahala ta zo mana, za mu sami ƙarfin da za mu jimre da ita?
13 Ella, wadda an sake ta da daɗewa, ta riƙe farin cikinta duk da wahala. Ta yi hakan, ba ta wurin nata ƙarfin ba, amma ta wurin ƙarfi da Jehovah ya ba ta. Daidai yake da manzo Bulus, wanda ya rubuta: “Na gwammace fa in yi fahariya cikin kumamancina, wannan kuwa da farinciki mai-yawa, domin ƙarfin Kristi shi inuwantarda ni. . . . Gama sa’anda ina rashin ƙarfi, sa’annan mai-ƙarfi ni ke.”—2 Korinthiyawa 12:9, 10.
14. Ka ba da misalin yadda Kirista zai iya kasancewa da ra’ayi mai kyau cikin yanayi mai wuya da kuma yadda zai iya samun sakamako.
14 Matsin da ka ke fuskanta a yau zai iya bambanta daga waɗanda muka tattauna a nan. Duk da haka, ko waɗanne iri ne, yana da wuya a jimre da matsi. Alal misali, maigidan aikinka zai fi tuhumar aikin da ka ke yi—fiye da na abokan aikinka da imaninsu ɗaya. Wataƙila ba shi da sauƙi ka nemi sabon aiki. Ta yaya za ka riƙe farin cikinka? Ka tuna da Adolf da abokansa, waɗanda zama cikin kurkuku ya koya musu su gina wasu muhimman halaye. Idan ka yi ƙoƙari na gaske ka gamsar da maigidan aikinka—ko idan yana da “wuya a gamsar” da shi—za ka iya gina halayen nan na Kirista na jimrewa da haƙuri. (1 Bitrus 2:18) Ƙari ga haka, za ka iya zama mai aiki wanda zai daraja nan gaba, haka kuma zai iya buɗe maka hanyar samun wani aiki dabam wata rana. Yanzu bari mu tattauna wasu hanyoyi da za mu iya riƙe farin cikinmu cikin hidimar Jehovah.
Sauƙaƙawa Tana Kaiwa ga Farin Ciki
15-17. Menene wata mata da miji suka koyi zai iya sauƙaƙa matsi, ko da ma ba za su iya guje masa ba gabaki ɗaya?
15 Wataƙila ba za ka iya canja aikin da ka ke yi ba ko wajen aikin, amma kana da fasalolin rayuwanka da za ka iya mallaka. Ka yi la’akari da wannan labarin.
16 Wasu Kirista mata da miji sun gayyaci wani dattijo zuwa gidansu don su ci abinci tare. Yayin da suke gidan da maraicen, ɗan’uwan da ’yar’uwan suka faɗa masa damuwarsu cewa a baya bayan nan matsin rayuwa yana rinjayarsu. Ko da yake suna da aiki na cikakken lokaci da ke cin dukan lokacinsu, ba sa neman wani sabon aiki. Suna damuwa ko za su iya cin gaba cikin yanayin nan.
17 Da suka nemi shawara daga wajen dattijon, ya ce, “Ku sauƙaƙa rayuwarku.” Ta yaya? Matar da mijinta suna ɓad da sa’o’i uku da rabi a tafiya da kuma dawowa daga aiki kowacce rana. Dattijon, da yake ya san su sosai, ya ba su shawarar cewa su ƙaura zuwa kusa da wajen aikinsu, domin su iya rage yawan lokacin da suke amfani da shi a tafiya da kuma dawowa daga wajen aiki kowacce rana. Idan aka rage lokacin, za a iya yin amfani da shi a wasu muhimman abubuwa—ko kuma don a ɗan huta. Idan matsin rayuwa na washe maka farin ciki, me ya sa ba za ka bincika ka ga yadda za ka sauƙaƙa ta wurin yin wasu gyara ba?
18. Me ya sa yake da muhimmanci a yi tunani sosai kafin a tsai da shawarwari?
18 Wata hanya ta rage matsi ita ce yin tunani sosai kafin tsai da shawarwari. Alal misali, wani Kirista ya zaɓi ya gina gida. Ya zaɓi gini mai wuya sosai, ko da ma bai taɓa yin gini ba. Yanzu ya gane cewa da ya guje wa matsaloli da yawa da ya ‘lura da al’amuransa’ kafin ya zaɓi gina irin gidansa. (Misalai 14:15) Wani Kirista ya yarda ya ɗauki hakkin wani aron kuɗi a maɗaɗin wani ɗan’uwa mai bi. Yarjejeniyar ita ce idan wanda ya ari kuɗin bai iya biya ba wanda ya ɗauki hakki ne zai biya. A farko kome na tafiya daidai, amma a kwana a tashi sai wanda ya ari kuɗin bai cika alkawarinsa ba. Sai wanda ya ba da aron kuɗin hankalinsa ya tashi kuma ya ce wanda ya ɗauki hakkin ya biya kuɗin duka. Wannan ya sa matsi sosai a kan mai ɗaukan hakkin. Da an guje ma wannan idan mai ɗaukan hakkin ya yi la’akari da dukan abubuwan da za su iya faruwa kafin ya yarda da ɗaukan hakkin bashin?—Misalai 17:18.
19. A waɗanne hanyoyi ne za mu iya rage gajiya a rayuwarmu?
19 Idan muka gaji, kada mu kammala cewa za mu iya rage matsi da ke kanmu ta samo wa kanmu farin ciki wajen yanke nazarinmu na Littafi Mai Tsarki, wa’azin fage, da kuma zuwan taro. Sam, waɗannan muhimman hanyoyi ne da za mu iya samun ruhu mai tsarki na Jehovah, ’ya’yan farin ciki. (Galatiyawa 5:22) Ayyuka na Kirista kullum suna wartsakarwa kuma ba sa gajiyarwa ainun. (Matta 11:28-30) Lalle ne cewa aikace-aikace ko kuma nishaɗi, ne suke jawo mana gajiya, ba ayyuka ta ruhaniya ba. Yin ƙoƙari mu yi barci da wuri zai iya sa mu ƙarfi. Samun hutu yana taimakawa sosai. N. H. Knorr, wanda ya yi hidima cikin Hukumar Mulki na Shaidun Jehovah har mutuwarsa, yakan gaya ma masu wa’azi na ƙasashen waje: “Idan kuna sanyin gwiwa, abu na farko shi ne ku sami ɗan hutu. Za ku yi mamakin abin da ba ku zata ba, bayan kun sami isashen barci daddare!”
20. (a) Ka taƙaita wasu hanyoyi da za mu iya riƙe farin cikinmu. (b) Waɗanne dalilai za ka iya tunawa da su don yin farin ciki? (Duba akwati a shafi 29.)
20 Kiristoci suna da gatar bauta wa ‘Allah mai fari ciki.’ (1 Timothawus 1:11) Yadda muka gani, za mu iya riƙe farin cikinmu ko idan muka fuskanci matsaloli masu tsanani. Bari mu riƙe begenmu na Mulki da ke a gabanmu, mu gyara ra’ayinmu inda ya dace, kuma mu sauƙaƙa rayuwarmu. Sai kuma kowane yanayin da mun iske kanmu ciki, za mu yi na’am da kalmomin manzo Bulus: “Ku yi farinciki cikin Ubangiji kullayaumi: sai in sake cewa, Ku yi farinciki.”—Filibbiyawa 4:4.
Ka Yi Tunani Sosai a Kan Waɗannan Tambayoyi:
• Me ya sa Kiristoci ya kamata su sa begen Mulkin a gabansu sosai?
• Menene zai iya taimaka mana mu riƙe farin cikinmu ko cikin yanayi masu wuya ma?
• Me ya sa ya kamata mu yi ƙoƙarin sauƙaƙa rayukanmu?
• A waɗanne hanyoyi ne wasu suka sauƙaƙa rayukansu?
[Box/Hotuna a shafi na 29]
Ƙarin Dalilai na Yin Farin Ciki
Mu Kiristoci, muna da dalilai masu yawa na yin farin ciki. Ka dubi na biyen nan:
1. Mun san Jehovah.
2. Mun koyi gaskiyar Kalmar Allah.
3. Mun sami gafarar zunubanmu ta wurin bangaskiyarmu cikin hadayar Yesu.
4. Mulkin Allah yana sarauta—ba da daɗewa ba sabuwar duniya za ta zo!
5. Jehovah ya kawo mu cikin aljanna ta ruhaniya.
6. Muna moran tarayya mai kyau ta Kirista.
7. Muna da gatar shagala cikin aikin wa’azi.
8. Muna da rai, muna da ɗan ƙarfi.
Dalilan yin farin ciki guda nawa za ka iya ambata?
[Hoto a shafi na 25]
Bulus da Sila sun yi farin ciki ko a fursuna ma
[Hotuna a shafi na 27]
Idanunka suna kan zato na farin ciki na sabuwar duniya ta Allah ce?