Ka Bi Isharar Da Yesu Ya Yi
“Na yi muku ishara domin ku ma ku yi yadda na yi muku.”—YAHAYA 13:15.
1. Me ya sa Yesu misali ne da Kiristoci za su yi koyi da shi?
ADUKAN tarihin ’yan adam, mutum ɗaya ne kawai ya ƙarasa rayuwarsa ba tare da ya yi zunubi ba. Wannan mutumin Yesu ne. In ban da Yesu, “ba mutumin da ba ya yin zunubi.” (1 Sarakuna 8:46; Romawa 3:23) Domin wannan dalilin, Kiristoci na gaskiya suka ɗauki Yesu misali ne mai kyau da za su bi. Kafin mutuwarsa, a ranar 14 ga Nisan, 33 A.Z., Yesu kansa ya gaya wa mabiyansa su yi koyi da shi. Ya ce: “Na yi muku ishara domin ku ma ku yi yadda na yi muku.” (Yahaya 13:15) A wannan dare na ƙarshe, Yesu ya ambaci hanyoyi da Kiristoci ya kamata su yi ƙoƙari su zama kamarsa. A wannan talifin za mu bincika wasu cikinsu.
Bukatar Tawali’u
2, 3. A waɗanne hanyoyi ne Yesu ya kafa mana misalin tawali’u?
2 Sa’ad da Yesu ya aririci almajiransa su bi misalinsa, yana maganar musamman tawali’u ne. Ya yi wa mabiyansa gargaɗi fiye da sau ɗaya su kasance masu tawali’u, kuma a daren 14 ga Nisan, ya nuna na shi tawali’u ta wajen wanke ƙafafun manzanninsa. Sa’an nan Yesu ya ce: “Tun da ya ke ni Ubangijinku, da kuma Malaminku, har na wanke muku ƙafa, ashe, ku ma ya kamata ku wanke wa juna.” (Yahaya 13:14) Daga baya ya gaya wa manzanninsa su bi misalin da ya kafa. Hakika wannan tafarkin tawali’u ne mai kyau!
3 Manzo Bulus ya gaya mana cewa kafin ya zo duniya, Yesu “surar Allah yake.” Duk da haka, ya ƙasƙantar da kansa ya zama mutum mai tawali’u. Fiye ma da haka, “ya ƙasƙantar da kansa ta yin biyayya, har wadda ta kai shi ga mutuwa, mutuwar ma ta [gungumen azaba].” (Filibiyawa 2:6-8) Ka yi tunanin wannan. Mutum na biyu a dukan sararin samaniya, ya yarda ya zama mutum mai tawali’u ya gaza ga mala’iku, aka haife shi jariri, ya girma a hannun iyaye ajizai, kuma a ƙarshe ya mutu mutuwar mai laifi. (Kolosiyawa 1:15, 16; Ibraniyawa 2:6, 7) Tawali’u ne ƙwarai! Yana yiwuwa kuwa a yi koyi da irin wannan “hali” kuma a koyi irin wannan “tawali’u”? (Filibiyawa 2:3-5) Hakika, amma ba shi da sauƙi.
4. Waɗanne abubuwa suke sa mutum ya yi fahariya, kuma me ya sa fahariya take da haɗari?
4 Akasarin tawali’u fahariya ce. (Karin Magana 6:16-19) Fahariya ta kai ga faɗuwar Shaiɗan. (1 Timoti 3:6) Ba wuya take kafuwa a zukatan ’yan adam, kuma da zarar ta kafu, yana da wuya a tuge ta. Mutane suna kasancewa masu fahariya domin ƙasarsu, domin launinsu, domin abin da suka mallaka, domin iliminsu, domin abin da suka cim ma, da kuma matsayinsu, siffarsu, iyawarsu wajen wasa, da kuma wasu abubuwa masu yawa. Amma, babu ko ɗaya cikin waɗannan abubuwa da yake da muhimmanci ga Jehobah. (1 Korantiyawa 4:7) Idan suka sa mu fahariya, suna ɓata dangantakarmu da shi. “Ubangiji yana can Sama, duk da haka yana kulawa da masu kaɗaici. Masu girmankai kuwa ba za su iya ɓoye kansu daga gare shi ba.”—Zabura 138:6; Karin Magana 8:13.
Kasancewa da Tawali’u a Tsakanin ’Yan’uwanmu
5. Me ya sa yake da muhimmanci dattawa su zama masu tawali’u?
5 Har aikinmu da kuma abin da muka cim ma a hidimar Jehobah bai kamata ya sa mu fahariya ba; hakki a cikin ikilisiya ma bai kamata ya sa mu fahariya ba. (1 Tarihi 29:14; 1 Timoti 6:17, 18) Hakika, kamar yadda yawan hakkinmu yake, haka yawan tawali’unmu ya kamata ya kasance. Manzo Bitrus ya aririci dattawa, kada “ku nuna wa waɗanda ke hannunku iko, sai dai ku zama abin koyi ga garken.” (1 Bitrus 5:3) An naɗa dattawa su zama masu hidima ne kuma su ba da misali, ba za su zama iyayengiji da shugabanni ba.—Luka 22:24-26; 2 Korantiyawa 1:24.
6. A waɗanne ɓangarorin rayuwar Kirista ne muke bukatar tawali’u?
6 Ba dattawa ba ne kawai suke bukatar tawali’u. Har samari, waɗanda za su yi fahariya da fahiminsu da kuma ƙarfinsu idan suka gwada da na tsofaffi. Bitrus ya rubuta: “Ku yi wa kanku ɗamara da tawali’u, kuna bauta wa juna, gama “Allah na gāba da masu girmankai, amma yana yi wa masu tawali’u alheri.” (1 Bitrus 5:5) Hakika, tawali’u na Kirista yana da muhimmanci ga kowa. Sai da tawali’u za a yi wa’azin bishara, musamman ma idan ana fuskantar ƙiyayya. Muna bukatar tawali’u domin mu bi gargaɗi ko kuma mu sauƙaƙa rayuwarmu domin shagala cikin hidima. Ƙari ga haka, muna bukatar tawali’u da kuma bangaskiya mai gaba gaɗi idan ana zarginmu, ko ana ƙaranmu a kotu, ko kuma tsanantawa.—1 Bitrus 5:6.
7, 8. A waɗanne hanyoyi ne za mu iya koyon tawali’u?
7 Ta yaya mutum zai guji fahariya kuma ya kasance mai ‘tawali’u, yana mai da ɗan’uwansa ya fi shi’? (Filibiyawa 2:3) Yana bukatar ya ɗauki kansa kamar yadda Jehobah yake ɗaukansa. Yesu ya yi bayanin hali da ya dace sa’ad da ya ce: “Haka ku ma, in kuka bi duk abin da aka umarce ku, sai ku ce, ‘Mu bayi ne marasa amfani. Mun dai yi abin da ke wajibinmu kurum.’ ” (Luka 17:10) Ka tuna, babu abin da za mu yi da za a gwada da wanda Yesu ya yi. Duk da haka, Yesu mai tawali’u ne.
8 Bugu da ƙari, za mu roƙi Jehobah ya taimake mu mu ɗauki kanmu yadda ya kamata. Kamar mai Zabura, za mu iya addu’a: “Ka ba ni hikima da ilimi domin ina dogara ga umarnanka.” (Zabura 119:66) Jehobah zai taimake mu mu ɗauki kanmu yadda ya kamata, kuma zai yi mana albarka domin halinmu na tawali’u. (Karin Magana 18:12) Yesu ya ce: “Duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Mai ƙasƙantar da kansa kuma, ɗaukaka shi za a yi.”—Matiyu 23:12.
Ra’ayi da ya Dace Game da Nagarta da Mugunta
9. Yaya Yesu ya ɗauki nagarta da mugunta?
9 Ya yi shekaru 33 a tsakanin mutane ajizai duk da haka Yesu “bai yi zunubi ba.” (Ibraniyawa 4:15) Sa’ad da yake annabci game da Almasihu, mai Zabura ya ce: “Kā ƙaunaci aikin adalci, kā ƙi aikin saɓo.” (Zabura 45:7; Ibraniyawa 1:9) A wannan ma Kiristoci sun yi ƙoƙari su yi koyi da Yesu. Sun san abin da ke nagari; kuma suna ƙin abin da ke mugu. (Amos 5:15) Wannan ya taimaka musu su yi fama da muradinsu na zunubi.—Farawa 8:21; Romawa 7:21-25.
10. Idan muna aikata ‘mugunta,’ kuma muka ƙi tuba, menene muke nunawa?
10 Yesu ya gaya wa Bafarisi Nikodimu: “Duk mai yin rashin gaskiya yakan ƙi hasken, ba ya kuma zuwa wajen hasken, don kada ayyukansa su tonu. Mai aikata gaskiya kuwa yakan zo wajen hasken, domin a bayyana ayyukansa, cewa da taimakon Allah ne aka yi su.” (Yahaya 3:20, 21) Ka tuna: Yahaya ya ce da Yesu “hakikanin haske mai shigowa duniya da ke haskaka kowane mutum.” (Yahaya 1:9, 10) Duk da haka, Yesu ya ce idan muka aikata ‘mugunta’—ayyuka da ba su da kyau, Allah bai amince da su ba—mun ƙi haske. Za ka iya tunanin ƙin Yesu da kuma mizanansa? Hakika, wannan shi ne matsayin waɗanda suke yin zunubi kuma suka ƙi tuba. Wataƙila ba su fahimci haka ba, amma Yesu ya fahimci hakan.
Yadda Za Mu Koyi Ra’ayin Yesu Game da Nagarta da Mugunta
11. Menene yake da muhimmanci idan muna so mu koyi ra’ayin Yesu game da nagarta da mugunta?
11 Muna bukatar mu fahimci abin da ke nagarta da abin da ke mugunta a ra’ayin Jehobah. Za mu fahimci wannan ne kawai daga nazarin Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki. Sa’ad da muke irin wannan nazari, muna bukatar mu yi addu’ar irin wadda mai Zabura ya yi: “Ka koya mini al’amuranka, ya Ubangiji, Ka sa su zama sanannu a gare ni.” (Zabura 25:4) Amma ka tuna cewa Shaiɗan mayaudari ne. (2 Korantiyawa 11:14) Yana iya kyawanta mugunta ta bayana ba ta da laifi ga Kirista marar kula. Saboda haka, muna bukatar mu yi bimbini mai zurfi a kan abin da muka koya kuma mu bi gargaɗin “amintaccen bawan nan mai hikima.” (Matiyu 24:45-47) Nazari, addu’a, da kuma bimbini a kan abin da muka koya zai taimake mu mu manyanta kuma mu kasance tsakanin waɗanda “hankalinsu ya horu yau da kullum, su rarrabe nagarta da mugunta.” (Ibraniyawa 5:14) Sa’an nan za mu kasance da muradin mu ƙi mugunta mu ƙaunaci nagarta.
12. Wane gargaɗi ne na Littafi Mai Tsarki ya taimake mu mu guji ayyukan mugunta?
12 Idan muka ƙi mugunta, ba za mu ƙyale muradin yin abin da ba shi da kyau ta yi ƙarfi a zukatanmu ba. Shekaru da yawa bayan mutuwar Yesu, manzo Yahaya ya rubuta: “Kada ku ƙaunaci duniya, ko abin da ke cikinta. Kowa ke ƙaunar duniya, ba ya ƙaunar Uba ke nan sam. Don kuwa duk abin da ke duniya, kamar su sha’awa irin ta halin mutuntaka, da sha’awar ido, da kuma alfarmar banza, ba na Uba ba ne, na duniya ne.”—1 Yahaya 2:15, 16.
13, 14. (a) Me ya sa ƙaunar abin duniya take da haɗari ga Kiristoci? (b) Ta yaya za mu guji ƙaunar abubuwan duniya?
13 Wasu za su yi tunanin cewa ba dukan abubuwa ba ne na duniya ba su da kyau. Ko da yake hakan gaskiya ne, babu wuya duniya da abubuwanta su janye hankalinmu daga bautar Jehobah. Kuma babu abin da duniya take bayarwa da aka tsara domin ya sa mu kusaci Allah. Saboda haka, Idan muka zo ga ƙaunar abubuwan duniya, har da abubuwa da su kansu ba su da laifi to muna kan muguwar hanya. (1 Timoti 6:9, 10) Ƙari ga haka, yawancin abubuwan da suke duniya ba su da kyau kuma za su iya lalata mu. Idan muna kallon fim ko kuma wasanni da suke nanata mugunta, son abin duniya, ko kuma lalata, irin waɗannan abubuwa za su zama karɓaɓɓu—sai su zama abin sha’awa. Idan muna cuɗanya da mutane da ainihin muradinsu shi ne su kyautata rayuwarsu ko kuma su kyautata zarafin kasuwanci, waɗannan abubuwa ne za su zama mafiya muhimmanci a gare mu mu ma.—Matiyu 6:24; 1 Korantiyawa 15:33.
14 Akasarin haka, idan muka ƙyale Kalmar Jehobah ta kasance abin farin ciki a gare mu, ba za mu yi “sha’awa irin ta halin mutuntaka, da sha’awar ido, da kuma alfarmar banza.” Bugu da ƙari, idan muka yi cuɗanya da mutane da suka saka Mulkin Allah farko a rayuwarsu, za mu zama kamarsu, za mu ƙaunaci abin da suke ƙauna kuma mu guji abin da suka ƙi.—Zabura 15:4; Karin Magana 13:20.
15. Kamar yadda yake ga Yesu, ta yaya ƙaunar nagarta da kuma ƙyamar mugunta za ta ƙarfafa mu?
15 Ƙyamar mugunta da kuma ƙaunar nagarta ta taimaki Yesu ya kafa idanunsa a kan “farin cikin da aka sa gabansa.” (Ibraniyawa 12:2) Hakan zai iya faruwa da mu. Mun sani cewa “duniyar kuwa tana shuɗewa da mugayen burinta.” Dukan wani nishaɗi da duniya take bayarwa na ɗan lokaci ne. Amma kuma, wanda ya “aikata nufin Allah zai dawwama har abada.” (1 Yahaya 2:17) Domin Yesu ya yi nufin Allah, ya buɗe wa mutane hanyar samun rai madawwami. (1 Yahaya 5:13) Dukanmu ya kamata mu yi koyi da shi kuma ya kamata mu amfana daga amincinsa.
Jimre wa Tsanani
16. Me ya sa bukatar Kiristoci su ƙaunaci juna take da muhimmanci?
16 Yesu ya faɗi wata hanya da almajiransa za su yi koyi da shi, yana cewa: “Wannan fa shi ne umarnina, cewa ku ƙaunaci juna kamar yadda na ƙaunace ku.” (Yahaya 15:12, 13, 17) Da dalilai masu yawa da suka sa Kiristoci suke ƙaunar ’yan’uwansu. A wannan lokaci, Yesu yana magana ne musamman game da ƙiyayyar da za su fuskanta daga duniya. Ya ce: “In duniya ta ƙi ku, ku sani sai da ta ƙi ni kafin ta ƙi ku. . . .‘Bawa ba ya fin ubangijinsa.’ In sun tsananta mini, ku ma za su tsananta muku.” (Yahaya 15:18, 20) Hakika, a wajen tsananta mana, Kiristoci suna kama da Yesu. Suna bukatar su ƙarfafa ƙaunarsu domin ta taimake su su tsayayya wa ƙiyayya.
17. Me ya sa duniya ta ƙi Kiristoci na gaskiya?
17 Me ya sa duniya za ta ƙi Kiristoci? Domin kamar Yesu, su “ba na duniya ba ne.” (Yahaya 17:14, 16) Ba sa saka hannu a batutuwan soja ko kuma na siyasa, kuma suna bin mizanan Littafi Mai Tsarki, suna tsarkaka rai kuma suna bin ɗabi’a mai kyau. (Ayyukan Manzanni 15:28, 29; 1 Korantiyawa 6:9-11) Ainihin makasudinsu na ruhaniya ne, ba abin duniya ba. Suna rayuwa a cikin duniya, amma kamar yadda Bulus ya rubuta, ba sa “ba da ƙarfi ga moranta.” (1 Korantiyawa 7:31) Hakika, wasu sun nuna sha’awarsu ga ɗabi’ar Shaidun Jehobah. Amma Shaidun Jehobah ba sa miƙa kai domin suna so a yi sha’awarsu ko kuma a amince da su. Domin haka mutane da yawa a duniya ba su fahimce su ba, kuma da yawa suna ƙinsu.
18, 19. Ta yaya Kiristoci suka bi da hamayya da ƙiyayya ta wajen bin gurbin Yesu?
18 Manzannin Yesu sun ga wannan matuƙar ƙiyayya ta duniya sa’ad da aka kama Yesu kuma aka kashe shi, kuma sun ga yadda Yesu ya fuskanci wannan ƙiyayyar. A lambun Gatsemani, abokan gaban Yesu suka zo su kama shi. Bitrus ya yi ƙoƙari ya kāre shi da takobi, amma Yesu ya gaya wa Bitrus: “Mai da takobinka kube. Duk wanda ya zari takobi, takobi ne ajalinsa.” (Matiyu 26:52; Luka 22:50, 51) A zamanin dā, Isra’ilawa sun yaƙi abokan gabansu da takobi. Amma yanzu abubuwa sun canja. Mulkin Allah “ba na duniya ba ne” saboda haka ba shi da yanki da zai kāre. (Yahaya 18:36) Ba da daɗewa ba Bitrus ya shiga cikin al’umma ta ruhaniya, da waɗanda suke cikinta za su zama ’yan mulkin sama. (Galatiyawa 6:16; Filibiyawa 3:20, 21) Daga wannan lokaci, mabiyan Yesu za su bi da ƙiyayya da tsanantawa kamar yadda ya bi da ita—ba tare da tsoro ba amma kuma cikin salama. Za su ƙyale sakamakon abubuwa ga Jehobah kuma su dogara a gare shi ya ba su ƙarfi domin su yi jimiri.—Luka 22:42.
19 Shekaru da yawa bayan haka, Bitrus ya rubuta: “Almasihu ma ya sha wuya dominku, ya bar muku gurbi ku bi hanyarsa. . . . Da aka zage shi bai rama ba, da ya sha wuya kuwa bai yi kashedi ba, sai dai ya dogara ga mai shari’ar adalci.” (1 Bitrus 2:21-23) Kamar yadda Yesu ya yi gargaɗi, Kiristoci sun fuskanci tsanantawa mai tsanani da shigewar lokaci. Kamar yadda yake a ƙarni na farko, a zamaninmu ma sun bi misalin Yesu, sun kafa tarihin jimiri da aminci, sun kuwa gwada cewa su masu riƙe aminci ne cikin salama. (Wahayin Yahaya 2:9, 10) Dukanmu mu yi haka, sa’ad da yanayi ya bukaci haka.—2 Timoti 3:12.
“Ku Ɗauki Halin Ubangiji Yesu Almasihu”
20-22. A waɗanne hanyoyi ne Kiristoci suka “ɗauki halin Ubangiji Yesu Almasihu”?
20 Bulus ya rubuta zuwa ga ikilisiya ta Roma: “Ku ɗauki halin Ubangiji Yesu Almasihu, kada kuwa ku tanadi halin mutuntaka don biye wa muguwar sha’awa tasa.” (Romawa 13:14) Suna ƙoƙari su yi koyi da halin Yesu da kuma ayyukansa iyaka gwargwadon ƙarfinsu ko da yake su ajizai ne.—1 Tasalonikawa 1:6.
21 Za mu iya ɗaukan “halin Ubangiji Yesu Almasihu” idan muka fahimci tafarkin rayuwar Shugaban namu kuma idan muka yi ƙoƙari mu rayu kamar yadda ya rayu. Za mu yi koyi da tawali’unsa, ƙaunar nagartarsa, ƙyamar muguntarsa, ƙaunarsa ga ’yan’uwansa, kasancewarsa ba na duniya ba, da kuma jimirinsa ga wahala. Ba ma ‘tanada halin mutuntaka don sha’awar jiki,’ wato, ba ma mai da ainihin dalilin rayuwarmu ya zama domin makasudi na duniya ko kuma gamsar da sha’awoyi na jiki. Maimakon haka, sa’ad da muke yanke shawara ko kuma muke magance wata matsala, mu tambayi kanmu: ‘Menene Yesu zai yi a wannan yanayi? Me zai so in yi?’
22 A ƙarshe, muna koyi da Yesu wajen shagala cikin “shelar bishara.” (Matiyu 4:23; 1 Korantiyawa 15:58) A wannan ma, Kiristoci suna bin gurbi da Yesu ya bari, talifi na gaba zai tattauna yadda suke yin haka.
Za Ka Iya Ba da Bayani?
• Me ya sa yake da muhimmanci Kirista ya kasance mai tawali’u?
• Ta yaya za mu koyi ra’ayi mai kyau game da nagarta da mugunta?
• A waɗanne hanyoyi ne Kiristoci suke yin koyi da Yesu wajen bi da hamayya da kuma tsanantawa?
• Ta yaya zai yiwu a “ɗauki halin Ubangiji Yesu Almasihu”?
[Hoto a shafi na 19]
Yesu ya bar gurbi mai kyau na tawali’u
[Hoto a shafi na 20]
Kowane ɓangare na rayuwar Kirista, har da wa’azi, yana bukatar tawali’u
[Hoto a shafi na 21]
Shaiɗan zai iya mai da nishaɗi marar kyau ya zama karɓaɓɓe ga Kiristoci
[Hoto a shafi na 22]
Ƙaunar ’yan’uwanmu za ta sa mu mu yi tsayayya da hamayya